Skip to content
Part 56 of 76 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Zaman su Husna da Halima gidan Adama zamane na hakuri duk da zukatan su ba sa tare da nutsuwa sai hakan Bai Basu damar Gane wacece Adama ba.

Ita dai Halima tana zaune ne kawai sai dai tabi mutum da ido Amma tana fahimtar abinda akeyi ko ake fada Kuma tanaji tana gani magana ce dai kawai Bata yi. Yayin da Husna ke Rike da wayar Salma tana neman layin muhsin Amma layin akashe. Ta mikawa Salma wayar ta tana share hawayen ta inda halima ta lura da hawayen da take sharewa har ta yafito ta da hannu Alamar tazo gareta.

Ta matsa tana Riko hannun ta tana tambayar ta me yasa ta hawaye? Sai ta Rushe da kuka har tana Dora kanta a cinyar Halima kafin ta Fara magana.

“Mama abubuwa sun faru da yawa bayan fakuwar ki aciki har da Aure na da muhsin na gidan Baba Aminu Wanda Ubangiji ya jarabi zuciya ta da kaunar shi shima Yana Sona mama Amma Yaya Mai Kano yace Babu Ni Babu Yaya muhsin sai ta Rushe da kuka inda Halima ta bita da kallon tausayawa. Ta San abinda Mai Kano yake nufi sai dai tana ganin kamar laifin wani baya shafuwar wani don Haka sai ta Soma shafa bayanta Alamar Rarrashi tana Mata maganar kurame wato nuni da ta Bari Mai Kano yazo ita zata Bashi hakuri ya barta ta komawa mijin ta. Sai kuwa shiru tana Kara gyarawa Halima daurin kallabinta ta kuma amsar wayar Salma ta Kira muhsin cikin sa a kuwa ta sameshi sai ta fice da sauri zuwa soron gidan tana Kiran sunan shi.

“Yaya muhsin ! “Uhummm ya sauke ajiyar zuciya Yana fadin, “Husna kina Ina don Allah? “Wai da gaske kike Akan abinda Kika fada? Wallahi husna ba Zan bar Mai Kano ya tabbatar da abinda ya fada ba kawaici da alkunya nayi mishi Wallahi idan na fito mishi a muhsin Dina ba zaiji Dadi ba.

“Ka fahimce Ni yaya muhsin ba Wai naki bin ka bane. Nazo ne don wanke Yaya Mai Kano daga zargi ya Kuma fita sai Kuma nayi karo da mahaifiya ta ta bayyana cikin wani hali Wanda ba Zan iya Barin ta ba har sai Naga ta dawo nutsuwar ta shine kawai Dalili.

“Yanzu kina Ina kenan?

“Zaka Zo ne?”

“Ko Baki bukatar zuwana?

“Ba na nufin Haka sai don gujewa haduwa da Yaya Mai Kano.

“Murnar bayyanar mamar mu zanzo Husna ai tunda mama ta bayyana basan matsalar mu tazo karshe don ai nasan gaba da gaban ta Kuma duk girman gona tana da kuyyar karshe duk taurin Ran Mai Kano Dole yayi taushi a gaban mama don Haka fada min inda kike zanzo yanzu.

Ta kuwa fada mishi gidan su Salma ya Bata tabbacin gashi Nan Zuwa.

Lauje da yaji tsayuwar motar Alh Aminu sai yayiwa kofar shigowa dakin zuru da ido har sai da Alh Aminu ya shigo kafin ya sauke kallon shi gareshi

“Lauje na Rasa yadda Zan bullowa wannan lamarin yanzu Haka na tura a dauko min yarinyar Nan da Kuma yaga Rayuwar Mai Kano Amma Wai sun bar inda na gansu Wai yaron Nan ko ya hada iri da jinnu ne? Ina Kuma ya Kai Husna?

Lauje ya dubeshi Yana murmushi

“Ai ka manta ne mutumina duk yadda kake zaton yaron ya wuce Nan. Kai dai baka iyawa dashi sai dai ko Yan dabar sune kawai maganin shi Kuma ka tabbatar kasa ka Wanda zasu aika maka dashi kiyama in kuwa ba Haka ba Wallahi a ko yaushe zaka iya ganin shi gareka.

“Yanzu ka Kira Zubaina ka ce ta komawa Halima duk inda take don in har Halima na lafiya to Ni Kuma na Gama Zama lafiya gara kawai a maido wa Halima kasanta ya koma sama sama ta koma kasa shine kawai Zan cika burina lafiya.

“Ka kuwa San na tambayi Zubaina ko ya ta Kare da sakarwa Husna jini shine take fada min wai yarinyar tana kasancewa cikin tsaro don Bata wasa da Addua shiyasa Bata sakar mata jinin ba Kuma ai har yanzu Basu kebe da mijin ba shine dalilin da take kintatar ta har Sai ta samu sa ar ta.

