Skip to content
Part 17 of 25 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

Hajja na dawowa cikin Gombe Alhaji ya sauyawa Maimuna makaranta daga na kwana zuwa na aje a dawo, Nura ma ya dawo gida amma shi Mustapha yaqi yace a makarantar zai zauna. 

Rayuwa na tafiya abubuwa da yawa sun faru masu daɗi da marar daɗi inda a cikin wannan halin Allah yawa matar Alhaji-baba rasuwa inda saqon na riskar Alhaji ya tarkata iyalansa duka suka nufi Maiduguri cikin motan su na kansu dan yanzu Alhaji ba abinda bai mallaka ba,sun isa lafiya sai da suka share wata guda har da ɗori kamun suka juyo kasancewar hutun yaran ya qare inda a hanyar su ta shigowa Gombe suka yi hastari kuma duka sunyi rauni, kwanansu biyu 2 a asibiti Allah yawa Maimuna rasuwa, wannan rashin ya jijjiga gaba-ɗaya iyalan Alhaji barinma Mustapha da ke staninin qaunar ƴar uwar sa kuma shaquwa mai qarfi ne tsakaninsu duk da kasancewar basu zauna mai stayi a waje guda ba.

Mustapha na kammala secondary Alhaji ya basa zaɓin inda yake son cigaba da karatun sa, shi kuma sai ya zaɓi India.

Alhaji ganin zuwa lokacin ya girma tunda ya kai shekaru sha biyar 14 sai ya amince ita kuma Hajja ba abinda tace sai addu’an Allah bada sa’a kuma ya kula, Nura dai ya zaɓi qarisa karatun sa a Maiduguri kuma Alhaji da Hajja sun amince da hakan sannan sunji daɗin hakan inda ya tafi Maiduguri yana karatun sa yana zaune a family house kuma hakan ba qaramin daɗi yawa baba-alhaji ba duk da zuwa yanzu ya stufa kucuf.

Mustapha anshirya masa komai ya tafi India yana karatun sa hankali kwance, Hajja zama ba yaranta abun bai mata daɗi ba amma kuma ba yanda ta iya a yanzu kuma tasan bata isa tace zata koma Ashaka ba haka ta haqura.

Sai da aka shekara biyar kamun Mustapha yazo gida inda ya tarar yayan sa ya jima da dawowa gida dan ya kammala degree da master’s nasa akan kasuwanci((business), Hajja tawa Mustapha faɗa sosai akan rashin zuwansa amma ya bata Haquri abinka da uwa da ɗa tuni ta haqura, nan suka ɗugunzuma suka tafi Maiduguri, suna zuwa baba-alhaji yace sam sai sun zaɓi mata a cikin yaran dangi sunyi aure kowa ya koma da mata barinma dai Mustapha dake garin mutanan da basu damu da AL’ADUN musulunci na rufe jiki ba, tunda ya kai shekara ishirin to ya kai riqe mata, Nura tunkan a iso kansa ya bayyana cewar yana son yarinyar Gwaggon sa mai suna Maryam dan tunkan ya koma suke soyayya, wannan abu ba qaramin daɗi yawa baba-alhaji da iyayen su Nura ba nan kuwa aka tsayar da komai tunda abu na gida ne kowa yasan AL’ADUN yaren nasu da yanda suke gudanar da biki sai aka aje nan da wata huɗu kamun Maryam ta kammala secondary.

An kaɗa an rawa da Mustapha amma yaqi yace shi dai a masa uzuri tunda saura masa shekara guda to sai ya kammala zai dawo ya dubi mata inyaso sai ayi auren, saboda qaunar da Hajja kewa yaron nata nan ta tayasa roqon baba-alhaji da mijin nata wanda da qyar baba-alhaji ya amince sannan ya jaddada masa kada ya wuce shekara 1 dan ba yanda za’a yi ya ɓata mata sunan zuria’a.

Sai da suka yi mako biyu sannan suka shirya suka dawo Gombe, Nura cike yake da kewar sahibar sa Maryam wacce yake qira da Habibty, amma kasancewan wayayyen zamani muke sai ya saya mata waya wanda zasu dinga gaisawa.

