Skip to content
Part 67 of 78 in the Series Hawaye by Hadiza Gidan Iko

Jirgi Daya suka yanki tikitin ba tare da muhsin ya yarda Daddyn ya San Haka ba . Shi Yana ganin Daddyn da cuku cukun shi shi Kuma Bai yarda ya ganshi ba don Haka AWA biyu Rak ta kammala musu shiri har jirgin ya samu lulawa sararin samaniya suka keta gajimare zuwa Legos

Washe gari Mai kano ya nufi kurmiyal gaisuwar matar Alh Dan iro inda ya Kira Alh sulaiman Dan sodangi ya tambaye shi inda zai tambaya idan ya Zo kurmiyal.

“Da baka taho ba Aminu don yau din muma zamu dawo tunda anyi ADDU AR uku Amma tunda ka taho karaso sai mu dawo tare ka Kuma samu ladar Zuwa. Ya iso kurmiyal yayi gaisuwa ga Alh Dan iro ya Kuma yiwa Alh sulaiman Dan sodangi.

Awa biyu sukayi shirin tahowa saboda hadarin da ya gangamo . Amotar kanin Alh Dan iro suka taho Wanda zai Kai su su yanki tikitin jirgi su wuce Legos.

Suna Kan hanya Ruwan sama ya kece kamar da Bakin kwarya . A daidai gadar ta garin kurmiyal suka hango Ruwa ya jawo wata Mata da Ruwan ke hankoron wucewa da ita Sai iyo take . Alh Dan iro yace
“Subhanallah Musa ku tsaya don Allah mu ceci baiwar Allah can da Ruwa ke kokarin wucewa da ita.


Mai kano da Bai gani ba ya maida kanshi ga matar da ake magana Akan ta sai yaji wani dukan kirji me kama da fasowar zuciya. Ai da sauri ya balle kyauren motar tun kafin musan ya gama Park don idon shi ke hasko mishi matar da Ruwa ke ja kamar mahaifiyar shi Halima.

Da gudu ya karasa gefen gadar Yana kallon matar kayan jikin ta su suka bashi tabbacin ko tantama babu mahaifiyar shi ce ai kuwa Bai jira komai ba yayi sufa cikin uban Ruwan dake hankoro ya Soma iyo har yayi nasarar Cabo Halima da Ruwa ke wurwurawa ya kuwa sabota a kafada ya biyo gefen gadar ta cikin Ruwan har ya fito da ita Yana HAWAYE na tausayin ta Wai itace a wannan garin na kurmiyal. Hawayen shi ya hade da Ruwan da ke sauka fuskar shi shiyasa Basu Gane kukan shi ba inda Alh Dan iro ke fadin .
Sauketa a baradar can ta Almajirai tunda anyi nasarar ceto ta.

“Alhaji mu wuce da ita don dama nemanta nake.

“Kasan ta ne dama? Cewar Alh Dan iro. “Mahaifiya ta CE Alh da ta bace yau sati biyar Kenan da batan ta yau gata a kurmiyal wannan zuwa yayi min Rana sai ya Soma share hawayen shi inda Alh sulaiman Dan sodangi ke fadin.

“Allahu Akbar kabeeran lallai Allah shine Allah. Kai sannu Mai Kano kaji Amma kamar har yanzu Akwai lalurar Nan tare da ita?

“Eh Alh Bata ida warware wa ba . Halima dake binsu da kallo Bata ce ko uhum ba sai Rawar sanyi takeyi jiki na hakora gwaruwa. Dole suka SHIGA mota suka iso filin sauka da tashi na malam Umar Musa yar Adua kafin su hattama Alh sulaiman Dan sodangi ya samo wa Halima Kaya Wanda zata sauya saboda na jikinta sai digar Ruwa suke wata ma aikaciyar wurin ce suka nemi Alfarmar ta sauya Mata suka SHIGA office dinta ta sauya Mata inda aka samo Mata abinci ta kuwa ci kafin jirgin su ya tashi suka wuce garin Legos murnar Mai Kano Bata faduwa cikin wata sa a Kuma Alh Dan iro Yake fada mishi da Akwai wani malami da zai hada Halima dashi kowane irin iska ne zai Rabu da ita in Allah ya yarda. Wannan albishir yayiwa Mai Kano Dadi ba kadan ba da Haka jirgin su ya dangwali kasar garin Legos.

