Skip to content
Part 12 of 22 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

Abiy ya isa Canada inda ya shiga taxi ya kai sa gidan yaronsa.

Mai taxi na horn gate man ya leqo ganin Abiy sai ya buɗe suka shigo Abiy ya sallami mai taxi da kuɗin qasar mai yawa, suka gaisa da gate man sannan ya shige cikin gidan.

A main palour ya samu sweedy na aikin rarrashin sweetie rigimanmiya. Ganin Abiy da gudu sweetie ta taso ta rungumesa tana sakin kuka cikin turanci take magana “Abiy ina Ammi na?

Shafa kanta Abiy yayi ya ɗagata sama suka qarisa cikin palourn ya samu kujera ya zauna, sweedy na masa sannu da zuwa cikin turanci, kallon sweetie yayi yace “Muheebbahn Abiy Ammin ki na gida yanzu ma nazo na ɗauke ki na kai ki wajan Ammin ki ne, amma kinsan me?

Girgiza kai sweetie tayi tana murmushi, jan kumatun ta Abiy yayi yace “good girl Muheebbahn Abiy sweetien Ammi, ina so kar wanda ya ɗau qiran yayanku ko da ya qira ku karku ɗauka inaso mu masa surprise shi da Ammi”.

Cikin gamsuwa da batun Abiy sweetie ta rungumesa ta masa peck a kumatu itama sweedy rungumesa tayi ta masa peck ɗin dan sun yarda da Abiyn su.

Sweerie ke sauqowa a benen da zai sada ka da ɓangaren su tana magana cikin harshen turanci “sweedy me kika bawa rigimanmiyan Ammi tayi shir… Maganan bakinta ne ya maqale ganin Abiy zaune a palourn, da mugun gudu ta gangaro ko takalmin hill’s da ta saka bata damu da shi ba tana isowa ta faɗa jikin Abiy tana cewa “Abiy surprise! sannu da zuwa”.

Rungume ta Abiy yayi ya mata peck a goshinta yace “Munawwaran Abiy ya school?

“School lafiya ba daɗi Abiy dan ma an bamu hutu”.

“Yauwá good dai-dai kenan kunga sai mu tafi Nigeria tare wajan Ammi”.

Waro ido tayi tace “Abiy! Darling fa ya hanamu yace kar ya kama qafanmu a Nigeria har sai sun dawo tare da Ammi in ba haka ba zai saɓa mana”.

“Wasa yake muku sweerie, yanzu zamu tafi gobe da wuri in Allah ya yarda amma kar ku faɗa masa muma mu masa surprise”.

Ɗaga kafaɗa tayi tace “shikkenan Abiy Allah ya kaimu amma tunda kazo Abiy ka kaimu yawo”.

Murmushi Abiy yayi yace “duk kuje ku shirya ba na wasta ruwa mu tafi”.

Sweerie tace “ni dai a shirye nake Auta da sweedy ne zasu shirya”.

Abeeyh sama ya haura, ɗakin da yake mallakin sa a gidan ya shiga ya wasta ruwa ya sanja kaya.

Qananun kaya yasa inka gansa ba zaka ce ya haifi DMD ba dan kaman matashi haka ya koma kayan ya amshe sa kuma Abiy ba dai kyau ba dan kusan a wajan sa yaran suka ɗauko rabin kyawun su.

Suka fita Abiy ya kaisu Park ne restaurant ne etc yawo suka dinga yi sune basu dawo gida ba sai bayan isha’i, suna dawowa kowa ta shiga ɗakinta sweetie kuma tabi Abiy dan ta dage a wajansa zata kwana.

Sallolin su suka yi kamun kowa yabi lafiyar gado ya kwanta tunda Abiy yace musu gobe da wuri jirginsu zai tashi.

“Wai me yasa ba zaka ci abinci ba son? Ko bai maka ba ne na dafo maka da kaina” cewar mummy da idanuwanta ke kan DMD.

Shafa kansa yayi mai cike da baqin gashinsa mai stayi yace “habibty na qoshi ne fa”.

“Ka qoshi me kaci?

“Uhmn ɗazu munje gidan Abiy to na ci a can”.

Mummy kallonsa take da mamaki domin kuwa qaryan ma bai amshe sa ba tunda kowa yasan ba shiri yake da matar Abiy ba balle yaci abincin ta, kallon Jay tayi tace “jabeer kunje gidan Abiyn naku?

Jay sosa qeya yayi yana kallon DMD dake lumshe masa ido alaman yace eh, hararan sa yayi kamun yace wa mummy “eh Habibty munje”.

