Skip to content
Part 1 of 3 in the Series Indo A Birni by Rasheedat Usman

Yara biyu na hango suna cin uban gudu, yayin da wacce ke gaba take gudun ceton rai, sosai take gudun saboda kar wacce ke bin bayan nata ta kamo ta. Wani gida naga yarinyar ta fad’a, binta cikin gidan itama yarinyar dake biye da itan tayi, da gudu ta fad’a wani madaidaicin d’aki, tana haki.

d’akin da yarinyar ta shiga, itama wacce ta biyo ta take k’ok’arin shiga.

Cikin sauri wata matashiyar mata ta tare ta tare da cewa.

“Lafiya Indo kuke wannan uban gudu, sannan kuma zaki bita har d’aki, aiko mutuwa ma tana kunyar idon uwar d’a, meye Zainabun ta miki? Kika biyo ta har gidan ubanta ba ko kunya.”

Huci wacce aka kira da Indo take cikin masifa da bala’i take cewa.

“Sai mutuwa taji kunyar Idon ki, ni kuma Indo banji taki ba, wallahi yau Babu mai hanani cin Uban Zainabu cikin gidan nan, gobe koda kud’i aka had’a ki bazaki k’ara nema na da tsokana ba, cemin fah ta yi Indo Bala’i. A gidan uban waye aka yanka min suna da Indo Bala’i? Kinga Goggo Hali ki kauce ki bani hanya, kar nayi gefe dake kiga rashin kunya ta, dan wallahi, na ture ki na shige cikin d’akin nan bazai bani tsoro ba, ehe sai dai duk abunda zai faru ya faru.”

Ta k’arasa maganar tana murgud’a baki, gum sukaji An rufe k’ofar d’akin tare da dannawa k’ofar sakata, daga rufen zainabu tace

“Ba zan fiton ba, kuma na fad’a Indo Bala’i ko k’arya nayi ke ba masifaffiyar bace.”

Matsawa wacce ta kira da Goggo Hali tayi tare da cewa ” To Kinga ma ta rufe d’akin sai dai idan ni zaki Kama ki daka, tunda ke baki da mutunci, kowa ya miki shaidar tsiya a cikin garin nan.”

Indo tace.

“Idan anga dama Amin shaidar Abunda yafi Rashin mutunci ma, kuma wallahi yau sai kinga yanda ake tsiya a cikin gidan nan, badai y’ar ki ta rufe d’aki ba” D’aga murya Indo tayi, tace ” Zainabu kina jina ai idan ba tsoro ba ki fito, mana shegiya y’ar matsorata, kuma wallahi Yau saina huce haushi na akan Uwarki.”

Juyawa Indo tayi, karaf kuwa sai idon ta yayi tozali da Randar k’asar Goggo Hali, wacce take cike fal da ruwa, da gudu tayi madafin Goggo Hali ta d’auko tab’arya, randar k’asar Indo ta nufa da gudu tare da buga tab’aryar akan Randar, fashewa randar tayi, take kuwa ruwan ya zube kasa, bokiti na k’arfe dake ajiye gefen randar k’asar Indo ta raruma tare da shek’awa a d’akin mahaifin Zainabu, tsayawa Goggo Hali tayi tana kallon ikon Allah a gun Indo domin kuwa Idon ne kawai tsakanin ta da ita, tasan Idan tayi gangancin zuwa ta tare Indo to Babu shakka zata iya sauk’e mata tab’aryar a kanta ba damuwar ta bane, domin kuwa tasan halin Indo tsaf ƙauyen babu wanda ta ƙyale, cikin huci Indo tace.

“Kuma na watsa ruwan a d’akin Malam Hamza idan ya dawo shima yasan cewa y’ar sa ta tab’o Indo.”

Bata jira mai Goggo Hali zata ce ba tayi ficewar ta tana rera wak’a.

“Ikon Allah.” Cewar Goggo Hali ” Yarinya ta Addabi gari, kowa yake Allah wadarai da Halin ki, Yanzu fa ki duba kiga b’arnan da yarinyar nan tamin, Amma dai wallahi Albasa batayi Halin Ruwa ba dan dai iyayen ki kam, mutanen kirki ne, Su kuma tasu jarabawar kenan, na Samun fitinanniyar yarinya, Allah dai ya shirye ki Indo.”