“Ai zata samu sa ar ta Kai dai Kira min ita din taje ta cika Aikin Nan na maida Halima Ruwa

Ai kuwa lauje ya hada garwashi ya na zuba maganin Sai ga Zubaina ta bayyana tana fadin me Kuma za ayi ake Kiran ta?

“Idan masu maganin Halima sun dakata ki koma jikin ta ki Bata aikin da suka Fara kima nuna Mata hanya ta fice ta bar garin katsina gabadaya don zaman ta lafiya tashin hankalin Alh Aminu ne ke Kuma sai ki saurari cika Miki alkawarin da Kika bukata na jinjirin Dan Husna da Alhaji Aminu..

Zubaina ta kyalkyale da Dariya tana fadin, “Yanzu kuwa Zan cika Aikin Nan Nima Kuma sai ayi maza a cika min nawa alkawarin.

Hayakin ta ya fice daga dakin lauje Wanda Yake jawo jakar fatar shi Yana fitowa da wani tandu

“Karbi wannan gadalin tozali ne Wanda zai jawo maka Husna cikin Ruwan sanyi matukar kunyi ido hudu da ita to ita da kanta ma zata biyo ka.

Da sauri Alh Aminu ya Cabo tandun Yana fadin, “Yi min Karin bayani uban Yan sharri.

“Kifil sunan shi irin shine Wanda na baka kwanaki da kake jawarcin Halima sai dai ita baiyi tasiri Akan ta ba to ka jaraba shi ga Husna matukar ka saka shi a idonka Kuma kukayi ido Hudu da mace to har Kan gadon ka sai ta biyo ka Kuma duk abinda kake so Sai ta yi maka shi don Haka ga shi Nan ka kasance dashi a ko ina saboda tsaro ba don tsoro ba da ka gano inda Husna take sai kayi maza ka shafa shi ka Kuma tabbatar kunyi ido hudu to ka saurari sakamako har Kan gadon ka sai ta iske ka.

“Wace irin godiya zanyi maka lauje? Me kake so na yi maka tukwici dashi?

“Komai ka bani zan so mutumi na Amma ba yanzu ya kamata a bani tukwicin ba a Bari sai Husna tazo hannu har an Sha Romon tukuna.

“Duk da Haka Rike wannan kafin zuwan lokacin ya fito da dammunan kudi ya aje mishi ya Mike ya fito Yana yiwa laujen sallama da fadin sai ya jishi

Muhsin kuwa ko minti biyar Bai Kara ba ya iso gidan su Salma inda Salma ta shigo dashi Kai tsaye inda Kuma Adama ta Dora tijara Wai Salma zata mayar mata da gida gidan magajiyar karuwai tana shigo Mata da maza gandam gandam.

Abinda ya kona Ran muhsin Amma Bai tanka ba suka wuce dakin Salma inda Halima take ya zube Yana gaishe ta cikin mutuntawa ta washe fuska tana mishi nuni da hannu Alamar amsawa yayi Mata jajen jikinta da bayyanar ta duk ta amsa shi cikin nuni irin na kurame
Yayi mamaki matuka da Rashin maganar ta sai da Husna ta fayyace mishi komai tun daga farkon ciwon har kawo yanzu da ake ganin an tako matakin nasara. Ya Kuma jimantawa ya Kuma tambayi Husna Nan din gidan waye da suke zaune da waccan tsohuwar Adama? Ta sanar dashi Yaya Mai Kano ne yace su zauna anan saboda baya son su koma gidan su inda babu kowa idan Halima taji sauki ne zasu koma. Kudi Muhsin ya ajewa Halima tana ta mishi nunin ADDU A ya fito husna ta biyo bayan shi suna Kara zantawa sai Dab magaruba ya tafi da alkawarin gobe zai dawo.

Ya fito kwanar gidan Adama kenan ya hau titi Yana tafiya sai ga Alh Aminu shima sun karaso kan traffic a tare Kuma cikin sa a idon su ya hadu muhsin yaga irin kallon da Daddy n ke mishi ya tabbatar akwai magana Wai gawa ta Rike Mai wanka har aka Basu hannu Amma suna kallon juna. Shi Yana kallon muhsin Wai wannan yaron har yasan yayi min abinda yayi
Shi Kuma muhsin Yana mishi kallon tsoron ukun da zai saka shi mussamman yanzu da ya ganshi duk boyon da yakw mishi yau dai sun hade.

Horn din da ake danno musu yasa muhsin yin karfin halin yin gaba inda Kuma Alh Aminu ya Rufa mishi baya

Ta gilashi muhsin ya hango Daddyn Yana biye dashi don Haka sai ya dannawa motar giya ya auna aguje inda shima Alh Aminun ya Kara fafarar tashi motar ya bi muhsin din aguje tamkar zai cafko motar tashi ya wurwura ya kwala da kasa.

<< Hawaye 55Hawaye 57 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×