Skip to content
Part 54 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Muhsin da ya nace da Kiran layin Salma da Husna ta Kira shi ya Dade Bai samu layin ba kafin can da yamma yayi nasarar samun shi ya Kuma azalzali Salma da ta taimaka mishi ta sada shi da Husna. Salma kuwa ta taho ta kawowa husna wayar inda Kai tsaye ya nemi address din inda take ta kuwa fada mishi ya bugo hanya sai gashi Ashe tana katsina Bata bar garin ba.

Ya danke hannayen ta ita kuka shi kunar zuciya.

“Husna idan har da gaske kina Sona to ki yarda mu wuce kawai don Banga dalilin da Mai Kano zai sheganta Mana Aure ba tunda Yake fadar Bai yarda da Auren mu ba to Nima fa ba yarda zanyi ya Raba mu ba don Haka in har da gaske kina Sona to ki taho mu bar garin Nan kawai dama saboda shi muka Zo sai Kuma Yake neman juyewa ya saka ALHERI da sharri wallahi da nasan Haka zai yi Mana da ban yarda munzo ba don Haka SHIGA mota kawai mu wuce..

“Yaya muhsin Ashe kana kokonto Akan soyayya ta da kauna ta gareka? Har abada baka da kishiya a zuciya ta sai dai ka sani ba Zan iya binka a yanzu ba ko da Yaya Mai Kano Bai haramta min hakan ba nayi maka alkawarin Zan Rayu da Kai har karshen numfashi Kuma ba Zan taba karbar wani mijin bayan Kai ba.

Mai Kano ano da ya karyo kwana ya gansu shine ya kada hantar muhsin Dole sukayi Duff kamar Ruwa ya cisu. Ya Zo ya shuda su ya wuce Yana murtuke fuska Alamar Ran shi ya motsu da ganin su don Haka muhsin ya Karanto tsana fal idon shi don Haka Yake Jin ba zai taba Barin husna ba ita Kuma tanajin ba zata taba Barin Halima a halin ciwo ba duk da ta Fara samun sauki ta bi miji ba don Haka ta ja ta kafe Akan Ra ayin ta shima ya kafe da lalai sai ya tafi da ita.

Yadda take Rike da hannunta haka ya nufi mota da ita tana fadin yayi hakuri zata bishi Amma ba yanzu ba Amma Ina sai dauko ta yayi daf tamkar Yar yarinya k’arama ya saka ta mota ya yiwa motar key daidai da Mai Kano ya gaji da jiran shigowar Husna ya fito don ya korata sai ganin sakata mota da muhsin yayi ya harba titi aguje.

Aikuwa da sauri ya tari napep yace ya bi mishi bayan motar muhsin wadda ke tsala gudu tamkar zata tashi sama

“Yaya muhsin wannan ba itace hanyar da zaka biyo ba ka sauke Ni Wallahi ba Zan bika ba a yanzu ko kaini wallahi sai na dawo Wai baka San zaman jinyar mahaifiyata nake ba? Itace Bata da lafiya nake jinyar ta kana ga ya Dace na barta a cikin Hali na bika?

Sai ya kalli maganar Tata a matsayin togacciya ba gaske ba sai Bai saurare ta ba Yana ganin zata goyi bayan Dan uwan ta ne su Yake shi.

Kuka take Sosai tana fadin ya sauke ta ba zataje ba Amma Bai saurare ta ba sai ta sheka gudu yake da fatan yaga ya fice ya bar garin katsina gaba Daya shine zai Bata amasa ya Kuma samu saukin fargabar dake kwance a Rai da zuciya.

Mai kano da yayi alkawarin kure malejin su a duk inda zasuje Yana biye dasu Kuma Basu San Yana biye dasu ba sai gashi traffic light ta tsaida su tana Kuma harba nombobin ta kamar Bata so yayin da muhsin Yake ganin nawar harbawar traffic din yayi Mata kyar da ido ko wace harbawa tana harbawa da bugun zuciyar shi yayin d husna Kuma tayi maza ta ta balle kyauten motar ta fito aguje tana neman guduwa daidai da karasowar Napep din Mai Kano Wanda husna tayi saurin fadawa ba tare da tasan Mai kanon ne ciki ba har sunayin taho mu gama inda Yake Shirin fitowa a fusace don ya keta muhsin sai kawai yaga Husna ta Fado itama idonta ya fada a nashi sai tayi maza ta Ruko hannun shi ta na kuka.

“Sake min hannu in yaga Gayen can ta yadda ko an ce ya Kuma yin abinda yayi zai karyata kansa.

Sai ta Kara Rike shi don yadda ta ganshi komai zai iya faruwa ita Kuma Bata son abinda zai taba Mata lafiyar Yaya muhsin.

Da duka karfin ta ta Rike shi.

“Ka yi hakuri Yaya Mai Kano Kar ka taba shi na Gaya mishi ba Zan bishi ba sai da izinin ka yanzu ma nice na fito daga motar don ba Zan iya Barin mama a wannan halin ba Kuma ba Zan iya binshi ba tare da izinin ka ba. Duk wannan Kare Kan da tayi Bai Hana ya wanke ta da Mari ba inda ta SHIGA nutsuwar ta ta tasho Baki tana Hana kukan dake son fitowa fitowa.

