Hayaki ya turnuke dakin lauje Wanda Yake kwance ya shanya Baki Yana kwasar barci har da munehari sai Jin Rigar jikin shi ta Kama da wuta har tana laso busasshiyar fatar jikin shi. A firgice ya farka inda yayi Arba da hayaki ya cika dakin shi har dai ya Gane Zubaina ce ta bayyana Kuma yau da wuta ta taho Alamar an tabo ta.
Ya Mike zaune Yana tunanin Jin ta inda Zubainar zata Soma inda Kuma wutar ta zagaye shi tana kokarin laso shi da sauri ya Debi Ruwan kwaryar dake gaban shi ya watsawa wutar sai ta mutu murus ya Soma nuna hayakin Zubaina da wata yizga me kama da gashin bindin doki Yana fadin
“Hattara Zubaina hattara yau Ni kike Shirin konewa? Zakiyi kuskure kuwa.
Sai kawai yaji Zubaina ta fashe da kuka tana fadin.
“Kune zakuyi kuskure don gashi Nan kun hada Ni da matar can na haukatar da ita yanzu gashi ana Mata magani har an Soma Kona Ni da Rubutun littafin Allah gashi yanzu Nan duk sun Fara Kona min jiki. Kuma na Rantse da mijina dodon kod’i yadda aka Kona Ni din Nan ba Zan kone Ni kadai ba Kuma sai wuta ta tashi Akan ku da duk abinda kuka mallaka ka fadawa wannan mutumin da baya tsoron Allah dashi da duk Ahalin shi da dukiyar su Wallahi sai na kone su.
Alhaji Aminu Wanda ya shigo a Rude saboda lauje. Ya lalubo mishi hanyar da zai samo me Kano da muhsin har da Husna sai ya iske sabon labari
Lauje ya dubeshi Yana fadin, “Gashi Nan ma ai yazo sai ki fada mishi da Bakin ki.
Zubaina ta Kuma Rattabo wa Alh Aminu abinda akayi mata na yiwa Halima magani.
“Waye da wannan Aikin Kuma? “Dan ta ne Mana wannan yaron.
“Wai Mai Kano? Zubaina taja tsaki “Shi Mana. Yadda aka Kona ni Kuma sai kun kone Wallahi har da iyalan ku da dukiyar ku yanzu kuwa Zan Fara na fada muku ne don kar kuga Abu daga sama.
“A a Zubaina ba fa haka za ayi ba ki Fadi abinda kike so yanzu ayi Miki shi kiyi hakuri ki koma jikin Halima idan Kika Bari ta warke ai mutuwar mu ce tazo har ke.
“An Fara Kona Ni din kake cewa nayi hakuri na koma? Hatta yarana da muke tare dasu ajikin Halima suna gida suna jinya Suma an Kona su.
“Duk kiyi hakuri Zan Baki wani magani Wanda zai taimaka muku akan kunar wutar yanzu ku fita jikin Halima har agama yi Mata maganin don kar ayi ta Kona ku in yaso idan suka gama maganin sai ku koma Kuma duk abinda kike bukata zai Baku.
“Zan yarda da hakan idan har zai bani tayin jinjirin da Bai wuce wata shida ba Kuma nashi na kanshi shi da Yar wurin Halima jinjirin da ya kwanta cikinta na ke so Wanda Kuma shine zai zamo Uban jinjirin.
“Zai Baki dama ai bashi da buri sai na ganin ya Auri Yar Halimar sai ki taimaka mishi har Auren ya kullu Kuma asamu cikin sai a Baki kinji gimbiyar dodon kod’i.
Zubaina ta kyalkyale da Dariya tana fadin to ta yarda da Haka ta fice da alkawarin ba zata sake komawa jikin Halima ba sai taga sun gama maganin kafin ta koma ta bata Aikin.
“Lauje zuwan fa da nayi yanzu don ka samo min inda Zan samu Mai Kano ne kaga Ashe Halima tana hannun shi har ya Fara Mata magani Amma Kuma yanzu ba Mai Kano nake son samu ba sai Husna wadda Zubaina ta Dora aiki akanta. Ita da muhsin sun yaudare Ni Amma yanzu meye abinyi ?
“Wayar ta zaka nema in ka sameta sai ka yaudare ta ta fada maka inda take har shi Mai kanon ba zaiyi wuyar samuwa ba tunda tare suke . Ya Mike Yana fadin ko muhsin ya samu yasan zai matse shi har ya Fadi Inda su Husna da Mai Kano suke da Haka ya fice.
Muhsin da Yake ta neman layin Husna akashe ya kasa hakuri da neman layin har dai yau da Yake kokarin Kiran sai Kuma ga Kira ya shigo mishi da bakuwar lamba har zai share Sai kuma yayi Shahada ya daga don yayi zaton ko Daddy ne
“Yaya muhsin ! Ya jiyo muryar ta cikin shesshekar kuka inda ya zabura ya Mike tsaye,
“Husna ! Kina Ina don Allah? Ina wayar ki da nake ta neman layin ki bana samu?
“Kayi hakuri Yaya muhsin Yaya Mai Kano ne ya karbi wayar yanzu ma da layin Salma ne na Kira ka.
