Skip to content
Part 1 of 3 in the Series Ibtissam by Aysha Galadima

Littafi Na Daya

The beginning

THE UNITED STATES

NEW YORK CITY

COLUMBIA UNIVERSITY

Cikin babbar harabar hall dake cikin Columbia university,mutanene zazzaune kowa kaga fuskarsa zaka ga farinciki da annashuwa a cikinta, daga saman stage suma wasu mutanene sanye da suit a jikinsu black colour , daga sama kuma gown ce a jikin su na graduation . Cikin tsantsan turanci da ke fito dako Wana kalma ake kiran sunayen daliban , bayan kowa ya karbi certificate din shi aka fara kiran wasu daga cikin daliban Domin basu award dinsu.

Zaune yake cikin shigar suit dinshi fuskarsa sanye da face mask ya dukar da kai sai gashinkansa daya sakko masa har wajan idanuwansa, time to time yana duba diamond watched din dake hannunsa kafun ya mayar kan dan kareriyar wayarsa kirar Samsung, “ADIL BIN MOHAMMED ALTAUFEEQ”, gabaki d’aya kowa jira yake yaga me sunan ya tashi amma kwata kwata Har yanxu babu Wanda ya mike , wata babbar macece ta kara kiran sunan tana duban daliban “ the most talented person of the session,”ADIL bin Mohammed Al taufeeq,are you around please “, wani na gefensa ne ya dan tabosa “ADIL ,MAAH is calling you”, banza yayi wa na gefen nasa kamar be san da wani halitta a wajan ba , gabaki d’aya idanuwansa nakan wayarsa ,Akaro na uku aka kara kira sunan adil Mohammed Al-taufeeq, yanxu ba mashi da alama ko niyar tashi, “YAYA PRINCE,“ sunan da ya bayyana akan screen din wayarsa , “finally” ya furta cikin wani daddadan muryarsa kafin ya mike a hankali, gabaki d’aya hall din tafi aka fara bakajin komai sai raf raf raf din tafi dake tashi, da ihu aka kiran “ADEEL, ADEEL” Wanda ya mike din cikin wani irin taku ya karasa inda ake kiransa, wani medium box ne brown colour da akayi rapping aka mika masa, kafun matar ta nuna masa wajan mic, har yanzu kansa a sunkuye yake bai kalli kowa dake cikin hall din ba, gabaki d’aya hall din shiru ya dauka kowa jira yake yaji speech dinsa,shi kuma ganin yanda kowa yayi shiru ne yasashi dauke kansa shima batare da yace komai ba kusan mintuna uku,”Little Boo”,kalmar ta sauka a kunnansa.

Da Sauri ya dago eyes dinsa da har yanxu gashi ya karesu,cikin sauri yake kallan mutanan wajan ko zai gansa, daga nesa dashi yaga an daga fingers guda biyu, murmushi ya saki duk da facemask din dake fuskarsa, a nutse ya fara bada speech din da ya dau hankulan mutanan wajan, gabaki d’aya cameras na kansa,yana kammala speech dinsa wajan ya kara daukar tafii da kalmar “ADEEL da ake ta faman kira, yana koma wa aka kara kiran sunansa as the most disciplined , dan guntun tsaki ya saki kamun ya koma, yana karba bece komai ba yayi wucewarsa, idanuwansa akan wajan da aka dago masa fingers dazu, so yake kawai yaga an kammala gabaki d’aya a ‘kage yake da ya bar wajan, akaro na uku aka kara kiransa , jiyay kamar ya make mekiran nasa , gabaki daya takaici duk ya kamasa,a karo na uku aka sake bashi wani gift din, Madam flora na kokarin bashi waje don yayi wani speech din ya bar wajan, a haka aka cigaba da kiran ragowar mutane 4 da zaa bawa gift suma, saida y karbi wasu gift din shima duk acikin student din ya fi kowa karbar gift din kowa ADIL TAUFEEQ zakaji yana kira kowa burinshi yayi hoto dashi, yana gani an gama ya mike da niyar barin wajan, duk yanda friends dinsa ke rokansa suyi hoto ba Wanda ya kula a cikinsu, cikin mutanan ya shiga kai tsaye amma be ga Wanda yake nema ba, kamar yayi kuka ya fita daga hall din, a tsaye ya hango wani black American sanye da black suits, idanuwansa rufe da ba’kin google, gabaki d’aya babu fara a cikin fuskarsa, da sauri ya karasa inda yake gift din hannunsa ya mika masa,cikin girmamawa ya amsa kafin ya sara musu,”captain” ya kira sunan mutumin, nuni mutumin yayi masa da wasu jerarrun motoci baka ke wuluk da suke zagane da wasu mutane masu kakin sojoji,batare da ya bari ya kuma cewa komai ba, cikin sauri sauri ya nufi wajan motocin, suna ganin sa suka sara masa,motocin ya fara bi da kallo yana jiran yaga ta ina zasu fito,daga bayansa yaji an furta “Little”, cikin wani daddadan murya, da mugun sauri ya juya tare da ware idanuwansa, beyi wata wata ba kawai ya Dane mutumin” yaya prince dina” shima Wanda ya ‘Dane rungumeshi yayi a jikinsa a hankali ya furta “ zaka karyani fa “, dariya ya saki yana sauka daga jikin mutumin, wani hadaddan guy ne fari tas dashi , kwata kwata rabin fuskarsa a kulle take sabida p-cap din data rufe masa rabin fuskarsa sai dan medium din bakinsa da ya fito pink dashi, kallan gefe da gefen mutumin yayi kafun ya furta “ basu dawo bako,” ya furta cikin sanyin murya kamar me shirin yin kuka , “why the pity face, so kake BIG BOSS da YAYA BOBO suyi farfesu nane, they’re at home fa”, kugu little ya rike kafun ya furta “ ka tabbata yaya prince”, girgiza masa kai yayi kafin ya furta “toh nayi maka karya , if you like ka yi ta zama, ni am going,“ yana kammala maganar sa wani black American ya bude masa mota ya shiga, da sauri ADIL shima ya zaga daya bangaran nan ma wani American guy ne ya bude masa kofa.