“Shikkenan to” mummy ta faɗa a taqaice suka ci gaba da cin abincin wanda a qarshe shikam miqewa yayi ya haura sama.

Bayan Jay ya gama cin abinci ya tashi yana sunne kai dan yasan mummy ta san qarya suka mata, ya haura saman shi ɗin ma. Yana shiga ɗakin ya tarar da DMD na ta aikin jan tsaki sai ya kalle sa yace “ka sa ni yiwa habibty qarya kai kuma kazo nan kana aikin tsaki kaman tsaka kai da waye?

Hararansa yayi yace “ni inba dalili ba har banson zuwa Nigeria kuma kai ma har da kai a masu hanani, surutu kaman parrot, ni da rabuwa da ciwon kai nasan sai nabar qasar nan”.

Jay ya taɓe baki yace “tunda ance maka bansan hanyan Canada ba dole kace haka, yanzu dai me kake wa staki?

“Layin sweedy nake ta qira baya shiga duka layukansu a gidan baya shiga na driver na kuma ba’a ɗauka, so bansan ko lafiya ba”.

“To ka bari zuwa safiya mugani amma nasan Insha Allahu lafiya lau ne”.

DMD tashuwa yayi ya fita a ɗakin ya tafi nasa dan shi baya iya kwana da wani a ɗaki ɗaya balle gado ɗaya in ba sweetie ba.

Yana shiga yayi shirin kwanciya ya kwanta dan so yake ya tashi da wuri ya samu yayi nafila anjuma.

Abiy da sassafe ya sako su a gaba suka dawo Nigeria inda qarfe sha biyu ya same su a cikin garin Gombe.

Da sallama ya shigo palourn riqe da hannun sweetie, Aunty Amarya na murmushi ta fito sashin ta tana musu sannu ta ɗaga sweetie tana cewa “my baby girl nayi kewanku”.

Sweetie dai taqi sake fiska dan damuwan ta taga Ammi.

Sweedy suka yi hugging Aunty Amarya ta musu peck a goshi tana cewa “babies nawa nayi kewanku”

Duk murmushi suka sakar mata taja hannun su har sashin ta, tasa mai aiki ta kawo musu komai suka ci tare da Abiy suka gama.

Sweetie ta kallesa tace “Abiy ina Ammi fa?

Murmushi ya mata yace “ku kwantar da hankalinku Ammi na Ashaka gidan Hajja jibi zata dawo okay”.

Sweedy da sweerie miqewa suka yi zasu fice a sashin sai Aunty Amarya ta kallesu cike da kirsa tace “babies na ba zamu zauna anan kamun Ammi ta dawo ba?

Kamun su buɗe baki yin magana Abba ya rigasu yana washe baki yace “a’a ki qyale su suje can su huta, Muhseenan Abiy kuje sashin Amminku ku huta ko”.

Qarisa ficewa suka yi ba tare da sunce komai ba, sweetie ta kalli Aunty Amarya ta harare ta sannan ta kalli Abiy tana tura baki tace “ni dai Abiy da kai zan zauna har sai Ammi ta dawo”

Abiy ba yanda ya iya da rigiman sweetie dan sun sakalta ta daga shi har Amminta da yayyunta dan haka dolen sa ya mata murmushi yace “sosai ma Muheebbahn Abiy gaki ga Abiyn ki har Ammi ta dawo my ƴar lukutan yarinya ta”

Tura baki tayi tace “Abiy bana so”.

Aunty Amarya dake zaune ta cika tayi fam ji take kaman ta rufe ta da duka amma sai murmushin yaqe take musu a ranta kuwa ayyana abinda za tawa Muheebbah in Abiy ya fita take “sweetie a wajan Aunty zaki zauna ma ba Abiy ba”.

“A’a ni dai wajan Abiy na tunda banga Darling ba halan shima yana tare da Ammi” ta faɗa tana shagwaɓe fuska.

“Karki damu Muheebbahn Abiy kina wajan Abiyn ki ko!

Sai sweetie ta gyaɗa kai alamun “eh”.

Aunty Amarya murmushin yaqe kawai take amma ji take kaman ta kamata ta cinye ta ɗanya dan tasan yarinyar da shegen sakalci yanzu ko ina Abiy zai je zata ce zata bi sa in dai ta bari yayi nesa da ita to sai in zai shiga banɗaki, shiyasa bata son suzo kuma ta gwammace yayyun ta suzo akan ita tazo gwanda ma in da Ammi ta zo.