Mustapha tunda suka dawo yayan sa Nura ke masa magiya akan baya so ayi bikin sa bayanan, ganin yayan sa ya damu kuma shima daman yafi qaunar yaga bikin wan nasa sai kawai ya tura saqo makaranta zai qara 2 months aka hutun su, to abinka da harka ta kuɗi nan take makarantar suka yarda tare da bashi daman yin komai na attending class a online.

Akwana a tashi asaran ma rai yau auren Nura da Maryam saura sati biyu, baba-alhaji ya buqaci da su koma cikin dangi ayi auren acan in aangama sai su dawo, suka tattara suka tafi Maiduguri.

Angudanar da shagulgula da AL’ADUN yaren nasu na kanuri kama daga events na Amarya da kuma Ango su Wushe-wushe da dai sauran su, an ɗaura auren NURA MUHAMMAD NURA & MARYAM TIJJANI ɗaurin auren da ɗumbin jama’a suka halarta kama daga abokanayen Nura har da na Mustapha da kuma manyan masu kuɗi jama’un Alhaji, aka kai Amarya ɗakinta wanda yake nasu aduk sanda suka zo garin Maiduguri.

Bayan mako guda ankammala komai Amarya tayi bankwana da mutan Maiduguri suka kamo hanya da su Hajja duka, anan gidan Alhaji dake anguwan federal-lowcost Nura ya zauna da Amaryar sa Maryam a sashin da dama Alhaji ya gina wa ko wannensu sashin sa a cikin gidan.

Bayan sati 1 da dawowan su Mustapha ya shirya ya koma India yaci gaba da karatun sa, mutan Gombe kuma rayuwa suke cikin farin ciki da girmama juna.

Bayan komawan Mustapha India garin Hyderabad, Telangana ana makarantar da yake take.

Watarana ya fito class da abokanan sa yana tafiya ba tare da ya kula ba sai ya buge wata baiwar Allah, juyowa yayi da niyan bata haquri amma kamun ya buɗe baki guard’s nata suka riqe sa suna surutu cikin Indianci wanda duk abinda suke faɗa yana fahimta, idanuwan sa ya ɗago dan ganin wacce ya buge “fatabarakhallahu ahsanul kaliq” shine abinda bakin sa ya furta ganin yarinya kyakkyawar gaske wacce kana ganinta kaga ba-indiya kuma ƴar mai kuɗi.

Fara ce sol, mai dogon hanci da kuma stayin gashi ga qaramin bakin ta, kayan dake jikinta kaɗai ka gani kasan ita musulma ce ba hindu ba, sanye take da riga da wando indian dress mayafin da yake babba ta rolling nasa yanda ba bar shape nata ko gashinta a waje ba, shigarta komai na mutunci ne sai dai abinda baza’a rasa ba abinka da AL’ADAR qasar da take.

Mustapha bai ce komai ba sannan guard’s nata basu sake sa ba, buɗe baki yarinyar ƴar kimanin shekaru 15 tayi tace “ku sake sa bada saninsa bane” cikin harshen Indianci.

Guard’s ɗin sake sa suka yi suna nuna sa da yasta alaman jan kunne, shi dai har lokacin bai ce komai ba dan Mustapha akwai zuciya, yarinyar ce ta dube sa da murmushi fiskanta tayi magana da English “kayi haquri da abinda suka maaka”.

Sai lokacin Mustapha ya samu daman magana, cikin harshen Indianci yace mata “bakomai”.

Cike da mamaki ta dube sa tace “Wow! So kai ba-indiye ne?

Girgiza kai yayi yace “Nigerian” ya miqa mata hannu alaman su gaisa.

Kallon sa tayi a karo na biyu da mamaki ganin shi ɗan Nigeria kuma yana bata hannu bayan ita ba muharrmar sa ba, a zuciyar ta tace “wannan dabi’an qasar tamu JAHILCI NE KO AL’ADAH oho musu duk wanda yazo sai ya ɗau banzan AL’ADAN su.

Maganan da yayi ne ya kaste mata maganan zuci da take yi.

“Am i not welcome?”

Murmushi ta masa tace “you’re welcome, amma addini na ya hana gaisawa da namiji”.

