"Allah shi ne kuma nima naji mamaki na tambaye sa Ammi fa sai yace bari ya dawo daga masallaci zai yi latti".
"To Allah dawo da shi lafiya dan na mastu na kalli Ammi".
"Amma fa inaga shi kaɗai yazo dan yace mun mu shirya kamun ya dawo wataqilan zai kai mu wajan Ammin ne".
Yana ficewa a gidan ya ɗauki motan sa qirar Toyota mai tinted glasses ya mata key sai babban masallacin juma'a na qofan Sarkin Gombe.
Yana zuwa Allah ya taimake shi ba'a fara salla ba nan ya samu ya lallaɓa har wajan. . .