Skip to content
Part 4 of 6 in the Series Izina by Hkadija B. Ahamad (Matar Sadiq)

Cike da mamaki ya kura mata ido,
“Aisha!”
ya ambata a hankali.

“Na’am Yaya!..”
“Karatun lauya kika-yi?”
kai ta jin-jina masa alamar eh?.
“Miye burunki akan wannan aikin naki?”
Ta murmusa kad’an tace,
“Babban burina bai wuce na taimaki mata ‘yan uwana ba masu matsala irin wacce ta faru dani a baya, zuciyata baza-ta’ba yin farin ciki ba hawayen da-suke zuba a idanuwana baza-su daina zuba har sai ranar da fara cika burina, naga an-rataye duk wani mai laifin keta-haddin ‘ya mace, a sanadin wannan bak’in cikin na rasa iyaye-na, mahaifiya-ta da wannan bak’in cikin ta mutu a ranta. bani da wata hanyar da zan-share mata hawaye duk tana kwance acikin k’abarinta sai-ta wannan hanyar. bani da wata hanyar da zan goge wannan bak’in fentin acikin zuciyata sai-ta wannan hanyar.
“abun-ka da mace mai rauni, tuni sabon kuka ya ‘balle-mata

“a baya idan na tino wannan takaicin zama nake nayi kuka, ganan mami, ita ke kwantar-mun da hankali, tana fad’amun cewar kuka bai-dace da mace kamata ba.

“Daga baya gane lallai kuka bashine mafita agare-ni ba, akwai sauran mata da yawa wanda hakan ke faruwa-dasu, kuma ba’a daina aikata laifin ba har-yanzu. tilas na tashi na yak’i wannan kata’barar. domin ceton sauran k’ananan yara mata masu tasowa..
“kuma nayi alkawarin bazan ta’ba bari mai k’arfi ya tauyewa mara k’arfi ‘yancin-sa ba..

“murmushi yayi-cikin lokaci k’an-k’ani ya-k’ara jin ta burge-shi kuma lokaci guda yaji ta shiga zuciyarsa!! niyar-ki mai-kyau “i’sha” allah zai tamake-ki, kuma insha allahu zan damk’a case d’in yarinyar a hannu-ki.

“Cike da tsananin farin ciki tace da gaske, ya malik?
. “Yeah but dole sai-kin daure!!

Yaya toh, miye sunan yarinyar?.”

“Ummita”

Ya-kamata muje gidan-su da wuri ya malik, ranar Monday zamu-shiga kotu, akan case d’in wata yarinya, kuma nida uncle zamu tsaya..
Ya-kamata na fara samun hujjoji akan ita ummita..
In-sha allah zan kai-ki gidan..

ABUJA
ISHAQ POV.

Tafiya cikin k’aton dank’areran gidan-nasa, wanda mislta had’uwarsa ‘bata lokacine
Zagaye gidan yake yana duba lafiyar duk wasu tsirai dake gidan, har yayi gaba ya hango-wata flower wacce yau da a-lamu ba’a bata ruwa-ba.
Rai a bace ya kwalla kiran mai-gyaran flower-n. da gudu dattijon ya ta-so dan yasan halin wanda yake-aiki a k’ar-k’ashin-sa.
Ciki da risinawa, ya durk’usa har k’asa yana fad’in allah ya taimake-ka gani..

