Skip to content
Part 1 of 6 in the Series Izina by Hkadija B. Ahamad (Matar Sadiq)

Jan Hankali

“Ni ‘yar wani ce a yau, gobe zan iya zama yayar wani, jibi na zama matar wani gata na zama mahaifiyar wani! Me ze sa ka lalata mun rayuwata a yau? Rashin imani shi ne yake sawa aci zarafin kananan yara. Jama’a ku taimake mu, mu zama yara na gari dan zama iyaye na gari. Mutum na gari shi ne allon kwaikwayo a cikin al’umma wanda ke daukan dan wani tamkar nasa.”

BISSIMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

ZARIYA ➡ STATE UMMY AYSHA POV.

“Innalillahi wa’inna ilahirin raji’un, Innalillahi wa’inna ilahir raji’un,, Innalillahi wa’inna ilahir raji’un Ubangiji ka tsayar mana dukkan wata masifa da yake tunkaro mu..”
Wani babban mutum wanda a kalla yakai shekara 40 da wani abu yana tsaye akan matashiyar budurwar yarinyar yake furtawa cike da tashin hankali a fuskarsa saboda samun mummunan labarin..
Ita kuma tana gefe tana shesshekar kuka kamar ranta ze fita

Umma dake tsaye zuciyarta kamar zata fashe saboda takaici ta kalli Malam tace,
“To kade ji..”
yayi ajiyar zuciya yace,
“Jummai yanzu wannan bala’in dame yayi kama?..”
Hawaye na gangaro mata cike da tsanar rayuwar ‘yarta ta tace,
“Ai ni Me-gida cewa nayi da, da haihuwar Ummy Aysha wallahi wallahi gara b’arinta, dana sani ma da Allah ya kawota sa fulo nayi na danne kanta kowa ya huta da wannan masifa data d’auko mana..”

Jin kalamai marasa dadi da Umma tayi yayi saurin cewa,
“Dan baki da hankali, kinsan abun da kike fad’a mun kuwa, waye ya haifi yarinyar?, bake kika haifeta ba?, to yanzun nan da kike nema ki tozarta kinsan me Allah ze mayar da ita gaba wannan ma ai kaddara ce, kaddara ce Allah ya kwo ya zamuyi..”

Ta watsa masa harara tace,
“Dallah dakata Malam, nifa bazan yarda a unguwarnan a dinga nunani kamar naci Senoter ba, ana gatacan ‘yarta tayi cikin shege, to ba dani ba tsakanina da Rahma daga yau bani ba ita acikin gidan nan..!”
Ummy Aysha ta kara sidda kai k’asa tana kuka cike da dana sanin rayuwar da ta tsinci kanta aciki
Umma ta wuce saboda ko kallonta bata son kara maimaitawa
Malam yace,

“Kinga zo nan, bana son magana irin wannan, kefa kika haifi yarinyar nan nine kuma wan ubanta dan haka baki i’sa kice bake ba ita ba, gidan ubanwa zataje ta fad’a?, ki fad’amun wanene baisan kaddara ba, waye besan larura ba?, kinsan ta yadda akai wannan kaddara ta sameta? To aima idan muka k’i karbarta tashiga mokota ai asirinmu ya tonu, to kinga ban yarda da wannan maganar ba idan zaki sanja ki sanja, mahaifin yarinyar kuma zezo har nan ya sameni, yarinyar nan tana zaune a gidan nan daram..”
Ta shige daki tana cewa,
“Kanka ake ji Malam ai ni na gama..”
yace,
“To shikenan kaina ake ji, shikenan kuma naga yadda zaki da yarinyar tana nan gidan zezo ya zaba koni ko ita ..”
Shima ya fice a gidan ransa a matukar b’ace..!
Aunty Jameela dake gefen Ummy cike da takaici tace,
“Ina tsoron ranar da Mutanen unguwar nan da irin kallon daza su dinga kallonki da zarar cikin nan ya tsufa, kuma ina tsoran ganin yaro ko yarinyar da zaki haifa ya taso yaji ko taji ana cewa wannan D’an d’an shegene, da wannan tinanin shiyasa na yanke hukuncin a zubar dashi, naje na samu kawata, ta fad’amun inda za’aje a zubar da wannan cikin, kawai abun da za’ai aje a zubar dashi shine samun mafitatar mu baki d’aya..”

Cikin tausayin kanta da rayuwarta da kuma fargaba tace,
“Gaskiya Aunty ina jin tsoro wata Likita tace zan iya mutuwa matukar akace za’a cire wannan cikin, gaskiya ina jin tsoro..”

