Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Hoton Mijina by Nana Aicha Hamissou

Na sha jin labari aljanu sukan yi siffar mutum har su zo mashi cikin bacci, amma ban taɓa ganin wanda ya taɓa yin mafarkin ba sai dai labari a bakin wasu mutane. Sai yau ya faru da ni, wanda ya haifar mini da mugun tsoro mai karyar zuciya da gangar jiki. Zan iya cewa tunda nake a duniyata ban taɓa yin mafarki da ya kaɗa hantar cikina kamar na yau ba. Babban abin tashin hankali yadda aljanu suka yi suffar ƙawata a mafarki har suke tsorata ni a mafi munin abin da na tsana a rayuwata. Watakila rashin yin addu’a yayin bacci ne ya haifar min da mafarkin nan sakamakon damuwar da ta addabe ni kwanan nan, har take hana ni gudanar da ibadata kamar baya. Tun ba a je ko’ina ba har na fara ganin sakamakon rashin yin addu’a yayin bacci.

“Allah na tuba, Ka yafe min.”

Na faɗa ina tashi zaune. 

Muryar maigidana Kabir ta ratsa ni yana faɗin,

“Amin ya Rabb uwar gidana.” 

Ban samu damar magana ba sakamakon tozali da aljanar da na sake yi a zahiri saɓanin ɗazu cikin bacci. Wani irin bugu zuciyata ta yi kamar za ta faso kirjina ta fito waje. Da sauri na rintse idanuwana haɗe da ɓoyewa bayan Kabir, don ba na fatan sake tozali da ita kamar yadda na ji ana faɗin duk wanda ya ga aljana sai ya mutu ko kuma ya haukace. Cikin wani irin yanayi na furta, 

“Don Allah Kabir ka ce ta rabu da ni, kuma ta daina zo min a siffar baiwar Allahr nan domin siffar ƙawata ce.” 

Na ƙarashe ina fashewa da marayan kuka mai tsuma zuciya. Muryar Kabir ta ratsa ni yana faɗin,

“Ki nutsu Rashida! Wallahi hankalina ya yi matuƙar tashi sakamakon halin da kika tsinci kanki.”

Ban ankara ba na buɗe idanuwana sakamakon jin abin da ya faɗa, ko shi ma ya san mafarkin da na yi ne har yake faɗin halin da na tsinci kaina?

“Ban gane ba Abban Husna? Wane hali kake magana? Ko kai ma ka yi irin mafarkin da na yi ne?” 

Na sake faɗa har lokacin ina ɓoye bayansa tsabar tsoron da ya cika min zuciya.

“Mafarki!” 

Ya furta yana juyo da fuskarsa gare ni mai ɗauke da mamaki, sannan ya ci gaba da faɗin,

“Ban san me ya faru ba, daga tozali da amaryarki Aisha kika suma, don Allah ki kwantar da hankalinki hubbyta, kin fi kowa sanin ban son ganin ki cikin damuwa.”  

Wata irin sarawa kaina ya yi jin abin da ya faɗa, hawaye masu zafi suka fara tsere saman fuskata. A lokacin na fahimci babu wani mafarki da na yi, tsantsar gaskiya ce duk abin da nake tunanin mafarki ne. Zuciyata sai zafi take yi min, hankalina ya yi mumunnar tashi sai na fashe da kuka ina faɗin,

“Wayyo ni Rashida! Kabir ka kashe ni! Ka zalunce ni! Ka rasa wacce za ka auro sai wannan? Me ya sa ba ka auro duka matan duniyar nan ba madadin wannan? Ka san ita ɗin wace ce? Me ya sa na ce!” 

Na karashe maganar cikin karaji ina mikewa tsaye haɗe da kallon Aisha ido cikin ido, ƙwaƙwalwata ta shiga tariyo mini wani al’amari a can baya.

******

“Na san mu da ganin ki sai mun zo suna in da rai.” 

Aisha ta faɗi haka ana gobe za a kai ni gidan mijina kasancewar muna Arlit yayin da shi kuma yake Niamey.

Na yi murmushi ina faɗin,

“Ko kuma sai na dawo aurenki ba?”

Da sauri Aisha ta furta,

“Ba yanzu ba! Ni da aure sai na haɗa mastas, kin ga kuma yanzu ne zan fara jami’a, da sauran lokaci.” 

“Wai har yanzu wannan burin yana nan?” 

Na faɗa ina kama haɓa,

“Me za a fasa? Mutuwa ko hisabi!” 

In ji Aisha tana harara ta. 

“Ko ɗaya kam! Allah Ya cika maki burinki. Ya kuma ba ki miji na gari kamar ustazuna.” 

“Raba ni da ustazunki da ya hana mu ganin shi! Yanzu a ce mijin ƙawata ban taɓa tozali da shi ba? Zan iya mashi uziri tunda ba gari guda muke ba amma ya dace ko a hoto ne mu gan shi, amma tsabar ustazanci ya hana mana hotonshi, har kike min fatan samun kamar shi.” 

Aisha ta faɗa kamar za ta rufe ni da duka kasancewar tunda nake ban taɓa nuna wa ƙawayena HOTON MIJINA ba, dalilin da ya sa na yi musu karyar shi ustazu ne kuma bai son hoto. Sai dai ba haka ne gaskiyar lamarin ba, zafin kishi ya rufe min ido na ƙi nuna musu hotonshi, ga shi ba gari guda muke ba balle in ya zo zance su gan shi. Ni ɗin ma zuwana hutu Niamey ne muka haɗu da shi har muka daidaita kanmu. Iyaye suka shiga lamarin aka ɗaura mana aure.

“Tunanin me kike yi ne haka?” 

Aisha ta katse min zancen zucin da nake yi. 