Mik’e-mik’e, mezan -gani dattijo-nace mezan-gani
Cike da tsananin tsoro, yace dan girman allah alhaji kayi hakuri.
Cikin tsananin bacin rai, da d’acin zuciya ya zabga masa wani gigitaccen mari.
Tsananin zafi da rad’ad’in marin yasa-shi dafe kuncin-sa
Dattijon banza dattijon wofi wanda baisan darajar dukiya ba, akan me na d’auke ka aiki? saboda ka-bawa flower ruwa dubi yanda ka kyaleta ta mutu!!
Wllh alhaji ba laifina bane, laifin-masu dashe-ne, sune basu dasata takama ba!!
Toh za-ka bar gidan-nan daga yau, ka kwashe naka ya naka na kore-ka
Cikin tashin hankali ya-fara magana dan allah ranka ya-dad’e kayi hakuri wllh ba laifina bane kayi hakuri. wllh yalla’bai a gidan-ka muka dogara nida iyalina.
“Kai tsoho bari nagaya maka rayuwar wannan flower-r tafi rayuwar ka kaida iyalin-naka gaba d’aya.
Saboda haka fice mun a gida, ko nasa karnuka suyi kaca-kaca da kai a nan wurin!!,
“toh na gode yalla’bai, ko kwana biyu ka barni na k’ara tunda yanzu saura kwana biyu ka biya-ni albashi-na.
Wani mugun-kalloh ya watsa masa, tare da cewa bazan biya albashin ba, na cinye..
Kuma kayi gaggawar ficemun a gida kafin na fito. yana fad’in haka ya juya ya barshi a wurin..
Kai-tsaye motarsa ya nufa, da sauri drivern ya taso, ba tare da yace dashi ga inda zasu-je ba, ba tare da shima ya tambaye-shi ina-zuwa-ina ba, yafigi motar.
Cikin tsoron amsar da ze-bashi ya-ce yalla’bai ina zamu je?.
Makaranta!!
haka kawai ya fad’a ba tare da ya-k’ara da cewa komai-ba cikin wata katuwar university suka-kutsa kai. mai dauke da manyan d’alibai kala-kala daban ‘yan-mata, samari, da zawarawa!! tunda suka sa-kai ya rage gudun motar ya fara driving d’in-ta cikin nutsuwa.
Wasu d’alibai daga nesa, suna hango motarsa suka koma gefe, suna famar tsine-masa albarka.
Wata wacce aka kira da suna zainab. tace wllh allah ya-isa tsakanina da wannan azalumin mutumin, mara mutunci wllh baze-ga dai-dai a rayuwar-sa ba..

‘Dayar gafenta tace “keh zainab wllh ai duk laifin-kine!! taya zaki kyale wannan maganar haka? hmm wllh inasa ran duk cikin class d’in bawanda yake cin fiye da makin-d’in da kike ci, amma daga zuwan wannan malamin ya fara cutar ki.. kuma a wannan exam d’in ta jiya da akayi bawan-da yayi sama da abun da kikai, amma ya kashe miki”.
. “Hmm sadiya kenam, ki bari kawai’ ai da-ga baya ya tura wai nazo same-shi a office”

“Ki-same-shi a office?”

“Eh haka-de yace!!”
. “Ok to kinje-ne?”
“A’a banje-ba!!”
“baki-je ba, toh miye amfanin hakan?”
“Haka kawai, amma inaso naje” “Ok toh ki-zo muje yanzu mu same-shi”
Tare suka jera da sadiya, suna tafe suna hira, har cikin k’aton office d’in..
Sallama sukai bakowa acikin office d’in sai shi kad’ai wanda shima yanzun-ne shigowar-sa.
Tun-kafin su ‘karasa shigowa, ya daka musu tsawa’ wanda tasa dukkan su razana. “Bance kizo-mun da kowa ba, ke kad’ai nake buk’atar na gani idan ba haka ba, ki juyo bazan gyara making d’in ba”
Kallon kalloh sukai da sadiya, zainab tace, “kiyi hakuri sadiya ki-jirani a waje”
“Ok bakomai, amma ki kula?”
“Kar-ki sake ki tsaya- mun a bakin office, ki tsaya acan”
Dogon tsaki ta-jahh a ranta ta fice..
Saida ya tabbatar tayi nisa da wurin yace da ita ke-kuma zainabu dawo nan ki zauna. cike da tsananin mamaki ta zauna a kujerar da-ke fessing d’insa.
Tare da mik’a masa takardar, “Malam na-kawo ne saboda a gyara mun wannan fefar, malam ka duba da kyau sosai’ ba abun da banyi ba wad’ansu-ma wanda basuyi komai a paper sun-fini cin marking”
Kar’ba yayi yana murmushi, cikin salon mugunta yace “ai wannan, takardar taki da akwai da babu duk d’aya ce!!”
Cike da mamaki ta kalle shi tare da cewa
. “Malam bangane ba, yazaka-cemun takardata da akwai da babu duk d’aya ce. Kar-ka manta wannan sakamakon takardar yafi kowane darasi muhimmanci, kuma wannan itace shekarar-mu ta karshe!!”

