Yau Najwa na zaune tana danna waya Ikram tayi sallama da yaranta wanda ba yau Najwa ta fara ganinsu ba, dan Abba yana kawo su gidan itace dai basu taba haɗuwa ba , bata taka kuma taje gidan Ikram ba tun dawowarta .
Amsawa tayi tana tsurawa Ikram ido sosai tayimata kayau ta dan kau da kanta .
Ikram ta shigo tana murmushi tace "Kace yau nayi sa'a na samu ƴar gidan Daddy saukar yaushe? Momint tace kintsaya karbar result sai ki taho baki daya " .
Najiwa tayi ɗan yi murmushi , haka kawai take jin nauyin Ikram din .
Momi ce ta fito. . .