Skip to content
Part 34 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Dakin Lauje ya turnike da hayaki tamkar wutar damuna.

Alhaji Aminu ya shigo gidan daidai hayakin na turiri saboda Kiran da Laujen yayi mishi. Ya zube Yana laluben laujen saboda hayakin da ya turnike dakin ba baya bukatar a sanar dashi Zubaina ce zata bayyana, Ilai kuwa sai gashi ta bayyana tana Rera kuka maimakon Dariyar da ta saba zuwa da ita “Me ya faru Kuma yau gimbiyar dodon kod’i?

Ta jima batayi magana ba kafin tace,

“Yaron wuri nane bashi da lafiya Kuma ba zai warke ba sai an Bashi tayin da baizo Duniya ba shine nake so abani Dan dake kwance cikin Halima na bashi.

“Jeki na Baki shi har Halimar ma idan kina bukatar ta ki tafi da ita cewar Alhaji Aminu.
Sai kawai sukaji Zubaina ta kyalkyale da Dariya kafin tace

“Har da Halima ka bani? Kayi dabara da ka bani ita Ni Kuma Zan haukatar da ita ne kawai don in har ta dawo gida Asirin ka ne zai tonu Kuma yaron ta din can shi zai girgiza ka kafin ya kayar da Kai.

Suka dubi juna shi da lauje “Kiyi gaba har da shi Dan nata Mana Zubaina?
“Yafi karfin mu na Gaya maka Amma Halima yau din Nan Zan dauko abinda ke cikin ta kafin nayi gaba da hankalin ta.

Da haka ta fice ta bar Alh Aminu Yana sheka Dariya.

“Amma fa Zubaina tana kaunar ka mutumina kaga sai ka huta neman Mai Kano.

“Kuma fa Nan dai Zubaina tayi min hikima idan Halima ta dawo nayi yaya da shegen Dan ta da ya gagara wurin su Zubainar? Amma kaga da ta haukace shikenan na huta har shi Dan nata babu ta inda zai tuhume Ni.

Kuma tunda Zubaina ta dauki jininka dake kwance cikin Halima Ina me tabbatar maka da sai ta Kara baka wata shaharar da bakayi zato ba.

Da haka suka yi bankwana da lauje Yana Jin dadin abinda Zubainar tayi mishi

Halima da kullum take cikin ciwo yau sauki gobe ciwo Amma Mai Kano Bai kasa ba da tace Nan? Zai dauketa su tafi Asibiti.

Kamar dai yau da ta tashi da matsanancin ciwon ciki tamkar zata mutu…

Mai Kano ya fita yayo Shatar motar da zata Kai su Asibiti kafin ma ya dawo jini ya kece Mata.
Cikin fita hayyaci suka Isa Asibiti akace Bari ne tayi Amma ga mamakin likitocin babu tayin dan inda sukayi zaton ko a can gida ta fitar dashi. Akayi Mata duk abinda ya kamata suka dawo gida.

Sannu ahankali tayi ta samun sauki har tsayin sati biyu ta dawo hayyacin ta tana godewa Allah da ya kawo Mata sanadin firar cikin Babu Wanda yaji bare ya gani inda take cewa Mai kano sati me zuwa gida zata koma.

“Amma mama da munje Nan zamu dawo don zaman ki acan kamar ba zai yuwu ba musamman wannan mutumin da ya gama sanin Asirin shi ne zai tonu.

“Haka NE Mai Kano sai mu dawo din don dai ina son ganin hajiya ne Amma da Ni kaina ba Zan koma garin can ba ko don wancan mutumin.

Saura kwana biyu tafiya garin katsina da safe ya fito bayan sun gaisa da Halima ta gabatar mishi da abin Karin kummalo inda ya kula tana dafe Kai Alamar ciwo

“Mama ciwon Kai kike? “Wallahi kuwa kamar ciwon Kai nake ji. “To Bari na gama mije Asibiti.

