Skip to content
Part 1 of 25 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

Bismillahir Rahmanir Rahim.

Yarinya ce karama wacce ataikaice ba zata haura shekara 14 da haihuwa ba, take ta aikin kwarara amai a tsakiyar ɗan madaidaicin gidan nasu.

Gidane madaidaici mai ɗauke da ɗakuna huɗu 4 sai kuma ɗan rumfa haka da alama na dabbobin sune sai madafi(kitchen) a gefe sai kuma bayi(toilet).

Amai take kan yi, wata mata ce naga ta futo daga banɗakin nasu, ta ajiye butan dake hanunta sai ta wuce ɗaya daga cikin ɗakunan gidan, tayi kaman ba taga yarinyar dake ta kakarin amai ba. Can wata mata a ɗaya ɗakin ta ɗaga labule ta leko, da taga shigewar wannan matar ɗaki sai ta taɓe baki ta ce “dangin jarababbu kawai haka zaku yi ta fama, idan ta mutu ma ke ce da asara”, sauqe labulen tayi ta koma cikin ɗalinta.

Wata yarinya ce yar shekara 12 ta shigo gidan tana ɗan tsallenta da alama daga aike take, ganin ƴar uwar tata a halin da take ya ta tahowa a saba’in ta yasar da ledar hanunta tayo wajan yar uwar tata tana cewa “Addah me ya same ki? Ina Inna da Mama?” Sai ta fashe da kuka ganin yadda ƴar uwar tan nan ta galabaita, ɗakin Innar tasu ta shiga na wacce ta fito daga bayi amma ba jimawa can ta fito tana kuka tayi ɗakin ɗaya matar.

Muryar matar naji tana cewa “ta mutu mana ina ruwana ita uwar ta bata kallonta ne dangin jarababbu kawai ba zan fito ba, ke hassu za ki fice mun a ɗaki ko sai na ɗau samira nayo kanki dashi” sai yarinyar ta fito tana kuka wanda qarshe ficewa ta yi a gidan gaba ɗaya tana kuka.

Wannan yarinya mai aman kuwa sulalewa tayi ƙasa ta faɗi dan da alama suma ta yi dan ta jikkata sosai.

Ba jimawa wannar yarinya da matar ta cewa Hassun ta shigo gidan ita da wata tsohuwa, salati wannan tsohuwar ta yi ta ɗaura hannu akai ta ce “na shiga uku ni Merama Daso uwar Isa, yanzu dan tsabar rashin kirki da mutanen gidan nan ke fama dashi ace akwai mutane a gidan amma aka bar mun jika za ta mutu” sai ta nufi wajan yarinyar da ta jima da sumewa.  

Mama ce ta fito ɗaki tana cewa “Baba sannu da zuwa yanzu nima nake son fitowa duba ta naga ko lafiya ina sallah naji kaman ana amai”

Ko ta kanta tsohuwar bata bi ba ta ce “ke Hansai zo ki kama mun ita mu kaita ɗakinku” Hassu ta zo ta tallafawa tsohuwar suka kai ta cikin ɗakin nasu jikinta gaba ɗaya ya sake kaman babu rai ajikinta, ita dai Hassu sai hawaye ita kuwa tsohuwa sai masifa take yi

Shigowa ɗakin Mama take ƙoƙarin yi ita kuwa tsohuwan na ƙoƙarin fita, kallonta ta yi ta ce “kin san Allah da girma yake Lami in kika shiga ɗakin nan sai na gwada maki ke karamar ƴar daba ce, munafuka kawai wato in dai ita Indon ba ta san zafin haihuwa ba ke da aka bawa yarinyan ba ki san zafin rashin ɗa ba, kuna gidan nan amma jikata na ƙoƙarin mutuwa.”

Sanin halin tsohuwar ya sanyata ja da baya bata ce komai ba.

Ruwa ta ɗebo a randa tazo ta wuce Mama Lami a kofar, kwafa ta yi ta shige ɗakin.

Yayyafa mata ruwan ta yi tana cewa “ke takwara tashi kin ji ta Allah ba tasu ba, tambaɗaɗɗun iyaye kawai”.

Dogon numfashi yarinyar ta ja, ganin haka sai tsohuwar taji sanyi a zuciyar ta, ta ce da Hassu “ke kuma kin wani tasa mu gaba kina hawaye kaman an ce maki ta mutu, to takwarata ba mai mutuwa yanzu ba ce, ke ma aniyar ki ta biki, tashi ki kawo mun ruwa a roba me ɗumi maza-maza yi sauri”.

Tashuwa ta yi ta fice a ɗakin, inda ta yi sa’an samun tukunya cike da ruwa akan murhu wanda har ya tafasa, roba ta duba ta ɗiba ruwan ta surka sannan ta kaiwa kakar tasu a ɗaki. 

Gefen kayansu tsohuwar taje ta jawo wani ɗan kwali babba, ta cirewa jikar nata kayan jikinta ta lullubeta da wannan ɗan kwalin. Share mata jikinta tayi tass duk inda ya ɓaci da aman da tayin, ta goge ta tass sannan ta ɗauko wani kayan Hassu na taimaka mata suka sanya mata.

Yarinyar ko ido bata buɗe ba, dan tana jin jiki gashi jikinta yayi zafi zau-zau kaman wuta.

