Ranar nan ba Haidar ba har hajiya Gwaggo sai da ta turo a ƙara mata ƙosai wai ya yi mata kaɗan su kai dariya dan sun san taji dadinsa ne.
Haka aka sukai sallah suka dawo kamar yadda suka saba tunda watan azumi ya kama suka ɗan yi hira suka kwanta lokacin sahur sukayi san nan suka zarce da ibada da rokon Allah kamar yadda suka sabarwa kansu.
Washegari ta ce masa Yaya dan ALLAH in ka fita ka kiramin Musa yau nakeson mu gama jakun kunan nan zuwa jibi na kammala.
Dan wata jiya tazo wai dan Allah. . .