Bayan shi tabi da kallo wasu hawaye masu zafi suka biyo idanuwantaa zahiri ta furta,
“Allah ya'isa tsakanina dakai Anwar, ka cuceni ka lalata-mun rayuwa, ka rabani da iyayena, ka jefa rayuwata cikin wani hali, wanda nake ji a yanzu bazan iya jure rayuwa ba tare da namiji a kusana ba, ka rabani da zaman gaban iyaye, soyayyar ka ta rud'eni na mance daraja da mutuncina na 'ya mace, karshe ka jefa rayuwata cikin mummunan hali na shaye-shaye, na neme ka da maganar aure ka nuna mun kai bazaka auri mace kalata ba, wacce ta lalata. . .