Skip to content
Part 40 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Duk inda yake zaton samun Husna yaje amma babu ita babu dalilin ta.

Ya dawo a Rude Yana tambayar Amal inda take hasashen Husna zataje?

“Gaskiya tunda Bata masanawa gidan hajiya ban San Kuma inda ta tafi ba Allah yasa ba garin ta Bari ba don Bata da inda yafi gidan hajiya.

Ya fice daga gidan da alwashin Nemo inda Husna ta je inda Amal ke tausaya mishi don ya fita hayyacin shi . Fitar da Kuma har yanzu Bai waigo gida ba in da Kuma su Anty maimuna suke hidimomin su don mukhtar ya tsaya tsayin daka wurin ganin komai ya tafi yadda Daddy Yake so.

Tuni Yake neman muhsin don an shirya fatika kala kala Amma wayar muhsin ma Akashe Dole ya hakura ya nufo gida inda Amal ce ta lura da Yaya muhsin Bai kwana gida ba inda ta sanar da Mami Yaya muhsin fa Bai kwana gidan ba.

Haj wasila tace. “Yayi min daidai ai dama bance ya SHIGA sabgar bikin Nan ba Kuma ko ya SHIGA Zan fidda shi ko don maimuna ta Gane daga daukar cikin muhsin zuwa nakudar shi Babu Wanda ya tayani Kuma na Isa da kayana don Haka kicewa mukhtar din dake neman shi ya fita idona idan ya Kuma zuwa gidan Nan da sunan yazo neman muhsin Akan bikin Nan Ranshi zai baci. Amal ta bar mamakin Rashin kwanan muhsin gida Ashe ya gujewa Auren Safina ne Amma ga zaton su wannan muhsin Yana can neman Husna.

Kaya Sosai Anty maimuna tayi na dakin Safina inda ta Kira Alh Aminu tace ya turo musu da makullin sashen da muhsin zai zauna zasuje ganin yadda gidan yake in akwai gyaran da zasuyi. Yace suje yana hannun haj wasila su karba . aka tafi har da ita uwar amarya.

A Dayan sashen gidan ya fada Mata ba Wanda ya gyara da sunan Auro Halima ba shi wannan yace Husna zai saka ciki don yadda ya kashe mishi kudi ba zai bawa muhsin din ba sai dai ayi mishi gyara Dayan.

Haj wasila na zaune Akan kujera tana kallon tashar arewa suka shigo tare da sallama ta amsa tana ma su sannu da Zuwa don dayawa daga cikin su dangin su ne shiyasa ma ta tanka su. Amma Anty maimuna ko kallon ta batayi ba bare zancen gaisuwa sai ma maganar da tajefo ta cewa,

“Abamu makullin sashen can zamu duba mu gani tunda Allah ya yarda Ashe akwai Rabo kura a takobi an siyar da takobin an siyo akuya ita kuwa akuya kura ta kashe.

Haj wasila tayi murmushi tana cewa.

“Anya kuwa maimuna Kare zai kashe Ragon layya ya zauna lafiya? Makulli Kuma kinci arzikin Yan uwa Amma da kingane Mai hankali ne kawai Yake Gane fushin Mai dogon Baki.

Ta dauko makullin ta Mika musu inda Yan uwan nasu ke ta basu magana Akan Kar su Bari lamarin Auren Nan ya shiga tsakanin su musamman ita maimuna da wasila take yayar ta to fa Bata da uwa bayan haj wasila.