Da mugun gudu motocin suka fita daga cikin Columbia university suka hau kan babban titin New York, mintuna 15 ne suka kawosu hadaddan street din FIFTH AVENUE dake cikin Garin new york, gabaki d’aya layin shiru kake ji kamar babu wani halitta da ke rayuwa a wajan sai sojojin da ke wucewa time time, Daidai wani babban area da mafi yawanci sojojin suka fi yawa suka nufa, gabaki d’aya sojojin mikewa sukai tare da sara musu, da mugun gudu wasu soldier su hudu suka fara bin bayan motar har suka karaso dai dai wani babban gate me shegen girma da tsaho, ba bata lokaci aka wangale musu gate din motocin su suka shiga ciki, kusan tafiyar mintuna biyu suka kara zuwa wani gate din da ya fi na farkon tsaro , awannan karan sai da aka caje motocin ta waje  saida aka tabbatar da lafiyarsu kafun a wangale musu gate dinshima,wata ni’imtacciyar iskace ta fara ratsasu sabida flowers din da suka fara cin karo dasu, a wannan karan tafiyan minti biyar sukayi kan dogon titin dake wajan, wata kafuwar gate ne da kanta take budewa, ta wani slide din waje motocin suka wuce bayan gate din ya aunasu.

Daga cikin motar ADIL ne ya dan kalli captain dake driving,” captain I give you 3 minutes ka karasar damu, if not zan fada wa big boss ya shigar da kai dakin duhu”, kafun prince dake gefensa yayi magana captain yaja motar da mugun speed “ azuciyarsa kuma yana auna irin horon da zai fuskanta idan ya karasa , sassaucin sama BOBO yayi mishi hukunci ba BIG BOSS ba, suma ragowar motocin suna ganin haka ko wannansu ya kara speed din motar, duk da sunsan dole su karbi hukunci wajan BOBO.ko gama parking ba ai ba Adil ya fito daga cikin motar ya arta a guje, masu tsaran kowa sunkuyar dakansa yayi cikin girmamawa, kofar babban masion din aka bushe masa , nan ma da mugun gudu ya shiga, wata kofar ya nufa me shegen kyau, yana shiga babban parlor ne ya bayyana me 4 set of designers , Aljannar duniya kenan gabaki d’aya falon sai ka dauka a wata nahiyar kake ba a duniya ba, falo ne da ya amsa sunan sa falo da ko me kudi be isa mallakar saba, naira tayi kuka ga wasu irin Logan modern stainless steel tiered crystal chandelier da ya kara haska falon, ko ina ka waiga haske ne tar, ga sanyin Ac dake busa ko ina na palour.

