Skip to content
Part 26 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Shatar mota guda Mai Kano yayi daga katsina zuwa garin Legos .

Suna tafe a motar shi Yana gaba tare da direba yayin da Halima ke baya kafar ta ta isheta da zugi inda wani yanki ya fado Mata Ashe ya koneta ita kanta dai tana Jin kafar na Mata zogi Bata San cewa wutar ce ba bare Mai Kano dake kokowa da zuciya Akan bakin cikin da gayen can ya kunsa musu musamman shi da Uwar shi

Yawu ya cikawa Halima Baki abinda ke Kara tabbatar Mata da lallai abinda take zato ya faru wato bayyanar ciki a jikinta

HAWAYE yayi ta zarya a fuskar ta inda Mai Kano ya juyo baya don yaji ajikin shi kuka take.

Yaga ta hade Kai da gwiwa ya Kira sunanta ta dago sukayi ido Hudu yaga HAWAYE na bin fuskar ta inda yaji wani turiri na tasowa tun daga kasan zuciyar shi Yana fita ta kofofin hancin shi.

“Mama me kike so na siyo Miki? Ga kankana ga nama ga Kuma abinci can na hango? Ta zubar da yawun da ya cika Mata Baki kafin tace. “Ruwa kadai ma ya Isa Mai Kano.

Ya tsaida direban ya fita sai gashi da tarin siyayya har direban sai da ya siyowa abinci yayin da ya siyowa Halima kayan fruit da nama har da lemun Roba da Ruwa Amma Bata iya taba komai ba sai Ruwa.

Da Haka har Allah Ubangiji ya kawo su cikin garin Legos Kai tsaye motar sai da ta dangane dasu har cikin Apapa bayan bankin zenith Bank a kofar gidan

Mai Kano ya Ciro makulli ya bude ya sallami Mai motar ya Riko hannun Halima da yaga tana dingishi saboda kafar har ta Haye da kumburi yayi zaton ko zaman mota ne

Suka SHIGA dakin Wanda Babu kowa ya jawo katuwar katifar shi ya baje Mata ya Kuma dauko fankar kasa ya aje Mata kafin ya Kai Mata Ruwa ban daki ta SHIGA tayi wanka shima ya SHIGA yayi wanka ya fito yaga har ta daura alwala inda tayi Arba da kafar ta ta Haye sai dai Bata fada mishi ba ta tada sallar ta .

Shima Ramakon sallolin ya bada ya shigo dakin ya iske Halima na kuka Riris Bai CE ko uffan ba don shima kukan ya ke bukata akan cin zarafin Uwar shi da akayi sai dai taurin zuciya ya Hana idon shi zubar HAWAYE

Ganin Halima Taki Daina kukan yasa ya Soma Bata hakuri. “Kiyi hakuri da kukan Nan mama duk da ban San Dalili ki na yin shi ba. Ko da Yake idan nace ban San Dalili ba banyiwa kaina adalci ba Amma kiyi hakuri don Allah ki Daina kukan Nan.

“Dole nayi kuka Mai Kano ko don baka San abinda nakeyiwa kuka ba? Mai Kano anci zarafina Amma na barwa Allah sai dai zanso don girman Allah ku yafeni ku yafeni Mai Kano na zaja muku abin kunya na zajawa kaina da iyayena har da mahaifin ku da Bai cancanci akasin abinda ba ADDU A ba a gareni.

“Me ya faru ne mama? Ya fada Yana kafeta da ido. “Mai Kano ciki ne dani Wanda na kusa haifewa cikin da bashi da tartibin asali. Cikin da akayi min a gidan da ka ganni.

Wani lugude da zuciyar shi ta dauka tamkar zata faso kirjin shi ta fito shi ya wanzu gareshi har Yana Jin wani yaji yaji a idon shi kafin kanshi ya Sara

“Dama manufar baba Aminu kenan akanki mama? Me yasa duk Matan Duniya ya Rasa wadda zaiyiwa Haka sai ke? Ciki mama? Sai ya Rushe da kuka duk taurin zuciyar shi wannan karon sai da ya koka

Kuka irin na inama ban Budi ido a wannan duniyar ba? Shi da Halima sukayi ta sharbar kukan su babu me bawa wani hakuri kafin Mai Kano ya takawa nashi burki ba don ya Kai inda zai tsaya ba sai don ya lalubo mafita.

Kafin yace komai ya lura da kafar Halima wadda wuta ta laso don Haka da sauri suka nufi Asibiti akayi treatment din kafar suka dawo gida

Duka zukatan su babu Dadi inda Halima take ganin zubar da cikin shi yafi ALHERI gare ta Akan ace ta haifi Dan gaba da fatiha.

Don Haka ta shawarci Mai Kano da maganar son zubar da cikin.

“Anya kuwa Mama in akayi Haka ba ayi kisan Kai ba? “Na San cewa anyi Miki hakan ba da son Ranki ba bana zargin ki da komai bana Kuma ganin laifin ki Akan hakan to ayi hakuri da zubar da cikin nan.

“Mai Kano in kalli dan ko diyar da wace fuska? Kuma ku kalle shi da wace kamar?