Wani abu ne ya dirar masa a zuciya tare da mamaki dan tabbas ta burgesa ya buɗe baki zai yi magana sai qira ya shigo wayanta, ɗauka tayi ta kara a kunne tayi magana cikin Indianci wanda kana ji kasan da mahaifiyarta take magana, tana gama wayan ba tare da ta bi takan Mustapha ba ta juya ta tafi guard’s nata na take mata baya.

Tundaga wannan rana har aka kwashe wata ɗaya, biyu har uku bai qara ganin giftawanta ba, kuma gashi soyayyan ta ta riga ya masa mugun kamu dan yarinyar ta shiga ransa shi ko takan AL’ADAN su na dole sai ka auri ƴar dangi kuma Kanuriya ba bi ba son baiwar Allahn nan yake bilhaqqi, ana haka kwastan ranan ya fita yawo da abokanan sa sunje wani Cafe suna zaune kowa yayi ordern abinda za’a basa, waitern ne ya tambaye sa mai yake so? Buɗe baki yayi ya faɗa sai dai da mamakin sa muryan ta ya jiyo a gefe itama tana faɗin “biryani” juyawa yayi yaganta tare da qawayen ta amma duka cikin su ita ce mai shigen mutunci dan yau ma irin shigan ranan tayi.

Yana zaune yana cin biryanin sa ganin suna qoqarin barin wajan sai ya miqe ya qarisa wajan su yana musu sallama, ita kaɗai ta amsa dan sauran kallonsa suke da mamaki, murmushi tayi tace “You again? Sorry that day i gone without saying byee, my Ammaah called me that’s why”.

Murmushi Mustapha yayi yana mamakin meeyasa take son masa turanci bayan ya nuna mata yana jin Indianci, roqon ta yayi ta basa numbern ta, ba tare da tayi musu ba ta basa dan tun kallon sa da tayi ya burgeta, domin Mustapha ya ɗauko kyawun Alhaji da na Hajja duka.

Cikin watanni huɗu masu kyau soyayya mai mugun qarfi ya qullu stakanin Mustapha da Maimoon, mastalan da suka fara samu tun farko daga mahaifiyar ta Hindu ce, dan Maimoon yarinya ce ga shugaban makarantar da Mustapha ke karatu, University of Hyderabad, Telangana.

Dr.Mufaddal shine sunan mahaifinta, babban mai kuɗi ne da India gaba-ɗaya keji da shi ba iya Hyderabad ba, matar sa ɗaya Hindu da yarinyar su Maimoon wacce suke wa soyayya ta duniya gaba-ɗaya kasancewan ita kaɗai suka haifa, su musulmai ne duk da asalinsu ƴan India ne amma ilimin addini ya sanya ba suyi wasti da abinda addini ya umurta ayi ba.

Mahaifiyar Maimoon ta dage nan duniya yarinyar ta ba zata auri ɗan Nigeria ba, dan ita a AL’ADAN su basa auren baqin fata, hukuncin mahaifiyar ta shi mahaifinta yabi yace ba zata auri ɗan Nigeria ba, wannan hukunci na iyayen nata ba qaramin tashin hankali ya haddasa mata ita da Mustapha ba dan har sai da ta kwanta ciwo, kusan wata guda tana asibiti akan soyayyan Mustapha wanda mahaifinta Dr.Mufaddal ganin yana qoqarin rasa yarinyar sa akan abinda bai taka kara ya karya ba nan yace ya amince, da amincewar mahaifinta ko kwana biyu bata qara yi a asibiti ba ta warke nan yasa ta aiko masa Mustapha, cike da ladabi ya amsa qiran Mahaifin Maimoon nan ya faɗa masa ya basa yarinyar sa inyayi ya turo iyayensa ayi baiko(saka rana), cike da farin ciki ya tashi ya tafi.

Yayan sa Nura ya fara qira ya sanar masa da komai cike da ɗimbin damuwan jin irin son da yarinyar kewa Mustapha ya ce “kana da hankali kuwa? Zaka sa yarinya ta faɗa sonka bayan kasan irin AL’ADAN mu, kaima ka sani ko mutuwa za kayi ba iya baba-alhaji ba ko Alhaji da Hajja ba zasu yarda ba, daga ni ba mai goyon bayan ka akan wannan lamari da ka kawo”.