“. “Eh baki-ci ba, amma idan kin-so hakan zakifi kowa ma cin marking a makarantar-nan, amma da sharad’i!!
sharad’i kuma malam!!, su sauran d’aliban kafa-musu sharad’i kai suka-ci paper!!”

. “K’warai wad’anda-ma suka fiki kyau-ma kuwa?.
“sharad’i ne bawani mai wahala ba, ba kuma na tashin hankali ba, mai sauk’i ne, kamar shan ruwa
Amma idan kni-k’i, ba abunda zan-iya taimaka-miki dashi, dole ki k’ara maimaita wannan makarantar, kuma kud’in da kika biya ya tashi a tutar babu. ni tahir ba ruwana dan kin fito da carry over!!”

. “Subahanallahi Malam bangane abun da kake nufi dani ba, nifa ba neman taimako nazo gare-ka ba, hakkina da ka danne-mun shina biyo sawu..
Sam bangane inda ka dosa ba?”

Dariyar mugunta yayi tare da cewa, abun-da nake nufi, saide ki-sayi wannan making d’in, amma kuma bawai da kud’i ba.. surar-jikin-kima kad’ai ta ishen..
A zabure mik’e tana fad’in
Subahanallahi a’uzubillahi, wa’iya zubillah, allah ya tsare-ni ai tunda ban fahimci inda ka dosa ba sai yanzu. to bazan amince da wannan yaudarar taka ba, kuma bazan bari ka cutar dani ba, sannan bazan yarda ka cinye-mun marking akan hakkina ba, to tabbas zan-kai k’arar ka izuwa sama, matukar baka gyara making d’in da ka zalunceni akayi ba. wllh baka-isa kaci bulus ba..

Da-wani mugun kalloh ya bita, tare da cewa kije ki turo duk uban da zaki turo-ya kwata miki marking a hannu-na, ina nan ina jira, ba sama ba kikai-ni k’asa, bawani ma’aikacin da ya isa yazo ya tinkare ni, akan na hanaki marking..
An fad’a miki sauran da suka samu marking din a banza suka same-shi

“Cikin muryar kuka tace, “Ok haka ka fad’a?”

“. “Haka na fad’a”
“Ok shikenan zaka-gani, wllh bazan kyale wannan maganar haka ba”
“Fi-ce ki bar-mun office, a sararriya, mara rabo’ kuma da kan-ki sai-kindawo nan wurin na baki daga nan zuwa sati d’aya”

Cikin tashin hankali ta fito daga cikin office d’in.
Da sauri sadiya ta tare-ta tana fad’in “innalillahi wa’inna illaihir raji’un zainab lafiya?”

“Sadiya ba lafiya, ina cikin tashin hankali, wannan ita kad’ai ce jarabawa-ta ta karshe, da ita kad’ai na dogara, amma wannan azalumin mutumin.. bansan haka yake ba!!”

“Subahanallahi k’awata wani abun yayi miki?”
“A’a wai sena yarda yayi amfani dani, kafin naci jarabawa!!”
“Wa’iya zubillah”

. “Kuma ya fad’a mun wai na turo uban wanda zai kwata mun marking d’in a wurin-sa. sadiya ya zanyi ko na kai report sama ba abun da za-suyi case d’in ya sha faruwa, amma abun bai saki zani ba”
“Zainab a matsayina na babbar aminiyar-ki ban-yarda ba, ban amince ba’ ko mezeyi kar ki yarda da bukatarsa, mu kuma zamu-san abunyi, allah ya-fi k’arfin shi. daina wannan kukan kwantar da hankalin-ki, Allah yana bayan mai-gaskiya.

Matar Sadiq

<< Izina 3Izina 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×