Skip to content
Part 66 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Muhsin da ya kasa samun nutsuwa ya dawo gidan su da son ya hadu da Daddyn Amma ko kyallin shi Bai gani ba. Ya zamo tamkar zararre hankalin shi ya gama tashi ya Rasa Ina zai saka kanshi yaji sanyi.

Gararam yaji an turo kyauren dakin ya juyo Yana kallon Safina dake shigowa tamkar wadda aka wurgo wani takaici ya kule shi ya bita da kallo ta karaso tana Rungume shi yayi maza ya zare jikin shi daga nata.

“Ba ka yi min adalci muhsin Wai me nayi maka Haka kake gudu na? Don Allah ka Soni ko Yaya ne.

“Ke ce baki yiwa kanki Adalci Safina da kin yiwa kanki adalci da Baki tsaya son maso wani koshin wahala ba ai ban boye Miki ba kece Kika nace kika makale yanzu idan kina son yiwa kanki adalci Zan Baki shawarar ki koma gida kawai.

“Wallahi baka Isa ba sai ka Soni ko don Dole duk Zaman Nan da nayi sai in bige da kunya ta akanka? Wallahi baka Isa ba.

Ya nuna Mata hanyar fita da ya tsa Alamar ta fita . Yadda taga fuskar tashi yasa Dole ta fice tana zuba maganganu har da su zagi dai Amma da Yake Bata gaban shi sai bai bi ta kanta ba fatan shi da burin shi Daddyn ya dawo ya tabbatar da inda Husna take shine kawai muradin shi a yanzu.

Ya fito farfajiyar gidan ya tsaya Yana kallon gidan kamar zai hango ta inda Alh Aminu zai bullo sai kawai yaga Mai kano ya shigo Yana wurga idanuwa ya Kuma dauke kanshi daga kallon muhsin din don Yana Jin ba wurin shi yazo ba Uban shi Yake nema ba shi ba.

Shima muhsin din sai ya bishi da kallo kawai yaga ya nufi cikin gidan da wata izza da son ta fashe kowa ya Rasa.

Amal tagan shi tamkar majigi ko gizo. Ta kwala mishi Kira. “Yaya Mai Kano!

Ya hararo ta idanu kamar suyo waje Amma Bata damu ba ta Mike tana mishi sannu da Zuwa. Kai tsaye ta nufi frij tana dauko mishi gwangwanin lemun shany me sanyi ta dire mishi gaban shi ya dubi lemun ya kuma dube ta.

“Ban taba kwata Shan ko Ruwan gidan Nan ba bare kiyi tunanin ko Yana burgeni ba Kuma Zan Bata recort dina ba Akan gidan Nan da Ahalin sa ya kamata ki Rike wannan Amal Ina kallon komai a matsayin halal Amma abinda ya shafi Ahalin Nan gidan giya ta fishi tsarki a idanuna.

“Na yarda Amma don girman Allah ka Sha abinda na kawo maka bani ko Ahalina bane suka baka soyayya ta CE ta baka Kar ka badawa soyayya ta kasa Yaya Mai Kano.

Wata Ashar ya antakawa soyayyar Yana fincikar gwangwanin lemun ya watsar

“Ina me gidan Nan Yake? Ya tambaye ta da Amon murya. Bataji ko dar ba ta amsa mishi da baya Nan.

Ya ciji leben shi idanun shi sun kada masifa kawai ke cinsa.

Sai ganin Amal yayi ta zube Agaban shi tana Ruko kafafun shi HAWAYE na bin fuskar ta.

“Ni baiwar soyayyar kace Yaya Mai Kano don Allah kayi min Alfarma ka karbi soyayya ta nayi maka alkawarin komai ka saka Ni zanyi maka shi na Kuma Roke ka don Allah ka fada min abinda Daddy yayi maka na tambaye shi ya fada min Bai San abinda yayi maka ba. Ka fada min don Albarkacin kyautar zuciyar da nayi maka wadda ban taba kwata hakan ba ga sauran maza. Wani Abu me kama da tausayi ya tsirga mishi har ya kamo hannuwan ta ya mikar da ita tsaye suna duban idon juna.