Ta watsa mata harara cikin jin haushin amsar da ta bata tace,
“Kina jin tsoro?, hmm lokacin da kikaje kika aikata baki ji tsoro ba sai yanzu?, to shikenan a barshi d’in..”
Cikin kunar zuciya da kuma danasanin amincewa da Zayd har ya cutar da ita irin haka, kuma ya gujeta a lokacin da ta fi kowa bukatarsa tace,
“To shikenan aje a zubar d’in..”
ta fad’a hawaye na gangaro mata
Lallai Zayd ya yaudareta, ya kuma gujeta lokaci guda
“Tunda hakane kawai a zubar ya zanyi?, amma ya cuceni..”
“Rufemun baki kika cuci kanki de, Wallahi idan kika yarda Baba yaji wannan maganar bake kad’ai ba mu kammu mun shiga uku dan wallahi barin gidan nan ya kama mu..”

“Wallahi Aunty Jameela fyad’e yayi mun wallahi ko bacci na kwanta bana iya yi Saboda irin halin damuwar da nake ciki yanzu kikala Umma kullum sai fushi take..”
“Ba fushi kad’ai zatayi ba, hawan jini ma seya sameta, wani uban ne yace, ki bishi har ya miki fyaden?, da baki bishi ba ai da yanzu mutuncin ki yana nan, kina ganin Baba idan ya samu wannan labarin hankalinsa ze kwanta ne, yafa manyata ya tsufa…”
Tace,
“To shikenan aje a zubar..”
ta fada hankalinta ba tare da ya kuma kwanciya ba, dan bazata manta maganar da Doctor ta fad’a mata ba, ita da Nana’ bata da laifi aciki wannan al’amarin iftila’in al’amarin, idan akwai be wuce kuskurenta na saurin amincewa da saurayi har tayi masa rakiya zuwa wani wajen ba, duk da zuciyarta d’aya akan shi..

ABUJA SATATE ➡ MU’ISHA POV.

Zaune suke a kayataccen Palourn wanda girman-sa da tsayinsa yakai 100%by50 kallo d’aya zakai kasan nera tayi kuka a gidan
Fira suke sosai ta jin dad’i a tsakaninsu!.., dan yau gidan acikin nishad’i yake, badan-komaiba, sai-dan zuwa gobe iwar-haka babbansu k’aramin-su na tare dasu!
Aisha da yanzu ta shigo cikin Palourn cikin sanyin halittarta da miskilancin-ta, ta zauna a gefen Momy tare da langwa’bar da kanta a saman kafad’arta,

Murmushi Momy tayi tare da cewa, “Uhmm Ma’isha sarkin shagwa’ba, kin fiye lalaci, yanzun kuma me-yafaru? naga yau weekend ne, ba aiki, dukkan-ku iyalina gaku a gida a kusa dani!, duk wannan miskilancin naki, da shegen son jjkin nan naki ajiye shi zaki a gefe. yau muyi fira, ga sauran ‘yan uwan-ki nanma, gobe in-sha allahu d’aya brother d’inki yana hanya”
A hankali ta d’ago da narkakkun idanuwanta, wanda idan ta kura maka su, sai ka-fita hayacinka saboda tsantsar kyawun-su.

Cikin sanyin muryarta tace,
“YA-MALIK?”.
“Eh shi mana, autar Momy, nasan baki wani wayeshi ba, domin tun baki da wayo, yabar Nigeria’ a lokacin da yazo-ma kin tafi Maiduguri, har ya tafi baku had’u ba..”
Kai ta girgiza, saboda hakane maganar Momy, bata wani san-shi a zahiri ba, a photo take ganin-shi.
Wayar-tace tayi kara, hakan yasata yin picking,

“Hellow, Eh ku shigar da korafin zuwa kotu in-sha Allah ni zan tsayawa yarinyar, kar-kuji shakar komai, ko kuyi tinanin cewa, sunfi karfin-ku, ta ‘bangaran dukiya ko wani abu, a’a Allah zaku-sa acikin tsarin!!, da yardar Allah zan tsaya muku akan shari’ar, sai na tabbatar an hukunta koma d’an-gidan uban waye!!”
tana fad’in haka ta sauke wayar, ta kara narkewa a jikin Momy

“Wallahi Momy, yawanci mutanan dake rayuwa cikin wannan zamanin, basu da imani, karamar yariya-ce fa, wani d’an mai arziki ya, yaudareta, ya kuma yaudari iyayenta!!, yayi mata fyad’e, dan kawai tana mazaunin ‘yar aiki a gidan-su. yanzun haka yarinyar tana kwance a gadon asibiti, da nayi bincike sai na gano wai ashema d’an gidan Senator ne, watam kenan a wannan zamanin talaka bashi da ‘yanci, bashi da wata makama, idan a cutar dashi, bashi da karfin gwiwar da za’abi a kwatar masa da ‘yancinsa, saboda corruption yayi babbar illah a kasar-mu ta Nigeria!!”