Tsohuwar ta ce “Ke Hansai tashi ki je ki kiramun Malam ko Magaji duk wanda kika gani nan ƙofa, ki ce ya zo ya ɗauka mun ita mu je gidana tunda nan gidan neman ranta suke ba sa sonta, to ya isa ni ba zan iya ba ina sonta, in su suna gani za su barta ta mutu to ni duk wata marar mutuncin da ta cika zan nuna mata nawa yafi nata, tambaɗaɗɗun iyaye kawai”.

Fita Hassu ta yi ta nufi kofan gidan, cikin sa a ta haɗu da Magaji, tana ganinsa tace masa “Hamma wai in ji Baba Mero ka zo” amsa mata ya yi suka shigo cikin gidan tare, suka nufi ɗakin su Hassun.

Jin shigowan Magaji gidan Mama Lami da sauri ta yi dakinta ta turo kofar.

Da sallama ya shiga dakin, ganin kakar tasu tsaye kan yarinyar da mamaki ya ce “Baba me ya sami Innai kuma?

Cikin hasala tsohuwar ta ce “to ubana Magaji za ka tsaya tambaya na ne ko zaka mun abunda na kira kamun?”

Sanin masifar tsohuwar sai ya ce “Allah ba ki hakuri tsohuwa” harara ta aika masa da shi ta ce “na ce idan ya ba ni kabi dare ka kwace, ɗan bokon tsiya kawai. Ni ka ɗauka mun jika mu tafi da ita gidana ba lafiyane da ita ba kuma in nabarta a gidan nan duka makiyanta ne kashe mun ita za su yi ɗan gwanda Hansai ma abunka da ƴar uwa har da kwalla ta yi na tausayin Addan ta”

Kwafa tsohuwar ta kuma yi ta ce “Magaji ina dalili in haifi abu in kasa ko kallonsa balle kulawa da shi, ko mutuwa zai yi, amma ni dai matar nan Indo abinda take yi yana cimin tuwo a kwarya, aradu ji nake wataran in bi dare in shaketa kowa ya huta da wannan kayan ciwon zuciyar, wai dan Allah ka haifi ɗa kai ga shugaban masu kunyan ɗan farko sai kaki kula dashi tun yaushe akabar wannan jahilcin ai al’adar ma taci kaniyar ta, mu dai a zamanin mu ba wannan tambaɗewan zagewa ake a kula da ɗa in baka kula dashi ba ubanwa ya maka nakudar sa da zai kula maka da shi? Allah dai ya bawa takwara miji nagari ta yi aure ko ta huta da takaicin wannan tambaɗaɗɗiyar uwa da Allah ya bata”

“Ameen” Hassu da Magaji suka amsa wa baabaa Mero. 

Ɗaukanta Magaji ya yi kaman baby suka fita a gidan suka kama hanyan gidan baba da yake basu da nisa tsakaninsu, suna tafiya sai sababi take har suka isa gidan nata ɗan madaidaici, ɗakin ta Magaji ya shige da Innai ya kwantar da ita a ɗan karamin gadon ciyawar dake ɗakin wanda dama na Innai ne dan mutuniyar baba Mero ce.

Baba ta ce “na gode ɗan nan Allah dai ya maka albarka duk da dai dama ba wani nauyin kirki ne da ita ba, yo to yaushe ma ta samu kwanciyan hankali da farin cikin da zata yi nauyi yarinya kaman a hure ta faɗi, watarana ma aka yi iska mai karfi idan ba sa a ba sai ya ɗauke ta, Allah ya saka miki takwara”.

Magaji ya ce “Allah kara sauki Baba, bari muje lokacin sallah ya yi”.

Ta ce “to angode, kema hansai jeki gidan ki gyara ɗakin naku ko da yake ke ai ɗiyar so ce, takwarata ce ba a son ta” kwafa tsohuwar ta yi ta ɗauki buta ta shige banɗaki”.

Hassu kaman ba taso haka ta kama hanyan gidan nasu ita kanta da take yarinya karama abun na damun ta yadda mahaifiyar tasu ke nuna halin ko in kula akan ƴar uwar tata, haka ma Mama Lami, “Allah ba ki lafiya Adda” cewar Hassu tana share ƙwalla ta shige gidan.

Ta samu mahaifiyarta ta idar da alwala kenan ta shiga ɗaki, Mama Lami ce ta fito dan itama tayi alwalar. Kallon Hassu ta yi ta ce “munafuka ƴar munafukai dangin jarababbu hankalinki ya kwanta ke gaki me ƴar uwa ba kin kira tsohuwar nan ta zage mutane burin ki ya cika, Ita uwar taku bata kula da ƴar ta ba sai ni a gayyan soɗi da shishishigi mtswwww” ɗaga murya ta yi dan mahaifiyar su Hassu ta jiyo ta “wai shi mutum gashi bafulatani a haka dai ƴar mutum za ta mutu in dai ni ce zan kula da ita aikin banza an jiqa ba’a tsame ba” Buta ta ɗauka tayi bandaki tana ta mita dan ta ji zafin faɗan Baba Mero. 

Ita dai Hassu ba ta ce komai ba ta nufi inda Addan nata tayi aman ta kwashe ta gyara gurin taje ɗakinsu ta gyara ta ɗauko kayan da aka cire wa Addan nata ta wanke su, Aikin da take kai ka ce ba yarinya ce ba.

Bayan ta kammala gyara komai ta ɗau buta ta yi alwala ta shige ɗakinsu dan itama ta yi sallah.

Jahilci Ko Al’ada 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.