Jin motsin mutum a bayan ta ne yasa Goggo Hali juyawa, zainabu ta gani tsaye tana sauk’e Ajiyar zuciya, ai kuwa nufar ta Goggo Hali tayi, tare da sauk’e mata rankwashi a kanta, tace.

“Yanzu ke Zainabu ki rasa wa zaki tsokana sai Indo sai kace wacce baki san Halin ta ba, to maza shiga d’aki ki d’auko min mayafi na, naje wajen Uwar ta wallahi sai sun biyani Randa ta, dan bazan yi Asara ba wallahi.”

D’akin Zainabu ta nufa tana cewa.

“Ki je ki wallahi Goggo a biya ki randar ki, tunda y’ar su bata da mutunci.”

Ita kuwa Indo fitar ta daga gidan su Zainabu, hanyar gidan su ta nufa, tun daga nesa ta hango motar sa, cikin murna da zuwan sa, garin nasu yasa Indo kwasa a guje, tana zumud’i, ta nufi motar, kasancewar Gudu baya bawa Indo wahala, kullum a cikin sa, take sam bata da nutsuwa, k’azanta kuma wajen Indo subhanallah! Ba’a magana, domin kuwa k’azama ce ta ajin farko, duk inda ake neman k’azama, to idan aka Samu Indo ayi fatiha a tashi, domin kuwa kaf fad’in K’auyen Babu wanda yakai Indo k’azanta.

A nutse ya fito daga cikin motar, tare da tsayawa jikin motar yana duba yaran da zasu shigar masa da Kaya cikin gidan, tsohuwa mai ran k’arfe Hahija Innah da gudu Indo ta k’araso wajen nasa tare da yin turus da k’afar ta cikin bak’ar kasa mai k’ura dake shinfid’e a wajen, take kuwa k’asar ta bulewa wannan bawan Allah k’afar sa.

Da sauri ya daga kansa ya dubi Indo cikin takaici ya daka mata tsawa.

“Wacce irin mahaukaciya ce ke, ki duba kiga yanda kika bule ni da k’asa, wawiya marar Hankali, Zaki kauce min da gani ko sai na makeki, useless kawai.”

Tura bakin ta Indo tayi, tace.

“Wallahi yau Kam bazan bar nan ba sai kace kana sona! shike nan kullum sai ni kad’ai zanta sonka, kai bazaka soni ba, wallahi yau sai kace kana sona, ko kuma kamin irin abunda nake gani y’an India suna yiwa y’an matan su, a tibin Hajiya Innah Bari ma na tuno sunan abun .”

A firgice ta doka tsalle ta cigaba da cewa.

“Yawwa na tuno kuss, suke cewa, sai kamin sannan zan tafi.” Turo masa bakinta tayi, ta kuma cewa ” Gashi kamin, kaji mustapha na.”

Zaro Idanunsa, mustapha Yayi tare da saurin kawar da kansa gefe, jin bugun warin bakin Indo ya bigi hancin sa, wani Irin hucin wari yaji mai tayar da zuciya, cikin k’yank’yamin ta yake cewa.

“Allah ya sauwak’a naso k’azama irin ki, k’azamar k’auye, waima tukunna uban waye zai miki kiss, da wad’annan yellow hak’waren naki, b’ace min da gani kafin na targad’a ki, mahaukaciya kawai, marar lissafi, Amma dai wallahi Allah ya isa tsakanina dake, ki rasa waye zakice kina so saini, to wallahi Allah ya isa kin cuceni.”

Murgud’a masa baki tayi tace.

“Niba mahaukaciya bace wallahi, kuma sai kamin kuss d’in nan.”

Rarumo rigarsa tayi, ta duk’unk’une a ciki.

kasancewar babbar riga yasa, sai buga k’afa take, tana ihu tana cewa.

“Wayyo Allah na shiga uku wayyo jama’a kuzo ku tayani rok’ar ya mustapha ya min kuss wayyo Allah Jama’a kuzo ni kad’ai nake sonsa shi baya Sona.”