“Nikam nayi alkawarin sai na kwatar mata hakkinta, sai na tabbatar an masa hukunci dai-dai da abin da ya aikata”
Lallausar sumar kanta, wacce ta zubo a gadon bayanta, Momy ta shafa tare da cewa,

“Allah ubangiji ya taimaka akan niyar alkairin da kike da ita, Allah ya baki sa’a!..”

“Ameen Momy, addu’ar ku nake fatan samu, dan-mu kam duk wasu lauyoyi dake aiki, akan koyarwar addinin musulunci, wato gaskiya, rayuwar mu acikin hatsari take, kullum ana cikin farautar rayukan-mune!..”

“Allah ya kare-ku da kariyar-sa, ya kauda idanuwan makiya agare-ku”

“Ameen Momy na gode!..”

“Ni bazan bari na ‘bata sunan kasata ba ko na siyar da k’asata ba, bazan yarda na bar rayuwar al’ummata, su ciga-ba da lalacewa ba, Domin mace, al’umma ce, mace uwa ce, mace yaya-ce, mace kanwa-ce. mace itace tushen kafuwar al’umma baki d’aya!..”

Abdul-aziz da yanzun ya shigo cikin falon, ya kalli m
Ma’aishan da har yanzun kanta, na saman kafad’ar Momy da dukkan alamu da mutanan da ya hana a shigo dasu, yanzu tagama waya!!, dogon tsaki-yaja kafin yace;

“Aisha bakya-jin magana, yanzun miye amfanin kar’bar shari’ar da tafi karfin ki?, sam wllh aikin Barrister bai dace da mace kamar ki ba, ni wllh-ma kunya kike bani, ji irin mutanan da kike zuwa kike tara mana a kofar gida, yanzun ya dace ki kar’bi shari’ar wa’ina’nan? kud’in da zaki sawa motar ki, fetir bazasu iya biyan-ki ba?..”

Cikin ya mutsa fuska, tace,

“Ai dama’ ban karanci aikin lauya domin a biyani ba, nayi ne domin na kare hakkin mata, naji labarin kaine lauyan da zaka kare, wanda ake zargi, to kasani bazan bi bayan-ka ko nayi maka biyayya a matsayin ka na yaya-na ba, kuma kaji tsoron allah kayi aiki bisa gaskiya, badan makudan kud’aden da za’a biya ka-ba”
Cikin rashin fara’a, yace

“Nide ina baki umarni da ki ajiye wannan case d’in ki dubi ayyukan ki na gaba”

“No yaya baze yuwu ba, a matsayin ka na babban lauya bai dace kazo-min da wata barazanar karyar ku ba, hmm ko-de ka fara-jin tsorone?, oh.. no.. no.. bai kamata a matsayin ka na babban lauya, mai matukar jida kansa ya karaya da wuri haka ba!..”

“Kuma maganar na watsar da wannan k’ara baze yuwu ba, kuma ina da tabbacin zamu-yi nasara akan duk wani azalumin da ya shiga cikin wannan case d’in matukar ba da gaskiya zeyi aiki ba.”

“Ke har yanzu karamar yariya-ce, baki san me duniya take ciki ba, kin fita daga nan har kasar paris kinyi karatun shari’a, amma har yanzu kanki a duhu yake, baki ajiye komaiba, baki tara komaiba.
Sai tilin file-file”.

“Eh na yarda, ki tsaya musu!!, amma ki-sani bana fuskartar fad’uwa duk case d’in da nasa a gabana sai nayi wining”.
Harara ta watsa masa, tare da cewa,

“Momy kiji abun da yake fad’i, wllh mutanan sune keda gaskiya, kiyi masa fad’a da yaji tsoran allah, yayi aiki da gaskiya!!, idan kuma baze iya ba, ya ajiye aikin duka, saboda kar ya fad’a cikin fushin ubangiji!!”

