Skip to content
Part 50 of 57 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Amal ce ta ci karo da katinan gayyatar a kofar inda tayi saurin karasawa tana dubawa don daga nesa ta hango su har suna Bata tsoro sai da ta matso taga Ashe katin gayyata ne

Ta tsura mishi ido tana kallo inda ta karanto sunan Husna da na Daddyn ta.

Da sauri ta sure su tayi cikin gida tana kwalawa haj wasila Kira, “Mami Mami fito don Allah ki gani yau magana ta ta tabbata.

Haj wasila ta fito inda tayi Arba da Amal Rungume da IV ta karba tana dubawa inda taga sunan Husna da Alh Aminu.

“Kan abun ubar Nan ta antaka ashar inda Kuma Safina ta shigo dauke da kula wadda ta zubo abinci Wai ta kawowa Alh Aminu sai kuma ta iske tsegumin dorawa.

“Ni mutumin Nan zaiyiwa Haka? Cewar haj wasila tana Kara jinjina katin fuskar ta dauke da takaici Wanda Yake dab da shaketa.

Safina ta zari katin tana dubawa kafin ta kyalkyale da Dariya.

“Wannan jifar gara da ta wuce kaina Allah ya Kara Kira Wai gwari ta hau jirgin sama dama Mami ai ke yafi Dacewa da karbar yarinyar Nan gashi Kuma kin samu Allah ya kawo kazantar daki.

Ta fice da gudu ganin yadda haj wasila tayo kanta.

“Da kin tsaya ko don na tabbatar ke din Yar iskar karshen Duniya ce . Daga bakin kofa Safina ta Bata amsa.

“Kwarai kuwa tunda dai iskancin nawa Bai gwamutsa da har nayi saken da wata ta shigo min a matsayin kishiya ba Bari Naga ke kalar naki I’manin da yadda Zaki tarbi yar Amaryar Nan Taki, Da Haka ta fice tana Dariya.

Haj wasila ta Soma safa da marwa tana naushin hannunta. Sai kuma ta kwasa aguje ta Haye saman Alh Aminu inda ta iske shi Yana waya da DPO taja tsaki tana jifar shi da wani matsiyacin kallo har ya gama inda Yake bada umarnin ayi ta dukan Mai Kano har sai ya Fadi inda ya Kai Husna . Da Yake ba da salama ta SHIGA ba sai Bata fahimci abinda ake magana a Kai ba ta wurga mishi katin tana fadin

“Amma dai an gama Jin kunya idan har Rakumi ne ya shanye Ruwan Yan tsaki. Yarinyar da ta tashi a gabanka itace ka ke Shirin kwabewa a gabanta? Wai don Allah in tambaye ka Mana Aminu? Wahayi akayi maka da da lallai sai ka Auri Halima ko ahalin ta? Da wane idon kake Shirin kallon Husna bayan ka so Uwar ta yanzu Kuma ka dawo ita kake so? To na Rantse maka yadda ban yarda Uwar yarinyar Nan ta shigo min gida ba itama na Rantse maka ba Zan taba bari ka kawo min ita a matsayin kishiya ba Ni kuwa Karen hauka ya cijeni? Idan har Husna ta tako gidan Nan da sunan matar ka don Allah kace ba Aure akayi aka haife Ni ba.

Bata jira abinda zaice ba ta fice aguje har tana hada step biyu uku tana tsallakewa da sauri ta fice a motar ta inda Kuma su Mubarak suka iso.

Amal ta tarbesu suka gaisa har tana tambayar Mai Kano suka ce Mata Yana Nan. Zaidu ne ya tambaye ta ko baban Yana Nan? Tace Yana Nan suna son ganin shi ne? Mubarak yace Mata Eh, Ta haura sama sukayi kicibus zai sauko don zuwa gidan lauje.

Suka zube suna gaishe shi ya amsa Yana tambayar su karatu.

“Baba dama munzo ne neman wata Alfarma wurinka saboda munzo sai muka samu wani Labari marar Dadi shine mukazo don Allah kasa a saki Mai Kano in yaso idan ma shi ya boye Husna zai fiddo ta.

Alh Aminu ya shafi kasumbar shi Yana fadin,

“Kana kokonto kenan Akan Mai Kano ne ya boye Husna.

“Bana kokonto Amma dai nayi mamaki.

“To Mai Kano da kake gani ya wuce duk abinda kuke tunani don babu abinda ya samo a Legos sai ta addanci don wuka ya nunawa haj Yana fadin sai ya kashe mu Ni da ita. Abinda na kawowa Raina Mai Kano ya haukace tunda Yana shaye shaye Amma Kuma an tabbatar da hankalin shi to ko Yana da hankali gaskiya zaman shi a sake mu barazana ne ga Rayuwar mu Ni da hajiya tunda yayi ikirarin kashe mu Dole ne ya zauna hannun hukuma har zuwa lokacin da ake ganin ya Dace ya fito Amma yanzu tunda kunzo Zan San abinyi. Amma idan kunje ku bashi shawara ya Fadi inda Husna take shikenan zai fito Kuma yanzu zanyi waya nace a barku ku gana dashi idan ya yarda ya Fadi inda Husna take to tare ma zaku tawo dashi Amma idan ya saka taurin Rai to zai tabbata a can don Haka ku tashi kuje yanzu zanyi waya nace abarku ku gana.

