Jay ne ya shigo ɗakin ya nufi inda yake kwance yana qiran sunan sa "Dude! Dude! Dude..."
Kasancewan bashi da nauyin bacci tun shigowan Jay qaran qofan ya tayar da shi, idanuwan sa a kulle yace "Jay meyasa ka cika rashin ji ne? Ka qira mutum sau ɗaya bai yi ba sai ka qarar min da suna" yana gama faɗa ya miqe ya zauna yana laluɓo wayansa.
Jay taɓe baki yayi yace "daɗin abun ba sunanka na qira ba, koma dai mene tashi mu tafi gida".
DMD bai ce komai ba ya miqe ya shiga toilet. . .