Cikin daga murya ya fara kiran “ UNCLE IRON MAN, YAYA BIG BOSS ,YAYA BOBO,Little is back”, yana maganar yana fincike mask din dake fuskarsa, fatabarakallahu ahsanin khalikin, kyakkyawa ne shi sosai da ya amsa sunan  kyau, fari ne shi sosai duk da ba wani babba bane amma kyawunsa ya wuce misali, har yanxu bana iya ganin fuskarsa sabida gashin kansa da ya rufe masa rabin fuska sai kadan daga hancinsa da zaka gane dogone daya fito, sai dan karamin ba’kin shi pink kalo daya fito shima, Prince ne yashigo falon bakinshi dauke da sallama da sauri Little ya kalleshi duk da ba ganin idanuwansa ake sosai ba zaka gane hararar Prince yake, P_cap dinsa Prince ya saki, kyakkyawar sumar kansa itama ta sakko masa har wajan idanuwansa,gyara gashin nasa yayi kyakkyawar fuskarsa ta fito waje , ware idanuwansa yayi a kan little take eyes dinsa dasuka kasance ash colour suka fito waje sabida ware idanuwansa da yayi, shima kyakkyawa ne na ajin karshe , fadar irin kyawunsa ma bata baki ne, fuskarsa bame fadi bace sosai sannan ba doguwa bace, dai dai jikinsa ga dogon hancinsa daya kara fito da kyawun fuskarsa, dan madaidaici bakinsa ya tabe yana kara bin little da kallo ,cikin wani yare ya furta “Ni kake harara”kamar mace little ya rike kugu tare da tura masa baki, a guje prince ya bi bayan little, shima little yana ganin hakan yasa gudu suka fara zagaye falon,”stop there “ Prince ya fada yana jefowa little pillow , shima little pillow ya dauka tare da jefowa prince “ I won’t , ba kaine kace mun my loves sun dawo ba”, wani pillow Prince ya dauka ya jefawa little a fuska, ganin hakan yasa shima little daukan pillow, gabaki d’aya sun bata falon duk pillows din kujerun sai da suka sakko da shi kasa,wani pillow Prince ya dauka zai jefa wa little yaji saukar muryar data sashi faduwa “ If you dare “, da Sauri ya jefar da abunda ke hannunsu, Prince ma mikewa yayi shida little suka hade waje daya , kana kallansu kasan basu da gaskiya , Cikin 3 quarter din wandan sojoji da bakar armless ya karaso cikin falon, kakkarfa surar jikinsa da kallo daya mutum zai yi masa yasan yana daga karfe, kyakkyawa ne sosai da ya amsa sunan kyau, har na kasa banbance wanane yafi kyau a tsakaninsu duk da fuskar little ma rabi ce a bude amma kana ganinsu zaka ga kamannin da suke da juna har ya kwayar idanuwansa  light gray ya zuba musu  , “YAYA BOBO” little ya fada da niyar nufar sa, wani gigitaccen kallo ya jefa masa kuskarsa kwata kwata ba fara’a “ if you dare ka kara one step kaga yanda zan karya kasusuwanku “, narai narai little yayi da ido, shikansa Prince tsoran magana yake kar lefin ya dawo kansa baki d’aya ,kallansu mutumin yayi kafun ya nuna musu 5 fingers dinshi “ just 5 minutes na baku , ku tabbatar falon nan ya dawo yanda yake kafun ku karbi punishment dinku”,  be karasa maganar ta saba suka fara gyara pillows din , jiya d’auke kansa yayi daga kansu kafun ya dakko wata roughly mobile phone army dake jikin 3quarter dinsa , number 3 kawai ya danna ko mintuna biyu ba aiba , su captain Suka shiga cikin babban parlourn, gabaki d’aya sara masa sukai ko kallan inda suke beyi ba, cikin kwarewa captain ya kara sarawa tun kafin BOBO yayi magana,

