Zaman su Husna da Halima gidan Adama zamane na hakuri duk da zukatan su ba sa tare da nutsuwa sai hakan Bai Basu damar Gane wacece Adama ba.
Ita dai Halima tana zaune ne kawai sai dai tabi mutum da ido Amma tana fahimtar abinda akeyi ko ake fada Kuma tanaji tana gani magana ce dai kawai Bata yi. Yayin da Husna ke Rike da wayar Salma tana neman layin muhsin Amma layin akashe. Ta mikawa Salma wayar ta tana share hawayen ta inda halima ta lura da hawayen da take sharewa har ta yafito ta da hannu Alamar tazo. . .