“Ina tunanin hanyar da zan bi ki ga HOTON MIJINA ko saboda gaba.” 

Na furta iya fatar bakina amma ko kaɗan maganar ba ta kai zuci ba. 

“Kada ki damu. In da rai da rabo watarana zan gan shi.” 

A haka muka ɗan taɓa hira daga bisani muka yi sallama da ita, washegari muka ɗaga daga Arlit sai babban birnin Niamey cike da kewar juna.

Ina da wata uku gidan mijina Aisha take faɗa min ta samu gurbin karatu a ƙasar Marako, na taya ta murna sosai duk da na so ta yi aurenta, ganin ta fi sha’awar karatun sai fatan alheri na yi mata. Rabona da labarin Aisha tun da ta ɗaga daga ƙasar Nijar zuwa Maroko. Na yi neman lambarta ta Maroko sosai amma ban samu ba, iyayenta sun yi ritaya sun koma ƙasarsu ta haihuwa Maraɗi ballatana gidanmu su amsa min. Sai yau da na yi tozali da ita a matsayin matar mijina.

Ina kawowa daidai nan da tunanina, na sake sakin kuka mai tsuma zuciya, nadama ta lulluɓe ni kamar na nutse cikin ƙasa tsabar kunyar ƙaryar da na yi wa Aisha a can baya.

“Ina ma a ce na yarda da ganin hotonki!”

Na furta dalilin tunawa da na yi yadda Kabir ya matsa min akan ganin hoton amaryarshi, amma zafin kishin ya hana ni kallon ta saboda ba na muradin tozali da duk wacce za ta kawo min farmaki a rayuwar aurena, musamman yadda nake ƙaunar mijina da kishin shi, sannan na ci alwashin sai na saɓa wa duk wacce ta aure shi don mijina nawa ne ni kaɗai. Shi ma da ya ga ba na son ganin hotonta, sai ya tabbatar min ita ma ba zai nuna mata nawa ba. 

Sake kallon ta na yi ina tuna kalaman Kabir ɗazu gare ni,

“Hubby ga amaryarki nan ta zo gai da ke.” 

“Amaryarka dai Malam! Me zan mata ne? Ka faɗa mata ba ni da lokaci.”

Na faɗa ina gyara kwanciyata don ban buƙatar ganin ta, ko jiya da aka kawo ta ban ga fuskarta ba, ba ta ɗaga fuskar ba ni ma ban muradin kallon ta, har suka yi maganganinsu suka gama ban tanka musu ba. Bayan an watse na saka wa ɗakina sakata, ina jin Kabir yana ta bugun kofar, daga inda nake ban tashi ba ballatana na buɗe mashi saboda kukan da nake sha, sai da ya gaji don kansa sannan na daina jin bugun kofar. Yanzu ma akasi aka samu uziri ya sa na buɗe ta kuma na mance ban rufe ta ba, har ya samu damar shigowa ɗakina yake faɗa min na fito falo wajen amaryashi.

Sai da ya yi da gaske yana roko na da kalaman masu sanyi sannan na fito ina cin magani. 

“Ke ce gidan nan!” 

Na furta da ƙarfi ina isa wurin Aisha a tunanina ta samu labarin inda nake ne ta zo gare ni, sai dai maganar da ta ratsa masarrafar sautina ce ta hana ni saurin rungumar da na so yi mata.

“Ga Ƙanwarki, abokiyar zamanki, amaryarki Aisha.” 

Kamar ruwan dalma a kunnena haka na ji amsa-amon muryar Kabir tana ratsa ni. Iya nan kaɗai nake iya tunawa sai farkawa na yi cikin tsoro da tunani mafarki nake yi.

Lumshe idanuwana na yi ina faɗin,

“Tabbas ba a yi wa Allah dubara! Na hana ƙawayena ganin HOTON MIJINA kada ya birge wata, na so hana shi aure amma yana nuna min ban isa ba, sai ga shi Allah Ya nuna min iyakata duk yadda nake da Aisha na hana ta HOTON MIJINA sai ga shi ita ce amaryar mijina. Allah na tuba Ka yafe min, Ka rage min zafin kishin nan da nake fama da shi tun da kuruciya, Ka ba wa mijinmu ikon yin adalci a tsakaninmu.” 

Na faɗa ina sake fashewa da kuka haɗe da rungume Aisha da take rakuɓe tamkar marainiya. Ita ma kukan ta fashe da shi tana faɗin,

“Ba zan iya rayuwa da mijinki ba kawata. Kabir ya zama dole ka sawwake min don ban zan iya cin amanar ƙa…” 

Da sauri na rufe mata baki ina faɗin,

“Ba laifinki ba ne Aisha, komai ya faru laifina ne, kuma rubutaccen al’amari ne. Ki gafarce ni karyar da na yi maki a baya. “

“Na yafe maki Rashida. Allah Ya yafe mana bakiɗaya.”

“Kun saka ni a duhu ban fahimce ku ba.” 

Cewar Kabir.

Cikin kuka na zayyane mashi duka abubuwan da suka faru. 

Nasiha mai ratsa jiki ya yi mana kafin ya ɗora da faɗin,

“In sha Allah zan raba muku gida gudun samun matsala.” 

A tare muka furta,

“Mun fi son zama tare.” 

Murmushi Kabir ya saki sannan ya ce,

“Allah Ya yi maku albarka matana.” 

Muka amsawa da amin muna sakar wa juna murmushi. Tun daga ranar duk wasu makaman yaƙina na zubar da su, har mamakin kaina nake yi da tambayar kaina anya kuwa ni ce Rashida? Zaman lafiya ya samu matsuguni a tsakaninmu tamkar ba kishiyoyi ba. 

Ƙarshe

©️Real Nana Aisha

2 thoughts on “Hoton Mijina”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×