Rasa Yaya mustapha zaiyi da Indo haushinta ya turniƙe zuciyarsa, gashi kuma yana hango wasu dattawa biyu suna, tahowa, ta inda suke,

“Innalillahi wa’inna’ilaihirraji’un Allahumma ajirni fil musibati! Ni dai wannan yarinyar ta zamo min masifa wallahi, duk randa zan zo k’auyen nan, da tsinkewar zuciya nake Zuwa, tunda nasan zan had’u da Bala’i.”

da k’arfi mustapha yasa Hanun sa cikin kyamar Indo ya b’anb’aro ta da kyar, tare da hankad’a ta, gefe.

fad’uwa tayi tare da bige kanta jikin bango, wani Irin zafi taji a kanta, Amma duk da haka bakin Indo bai mutu ba, cikin rashin kunya, ta taso kamar wacce zata doki Mustapha, tace.

“Ka ture Allah ya Isa wallahi, mungun azzalumi, kuma wallahi bashi ka d’auka, sai na rama wallahi.”

Tana gama fad’in haka ta juya ba tare da ta k’ara Kallon mustapha ba.

Tsuka mustapha yaja, tare da tab’e bakin sa, yace.

“Wawiya kawai marar Hankali da nutsuwa, ai ko d’aura min ke Akayi a wuya, saina sinke ki da k’arfin tsiya, nayi wurgi dake gefe, k’azamar k’auye kawai.”

Yara biyu ya hango, kira ya k’wala musu, bayan sunzo ne, ya umurce su, da su kwashi kayan sukai masa gidan Hajiya Innah.

Tsayawa yayi har suka gama shigar da kayan sannan yasawa motar sa security, yayi gidan Hajiya Innah.

Sauk’ar Ruwa a jikin sa mustapha yaji’ wani Irin shid’ewa yayi, a gigice ya bud’e Idon sa, karaf suka had’a Ido da Indo tsaye da bokitin Ruwa a Hanun ta wanda ta juyewa Mustapha a jikin sa, takaici da haushin ta, shine ya hanasa magana, saima wani mungun kallon daya tsaya yana aika mata.

Juyawa Indo tayi a guje tana dariyar k’eta tace.

“Na rama tureni da kayi, daman ai na fad’a maka Bashi kaci, kuma na rama yanzu babu bashi tsakanin mu, duk wanda yaci ladar Kuturu, dole sai ya masa aski masoyina mustapha, ina sonka aradu.” Ta na gudun ne take wannan zancen.

Kad’a kansa mustapha yayi, cikin jin haushin Indo da mamakin ta, yake cewa.

“Anya kuwa wannan yarinyar bata da Aljanu, don ba k’alau take ba, kam, wai masoyina mustapha ko a gidan uban waye na zama masoyin nata, sai Allah.” shigewa yayi cikin gidan, tare da sallama.

Tana zaune gefe tana b’arar gyad’a ga kuma tarin kayan da mustapha yasa aka shigo masa dashi a gefen ta, d’aga kanta tayi tare da cewa

“Lale maraba’ da mutanen birni.” Sai kuma tayi shuru tare da tsurawa jik’ak’k’un kayan jikin sa Ido, cikin mamakin meya jik’a masa kaya, kasa hakuri Hajiya Inna tayi tace.

“Muhammadu menene ya jik’a maka kayan ka, kodai ka biya Rafi ne kayi wanka?”

Tambayar Hajiya Innah ta k’arshe itace ta bawa mustapha haushi, wai ko ka biya Rafi ne kayi wanka sai kace ta tab’a ganin nayi hanyar rafin nasu, cikin gatse ya mayar mata amsa da cewa.

“A’a ba Rafi Naje ba, tekun Maliya na biya nayi wankan na dawo.

“To uban y’an bak’ar magana da zafin zuciya, idan da Akwai inda yafi tekun Maliya ruwa ma kaje kayi wankan, aikin banza kawai daga tambaya sai cibi ya zama k’ari.”

Tabe bakin sa yayi tare da d’aga kafad’ar sa, alamun wannan damuwar kine, shigewar sa yayi d’akin daya kasance nashi idan yazo k’auyen.

D’akin fess dashi gwanin ban sha’awa komai a tsare kamar d’akin mace, kan dressing mirron shi kuma kayan shafe shafe ne kalakala masu tsadar gaske na maza.

Wanka ya shige yayi a ban d’akin Hajiya Inna dake tsakar gidan ta.

