Skip to content
Part 2 of 6 in the Series Izina by Hkadija B. Ahamad (Matar Sadiq)

INDIA ➡ ABDULMALIK POV.

“Abdulmalik….”

A-hankali naji baturen ya kira sunan-shi, amsawa yayi tare da kara-sowa ya mika masa hannu-suka gaisa, cikin nutsuwa baturen ya ciga-ba da tambayarsa

“A ina suka kwana akan maganar-su ta jiya?”

Ajiyar zuciya ya-yi sannan ya-fara masa bayani cikin yaran indian-ci;

. “An bani damar zuwa Nigeria domin na gabatar da wani bincike, akan mutuwar wani babban jami’in tsoro, kuma ina-saran in-sha Allah zamu-yi nasara!…”

ajiyar zuciya baturen ya sauke, cikin sanyin murya yace

“Allah Ubangiji ya taimaka”
“Ameen”
ya amsa
“Abdulmalik amma nasan zanyi kewar-ka!!”

“Na gode Betron”

Duk cikin yaren indian-ci suke wannan hirar, betron ya kama hanyar-sa ta komawa gida.
shikuwa kai-tsaye cikin barrack d’in ya nufa.

Ta-baya yaji an-rugume shi, hakika ya gane kamshin turarenta hakan yasa-shi juyo-wa a fusace, k’ara d’aure fuska yayi sosai, ita-kuwa cikin tsananin jin dad’i ta saki wani lafiyayyan murmushi, Sanye take da riga da wando na ‘yan sanda, saide iya wandon-ne na Uniform, kowa de yasan kalar kayan aikin ‘yan sanda na-india sai wata matsatsiyar top dake jikinta blue color wacce ko cibiyar-ta ba ta rufe ba, sai farar jacket a saman top d’in. hannu tasa zata shafi lallausan sajen da yayiwa fuskar-sa kawanya. a-zafafe ya buge hannun-ta.

cikin bacin rai ya fara magana,

“Wai-ke Anushka How many times, zan daina fad’a miki da ki dena kuskuren ta’ba jiki-na?”

Murmushi tayi kafin tace,

“No the first time sannan Abdulmalik, I will never tried, am say I love you duk fad’in barracks d’in-nan, nafi kowa son-ka, In-fact duk wata Macen da zata-ce tana Son-ka a fad’in duniyar nan, karya take ni-ce nan masoyiyar-ka ta gaskiya”

Ya yamutsa fuska tare da dauke idanuwansa daga kanta
Cikin sanyi tace,
“Plz I beg you Malik, ka-soni koda kad’an ne!..”

ta karisa maganar kokarin shigewa jikinsa, da sauri ya ban-kad’eta, har ta kusa kifawa k’asa…

“Plz Help me Dan Allah ki daina, sam addini-na ya-yi hani da hakan’ kuma aure baze-yuwu tsakanina dake ba. tun-da addina-na da naki ba d’aya bane!!”

yana fad’in haka ya-jahh dogon tsaki, ya wuce. Anushka kuwa bak’in ciki-ne ya cika zuciyarta, nan ta durkushe a wurin ta saka wani marayan kuka.

“Sam yak’i gane, cewar ba laifina bane- meyasa na kasa cire-shi a raina? In-fact da ina da ikon cire soyayyar-sa a raina dana cire!! “oh my god” what happen Anushka?. me-ke faruwa dani?”

kaitsaye babban office d’in shugaban shi ya nufa, cikin risinawa yayi masa gaisuwa irin tasu ta ban-girma, mumurshi yayi tare da-masa alamar ya zauna.
Cikin yaran da yafi kowanne fahimta ya fara masa bayani wato turanci.
Malik mun za’be kane a matsayin ka na hazikin d’an sanda deputy commissioner, mai gaskiya kuma wanda ya-san aikin-sa. kuma aikin da zaka-yi, ba’a iya al’ummar ka bane, itama kanta nigeria k’asar kace!!, na yarda da aikin-ka kuma na aminta da gaskiyar-ka.. kuma ka-k’ara gujewa kar’bar corruption a wurin al’umma, domin hakan na matukar ruguza k’asa tare da al’umma.
gobe iwar haka jirgin-ku zai tashi, zuwa nigeria, nasan kana cikin farin ciki da wannan tafiya, dad’i da k’ari za’aje ka kalli ‘yan uwa da abokan arziki!!.
.. wasu manyan files ya mik’o masa guda biyu, kar’ba-yayi tare da sa hannu, ya ajiye masa a gabansa.
Mikewa ya-yi, tare da alamar jin-jina masa, tare da bashi hannu sukai musabaha a tsakaninsu.
Cike da farin ciki, ya juya zai fita.
Cike da kulawa, ya furta cewar, malik ka-kula da kyau, kuma kasan aikin da ya kai-ka…
murmushi yayi kawai, ba tare da yace komaiba’ ya fi-ce.

NIGERIA K’ASA ‘DAYA AL’UMMA D’AYA

ABUJA STATE POV.