“Da kamar da Allah ya bashi Mama kiyi hakuri ki karbi kaddarar da Ubangiji ya nufeki da ita Ni kaina ba zanso akalleki da wata fuska ba akasin fuskar da kike da ita. Don Haka idan kin haihu Zan karbi Dan na Kai shi gidan marayu Kinga Babu Wanda yasan hakan don ko naje katsina ba Zan taba nuna kina tare Dani ba bare har wani San halin da kike ciki.

Halima ta yarda da hakan take Kuma Rokon Allah da ya kawo Mata dauki.

Haka Rayuwa ta Mika duk da damuwar da suke ciki inda Mai Kano ke tunanin meye abinda zaiyiwa Alh Aminu ya huce Bakin cikin da ya kimsa musu?

Alh Aminu ya iso masanwa gidan hajiya da son ya bugi cikin ta yaji inda Mai kano Yake

Bayan sun gaisa hajiya na ta binshi da ADDU OIN fatan ALHERI ya Dora da tambayar inda mazaunin Mai kano Yake.

“Humm ka Rabu da wannan yaron marar mutunci Aminu kaji duk cikin yaran Halima Banga marar kunya irin Mai Kano ba sai akayi sa a ya SHIGA garin Legos inda ya sake taurarewa ka barshi kawai duk Duniya Mai Kano baya ganin Kan kowa da gashi daga Halima sai mu azu . Ka ga inda yaron Nan ya zauna Yana fada min magana Anya ko baya shaye shaye ma?

“Yaro ne hajiya har da kuruciya ke damun shi dama kudine na ware na zakka shine Zan bashi ya Kara jari tunda shi sana a Yake akasin Yan uwanshi dake karatu.

“Kar ka bashi Aminu gara ka bawa bayin Allah ka Rabu dashi kawai.

“Ba za a biye mishi ba hajiya har gobe ina kallon Ya’yan mu azu basu da banbanci da nawa shiyasa nake so naje inda yake nags irin Sana ar da Yake da taimakon da Zan iya yi mishi.

“Legos yake ko me ma yakeyi? Oho na manta da yake ba kirki gareshi ba shiyasa tawa da tashi ba tazo Daya ba.

“Abani lambar shi hajiya idan na SHIGA garin sai na neme shi.

“Bai taba kirana ya gaishe Ni ba Aminu shiyasa ma da aka saka min lambar nacewa Amadu ya goge min Yar banza Amma Husna ba zata Rasa ba don suna waya dashi Dan iskan Rijiyar lemun.

Da haka ya ajewa hajiya kudi masu auki ya taso ya taho tana ta kwarara mishi ADDU A da fatan ALHERI

Da ya iso gida ya Kira Husna wadda ya wuto ita da muhsin suna zaune Akan lilon farfajiyar gidan suna fira cikin nishadi ta taho da gudu tana mishi oyoyo.

“Kina da layin Mai Kano kuwa Husna? “Eh Daddy ko jiya munyi waya dashi.

“Kuma Bai fada Miki wani Labari game da Halima ba ko ? Ta dubeshi da son yayi Mata albishir da cewa mahaifiyar su ta bayyana .

“Baba ko an samu ganin ta ne? “Ba a ganta ba Husna muna fatan hakan dai shine dalilin da Zan nemeshi ma bani lambar.

Ta karanto mishi ya shigar ya Soma Danna mishi Kira amma cikin Rashin sa a wayar a kashe inda yaja tsaki

Sai dai Bai hakura da Kiran wayar ba har dai yayi nasarar samunta Amma Nan ma Bai daga ba Kiran Duniya Amma Mai kanon yaki pick inda ya Kuma neman Husna Wai ko Mai Kano Yana da wasu lambobi ne? Ta sanar dashi wannan layin kawai yake amfani Kuma dashi yake Kira itama dashi take Kiran shi.

To Kira min shi da layin ki. Ta Danna mishi Kira Kara biyu a na uku sai ga muryar Mai kanon ta bayyana Yana fadin Husna ya kayi ne? Suka gaisa inda take fada mishi baba Aminu ne ke son magana dashi.

“Waye kikace ? Ya tambaye ta a zafafe Amma da Yake ba a gabanta yake ba sai ba ta fahimci hakan ba ta sake maimaita mishi baba Aminu ne ke son magana dashi inda ya yanke Kiran ya bar Alh Aminu da Kiran hello hello Mai Kano?

Sai da ya duba yaga Ashe ya yanke Kiran ya bi sahun shi da dai layin na Husna Amma kememe yaki dagawa inda Kuma wayar shi ta dauki tsuwwa ya duba yaga sunan lauje ne ke Kira sai ya mikawa Husna wayar ta yace taje zai nemi Mai Kano da layin shi.

Ya dauki wayar lauje jikin shi har ciri yake inda ya jiyo lauje na fadin.

Wato Aminu ka dauki maganar Nan da wasa ko? Har yanzu cikin matar Nan Yana Nan jikinta Bai a zubar ba ko?

<< Hawaye 25Hawaye 27 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.