Da haka dai suka ga sashen Wanda Babu abinda Yake bukata komai a gyare tsab da Haka suka juya da key din don maimuna tace yazo Kenan Kuma da zasu tafi batayiwa haj wasila sallama ba sai dai wasu daga cikin dangin su suma ba duka ba don maimuna ta fanfasu Akan Wai wasila ce ke adawa da Auren shiyasa suka shata layi

Ranar farko da za a Gabatar da fatyn Safina ta matsawa mukhtar da lallai ya kawo Mata muhsin don in har Babu Ango ai an Fado sai dai duk kokarin mukhtar din Baiyi nasarar ganin muhsin ba Haka wayar shi ma Bata samu ba gashi duk Yan Uwa da Abokan Arziki sun hallara Amma Ango Wala

Safina me tarin kawaye har da na hauka Wanda suka Zo Amma Babu Ango don ta gama kambama yadda Wai Angon ke son ta Amma Kuma gashi tana Shirin Shan kunya

Haka akayi taro aka watse babu muhsin sai dai mukhtar ne ya maye gurbin shi abinda Kuma ya fusata Safina da maimuna don da kuka Safina ta shigo take fadawa uwar ta muhsin ya watsata baije wurin fatyn ba.

“Duk ki barsu sun makara nasan Aikin Yaya wasila ne ita ta hanashi zuwa Kuma don anyi zazzabi an warke ai ba a bawa mutuwa haushi ba. Kar ki sake zubar da hawayen ki Akan Bai SHIGA Sha anin Nan ba tunda kikayi nasarar Auren shi ai kin gama Babban Dace. Ki barsu dashi da Uwar shi sun kusa zuwa hannun ki da Haka Safina ta bar Abun ba don ya wuce ba sai don zata Rama abinda akayi Mata.

Shiru shiru muhsin har haj wasila ta damu da son sanin halin da yake ciki Amma tayi ta Kiran wayar shi Akashe. Tana cikin zullumi da Tararrabi Alh Aminu ya shigo Yana zuba Ruwan tijara Wai ta Hana muhsin ya je Sha anin Safina to kin zuwan kawai zaiyi Amma Bai Isa ya Hana Auren su dauruwa ba.

Amal ta shigo take fada mishi tun Ranar fa da Husna ta bar gidan shima Yaya muhsin ba a Kuma ganin shi ba.

Ya tari Amal din da tambayar “Tun yaushe ne Husnar ta bar gidan ? Don shi Bai San Husna Bata gidan ba.

“Tun Ranar da taji Auren Safina da Yaya muhsin tayi tafiyar ta Kuma duk inda ake zaton taje din bataje ba.

Ya kadu matuka Gaya da jin cewa husna ta bar gida da sauri ya nufi masanwa inda hajiya ke shaida mishi batazo ba sai Kuma hankali ya tashi aka SHIGA jaje da bada Cigiya har kafafen yada laharai yayin da Kuma biki ya Rage Armashi daga Uban Ango saboda Rasa nashi farin cikin wato Husna inda kuma aka gangara biki daga maimuna da Safina Babu abinda ya shalle su da Rashin muhsin don suna ganin laifin haj wasila ne Kuma zatayi bayani da yaren hausa idan ta ga muhsin din da take takama ya zamo hadimin Safina don anyiwa Safina shiri na mussamman Wanda suke fatan kwalliya zata biya kudin Sabulu.

Ranar da aka daura Aure Ranar Safina taji ta tamkar wata sarauniya Wai yau itace a matsayin matar muhsin abinda ta cire Rai sai murna da farin ciki take Amma da ta tuno da haj wasila sai taji Duk ta damu.

Da Haka aka sada Safina a Dakin muhsin inda duk shige da ficen da akeyi akan idon haj wasila da Amal da zuwa yanzu sun aje Safina da Uwar ta a gefe ta tadda za ayi su gano inda muhsin ya lakafe itace damuwar su ba kamar da da suke damuwa da batun Auren ba

Akayi walima aka watse ba tare da an sada Safina sashen haj wasila ta sakawa Auren Albarka ba don kuwa daga Uwar Amaryar ne na babu Ruwan kowa da kowa Kuma idan har haj wasila ta shugo gonar ta ba tace ta Rage Mata ko na sisi ba Kai karshe ma ce mata tayi da tace Mata kulle tace Mata casssss.

<< Hawaye 39Hawaye 41 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×