Ta cikin katon glass d’in motar, ya-ke karewa Nigeria d’in tamu kalloh, tunda ya-shigo cikinta yake jin wani irin zafi duk da tsananin sanyin Ac din da motar ke dashi, ba abun da zuciyarsa ta karantar-dashi illa, wannan irin tsananin zafin da muke fama dashi, bakomai ya-jawo shi ba, face aikata tsananin fasadi a bayan ‘kasa.
zina, shaye-shayen miyagun kwayoyi, kashe-kashe, fyad’e a kananun yara mata, shirka, zalunci, lallai allah ubangiji mai hakuri-ne da bayin-sa, allah ubangiji yasa mufi k’arfin zuciyar-mu.

Yana cikin wannan tinanin, yaji drivern da ya d’auko shi airport na rangad’a salati, hankali a tashe, ya zare glass d’in dake idanuwan-shi.
cikin tashin hankali yace da drivern
“Dakata!! dakata!! motar na dakatawa sauran motocin jami’an tsaron dake biye dashi, suma suka-ci burki.

Da sauri ya fito daga cikin motar, -hankali a tashe yayi kan wannan matar da a-gaban idonsa, wani mai mota ya bigeta kuma ya tsere. Mutane sosai a wurin kuma an rasa mebin sawun motar, ko kuma a samu mai d’aga dattijuwar matar.
Illah wata kyakkyawar matashiyar budurwa da take sanye da bakar doguwar riga ta abaya.

Cikin tashin hankali ya juyo a fusace ya bi jami’an tsaron da kalloh, cikin takaici yayi musu alama da-subi bayan motar.

Hankali a tashe take ko’karin d’aga matar amma ta kasa!!, ganin hakan yasa dole yasa hannu ya taimaka mata, kai-tsaye cikin motarsa aka nufa da-ita, kaitsaye babban asibiti suka nufa.

Cikin tashin hankali, yarinyar tace, “Dan allah ka k’ara sauri, numfashin-ta d’aukewa yake, zata iya rasa ranta!!” ganin numfashin-nata yana k’asa sosai, ba tare da taji wata kyama ba, ta saka bakin-ta tana me kara zuk’o mata numfashin tare da daddana saman kirjinta!

Cike da tashin hankali shima ya fara yi-wa drivern magana, cikin kankanin lokaci da bai wuce minti biyar zuwa wasu dak’ik’un seconds, suka karisa cikin asibiti mafi kusa dasu
Kai tsaye emergency ward aka-yi da ita, nan take ya saki kud’i da yake privet hospital ne, ganin hakan yasa aka fara bata taimakon gaggawa.
Bai iya barin asibitin ba sai-da yaga ta far-fad’o, tare da barin wannan matashiyar budurwar da ta tsaya akan komai kafin ya dawo. har ya tafi, ya kuma juyowa ya tambayi sunanta.

Cikin in’ina ta-bashi amsa da “INTASAR ni ‘yar jari….” shuru tayi batare da ta-k’arisa maganar ba.

Bai-gane me-take-son fad’a ba, kuma bai damu da hakan ba. juyawa yayi, kafin ya iso drivern ya bud’e masa motar.

Cikin wata katuwar unguwa ta masu kud’i, mulki, ‘yan siyasa, ba-wanda bai tara ba. tun daga farkon mashigar-ta gate ne, har zuwa karshenta. ana kiranta da suna (ESTATE)

“Hajiya! wai ina yaron-nan ne ya tsaya haka?.”
ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa toh kaima de ka fad’a, tun d’azun mukai waya dashi, yace dani gashi nan nanda minti goma zai shigo gida, amma yanzun kusan awa biyu da maganar!!

Daddy-ne ya zaro wayarsa daga cikin aljihu, kai tsaye numbern-malik ya danna.
Da sauri ya kalli mami dake tsaye tana jiran amsar-sa, kinga-fa hajiya wayar yaron-nan a kashe, anya lafiya kuwa?.
Daidai lokacin ya turo katuwar kofar yana fad’in lafiya lau daddy.
Da sauri mamin nashi ta rungume-shi tana fadin.
“Oh yo-yohhhhhhh”-
. “oh-yo-yooooh!!!”
. “Abdulmalik sannu da zuwa!!, sannu da zuwa, kai!! Abdul-malik mutanan india kaga yanda kayi kyau?”
Murmushi yayi cikin harshen turanci ya fara magana,,
“I was annoyed whenever i remembered you!!, so I think sai naga abun da na-tafi nema-ma yana da amfani!!”
Dariya daddy yayi tare da cewa “kinji-maganar deputy commissioner!!”
Dariya yayi kad’an har fararan hakoranta suka bayana
dai-dai lokacin ma’isha ta turo kofar ta shigo, cike da mamaki takura masa ido, dan har-yanzu bata waye shi ba, sai-de ta tabbatar wannan shine YA MALIK.
Cike da risinawa tace,
“Wow Welcome My Broz, I am very happy gaskiya nayi farin cikin ganin -ka”
Murmushin yayi tare da cewa,
“Hope you everybody is fine”
“Yes is fine!…”
. “Mom wannan Aysha ce ta girma haka?”,
“Eh wllh, kasan girman d’an mutum ba wahala..”
dariya tayi, tare da maida kanta k’asa tana murza fararan yatsun hannunta wanda suka-sha jan-lalle
. “Ya karatu?”
Fad’ad’a murmushin dake fuskarta tayi tana fad’in, “hmm yaya ai mun-gama karatu, yanzun haka munfara aiki”
. “Toh allah ya taimaka!”
Amin!!
“Ina sauran ‘yan uwan-naki?”
. “Dazun suka fita da ya mohuseen!!” “ayya basu san dawowa ba koh?” “a’a sun-sani mana!!”
kafin ta karisa rufe bakin-ta, ya saki murmushi jin muryar kamal ya shigo!!
“Wow!! Wow!!! longest time dear, jami’in India..” da sauri kowanne-su ya tafo kuma aka rasa waye yafi wani farin cikin ganin wani a tsakaninsu!! cikin tsananin kewa da begen juna suka rungume junansu.. ko wanne acikinsu fuskar-sa d’auke da murmushi da tsananin farin cikin ganin junan-su..

