Skip to content
Part 2 of 3 in the Series Indo A Birni by Rasheedat Usman

Ilu d’an Lami ne da Baffah sai Innar Hansai sukayo ban d’akin da gudu jin ihun Lami. Turus suka tsaya sakamakon ganin INDO zaune saman katanga sai washe yellown Hak’waren ta take, tana cin dariya. Salallami Innar Hansai ta d’auka cikin Al’ajabin meya kawo Indo ban d’akin su.

“Ke Indo meya kawo ki nan, yau kuma tsiyar taki cikin gidan na kika kawo mana.” cewar Baffah. Jin an Kira Indo ne yasa Lami saurin bud’e idon ta, fes kuwa ta sauk’e su kanta dake ta famar dariya ta mayar da su mahaukata, Cikin Haushin Indo Lami tace. ” Amma dai Allah ya isa tsakanina da ke Indo, tsabar rashin mutunci duk k’ofar gidan nan bai isheki shigowa ba, sai kin diro ta ban d’aki, baki sani ba koda mutum koko Babu, ki shigo ki sami mutum a Halin da bai dace ki samesa ba.” Dariya INDO ta sake shek’ewa dashi, cikin dariyar take cewa ” Kamar dai yanda nazo na same ki kina burkuta kashin ki, kai Amma Lami Anyi matsoraciya, duba fah kiga yanda kika jik’e zanin ki da fitsari.” Sai kuwa ta k’ara shek’ewa da dariya “Aradun Allah Lami kashin ki wari gare sa, ni kin gama ma cika min ciki da warin kashin ki.” Ilu ne zuciyar sa tazo har wuya, cikin haushi da hasala yayi kan Indo da gudu, da niyar ya mata dukan da sai anzo an kwashe ta.

Ganin ilu yana nufo ta yasa Indo dirawa daga katangar. Ta kwasa a guje shima ilu ya rufawa ma ta baya da Gudu,l.

Babu inda Indo ta nufa sai gidan Hajiya Innah tasan a nan ne kawai zata tsira daga Hanun Ilu.

Hajiya Innah dake Zaune gindin murhu tana iza wuta ne taga shigowar Indo da gudu a birkice Hajiya Innah itama ta tashi tabi bayan indo da gudu.

Gudu suke sanda suka shiga cikin d’akin Innah, sannan suka tsaya suna haki, Hajiya Innah ce tace ” Ke indo gudun me kike haka, meya faru macijin nan ne, yauma ya k’ara biyo ki.?” Dariya indo ta shek’e dashi tana nuna Innah da Hanu, tace. ” Amma dai Inna ke ba k’aramar matsoraciya bace wallahi, daga gani na Ina gudu sai ki biyo baya na.” K’ara shek’ewa tayi da dariyar tana nuna Innah yanda taga Innah tayi tsamo tsamo gefe kamar kazar da aka tsamo a ruwa. Kamar dai wanda za’a ce fit ta D’iba da Gudu. ” Yanzu ke Inna Idan macijin ne, sai na tsaya harki iso ban rufe ƙofa ba, ai wallahi kafin ki ƙaraso na juma da rufe ƙofar nan sai dai Kuma kisan tayi.” Ranƙwashi Inna ta kai ma ta, ta gauce tana dariya ” Amma ke dai Indo akwai ja’irar yarinya, yanzu dan baki da mutunci, sai ki rufe ƙofar ki barni a waje, idan ma kasheni macijin zaiyi ke baki damu ba Koh?”

“To me zai dameni Inna, dan kin mutu ai ba Abun damuwa bane, tunda kin mori duniyar, wlh Innah na rufe ƙofar nan baki iso ba shi yafi komai sauki a wajena.” Haɗa fiska Hajiya Inna tayi kasancewar ta tsani taji ana kira ma ta mutuwa muraran, tace. ” Bari muga idan na mutu a ina zaki dinga samun taliyar turawa mai harɗe ki dinga ci, tunda gani na ne baƙya ƙaunar gani ina shaƙar iskan Duniya.” Shuru Indo tayi tana rufe bakinta ” Allah na tuba! Ehhh fah haka ne, kuma Inna wallahi Idan kin mutu Babu inda zan samu taliyar turawan Nan, to Gaskiya Allah ya Raya min ke Hajiya Inna kodan karna Rasa taliyar turawa.”

Washe Baki Innah/ tayi tace ” Ameen ƴar Albarka shiyasa nake sonki, faɗan mu baya nisa, saboda kin iya farar Addu’a yanxu….” Shigowar Ilu yana Banbami ne ya hana Hajiya Innah ƙarasa maganar ta.