“Yaya gaskiya nikam bazan iya da wani AL’ADA ba, wacce nake so ita zan aura inma menene sai su bari daga baya insunga bata da hali mai kyau sai su saka ni auren Kanuriyan, wannan yarinya yaya da ka ganta ba kaman sauran ƴammatan indiyawa bane ba ruwanta da wani AL’ADUN indiyawa da ya saɓawa addini, ranan na taɓa gwada ta amma har muka kusa samun damuwa tayi ta surutu wai wannan abinda nake yi JAHILCI KO AL’ADAH za’a qira sa”.

Nura a ɗaya ɓangaren yace “shikkenan fatan alkhaeri Allah kawo komai da sauqi ya kuma tabbatar da alkhaeryh”.

Bayan kwana biyu ya qira Hajja ya sanar mata, nan ɗin ma wani faɗan ya tarar.

“Hajiya wallahi yarinyar na so na kuma mahaifanta sun amince, ai ko dan amincewar su ya kamata ku amince min tunda dai AL’ADUN su sunfi naku stauri kasancewar su indiyawa” faɗin Mustapha da ke kare da waya a kunne.

“Mustapha ba indiyawa suke ba koma menene ni ba ruwana kuma karka bari maganar nan yaje kunnen mahaifinku balle akai ga kunnen baba-alhaji, kana gani dai kuma kana sane sai da nasa baki kamun ya barka kai ma ba’a yi aurenka ka koma da mata ba, kuma ko tafiyanka wannan qasar sai da aka sha daru da shi, to karka yarda magana ya kai kunnen sa ni bansani ba kuma karka sako ni ciki, nasan duk abinda kake qullawa ɗan uwanka yana sane to kuje ku fama” Hajja na gama magana ta kashe waya kittt.

Dafe kai Mustapha yayi gaba ɗaya ya rasa yaya zai yi kansa ya qulle, qira ne ya kuma shigowa wayansa ya duba ganin ita ce sai yaqi ɗauka.

Abubuwa sun taru sun masa yawa ga kuma final-year exam’s nasu dake kusantowa wanda bai wuce watanni biyu ya rage musu ba kuma sunayi ba jimawa makaranta zata sallamesu kowa ya kama hanyar sa.

Wasa-wasa har aka yi sati guda baya ɗaukan qiran Maimoon, abubuwa ne suka kacame masa dan ko ya ɗau qiranta baisan me zai ce mata ba.

Yana zaune a wani ɓangare na cikin makarantar kwastam yaji an rungume sa, juyowa yayi amma bai sha mamakin ganin ita ɗin ce ba, nan ta dinga masa kuka akan me yake shareta? Ba tare da ya ɓoye mata komai ba ya faɗa mata halin da ake ciki, nan suka rarrashi juna suka yi hira ya rakata har gida ya wuce gidan da yake.

Bayan Papanta ya dawo ba tare da ta ɓoye masa komai ba ta faɗa masa abinda iyayen Mustapha suka ce, Dr. Mufaddal nan ya lallaɓata ganin tana kuka.

Ko da mahaifiyar ta taji abinda ke faruwa nan tayi hamdala tace “shikkenan kowa ya huta, ita ta auri ba-indiye ɗan uwanta shima yaje can ya auri ƴar Nigeria ƴar uwar sa”.

Papanta ya qirata ya bata haquri saboda abinda mahaifiyarta ta faɗa, su haqura Allah bai yi zasu auri juna ba. Nan fa hankali ya tashi dan ko makaranta taqi zuwa qarshe ma ba tare da kowa ya sani ba har guard’s nata ta fice ta tafi gidan kakarta mahaifiyar mamanta dake cikin Bangalore.

Dr. Mufaddal suka neme ta suka rasa, har ya kori wasu daga cikin masu staronta dan aganinshi basu da hankali tunda zata fita ba tare da sun sani ba, ya nemi Mustapha ko tana wajan sa shima yace baisan bata gida ba, nan fa hankalin su ya tashi dan duk basu kawo wa ransu tana Bangalore ba.

<< Jahilci Ko Al’ada 16Jahilci Ko Al’ada 18 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×