Suka taso suna mishi godiya Yana fadin babu komai Wai su din Diyan shi ne na halak . Suna tafe Mubarak na gwada layin Husna Wanda yaki shiga tun jiya Yake Kiran ta Amma a kashe.

Suka iso station aka Kuma Basu damar ganin Mai Kano Wanda sai da suka koka saboda ganin yadda ya sauya saboda dukan da akayi mishi duk jikin shi ya fashe jini Kuma ya bushe ajikin shi

Mubarak ya Rungume shi Yana HAWAYE.

“Don girman Allah idan kasan inda Husna take Mai Kano ka fada ko don ka tausayawa gangar jikin ka…..

“Wallahi tallahi ban San inda take ba Mubarak sharri ne kawai na hajiya da wannan mutumin Amma babu komai Akwai lokaci matukar na fita a wurin Nan SAI NA RAMA abinda mutumin Nan yasa akayi min idan Kuma na mutu kune da alhakin dauko min fansar abinda yasa akayi min don Haka kuje abinku.

Mubarak na gode ina godiya ga duk yadda Allah yaso Dani a Kuma kowane Hali matukar ban Rasa imani na ba.

Zaidu ne yace tabbas ya yarda da maganar Mai Kano don baya karya maganar shi guda ce ko da ba zatayi Dadi ba Amma ba zai yuwu su barshi a wannan halin ba. Ya karbi wayar zaidu ya Kira Alh sulaiman Dan sodangi Wanda shine ubab gidan shi wanda ya Kai shi Legos.

Suka gaisa Yana tambayar shi inda ya shige Yana ta Kiran wayar shi Amma baya samu

Mai Kano ya fada mishi halin da yake ciki inda yayi ta mishi fada Akan me yasa Bai sanar dashi ba .

Kayi hakuri alh sun karbe wayata ne yanzu ma da ta Dan uwana na Kira ka.

“Kar ka damu Zan Zo katsina gobe in Sha Allah . Da haka sukayi sallama yacewa su Mubarak suje kawai kokarin da Kawai zasuyi mishi shine su samu wayar Husna suji inda ta tafi don a yanzu itace kawai Raba gardama. Da Haka sukayi mishi fatan ALHERI suka taho suna mamakin wannan jumurda wadda ke bukatar warwara.

Kai tsaye garin kurfi muhsin yayiwa tsinke inda suka dire ga Dan tsoho malam Magaji Wanda shine asalin uban marigayi mu azu shine kuma kakan Husna. Wata ganawa ta sirri da sukayi da tsohon Wanda ya nemi wani nashi da sauri Muhsin ya Kira wayar yayan haj wasila baba isuhu ya Kuma Zo garin kurfi shima akayi ganawar sirri Kan kace me? Sai ga gangami ana hadawa Wanda Gama sallar azahar ya tabbatar da Auren Husna da muhsin Wanda shi muhsin din ya sanar da su malam Magaji da suka ce mishi ba Uban shi ne ke son Auren Husna ba shi Kuma yazo da bukatar Auren ta? Sai yace ai dama shi ake nemawa Basu fahimta bane. Da Haka ya dawo gidan Anty bashariyya inda Husna take cikin Tararrabi sai ji tayi Yana fada Mata Wai an daura Auren su…

Bata San lokacin da ta fada jikin shi tana Rungume shi ba.

“Ashe da gaske kana Sona Yaya muhsin? Ta fada HAWAYE na biyowa fuskar ta.

“Ni kuwa nasan Ina sonki husna tunda gashi nayiwa Daddy wayo shi Yana can Yana jiran jibi ya aureki Ni Kuma na Rigashi.

“To amma sai dai mu samu inda zamu boye don a yanzu komai zai iya faruwa.

“Ai Nigeriar ma zamu Bari sai mun samo baby ko da zamu dawo Kinga Dole Daddy ya kyale mu. Ai kuwa basu kwana a garin kurfi ba suka daga garin kaduna inda zasu kammala shirye shiryen barin Nigeriar.

Muhsin kuwa doguwar wasika ya Rubuta ta text message ya turawa haj wasila ya Kuma turawa Daddy.

Haj wasila da taji shigowar sako a wayar ta ta jawo ta duba inda taga sakon muhsin dake fada Mata tayi mishi ADDU A don ya nemi Auren Husna ya Kuma samu yanzu Haka Yana Shirin barin Nigeria ba Kuma zai dawo Nan kusa ba.

Wata shegiyar guda me karfin gaske ta Rangado kafin ta kyalkyale da Dariya.

“Kai Allah na gode maka Ashe don anyi ciwo an warke ba a bawa mutuwa haushi ba Kuma tukunya me bori jikinta yake karewa. Haka Kuma girma ba shine hankali ba duk da dai Raina ba son Auren Nan nake ba muhsin Amma wata kusan tafi wata Allah yayi maka Albarka. Ta fada tana Danna Kiran wayar shi ta Kuma yi sa ar samun shi.

“Ki gafarce Ni Mami nayi muku laifi sai dai gaskiya ban shiryawa abinda Daddy ya zaba min ba.

“Kayi min daidai kudi ma Zan turo maka ka Kara wucewa kasashe biyar yawon honey month Allah ya tsare.

Da Haka sukayi sallama inda ta Kira wayar Alh Aminu tace an Bata sako ta bashi ya dawo gida don sakon zaiyi surprised din shi har tukwici ma sai ya Bata.

Ai kuwa da sauri ya dawo don a zaton shi sakon Husna ta bayyana zatayi mishi.

<< Hawaye 49Hawaye 51 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×