sun dad’e a falon suna hira, kafin momy ta umarce shi da ya tashi yaje-yayi wanka,
tunda ya shiga bangaran da aka ware masa, yake bin wurin da kalloh badan komaiba sai dan irin tsananin dukiyar da aka kashewa iya wannan ‘bangaran!! hmm rayuwa kenan kamar baza’a a mutu ba. ya dad’e a zaune a bakin katon royal bed d’in, kafin ya mik’e ya nufi bathroom.
Yakai tsawon minti goma zuwa shabiyar, daga bisani ya fito d’aure da towel a jikinsa. jikin katon glass mirror d’in ya tsaya yana goge sauran ruwan da ya kwanta saman gashin faffad’an kirjinsa,

Sai a yanzun na kare masa kalloh farine sosai dogo bafulatani gaba da baya, kyakkyawan gaske-ne irin kyawun nan mai masifar d’aukan hankali, wanda idan ba sani kai-ba sai ka iya rantsewa da allah tun asalinsa ba’indiye-ne yana cikar zati da tsananin kwar-jini. ko ina na jikin-sa na murd’e ne irin na cikakkun maza. Cikin Kanan kaya ya shirya, farin jeans da blue d’in jacket. wani matsiyacin turare mai dad’in kamshi da tsada ya shafa a jikinsa!!
A k’agauce ya-fito saboda yanda ya tina, yabar INTASAR acikin asibiti, duk yanda mami taso ya tsaya ya-ci abinci k’i yayi, dole ta hak’ura ta barshi.

A tsaye ya sameta a bakin emergency ward d’in, hankalinta tamkar a d’age, agogon hannuta take ta faman dubawa,
Da sauri ya k’ariso inda take,
“Yadai lafiya kuwa?.”
“Eh lafiya”
“Ya me-jikin?.”
“Da sauki harma ta far-fad’o ma, yanzun haka an-kaita d’akin hutu.” bayan-ta yabi dasauri, har cikin ward d’in!!
““Sannu Mama ya jikin naki?.”
Dakyar ta iya furta cewar, “Sannu yaro allah yayi maka al-barka!!”
Cikin dagulalliyar hausar-sa, yace “Amin Mama, abune yazo da ta-kaddara!!”
“Hakane Allah ma ya kare..”
“Yanzun haka an kirani-cewar an kama yaron da ya bige-kin.”
“Hmmm, ku-sake shi yaro ba laifinsa bane laifi na-ne, ni-ce bana cikin hayacina!!”
cike da mamaki yace, “Bangane ba Mama, kince hankalin-ki baya tare dake..”

Tayi ajiyar zuciya sannan tace,
“Y’ata-ce a kwance a gida ba lafiya!!, wannan shi yafi d’agamun hankali.”
Cikin takaici, yace “But why can’t you take her hospital?. dan meyasa mara lafiya yana kwance a gida ba lafiya, baza’a kawo-shi asibiti ba, Why?”
cikin muryar kuka tace, “Ni rashin lafiyar ta-ta shi yafi damuna a-yanzu!!, ya cuceta ya keta-mata haddi!! ya ‘bata mata rayuwa, Allah ka sakama-na, ya ‘bata mata rayuwa Allah kasa-kawa ummita!!”
cike da tausayawa, ya maida hankalinsa gareta sosai,

“Stop crying please, ba kuka zaki ba Mama, Plz tell me what happen? sanar mun me-yafaru, yanzu wani hali ake ciki?”
A hankali ta yunkura ta tashi, zama tayi tare da mike sawayen-ta saman gadon, da taimakon Intasar ta sanya mata pillow a bayanta.
Cikin kuka ta fara magana,
. “Kona fad’a maka yaro ba abun da zaka iya-yi, domin wannan azzalumin talaka bai ta’bayin shari’a dashi ba!!, yaci nasara-ba.saide allah-ya’isa allah yabi-mana hakkin-mu.

Matar Sadiq

<< Izina 1Izina 3 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×