Bismillahir Rahmanir Rahim.
Yarinya ce karama wacce ataikaice ba zata haura shekara 14 da haihuwa ba, take ta aikin kwarara amai a tsakiyar ɗan madaidaicin gidan nasu.
Gidane madaidaici mai ɗauke da ɗakuna huɗu 4 sai kuma ɗan rumfa haka da alama na dabbobin sune sai madafi(kitchen) a gefe sai kuma bayi(toilet).
Amai take kan yi, wata mata ce naga ta futo daga banɗakin nasu, ta ajiye butan dake hanunta sai ta wuce ɗaya daga cikin ɗakunan gidan, tayi kaman ba taga yarinyar dake ta kakarin amai ba. Can wata mata a ɗaya ɗakin ta ɗaga. . .