Itako Hajiya Inna sai mita take ita d’aya.

“Yaro ace sai shegen Bak’ar Zuciya gare sa, ga rashin hak’urin tsiya, shiyasa nake Allah Allah Habeebu ya dawo ya dinga ziyarta ta, sai munfi shiri dashi, fiye da wannan mai Bak’in Ran tsiyar, nan Habeebu yaron kirki ne d’an Albarka, na Rasa wani Irin Aiki yake a k’asar wajen Nan, da yak’i dawowa k’asar sa ta haihuwa.”

Mustapha daya fito daga ban d’aki ne, yana jin duk mitar da take yi, yake ce mata.

“Kamata yayi ki bisa k’asar wajen ai, ki dawo shi wannan k’auyen da zama k’arshen k’auna, hakan ne zai tabbatar da kina sonshi, nima banda k’addara da biyayyar iyaye mai zai kawo ni wannan, Bak’in k’auyen harma wannan jarababbiyar yarinyar ta addabe ni,

Kuma wallahi Hajiya koda wasa naga k’afar yarinyar nan Indo cikin gidan nan sai na b’allata.”

“Kan uba! To a bak’in k’auyen aka binne cibiyar uban ka, kuma baka da wajen daya fi wannan k’auyen tunda shi ne asalin ubanka Haruna, da kake maganar cewa Indo karta shigo cikin gidan nan, gidan kane koko akwai kud’in ka cikin ginin gidan, to ko ubanka Haruna bai isa ya hana Aishatu shigowa cikin gidan Nan ba, bare kuma kai karan kad’a miya, sai dai kuma kai kabar min gidana, badai Indo ba zan kuma ga uban da zai hana ta shigowa.”

Hararar Hajiya Innah Mustapha yayi, tare da shigewa cikin d’akin nasa ba tare daya k’ara tankawa ma ta ba.

Itama d’akin ta ta shige tana ci gaba da zagin mustapha, wanda shine gaisuwar da sukayi daga isowar sa.

“Gafaran kudai masu gida.” cewar Goggo Hali, dake tsaye k’ofar d’akin, Mama mahaifiyar Indo.

Fitowa mama tayi, tare da cewa

“Lale marhaban da Halima, kece yau tafe a gidan nan.”

“Eh nice na sameki lafiya”

Cewar Goggo Hali

“Lafiya lau Halima ki zauna mana, mu gaisa, naga kin tsaya bayan ga shimfid’ar taburma.”

Cewar Umma.

Kad’a kanta Goggo Hali tayi tare da cewa.

“Ba zama bane ya kawo ni Mairo, y’arki ce tayi min d’ibar albarka, yau a cikin gidana tare da kuma b’arna, shine nazo a biya ni, dan bazan iya Asara ba wallahi, tunda ku y’arku tafi k’arfin ku.”

Mama taji zafin maganganun da Goggo Hali ta mata, sai dai kuma ba laifin ta bane d’an kuka ne mai jawa uwarsa jifa da Indo mutum ce mai jin magana da tuni ta daina jawo musu zagi a gari, amma kunnen k’ashi gare ta, sai dai kullum tana mata addu’a tare da fatan shiriya, ta kintsu ta dawo y’a ta gari wacce kowa zaiyi alfahari da ita, kuma tasan Allah maji rok’on bawan sa ne, yana jinta yana ganin ta kuma zai amshi addu’ar ta.

Bata tsaya tambayan Goggo Hali me Indo tayi mata ba gudun kar taji abunda zai b’ata mata rai, yasa ta cewa goggo hali.

“Kiyi Hkr Halima, d’an yaune ka haifesa baka haifi halin sa ba Nawa ne kud’in b’arnan da Indo tayi Miki.”

“Randata ta fasa min, sabuwa gal ranar da naje, garin sauro na sayo ta, Naira d’ari uku da hamsin 350.”

Kunce bakin zanin ta mama tayi, ta ciro gudan d’ari biyar ta mik’awa Goggo Hali, tace.

“Gashi Idan kin sanja sai ki aiko min da d’ari da hamsin.”

Karb’a Goggo Hali tayi babu ko kunya ta fice tare da cewa zan aiko miki sanjin ki anjuma.