Ajiyar zuciya Momyn ta sauk’e tace

“Abdul ba yau-ba na saba yi maka, nasiha da kaji tsoron allah kayi aiki bisa gaskiya, kar rud’in son zuciyar-ka ya kai-ka ya baro ka!!. kuma ina baka shawara ka ajiye wannan case d’in matukar ba da gaskiya zaka kalubalan-ce shi ba”.

Dariya yayi tare da cewa,

“A’a Momy, kinsan tsakanin-mu da ma’isha, akwai adawa ne kawai, kowa abokin takarar kowanne fanni ne, shiyasa kishinta ya motsa a fili. kawai ki tayamu da addu’a”.

“In-sha allah, kuma kusani dukkan ku ‘yan uwan juna-ne, kar yarda ku bari, kalubalen aikin-ku ya sauya muku alkibla, ma’ana kuyi adawa da junan-ku.
amma dole kowannen-ku yasa tsoran allah, acikin al’amuran rayuwar-sa!!, bani kad’ai ba mahaifin-ku-ma yana yi muku nasiha irin wannan”

Tana fad’in haka ta mike, saboda kosawa da halin-nasu, kuma inda sabo sun saba, kullum suyi ta sa’in-sa tsakaninsu, anjima aji-su, suna hira da k’us-k’us..

Abdul-malik Ibrahim ahamad!! ya-kasance mai zarar da sauran hazukan sojoji basu da ita, rayuwar-sa madubine ga dukkan mutane masu aikin d’amara, kana abun so da burgewa ga dukkan mai-sha’awar aikin tsaro a kasar sa!!, kana abun so da sha’awar kowanne mai imani!
Inda sunan-shi yake haka zahirin da bad’inin shi yake!!, Abdul-malik Ibrahim-ahamad: managar-cine salihi mai yawan fasaha da tawakalli, kyakkyawa irin kyan dake tsantsar haiba,

Da ginin tushe da asalin su, Abdul-malik, asalin mahaifin-sa fulanin jumaita ne-jihar adamawa, JUMAITA!! wani yanki-ne daga yan-kunan adamawa: wanda ya kasance yankin fulani masu asalin kyau. uwa uba fulani masu fafutukar neman ilimi da ‘bangare biyu duka; wato ilimin Arabic da kuma boko, al’umar jumaita sunyi fice ta kowanne sashi,

shiyasa ake musu kallon masu kima da cikar kamala malam ahamadu shine kaka gasu Abdul-malik,
malam ahamadu asalin sa fulanin yola ne gaba da baya, nan-ne tushensa iyaye da kakanni, babban me kud’i kuma malami da babu kamarsa a fad’in jumaita, a wancan lokacin, mafi akasarin yara da manyan garin a wajensa suke d’aukar karatu, saboda yana da makarantu a garin masu girma, shiyasa yaran dake nesa da su-ma suke zuwa karatu. wannan yasa ya shahara acikin garin jumaita!!,
Allah ya azurta-shi da tarun kadarori, gonaki da filaye….

Ibrahim-ahamad
shine mahaifin Abdulmalik, mutum ne me matukar mutunci da cikar kamala.
Alhaji Ibrahim Ahamad, allah ya wadata shi da mata d’aya me suna halima da yara uku, babban shine Abdul aziz, suna kiran-shi da habib, sai-ma biyin-shi Abdul-malik, sai karamin-su,Abdul-jabar, suna kiran shi da kamal, sai Aisha da ta kasance ‘yar ruko Abdul-jabar, sun taso cikin wadata da had’in kai da tausayin juna, babu raini ko kad’an a tsakaninsu sai girmamawa da tausayin junan-su,..
suna rayuwa ne acikin garin Abuja…

Abdulmalik Ibrahim Ahamad, gawurtaccen jami’in tsaro ne na kasa da kasa, jarumin gaske mai aiki da dukkan nin gaskiyar-sa, ya kammala karatunsa a kasar India tun daga matakin secondary har zuwa matakin da yake yanzu, inda ya-samu horo mai tsanani tare. da takardar shaidar cika (Deputy Commissioner of police) saboda tsananin jajir-cewar sa-ne, ta fannin gaskiya, rukon amana, gomnatin kasar India ta nemi alfarmar yayi mata aiki a nan..

Jami’an tsaro ne kewaye da gawar wani babban jami’in tsoro na ‘yan sanda, inda sauran mutane ke hargowa, jami’ai na tattare-su wad’ansu acikin su kuka suke sosai, kowa na fad’ar albarkacin bakinsa, wasu kuwa na fad’ar kyawawan d’abi’un babban jami’in. tare da tsananin aiki da gaskiyarsa.