“Lafiya Malam ƙaton gardi da kai ɗimeme duk ka gama cikar balaga zaka shigo min cikin gida, kamar wanda aka jeho daga sama, ko arzikin sallama Babu, kamar wanda ka shigo gidan Ubanka.” Nuna Indo Ilu Yayi, yace.

“Ga Wacce na biyo, ki fito Indo wallahi idan kika yadda na shigo ɗakin Nan, sai na karya ki.” Tsuka taja tana leƙo kai ta ce ” To Uban ta, Bismillah shiga ɗakin tunda ɗakin Ubanka ne, har wani cewa kake zaka ƙarya ta, to idan ka fasa ƙarya ta ka raina Uwar da ta haife ka.” Kallon Hajiya Inna ilu yake cikin mamakin ta, yace ” Hajiya kinsan Abunda ta mana kuwa, kike ƙoƙarin shigar mata faɗa.”

Inna ta taɓe bakinta ” Ban sani ba kuma bana son Sani, dake ku mutanen garin nan, manyan ku da yaran ku kun tsani ƴar taliƙar yarinyar na ko wani laifi ku ɗauko ku nana ma ta a kanta, to wallahi ta Allah ba taku ba, aniyar ku ta biku, har gadon Baccin ku wlh Indo dai tafi ƙarfin ku.” Hayaniyar da mustapha yaji ne yasa shi fitowa daga ɗakin nasa, yayo wajen Inna, turus ya tsaya yana kallon Inna yanda ta zage, sai zagin Bawan Allah take, ƙarasawa mustapha yayi tare da dafa kafaɗar Ilu yace ” Abokina lafiya me yake faruwa.?” Juyowa ilu yayi, ya fara bawa mustapha labarin abunda Indo ta yiwa mahaifiyar sa, ya ƙarisa da cewa ” Wallahi da gaske na ke, har banɗaki ta faɗa ma ta.”

Shi mustapha baima san da Indo a gidan ba sai dai yaji akanta ake Case ɗin tukunna, A zuciyar sa yake cewa ‘Wannan yarinyar itace Iblis ɗin wannan ƙauye, yanzu tsabar shaharan yarinyar nan a fanni Rashin hankali har ki dirƙawa mutane katangar tollet ɗinsu.’ yayi maganar zucin yana cewa Ilu. ” Shiga ka jawo ta kaci Uban ta, wannan ɗan iskan bakin nata wanda kullum yake cikin ƙazanta, ka tabbatar kayi rugurugu dashi.” Daga cikin ɗakin Indo tace. ” Nidai wlh ba Uba na ba ehe.” Zaro Ido mustapha Yayi yace ” Sai Uban waye kenan?”

Babu tsoro fiskarta ta mayar masa da amsa ” Sai dai Uban Wanda ya tsargu.” Kallon ilu yayi yace ” Ka shiga ka sanja mata kamanni nace maka.” Tare ƙofar Innah tayi tace sai “Naga shegen da zai wuce cikin ɗakin nan, munafiki, idan banda munafurci, meya fito da kai daga ɗakin ka sai ya fasa ma ta bakin mu gani.” Jawo Inna Mustapha yayi suka hau kokuwa, yayin da ya riƙe ma ta Hannayen ta gam yana cewa Ilu ya shiga. Ganin da Indo tayi da gaske, Ilu zai damƙe ta yasa ta daka tsalle sai ƙarƙashin gadon Inna can ƙarshe. Neman Indo Ilu yayi sama da ƙasa ya Rasa, ko motsin ta, baiji ba cikin ɗakin, fitowa Yayi cikin Huci yace ” Ta fa ɓace babu ita cikin ɗakin nan.” Cikin mamaki Mustapha ya ce ” Babu ita kamar Yaya Yanzu na hango yarinya, kace bata nan ta ɓace sai kace Aljana.” Kansa Illu ya ɗaga” Wlh Babu ita, kazo ka duba ka gani.” Sake Inna Mustapha yayi, yasa kansa Cikin ɗakin, bai ganta ba dube dube ya hau yi Amma Babu ita sama da ƙasa, ko a ransa bai kawo Indo zata shige ƙarƙashin gado ba ” Haba ai daman Biri yayi Kama da Mutum yanda yarinyar nan, take dole tana Aiki da Aljanu ne Idan ba Aljani ba waye zai ɓace ɓat lokaci ɗaya.” Kallon sa ya mayar kan Ilu yace kaje kayi Hak’uri kawai ka barta da Allah dan yarinyar nan tafi ƙarfin mutum sai dai Aljani.” Shigewa Ilu yayi yana cewa wlh ido na Idon Indoe, sai na ma ta shegen Duka.” Inna ce ta ce ” Kama kashe ta idan kaga dama kuma zanje har wajen Ubanka naji idan shiya turo ka gidan nan kamin rashin mutunci.”