Shuru mama tayi tana tunanin Halin, Indo ita tsoron ta ma kar wani ya ma ta mungun baki ya kamata, domin kuwa ita kanta da ta haifi Indo hakuri take da ita, bare kuma al’ummar gari.

Tana cikin tunanin ne Indo ta shigo gidan da gudu tana dariya, tare da zama kusa da Mama tace.

“Mama ina Abinci na, yunwa nake ji wallahi, d’azun nan naci abinci amma wallahi yanzu ji nake kamar na kwana biyu banci abinci ba.”

Kallon ta Mama tayi, tare da cewa.

“Za kuma yau ki kwana baki ci abinci ba, domin kuwa kud’in cefenen da Malam ya bani d’ari biyar, na d’auka na biya, Halima kud’in randar ta, da kika fasa, kinga yau sai mu wuni da azumin dole d’ari da hamsin ta saura, kuma k’annen ki, zan sayawa garin rogo da suger su sha.”

“Kutumar uban nan, Goggo Halin ne tazo tace na mata b’arna, ita bata gaya miki abunda Zainabu tamin ba.

To wallahi Mama sai Goggo Hali ta gwammace bata karb’i kud’in nan ba, dan wallahi sai nayiwa Zainabu mungun dukan da sai sun kashe dubu a kantin Hassan mai magani.”

Gwanb’are bakin ta Mama tayi tare da cewa.

“Ke dai Indo bakya nemawa rayuwar ki Albarka wallahi, yanzu ma sake komawa zakiyi gidan nasu, ki jawo min wani maganar ne, to wallahi ko a hanya kika had’u da Zainabu, karki kuskura kisa hanu a jikin ta, idan kuma kika sa hanu jikin ta, to kuwa ranki zai b’aci a wajena shashashar banza marar kunya.

Tashi Indo tayi tana tura baki tare da maganganu k’asa k’asa, wanda bakin ta ne kawai ke motsi, sanda tazo daf da k’ofar barin cikin gidan nasu tace.

“Wallahi Mama babu mai hanani cin uban Zainabu yau, sai dai Idan bamu had’u ba, gara ma kiyi hakuri kawai.

Tashi Mama tayi tana “Dawo ki samu waje ki zauna Indo yau wuni zakiyi cikin gidan nan tunda Allah ya yoki mai kunnen k’ashi.”

Indo bata tsaya sauraron Mama ba ta fice a d’ari tana dariya.

Gidan su k’awar ta Hansai, shigar ta zauren gidan su hansai ta jiyo muryar Baffah mahaifin Hansai, tsayawa Indo tayi tare da dafe k’irji tace

“Alhamdulillah Allah yaso ban shiga ba, ashe wannan masifaffen tsohon yana nan.”

Kasancewar Baffah mahaifin Hansai ya hanata kula Indo acewar sa zata lalata masa tarbiyar yarinya.

Juyawa Indo tayi tare da zagawa, ta katangar ban d’akin su Hansai da nufin ta dirk’a ta ban d’akin yanda zata samu shigewa d’akin Innar su Hansai ba tare da Baffah ya ganta ba.

Kama katangar Indo tayi, kasancewar katangar guntuwa ce, ta dira cikin ban d’akin.

Lami kishiyar mahaifiyar Hansai dake tsugunne kan shadda tana bayan gari, taji dirowar mutum cikin ban d’akin, cikin tsoro ta fara bin k’afar Indo da kallo, ba tare da ta d’aga kai ta kalli fiskar taba, ihu Lami tasa cikin tsoro, tana cewa.

“Na shiga uku ni Lami, dan Allah kuyi haƙuri wallahi mantawa nayi, na shigo ba tare da nayi addu’a ba, kuyi hakuri dan Allah ku kuke ganin mu, ba muke ganin kuba ba wayyo Allah ku kawo min agaji yau kuma na yi gamo.”

Yayin da fitsari ke bin k’afofin Lami.

Dariya Indo ta shek’e dashi har hawaye na fita cikin idanun ta, ganin yanda Lami ta gigice ta fice hayyacin ta har tana fitsari a jikin ta, yayin da Idon ta, ke rufe gam tak’i bude su.

D’alewa saman katangar Indo tayi ta zauna tana cin dariyar ta, tare da nuna Lami da yatsa.

Indo A Birni 2 >>

1 thought on “Indo A Birni 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×