“A a bari kawai nasha sudrex zan ware

Da Haka ya nufi wurin harkokin shi Amma Kuma sai yaji ya kasa samun nutsuwa duk tunanin shi ya na gida wurin mahaifiyar shi.

Karfe uku na rana ya baro kasuwar ya nufi gida inda ya taho yanajin matsanancin faduwar gaba.

Titin da zai maido shi hanyar da zata sada shi da unguwar tasu yaga ya cika dankam da mutane.

Ya dubi Dan napep din da ya dauko shi ko su juya ya keyawo dashi don sauri Yake.

Wani mutum yajiyo Yana fadin Kai Mai Rai dai ba bakin komai yake ba matar Nan ga Alama sabon kamun hauka ne matukar tana cikin garin Nan indai ba Ubangiji ya kiyaye ba yanzu ne zaka ganta da uban ciki an samu wani marar tsoron Allah ya far Mata.

Wannan maganar ita ta daki kirjin Mai Kano har yaji zai bawa matar Nan taimako don Haka sai kawai ya fito daga napep din ya kutsa cikin mutanen inda yayi mugun gani domin ko Halima ce kwance shame shame Akan titi wani Mai mota ya banketa Amma Kuma Taki tashi Akan titin shine ma ta hada go slow.

Da sauri ya karasa gabanta Yana kallon yadda goshin ta ya fashe jini na zuba Amma Kuma Taki yarda wani ya taba ta bare ta matsa.

Hawaye kawai Mai Kano yaji suna tsere a fuskar shi. Suna yin ido Hudu da Mai Kano sai ta taso da sauri ta rungume shi.

Yana Rike da ita yana hawaye suka shiga napep din inda wani mutum ya biyo shi Yana tambayar shi.
“Kasan ta ne Dan samari?

“Mahaifiya tace . Ya bashi amsa.

“Yauwa to nine na banke ta da mota saboda ta taho a guje fito muje Asibiti ayi Mata diresin din wannan ciwon na jikinta.

Suka SHIGA motar ya jasu suka tafi inda Mai Kano ya zuba Mata ido tayi kwance ajikin shi duk jikinta ya koje babu Dan kwali a kanta sai Riga da Zane kawai.

Yana cikin matur mamakin abinda ke faruwa ga mahaifiyar tashi wadda ya Bari lafiya Lau Amma yanzu gata a wani yanayi me nuna bata cikin hankalin ta.

Duk cajin da aka nema Asibiti mutumin nan da ya kade ta shi ya biya inda kuma aka tabbatar musu da tabin hankali ta samu Wanda Dole sai dai su Mika ta Asibitin masu lalurar tabin hankali.

Mutumin Nan shi ya bawa Mai Kano shawarar ya kai ta Asibitin masu lalurar tabin hankali Kano ko katsina inda za a binciki lafiyar kwanyar ta su Kuma kiyaye da fitar ta daga karshe yayi wa mai Kano fatan ALHERI ya Kuma kawo kudi ya bashi Amma yace ba zaya karba ba shi kuma ya aje mishi yace shima ba zai dauka ba

Kuka Mai Kano yake yi bayan tafiyar mutumin inda Halima ta zuba mishi ido bata uhm bata um um sai da yayi kuka har ya godewa Ubangiji kafin yayi mata fatan Ubangiji yasa ta cinye jarabawar ta da haka ya dauko ta suka nufo garin katsina garin da tayi burin shigo shi cikin hankalin ta nan da jibi sai gashi ta shigo shi cikin gushewar hankali ba tare da tana fahimtar komai ba inda kuma kai tsaye Mai Kano ya wuce da ita sakat Rum inda dukkan bincike dai ya nuna Halima tayi batan dabo akan hankalin ta Dole aka karbe ta har aka Bata daki tare da sauyin kayan jikin ta ba don sunyi wani Abu ba A a sai don dokar gidan ce Haka inda Mai Kano Yana kallo aka saka mahaifiyar shi dakin aka maida kwado aka datse.

<< Hawaye 33Hawaye 35 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×