Ficewa waje shima mustapha yayi ba tare daya kalli Hajiya Inna ba. Ɗakin ta shiga, tace ” To fito ja’ira marar Kunya nasan ai kina cikin ɗakin, ashe daman Bala’i kika nemo shiyasa kika shigo a guje, har nima kika Sani gudu, yau da sun kamaki sai dai wani bake ba wallahi daman haushin ki, wannan uban baƙin halin yake ji.” Fitowa Indo tayi tana dariya tace ” To yaya suka iya dani Inna, ni ɗin tsayuwa zanyi su jibge ni, ni dai yanzu Inna ki bani taliyar turawan Nan, naje gida na tafasa dan baxain tsaya gidan nan ba, ya Mustapha yazo ya ritsani.”

Dariya Inna ta yi ta ce ” Ja’ira ai kuwa yau da kin faɗawa ƴan alewar garinku, ki ɗauki wannan, kwalin ki kaiwa Uwar taki ta tafasa muku keda ƙannen ki.” Ɗauka Indo tayi tana cewa, shiyasa nake sonki Inna, kodan wannan taliyar.” Tayi maganar tana ficewa tana waige waige kar Ilu ko Mustapha su riƙota, cikin sa’a kuwa har ta shiga cikin gidan bata haɗu da suba.

Zaune Malam Sa’idu mahaifin Hansai yake gaban mai gari, yayin daya kawo ƙarar Indo kan Abunda ta shiga cikin gidan sa ta aikata masa. Nisawa mai gari yayi tare da cewa ” Ita Indon ce tayi wannan ɗanyen Aiki.”? Malam Sa’idu ya amsa da eh umurtan Dogari Mai Gari yayi akan cewa yaje yazo masa da Malam Musa mahaifin INDO. Da sauri dogari ya tafi aiken da mai gari ya masa. Sallama Dogari yayi tare da kwalawa kira a ƙofar gidan su indo, Yayan Indo Tanimu shine ya fito. Jin sallamar da ake yi. Dogari ya gani tsaye. “Lafiya kuwa Dogari.” cewar Tanimu. “Lafiya lau mlm Musa Nake nema, mai gari ke kiran sa, yanzu a fada.”

“Me gari kuma, Allah dai yasa lafiya.?” Dogari ya ce. “Koma menene idan yazo yaji, ka shiga kamin Sallama dashi.”

“Baya nan Amma bari naje kasuwar na kira sa, zaizo yanzu insha Allah.”

“Shikenan bari na koma, ka tabbatar yazo yanzu.”

Tanimu ya amsa. “Insha Allah zaizo.” Tanimu bai koma cikin gida ba, ya shige, kasuwa wajen, Malam Musa, yana zaune bakin shagon nasa na tireda, yana jin rediyo, yaga Tanimu ya masa Sallama. Amsa Sallamar yayi yace. “Tanimu kaine cikin shagon nawa, yaushe ka dawo daga wajen Raken naka.”

“Yanzu na dawo Baba bamma daɗe da dawowa ba, naji sallamar dogari, shine yace min mai gari na son ganin ka yanzu.”

Malam Musa baiyi mamakin jin kiran mai gari ba, yasan Tatsuniyar Gizo bata wuce ta Ƙoƙi wannan kiran da mai gari ya masa bazai wuce wata maganar Indo ta jawo masa a gari ba, tashi yayi ya kulle shagon nasa ya cewa, Tanimu muje.

An taro fadar mai gari, ana jiran isowar Malam Musa, sai Kuma ga shi ya iso. Zama yayi tare da gaishe da mai gari, sannan mai gari ya dubi, malam Sa’idu yace “Maimaita masa Abinda ke tafe dakai. Duban Malam Musa, Malam Sa’idu yayi tare da fara jero masa tijarar da, Indo ta masa cikin gida. Ya ƙarasa zancen da cewa “Na gaji kawai mai gari ya min tsakani da Indo da Kuma ƴata, babu mu Babu ita, ko a hanya taga Hansai, karta ƙara koda kallon ta.”

“Allah ya huci Zuciyar ka, Malam Sa’idu, duk Abinda kace Indo tayi banda musu ko ja akan haka, fiye da haka ma zata aikata, Kuma insha Allah daga yau na maka Alƙawarin cewa, Indo ko ƙofar gidan ka, bazata ƙara kallo ba.” Duban sa ya mayar kan mai gari yace “Yallaɓoi dan Allah Ayi hakuri insha Allah hakan ba zata ƙara kasancewa ba.” Nisawa mai gari yayi yace.