DMD sakamakon nafilfilun da yayi tun da ya dawo sallahn asuba ya kwanta shine bai tashi ba sai wajen qarfe sha-ɗaya 11, yana ganin time da mugun sauri ya sauqa a kan gadon sannan ya shige bayi wasta ruwa yayi ya fito ya shirya sama-sama ya leqa ɗakin Jay bai gansa ba sai ya sauqo palour nan ma bai tarar da kowa ba, hanyan ɗakin mummy yayi yana isa yayi sallama aka masa izinin shiga ya shiga ya tarar da ita tana gyara ɗakin nata sai ya stugunna ya gaishe ta yana cewa “habibty kawo na gyara miki”.

Murmushi tayi tace “aikam son ni sheda ce yanda kake gyarawa Ammi ɗaki yayi kyau ɗin na amma dai na hutar da kai zauna abinka na gama ma”.

Zama yayi a bakin gado yace “habibty Jay fa ban gansa ba kuma na qira layinsa bai shiga ba”.

“Yanzu dama bai faɗa maka ba, ɗazu Afreen ta dawo kuma sun tafi Ashaka dan kana bacci ne ma dama Daddyn ku yace aje da kai dan tun ba yau ba yake binsu suje”.

Taɓe baki yayi yace “Alhamdulillahi ina bacci ma suka tafi dan ba inda za ni, yanda halin stohuwar nan yake haka halin Abiy yake ina zuwa za tabi ta isheni da surutu tana zagin baiwar Allah bata ji ba bata gani ba”.

“Allah shirya ka son, mahaifiyar mu ce ke masifa ko?

Shiru yayi bai ce komi ba ya miqe yana cewa “habibty ban karya ba” ya qarisa ficewa.

Tashuwa mummy tayi ta biyo bayansa ta same har ya shiga kitchen da mamaki take kallon sa tace “son ba dai girkin za kayi da kanka ba?

“Eh Habibty yanzu zan gama inaso na fita da wuri naje masallaci akan lokaci na bada abun sadaka a tayamu da addu’a”.

“Oh to shikkenan, amma je ka zauna zan dafa maka me kake so?

“Habibty Allah ki huta indomie ne yanzu-yanzu zan gama nazo muci sai na tafi”.

Mummy tayi-tayi amma yaqi bari ta dafa masa, haka ta haqura ta koma palourn ta zauna tana jiransa.

Indomie ya dafa sai ya soya qwai ya juye duka a plate ya kashe gas ɗin ya fito, a kujera ya samu mummy na zaune, sai ya jawo center table ya ajiye plate ɗin yaje fridge ya ɗauko wa mummy abun sha ya ɗauko nasa.

Mummy tana 1 spoon ta kalle sa tace “son wai kai ka dafa?

Yana murmushi yace “eh habibty ai har rice na iya dafawa”

“Eh lallai in-law tamu ta huta wannan iya girki kace in kana amarci na ɗan 1 month da ake kai abinci ka hutar da mu zaka dinga muku, indomie har da hanta da kifi ga cabbage ni Maryam ina na taɓa gani gwanda in Afreen ta dafa nakan ga tasa hanta wani lokacin amma bansan ana sa wannan duka ba”

Murmushi yayi yace “habibty ki staya santi zan cinye ne yanzun nan”.

Suka gama ci ya tattare komai ya kai kitchen ya dawo palourn suka ɗan taɓa hira kamun ya mata sallama zai je gidan Abiy, mummy ta masa a dawo lafiya.

Yana fita yasa driver ya kai shi gidan Abiy, suna isa ya sallami drivern ya dawo dan dama so yake yazo ya ɗau motan sa dama da na Jay suke yawo kuma ya tafi Ashaka.

Ba tare da yayi knocking ba ya tura qofan palourn ya shiga dan Sallaman ma a ciki-ciki yayi shi.

Hanyan da zai sada shi da sashin sa ya nufa sai kaman ance juyo ya kalli qofan sashin Ammi a buɗe, da mamaki yake kallo yasan dai Ammi ke da key sai Abiy kuma shigowansa bai ga motan Abiy ba dan shiyasa ma ya shigo da qarfin guiwansa don baison abinda zai sa ya haɗa hanya da Abiy gudun kar a samu mastala.

Sharewa yayi ya wuce sashin sa ya bari akan ko Abiy ya sa a gyara sashin ne tunda dama ko bata nan ana mata shara.

Yana shiga ya kullo qofan sa, kallo ya qarewa sashin nasa ganin duk qura alaman anjuma ba’a shigo ba.

Kwaɓe fiska yayi yace “yanzu da Ammi na nan nasan da an gyaramun tunda ita kam na bata key na kuma na hana kowa shigowa in ba ita ba, da ace ma Ammi nanan me zai kawo ni wannan trouble Nigerian rashin Ammi ya kawo ni, Allah ya bayyana ta mu koma”.