Jirgin da ya sauka nasu Alh Aminu da muhsin Alh Aminu ya Riga muhsin fita don Haka ya Riga shi Isa gidan Dan sodangi inda shima muhsin din ya karaso gidan Amma Kuma daga nesa ya tsaya da son sai Husna ta fito ya karasa. Husna kuwa da take Rike da wayar zulaihat Yar gidan haj Laila gangaro farfajiyar gidan tana leke da fatan ta hango Daddyn ya taho sai ta Soma zarya kadan kadan zata leka har dai yanzu da tayi sa a tana lekawa ta hango Daddyn Yana latsa wayar da zai Kira ta aikuwa da gudu ta fito tana fadawa jikin Alh Aminu shi Kuma ya Rungume ta Yana shafa bayanta Alamar Rarrashi inda Kuma Muhsin dake boye a maboyar shi Yake hango wani Abu Mai Kama da mafarkin sanyi Bai tsinke ba ma sai da yaga Husna na kissing din Daddyn Wanda yaji tamkar wutar nepa ce tajashi.

Bai San abinda suke fada ba yaga dai suna magana Husna na shagwabe mishi inda Kuma yaga Husna ta sheka gidan aguje ta mayar wa da zulaihat wayar ta ta Kuma dawo.

Me napep din da ya dauko Daddyn shi suka SHIGA suka cilla aguje muhsin da idanun shi suka Rikide jajur ya fito Yana fadin me ke Shirin faruwa? Shima Dole bashi da zabi ya nemi komawa inda ya fito da mamakin abinda ke faruwa da Husna.

Zuwan su filin jirgi yayi daidai da saukar su Mai Kano Wanda idon shi ya hango mishi Alh Aminu Kuma har da Husna. Gaban shi ya amsa Amma sai ya ture mamakin hakan.

Motar da tazo daukar su Alh sulaiman ta karaso inda Mai Kano ya saka Halima da baya fatan idob Alh Aminu yakai kanta yace suje gidan shi zai SHIGA kasuwa ya samowa Halima kayan da zatayi amfani dasu.

“Kar ka wahalar da kanka Mai Kano akwai kayan naja na Nan gida babu abinda za ayi dasu sai mahaifiyar ka tayi Amfani dasu sai dai idan wani Abun zaka samo Mata don Haka jeka in ka gama sai ka samemu gidan sodangi.

Da Haka motar tayi gaba ta bar Mai kano Wanda ya take sawun su Alh Aminu ya bisu abaya
Muhsin da ya kula da bin bayan da Mai Kano ke musu sai yaji wata Rahama ta sauko mishi don yafi son su Rasa Husna shi da Daddyn da dai Daddyn ya sameta wani Abu ke mishi yawo aka na yadda Husna ke neman sauya mishi daga sanin da yayi Mata na kin Daddyn zuwa yanzu da take yarda Yake kissn din ta Wanda Yake tunani lallai ba Haka Nan bane daga Ruwa Sai kuka akwai dalili.

Suna Shirin Hawa step up na benen da zai sada su da office din da zasu yanki tikitin Husna taji an finciko ta ta baya.

Suka juyo su duka a tare suna kallon Mai kano Wanda ya Fara faskawa Husna Mari Yana Jaye da hannunta inda Alh Aminu yayi mutuwar tsaye don yanzu ne Yake yarda Mai Kano ya hada jinsi da aljanu. Kafin ya farga sai ganin su yayi napep ta fice dasu abinda Kuma ya bawa muhsin dariya Yana Kuma Jin dadin da Ubangiji ya kawo Mai Kano.

Isar su gidan sodangi ne yaba shi damar jibgar ta inda haj Laila ke ta nemanta sai da zulaihat ta fada Mata ai ta fita sai Taji Bata kyauta wa Mai Kano ba da yace ko kofar waje Kar abarta taje.

Sai da kyar haj Laila ta kwace ta Yana Kuma bashi hakuri da cewa laifin ta ne Amma ba za a sake ba. Shi kanshi ya Fara tunanin ba banza Alh Aminu ya bar Husnar ba Amma zai iskeshi yaji idan wahayi akayi mishi da su.

Alhaji Aminu ya dawo da alwashin lallai sai ya San yadda yayi da Mai Kano tunda Kuma yayi sa ar da Husna ta kamu ai ya gama Dacewa har gida ma sai ta iske shi.

Haj Laila kuwa ko Rakiyar fata kasuwa Bata Kuma Bari Husna ta fita ba inda Kuma aka sada Halima da malamin Wanda yace zata Fara Shan Ruwan Rubutu Wanda za a sauke Mata Alkur ani Kuma a Rubuce Mata shi ta shanye kafin ayi Mata Rukiyya Wanda in Sha Allah ko wane irin hauka ne zai barta da yardar Ubangiji.

Tuni kuwa Mai Kano yaji yayi na am har ya Soma biyan abin sadakar Kuma cikin nasara Halima har ta fara magana duk da wata maganar soki burutsu ce Amma Kuma wata ta hankali ce.

<< Hawaye 66Hawaye 67 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×