“To malam Sa’idu kaji bayanin malam Musa, nima ina ƙara baka hakuri tabbas kam yarinya bata kyauta ba, kayi hakuri gaba idan ta sake zamu ɗauki ƙwaƙwaran mataki a kanta.”

“Shike nan mai gari, Nayi hakuri, Allah ya yafe mana duka.” Godiya Malam Musa yayiwa malam Sa’idu da mai gari, sannan ya cewa Tanimu ya tashi su tafi.

Tanimu Allah Allah yake, ya isa gida ya samu Indo, yau kam mai ƙwacen Indo a hanun sa Sai Allah. Cikin Sa’a kuwa Tanimu suna shiga shiga cikin gidan itama Indo tana shigowa, da kwalin Indomie ɗinta a kayi, karɓar kwalin Tanimu yayi ya ajiye a gefe sannan yaja Indo har ɗakin da Mama ke kiwon tumaki, rufe ƙyauran Tanimu yayi, Malam Musa na ganin haka, yayi murmurshi tare da shigewa cikin ɗakin sa, dan yasan yau Indo ta shiga Uku hanun Tanimu.

Kallon Tanimu Indo tayi tace. “Me zamuyi Anan ɗin yaya, naga ka rufe ƙyaure, kayi sauri ni zanje na dafa taliya tace.”

Tanimu bai tanka Indo ba, sai ma sunkuyawa da yayi ya ɗauki bulala, ya hau zabgawa Indo, ihu Indo take tana ƙoƙarin riƙe bulalar Amma Tanimu bai bari ta riƙe bulalar ba, sosai Tanimu yake dukan, Indo, ita kuwa sai cewa take. “Allah ya isa zai kasheni mungu, azzalumi, wayyo Mama, yaya zaiyi kisan kai cikin gidan nan, ka sakeni shege mugun banza ba bayin Allah ne a cikin gidan zai kasheni!.” Sai da ya ma ta lilis sannan ya ajiye bulalar ya daki bakin Indo da ƙarfi sanda ya kawo jini, take kuwa bakin ya kunbura suntum, sannan ya buɗe ƙyauren ya fice, yabar Indo tana birgima tare da ihu, Mama da Malam Musa ya sanar da ita abunda ya faru, ko kollon inda Indo take ba ta yiba saima ɗage kwalin Indomie da tayi ta mayar gefe, tasan bazai wuce Hajiya inna bace ta bata taliyar. Har dare Indo tana zaune ɗakin tumakin nan taƙi fitowa, zagi kuwa Babu irin wanda Tanimu baisha ba, Jauɗo kuwa ƙaninta daya leƙa da duwatsu ta jefe sa. Babu wanda yace ma ta fito, kowa harkar gabansa yake, koda Mama ta gama abincin dare ma Indo ƙinci tayi, mama dai mayar da abincin ta tayi cikin madafi, cikin dare kuwa da yunwa ta Addabi Indo Babu wanda ya sani ta zaga ta ɗauki Abincin taci.

Washe gari da safe Mustapha ya fito cikin shirin sa na komawa cikin dutse dake Garin Jigawa, Hajiya Inna ya samu tana cin ɗumamen tuwon ta, zama yayi gefen ta, tare da Gaishe ta, Amsawa tayi ta ce. “Muhammadu har ka fito bazaka bari kayi karin kumallo ba.” Kansa ya kaɗa ya ce. “A’a inna idan na koma gida na karya, kuɗi ya ciro dubu ashirin ya ajiyewa inna, tare da ma ta sallama. “Allah ya kiyaye hanya ka gaishe da iyayen naka, habibu kam wannan karon baka haɗamu munyi magana ba.” Tayi maganar tana basa su daddawa kuka harda kuɓewa bushashiya tace “Ga shi ka kaiwa uwar taka sayi Amfani dashi.” Karɓa yayi yace “Inna kwana biyu wayar Habeeb idan na kira bata tafiya, ina ga babu network ne cikin garin naku.” Ta ce “Shike nan to sai Allah ya ƙara dawo dakai ka haɗamu.’

Har zauren gidan ta rakosa sannan ta koma.

Mustapha ya buɗe motar sa da niyar shiga kenan yaji Muryar Indo na cewa. “Masoyina komawa zakayi kuma, ni dai wlh ban gaji da ganin kaba ka bari sai gobe ka koma, kafin nan zan maka kafi tsire sai ka kai tsaraba gidan ku.” Juyowa Mustapha yayi a fusace da niyar make Indo, sai kuma yayi tozali da bakin Indo dake kumbure sun tum harya sanja mata kammani, dariya ce ta kwacewa Mustapha yana nuna Indo, yace yau kuma waye ya iya jada Aljana.

<< Indo A Birni 1Indo A Birni 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.