Duba time yayi ganin har 12 yayi sai ya ɗauko mooper da abun shara sama-sama ya gyara palourn nasa ya wuce cikin ɗakin sa ya share ya gyara shima da kyau ya shiga banɗaki ya wanke tass, shine bai gama aikin ba har qarfe ɗaya da rabi 1:30 sannan ya cire kayan jikin sa ya ɗaura towel ya shige toilet.

Yana gama wanka ya fito ya je gaban dressing mirror ya shafa mayukan sa ya shafawa kansa ya taje ya taje gemun sa duba lokaci yayi yaga qarfe biyu saura sai ya wuce ya ɗauko manyan kaya wata dakakkiyar jamfa milk color ya saka ya ɗau hula ya kafa.

Masha Allah! Manyan kaya ba qaramin kyau suke masa ba wanda shima kanshi ya sani kawai yanayin rayuwan outside ne da kuma shima bai dame sa ba yafi son qananan kaya.

Ya gama shirin sa da komai qarfe biyu ciff 2:00pm ya feshe jikin sa da turarukan sa iri da kala wanda sanyin qamshin su da daɗin su har hawa kai suke ga kuma sanya nistuwa ga mai shaqan su.

Sweerie na zaune a palourn Ammi sai taga kaman giftawan mutum yayi hanyan sashin yayansu, kamun ta fito kuma ba taga kowa ba taje jikin qofan ta murɗa handle nan ma taji a kulle sai ta juya tana cewa may be idon ta ne kawai.

Aunty Amarya da fitowanta kenan a sashinta tun da taji an buɗe gate kuma ta ga shi ya shigo sai tayi sauri ta fito amma sai ta tarar sweerie ce kawai a palourn, qwafa tayi fuska a haɗe tace “Munawwara tashi kije kitchen ki taya mai aiki girki, ko so kuke mu aurar da ku a dawo mana da ku baku iya komai ba mun sakalta ku?

Sweerie kallon Aunty Amarya tayi kawai ta miqe ba tare da ta mata musu ba tayi hanyan kitchen dan dama ita girki bai dame ta ba ko a can Canada suna girkinsu Ammi ta hana masu aiki yin girki, sai share-share da sauran ayyukan.

Aunty Amarya cije leɓe tayi dan taso ace ta tanka mata ta koya mata hankali amma abun haushi yake bata ko tayi abu basa tanka mata balle ta samu daman ce wa sun mata reni dan yaran staff halin uwar su gare su na haquri da kawar da kai ba ruwan su, juyawa tayi cikin jin haushi ta koma ciki.

Sweerie sun gama girkin tare da mama mai musu aiki sai ta fara jidowa tana kawo wa dinning, ta ɗauko kulan qarshe me cike da ferfesun naman zabuwa(Abiy baya cin kaza) tana fitowa a kitchen kaman daga sama aka jefo sa ta kalli mutum a stakiyan palourn ya nufi waje sai kawai ta sake kulan hannun ta tace “Darling!!

Ɓangaren DMD fitowa yayi ya kulle sashin sa ya nufi hanyar fita har ya kusa qofan palourn ya jiyo qaran faɗuwan abu sai kuma yaji muryan sweerie na faɗin “Darling!

Juyowa yayi mamaki fal ransa yace “sweerie, ke kuma a Nigeria ke da wa?

Qarasowa tayi tace “Darling kayi kyau, Abiy ne yaje ya ɗauko mu sweedy na ciki sweetie kuma sun fita da Abiy ta bisa masallaci”.

Maimaita kalman “Abiy ne ya ɗauko mu” yayi sannan ya kalle ta ransa a matuqar ɓace yace “yaushe kuka zo?

“Ɗazu da safe muka zo, Darling wai kuna tare da Ammi ina take? Ko ka baro ta acan ne?

Kallon ta yayi kawai bai ce komai ba sai ya duba agogon hannun sa yaga ya kusa yin latti, cikin sauri yace “before na dawo ku tabbatar kun shirya” yana faɗa ya fice.

Ko ta kan kulan da ta yasar bata bi ba ta juya ta shige sashin Ammi tana qwala wa sweedy qira “sweedy! sweedy! sweedy!”

Fitowa tayi a ɗakin su tana cewa “irin wannan qira lafiya?

“Sweedy yanzu na ga Darling zai tafi masallaci”.

Da mamaki take kallon ta tace “Darling dai sweerie ba Abiy yace mana suna tare da Ammi ba?”

<< Jahilci Ko Al’ada 11Jahilci Ko Al’ada 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×