Aguje ya fito ya nufi motar muhsin daidai ya sauke gilas din motar sai kawai yaji shak’a Mai Kano ya cakumo shi Yana neman zaro shi ta gilashi

“Me yasa ne Ina maka kawaici baka San Ina yi ba? Wai wahayi akayi muku da mu ne da kuke bibiyar mu? Kai a yau nayi nadamar haduwar mahaifina da mahaifin ku don Bai Kare Ni da komai ba sai bakin ciki.

“Aure kake takama dashi na Husna ko? To ka aje a Ranka daga yau zai yanke in ma don zaka sake ta ne saki Kuma har uku in ma baka sake ta ba to Zan Kai ka gaban Alkali ka sake ta. Kashedin karshe da zanyi maka shine Kar ka Kuma zuwa inda Husna take na Raba ku Rabuwa Kuma ta har Abada idan kuwa tsautsayi ya kaika sake kusantar husna duk abinda nayi maka ka kalle shi a laifin ka ne !

Ya sake shi ya juyo ya shigo napep inda Husna ke ta Rera kuka ganin yadda ya shake muhsin yana zaro mishi idanu.

Tuni traffic ta bada hannu Amma saboda tsayuwar muhsin Wanda Mai Kano ya shake ya Hana ya motsa ya Tara go slow ba kadan ba sai danno musu horn ake.

A cikin Wanda go slow n ya tsayar har da Alh Aminu Wanda ya leko daga motar don yaga abinda ya Rufe hanyar sai kawai ya hango fitowar Husna daga motar muhsin da Kuma shakar da Mai Kano yayiwa muhsin inda yaji wani Abu Mai Kama da farin ciki don su duka neman su yake ba Mai Kano ba bare Husna bare Kuma muhsin don Haka yayi saurin daukar waya ya Kira Yana fadin ayi maza a sameshi titin government house.

Sai dai Kuma wani Arashi shine kafin Wanda ya Kiran ya Zo tuni Mai Kano ya SHIGA napep sun cilla shi da Husna inda Kuma muhsin ya ja tashi motar ya yi gaba da Shan alwashi sai ya Rasa wa zai bi tsakanin Mai dake tare da Husna da Kuma muhsin da yafi tsaya mishi a Rai saboda duk ya tattare dukkan abinda ya faru ya Dora shi akan muhsin Wanda ya zamo kanwa da baiyi abinda yayi ba da yanzu Husna ta Dade a gidan shi don Haka sai kawai ya bi bayan su Mai kano ko ba komai tsuntsun biyu ne zai jefo da Dutsi Daya akasin Mai Kano da Yake shi kadai Kuma in husna ta bayyana ba zai wahalar bayyana don Haka sai ya bi bayan su Husna ba tare da ya Bari su Mai Kano sun San Yana biye dasu ba har zuwa gidan da Halima take karbar magani da sauri Kuma ya juyo dama don yaga gidan sai Kuma gashi ya gani.

Safina kuwa da taji rade radin Wai muhsin ya Auri Husna ta gazaryo aguje wurin haj wasila
“Wai Mami da gaske ne abinda naji Amal tana fada Wai an daura Auren Husna da muhsin? Haj wasila ta kwabe Baki tana fadin.

“Nima fa kamar hakan naji don har na bashi kudin tafiya honey month don yace min kasa biyar yake son zuwa.

“Mami Kuma Kika yarda saboda Allah?

“To ya kike so nayi na Hana shi ko kuwa? Ke Ni in ma zai yarda wallahi Zan Kara mishi da wasu Matan guda biyu don ke da Uwar ki ku yarda bana yin ku don Haka sai ki saurari sakon ki a ko da yaushe daga muhsin don kin San yadda yake yin Husna zai manta ne kawai dake Kinga sai a bi wani sarkin ba na katsina ba.

Safina ta Mike jiki na Bari don har ga Allah ba ta kawo hakan Nan kusa ba sai gashi ta faru har ta Kare.

“Uhummm wasila kenan kinyi nasara a wannan karon nasan ke Kika hada muhsin da shegiyar yarinyar Nan don ki cusa min takaici Ni Kuma Zaki ga inda Zan hudo Miki Ina Nan kuwa muhsin zai sameni ke dashi zakuyi mamaki Wallahi ai kuskuren da kuka Fara kenan ke dashi..

“Uban muhsin ya kamata ki nema ku tauna dashi don shine yafi Dacewa kuyi maganar Nan da shi tunda ai kin Dade da sanin inda na aje ku . Kuma kamar yadda nace muku ke da maimuna na saka muhsin ya sake ki to yanzu Kuma ya Rage tsakanin ku Ashe jifar Nan dai da kikace Ashe akanki zata sauka don Haka fice ki bar Nan in Kuma uban muhsin na burge ki sai na marabce ki a dayan dakin.

A guje Safina ta fice tana kuka inda ta Kira Uwar ta maimuna tana zayyane Mata Auren da haj wasila Wai ta hada muhsin da Husna.

“Wa ce Husnar? Ba dai kareren yarinyar Nan ba? Sai ta antaka ashar tana fadin gani Nan Zuwa gidan naku yanzu ai tunda haj wasila ta nuna Bata muradin Auren Nan komai zata iya aikatawa to barni da ita Wallahi sai na dauko Miki fansa don Haka kazanta.

<< Hawaye 53Hawaye 55 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×