Ta bangaran ‘yan jarida (jonalist) kowa burin shi ya d’auki rahoto akan kisan gilar da aka-yiwa wannan babban jami’in tsoro. G I G d’in ‘yan sanda Muhammad isma’il adam!!
Duk da cewar ba’asan wanda ya aikata wannan laifin ba, kuma ba-wanda zasu iya tuhuma da aikata, wannan kata’barar. cikin kankanin lokaci labarin ya baza duniya, gidajen-tv, radio, social media.
Yayin-da yanzu ba’asan manufar kashe wannan d’an sanda ba, rikici ya barke sosai acikin garin.

Babbar government house d’in a cike take makil, manyan mutane alkalai, ‘yan jaridu, sojoji ‘yan sanda.
Hayani-ya sosai ke tashi a cikin ta.

Ta cikin mutanen nake ratsawa dakyar nasamu wurin fakewa domin kwaso muku labari,
Wani babba daga cikin manyan, SPEAKER dake wurin, ya fara magana kamar haka
“Da Allah ya isa, a saurara” A halin yanzu mai girma babban minister zaiyi jawabi.
lokaci guda wurin yayi tsit, tamkar ruwa ya cinye mutan -wurin.

gyaran murya-yayi kafin yace, “Nida mai girma mataimakin governo, mun had’u akan hukunci d’aya, idan wannan majalisa ta amince, nan da wata biyu ko uku, zamu kama wanda ya kashe G I G d’in ‘yan sanda. sannan zamu-san miye manufarsa, daga karshe muna mika sakon ta’aziyar mu ga iyalan gidansa!!, shi-kuma allah ya gafarta masa, hakika munyi rashin adalin d’an sanda, mai aiki da gaskiya, kuma wanda yasan aikinsa.”

d’aya daga cikin manyan ‘yan jaridun ne ya mike, tare da cewa, “Allah ya taimake ka, amma kafin wannan mu al’umma muna-so muji wanne hukunci kuka yanke?.”
“Munyi magana da babban Commissioner-nan ‘yan sanda na kasar India, sunce zasu turo mana babban jami’i mai na garta zuwa wannan jiha-tamu…”
D’aya daga cikin manyan ‘yan majalisun ne, ya mike yana fad’in, “Nagartattun jami’an da muke dasu a nan (Nigeria) basu isa bane?.”
“Babu shakka muna dasu, amma yanzu an samu sama da wata guda ko bayani d’aya basu kawo ba!!”

“Me za’ayi to?”

. “Kamar de yanda akai a jihar kaduna, kan hanyoyin mu na tafiye-tafiye, da sauran garuruwa sun ‘baci da miyagun mutane ‘yan ta’ada kidnapping, jami’i me tarun lambobin yabo, yazo har kasar nigeria ya fatattaki wasu daga cikin masu garkuwa da mutane, ya kama babban tantirin da ya d’aure musu gindi. Magana nake akan, jami’in da yafi kowanne cikar gaskiya izza da nagarta.”
“Waye kenan?.”
“Amma kusani-doka da Oder bata amince a kawo wani jami’in bincike daga wata kasa zuwa wata kasa ba!!,
Shima ai d’an nigeria ne!! kuma yana da hakki ya jagoran-ci kasar-sa.”

ABDUL-MALIK IBARAHIM AHAMAD!

wanda asalin-sa d’an yankin nigeria ne, karatu ne ya-kai shi can.
“Toh duk da haka baa amince da wannan, shawara ba kuma bamu amince da kawo d’an-sanda daga wata jihar ba”

“Toh sai mu mika al’amarin ga cibiyar bincike ta kasa! a karkashin ita wannan cibiya sai a kawoshi cikin wannan jiha. ta yanda zeyi bin-cike akan wannan kisa kuma ya dakatar da duk wani cin hanci da rashawa da muke fama dasu a cikin wannan kasa, tare dakatar da shaye-shayen miyagun kwayoyi da aikata fyad’e a kananun yara mata. Idan cibiyar bincike ta amince zamu aika da wasikar amincewa zuwa ofishin ‘yan sanda na kasar India.”

Kai ya jinjina alamar godiya ga jama’a.
nan wurin ya rud’e da tafin al’umma, ‘yan jarida kuwa, haska na’urar aikinsu suke a wurin.

Matar Sadiq

Yar Mutan Bauchi

Izina 2 >>

2 thoughts on “Izina 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×