“Na so na kwata yi Miki Alfarmar da Kika Roka Amma sai inji jigon Ahalin ki shine Abu guda Daya Tak da nakejin ko duka Duniya afuwa da Alfarma zasu zamo su kadai ba Zan taba yiwa mahaifin ki ba Amal. Ba Kuma zakiji komai a bakina ba tunda ya Rufe ki nasan dama ba zai taba furtawa dayan ku ba saboda Muni Nima Kuma idan nace Zan fada muku to mutuwa kawai zanyi saboda bakin ciki Amma ki Rike a Ranki Akwai lokaci ! Don Haka na gode da KYAUTAR ZUCIYA Amma ki bawa wani Ni ba Zan iya karba ba in ma na karba karshen ta na jefar a kwatami. Yana Gama fadin Haka ya juya ya fice ta bishi da kallo.

Muhsin na tsaye inda Yake yazo ya shuda shi ya fice shima da idon ya bishi

Lauje ya zubawa Alh Aminu ido Yana sauraren bayanin shi na zubar jinin Husna.

“Ka ce daudar gora ce da ciki Yake shanyewa Ashe Kai Zubaina ta jikawa Aiki.

“Ni yanzu Kira Zubaina taje ta tsayar da zubar jinin Nan Kar ta kashe min Husnar don baccin da jinin Nan da yanzu ban fito ba Amma Dole tasani zuwa Nan ban San Haka abin zai zamo ba ai da Ban yarda Zubaina ta sakowa Husna jini ba.

Lauje ya kyalkyale da Dariya Yana Fadin

“Kai wannan jini yazo da kancal kace da yanzu kana can kana morewa mutumina? Kana wuta fa Kaine ke son Uwa kaso yarta in ba Kai ba Ina ake Haka ai sai Duniyar awaki.

Ya cacumo wuyan lauje ya shake.

“Me kake son fada min lauje? Ni kake wa Gori Akan abinda zuciya ta ke muradi? Uwar ta da kakarta ma idan sukayi min Zan neme su bare Uwa da Yar Ya saki lauje Yana mayar da numfashi.

“Daga fadar gaskiya kake neman kasheni? Anya kuwa zaka iya da abinda ke kaina idan ka kasheni?

“Kaga Ni yanzu Kira min Zubaina da Allah
Ya hada garwashi ya zuba garin magani hayaki ya turnike a dakin Zubaina Kuma ta bayyana Amma a yau bayyanar Tata Babu kuka babu Dariya ta bayyana ma Amma tamkar Bata bayyana ba. Lauje ya Kuma zuba wani kalar maganin Kiran nata inda ta amsa a kufule cewa.

“Haba gani Nan fa nazo. “Kuma yau hanyar Taki Babu shaida Zubaina ba kuka ba dariya?

“Mun fa gaji da Aikin mutumin Nan komai muna biya mishi bukata Amma shi baya biya Mana tuni yayi Mana alkawarin tayin da zai kwanta acikin yarinyar can Amma har yanzu Bai cika alkawari ba.

“Ki yi hakuri akasi aka samu yarinyar ce da Kika sakarwa jini Yake so ki tsayar da jinin har a cika Miki burin ki yanzu tashi kije zaiyi Miki yadda kike so indai ki tsayar Mata da jinin.

Basuji ta tanka ba Haka ma Basu ga fitar hayakin fitar ta ba.

Shida lauje suka dubi juna Yana mikewa ya fice bayan ya fadawa laujen zai dawo ya fada mishi komai kenan.

Ya taho Yana dokin yau din zai angwance da Husna ya tsaya ya Kuma yin siyayyar kayan kwalam da makulashe ledodi fal Kaya
Mai Kano da ya fito Bakin titi ya hawo napep suka sheko a guje kamar daga sama ya hango Alh Aminu ya bude mota Yana saka ledodi amotar kafin ya SHIGA ya figi motar
Mai kano da yaji kamar yayi tsuntsuwa ya tashi sama Haka ya dangwari me napep din Yana fadin bi min bayan motar can yi sauri Kar ya bace Mana.

Ai kuwa me napep ya Rareta da karfi ya cilla aguje Yana bin bayan motar Alh Aminu da ya dauki hanyar lambun Khadija wadda zata kaishi a huta hotel har motar ta karya kwana ta SHIGA a huta inda Mai Kano ya sauka tun abakin gyate din ya sallami me Napep din ya tausa kanshi cikin farfajiyar inda ya hango Alh Aminu ya kwaso ledodin shi ya nufi dakin me lamba ta Sha takwas asaman bene VIP.

<< Hawaye 65Hawaye 68 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×