San da ya sauko kasa ga mamakinsa har ta bude zata fara zuba masa, kusan suman zaune yayi bai taɓa tunanin zata sako da wuri haka ba ko ma yace gaba daya .
Zuba mata ido yayi ta gama ta bashi ta kawo ruwa ta ajiye masa sannan ta diba ita ma ta tashi zata shiga daki yace" kifin fa tace a'a kaci kawai "
Yayi murmushi ya mike ya zuba mata a gefe yace" ki zauna mana kici a nan" tace" uhumm tohm ta matsa can gefe ta fara chi ,haka har tsawan lokachi sannan suka gama ta wanke. . .