Cikin yaran turanci Captain ya furta “ reporting !!! Tukin ganganci a harabar gida hukuncin bulala dari tare da zagayen gida sau dari shine hukuncin mu”, ga baki d’aya sauran soldiers din suka hada baki wajan furta “salute”, hada ido Prince da adil sukai, cikin zuciyar sa prince yake furta “shikenan little ka kashe ni da raina, yanxu idan me kirar samu dawan nan ya dawo kan mu ai mummutu, “su captain suna fita Prince be karasa maganar zucin saba Bobo ya maida kallansa akansu, gabaki d’aya sunkuyar da kai kasa sukai, kan one sitter ya zauna kafun yayi crossing legs dinsa yana duba a gogo “ zagaye dari!!! Starts “ kamar zasuyi kuka suka fara zagaye falon gashi ba damar su bashi hakuri ya kara nunka musu wani wahalar, a zagaye na 20 suka fara layi kamar zasu fadi, a hankali suka fara tafiya yanxu, mikewa bobo yayi daga kan kujeran tuni suka manta da gajiyar tasu suka ci gaba da zagaye falon, da sunyi kokarin tsayawa zasu ga bobo na binsu da kallo, a 80 adil ya fadi kasa tare da fashewa da kuka “ yaya bobo please kayi hakuri, kamanta little dinka ne ni kuma yau graduation dina fa, “ shima Prince zubewa yayi a kasa cikin pleading ya furta “ yaya bobo we’re sorry “, babu Wanda ya kula acikinsu, “ zagaye hamshin!!! Starts”, sakin baki Prince yayi “ wani lokaci har tunanin tsakanin big boss da yaya bobo wanane yafi wani iya mugunta dan hukuncin big boss ya fi na kowa tsauri, ba karamin aikin sa bane yasa a jefaka caged din zakinsa  kuma babu Wanda ya isa ya futar da kai sai ta Allah. Zasu mike wani mutumi ya shiga black American da shi, jikinsa sanye da kananan kaya shima, little na ganinsa ya kara fashewa da kuka “ Uncle iron man , please ka bawa yaya bobo hakuri kafata ciwo take mun”,kallan bobo mutumin yayi yaga ya dauke kansa, murmushi ya saki kafun ya karasa inda little yake “ kunyi lefi kenan, ku bashi hakuri idan ya ki hakura ku kira masa big boss sai ayi ya’ki kowa ma ya huta”, yanda suka zaro idanuwane yaso bashi shi dariya , zasu kara magana bobo ya nuna musu hanya dan hayaniyar su har ta cika masa kunne “ leave this place now”, ai be karasa ba ko wannansu ya arta a guje, yanxu kam kasa rike dariyarsa mutumin yayi saida ya dara kafun ya kalli bobo “ why are you punishing yourself, kai da big boss kunfi kowa jin zafin punishment din da kuke sasu amma hakan baya hana gobe insunyi lefi ku hukuntasu, ynxu da dan gwarzane sukai sai kunfi kowa jin ciwo, in wani kuma yayi gigin koda mintsuninsune tsaf zaku harbe mutum,please ku sassauta wannan zuciyar taku”.shafa keyarsa bobo yayi kafun ya furta “ok uncle”, girgiza Kai uncle din yayi kafun ya nufi wata kofa , shima bobo wajan elevator ya nufa da zea kaishi sama.

A bangaren Prince da little kuwa suna shiga dakin su kowa ya haye kan gadonsa yana maida ajiyar zuciya Dan ba karamun horuwa sukai ba, babu Wanda ya kula junan su ,musamman little da yake fushi, ko wannansu wanka yayi cikin kayan shan iska, duk yanda Prince yayi da little su sakko kasa yaki, ya ma ki yi masa magana kwata kwata sai ma Hayewa kan bed dinsa da yayi yana lullube kansa. Kusan tsawan 30 minutes yaji an bude door din, a tunaninsa Prince ne yace “ yaya Prince just leave me alone”, shirun da yaji ne yasashi kara furta “ please yaya Prince ka tafi, yaya bobo baya sona yanxu”yaye blanket din da akai ne yasashi waro ido ganin bobo tsaye hannunsa dauke da babban tray, akaran farko da kyakkyawar fuskar little ta fito, a shekaru bazai wuce shekara 21 ba dukda kyansa be gama fitowa ba kamar yan uwansa amma shima kyakkyawa ne na karshen karshe, dauke blue eyes dinsa yayi daga kan bobo zai koma ya kwanta “ stay still” cewar bobo, sunkuyar da kai little yayi kamar zeyi kuka , ajje tray din bobo yayi kan wani table me zaman mutum 3,kafun ya karasa inda little yake , a gefensa ya zauna shima kafun ya kama hannun little “ yaya bobo yayi lefi, am sorry kar a fada wa big boss ya harbeni “, dariya ce ta kwace wa little besan lokacin da ya rungume bobo ba, shima bobo rungumesa yayi kafun ya mikar dashi tsaye, dakansa ya dunga feeding ADEEL abincin da ya kawo masa shima ADEEL din na bashi abaki, saida suka kammala cin abincinsu kafin little ya kalli bobo” yaya bobo , big boss ya dena sona har yanxu ya ki dawowa fa”, bobo be ce masa komai ba sai wata karamar phone da ya dauko wasu number guda Hutu ya danna take a wajan aka dauka, little dake binsa da kallo, tsawan mintuna biyar Ba’ace komai ba kuma babu alamun za ayi magana ,”yaya” shiru yaji ba ayi magana ba “ Assalamu Alaikum “ ya kara fada kusan mintuna biyu kafun wata ratsatstsiyar murya ta daki dodon kunnansu “

Wa’alaykumussalm “, daga nan ba a kuma cewa komai ba “ Yaya” little ya fada kamar me rada “ little I will called you back!” “ kafun yayi kokarin yin magana aka kashe kiran gabaki d’aya ,” karbar wayar bobo yayi “ kaga yayan naka yana meeting and zai kiraka , so don’t worry, and ya bani gift dinta , and if you guys need anything ku duba dakina ko na big boss, but ba fa kyauta na baka  ba , kana fara aiki zaka biyani kudi na “ rungumeshi little yayi cikin yaran larabci ya furta “ Ina  sanka yaya bobo na ,” love you too “ yana gama maganar sa ya bar dakin.