Ya sauke ajiyar zuciya Yana fadin, “Wai me mukayiwa Mai Kano ne da Yake son kashe mu da Rayuwar mu Husna?
“Wallahi ban sani ba Yaya muhsin don Allah ka Adana min kanka nayi maka alkawarin ba Zan taba karbar wani mijin bayan Kai ba don Allah Kar ka Daina Sona wallahi duk bugun numfashi kana Raina Kuma Ina tare da Kai.
“Nayi Miki alkawarin hakan Husna Kar ki damu idan Mai Kano Yana kusa ki bashi wayar zamuyi magana koma fada min inda kuke nazo na same ku.
Duff wayar ta mutu charge din ya sauka tayi ta hello hello shima yayi ta hello hello har dai ta gane wayar Salma ta mutu.
Dole ta hakura ta mikawa Salma wayar ta Amma fa hankalin ta ya tafi ga halin da muhsin take ciki don ta San yafita SHIGA Hali.
Shehin malamin har rukiyya yayiwa Halima wadda ko tari batayi ba har dai ya Gane anyi nasara Akan aikin sai aka SHIGA Bata taimakon magani cikin ikon Allah sauki yayi ta samuwa Amma fa Bata magana bare tace uffan sai dai tayi ta kallon mutane.
Mai Kano da yazo Ranar juma a ya iske jiki yayi sauki murna ta cika shi yayi ta godewa Allah Halima sai kallon shi take tana kallon Salma da Husna.
Ya dubi Salma wadda yace suje gidan su ya gaishe da iyayen ta yayi musu godiya Akan hidimar ta ga mahaifiyar shi..
Suka nufo gidan masu inda Adama ta Fara tarbar su da ashariya.
“Wace shegiyar ce Hala tambadaddiyar yarinyar Nan ce Salma? Ke Kam uwarki ta cuce ki da Bata bar Miki gadon komai ba sai na karuwanci Hala kina can bin dakunan samarin? To in ma Kika kwaso tsiyar ki ta cikin shege na Rantse Miki ba dai Nan gidan ba Zan koraki Ni Wallahi.
“Kiyi kokari Adama mutumin Nan ne da nafada Miki mamar shi na Asibiti shine yazo gaishe ki.
“Kice Dan iskan ki Kika kawo min to Allah ya baku nasara Yan iskan karshen Duniya.
Mai kano ya Soma da gaisheta ta amsa tana kwabe Baki kamar tana ganin shi.
“Dama nazo nayi muku godiya akan abinda Salma tayi min Akan mahaifiyata nagode kwarai Ubangiji ya Kara girma da lafiya.
“Oh ni Adama har Ni za a nunawa bariki da iya iskanci Kai Kuma da Yake baka da kunya har ka ke sakani gaba kana neman linke Ni Bai Bai to na Rantse maka babu inda zakaje sai ka fada min sau nawa ka taba musu yarinya sai kawai ta cacumo Rigar shi cikin sa a kuwa da hasaso inda muryar shi take fitowa ta damko shi.
Sai ka fada min Wallahi ko yanzu na Tara maka mutane nace cikin shege kayi Mata.
“Kiyi hakuri baba in har nayi abinda kike magana akai ai ba Zan Zo har gidan su ba.
“To naji biya kudin tabawar da kayi mata ko Kuma yanzu in fasa ihun kwarto kaga yadda Za ayi da Kai.
“To baba nawa Zan biya sai na biya din. “Dubu Ashirin zaka biya.
Ya kuwa zura hannu aljihu ya debo kudin zai Mika Mata Salma dake kuka tace,
“Kar ka bata Yaya Mai Kano don Allah Kar ka Bata.
“Shegiya wadda batayi gadon Arziki ba to Kar ya bada din kiga yadda ke Kuma zamu Kare.
“Gasu ma Baba har da wata dubu goma ma na Kara Miki talatin kenan ya fada Adama Kuma ta warce kudin tana fadin jeka ma ba cikin da Daya ba in katashi yi Mata cikin Ya’ya goma . Ya Mike Yana mata sallama da cewa zai dawo ya Kara gaishe ta.
“Wannan Kuma Kai kajiyo . Cewar Adama
Ya fito Salma ta biyo bayan shi tana mishi godiya idonta taf da HAWAYE.
“Karki samu damuwa Salma ban San Haka kike fama ba agida ai da na San abinyi duk da Baki fada min ba na fahimci wannan matar ba mamar ki bace ko?
Ta share hawayen ta tana fada mishi mamarta ta Rasu Adama Kuma kishiyar uwar su CE wadda tayiwa uwar su sanadin barin Duniya.
“Kici gaba da hakuri Salma Zan Baki tallafi in Sha Allah fatana dai kiyi ta Rike mutuncin ki kinji ko? Ta gyada mishi Kai tana fadin in Sha Allah.
Da haka yayi Mata sallama bayan ya bata kudin Wanda Taki karba sai da ya matsa kafin ta karba da Haka ya wuce Yana tunanin ta inda zai taimaki Salma?
Ya komo gida inda ya iske motar muhsin shi da Husna a motar suna magana wani bakin ciki ya turnike shi yaji kamar ya shake su. Bai CE musu komai ba ya shige gidan Yana jiran shigowar Husna wadda ya tabbatar da sai ya taba lafiyar jikin ta ko zata fita hanyar muhsin.