Shima tittle wani choco ya dakko cikin sauri ya sakko downstairs, “yaya Prince “ yake kwallawa kira ,”Menene kake faman kirana ka gama fushi”, amaimakon ya amsa masa sai kashe masa ido daya da yayi “ yaya Prince wajan simba zaka rakani , yau kwata kwata banganshiba “,kallan tara saura kwata Prince ya bishi dashi “ dan iska ne Ance maka da zanje wajan wancan zagin, Kai da ka ga zaka iya ai  sai kai tayi “, shima kallansa Adil yayi “ shikenan Allah sai na fada wa yaya bobo , shima big boss sai na fada masa “ da Sauri Prince ya riko hannunsa “ Haba auta, wasa fa nake maka zo muje wajan simba din”, fitowa sukai cikin babban mansion kafun su nufi wata kofa, duk inda suka wuce sojoji suna sara musu, cikin wani babban cage suka shiga , Prince da ya shiga karshe sai be kulle kofar cage din ba, “Simba!!! Simba !!!” AdIL yake kira,wani gurnanin zaki ne ya fara tashi me tsoratarwa, inda gurnanin yake fitowa adil ya nufa ba ko tsoro tattare dashi,”Simba “ ya kara kiran sunansa , wani katon zaki ne ya fito , yanda naga girmanshi nikaina sai da na razana, bakinsa ya bude kafun yayi wani kuka amaimaikon su gudu sai nufar kusan tosa da sukai kai, kansa Adil ya shafa “Simba yau duk ban gankaba “ Abun mamakin shima Zakin da aka kira da simba, gashin kansa ya karkada masa kafun ya daga hannayensa ya dora ajikin Adil, wani irin farinciki ne ya kama adil kamar Wanda ya samu mage haka yake wa zakin wasa, Prince na gefe sai faman vidoe yake musu, ganin lokacin sallahr magariba ya kusa ne yace wa Adil suzo su tafi kar yaya bobo ya ne mesu, ba musu kuwa suka bar cage din.

ABUJA

ADEMOLA ADETOKUMBO STREET

Cikin wani babban gida dake cikin ademola , maza da mata ne ke faman shige da fice gabaki d’aya wajan fitula ya haska , ko ina ka duba zaka ga mace da namiji rabe da junansu, daga gefen gidan da akai wa lakabi da UWAR BARIKI, wasu kyawawan yan matane guda 4 da a kalla shekaru baza su wuce shekara 15 ba, ko wannan su ka kalli fuskarta zaka ga tashin hankali tattare da ita , d’aya daga cikin yan matan da tafi kowa shiga tashin hankaline ta rushe da wani saban kuka ,” shikenan na shiga uku, yanxu me zancewa UWAR BARIKI, na tabbata in bankai mata kudin yau ba kashe ni zatayi “ kallanta d’aya daga cikin yan matan da ita ma zaka ga tashin hankali tsantsa a fuskarta tayi kafun ta furta “ ki dena kuka ARWA nasan ABLA in tazo zata neman mana mafita “, girgiza Mata kai wacce aka kira da arwa tayi “ kinsan yanda uwar BARIKI ta tsani Abla fiya da kowa musamman yanda taki yarda tayi kudi da ita shiyasa tafi kowa shan wahala a cikin mu, yanxu idan Abla taji bansan me ze faru ba, kawai ina tunanin zan bawa wani kaina ne kamar yanda uwar BARIKI take bukata, ko hakan zaisa mu fita daga kangin rayuwar nan” saukar mari taji a fuskarta da yasa ta hadiye  sauran maganarta, gabaki d’ayansu maida hankalinsu kan wanda tayi marin sukai, Wata kyakkyawar matashiyar budurwace tsaye a gabansu, gabaki d’aya wahala ta bayyana a jikinta ga wasu matattun kaya a jikinta daya fi na sauran munana sabida yanda suka mutu , gabaki d’aya  hada baki yan matan sukai wajan furta “ABLA”

Ibtissam 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.