Skip to content
Part 18 of 25 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

Ko da taje nan ta faɗawa kakarta duk abinda ake ciki na abunda mahaifiyarta take faɗa.

Faɗa kakarta ta dinga yi kaman zata ari baki.

Sai da tayi sati biyu a gidan kakanta, ba tare da tayi waya da iyayen ta ko Mustapha ba dan wayan nata kashe shi tayi ta baro sa a gidan su, saboda tasan in tana waya da Mustapha za’a san inda take ta wajan shi.

Shiryawa suka yi suka kama hanyar Hyderabad da kakarta, ko da suka isaa kakarta ta dinga aikin surfawa yarinyarta masifa tunda tasan ba laifin Papa bane Ammaan ta ke hanawa, nan tasa Papa ya aika qiran Mustaphan saboda shi da kansa take so yaje Nigeria akan maganan auren.

Qiran Mustapha tayi bayan ya gama mata faɗa akan tafiyanta ya ɗaga masa hankali sai ta bashi haquri nan ta faɗa masa Papa na nemansa, suka yi waya suka yi sallama.

Mustapha yazo ya samu Papa nan ya tambaye sa halin da ke ciki ba tare da ɓoye-ɓoye ba ya faɗawa Dr. Mufaddal komai akan abinda iyayen sa suka faɗa, nan yace ya basa address na gidan nasu zai je, amma sai kakar Maimoon tace ya bari in Mustaphan ya gama exam’s su tafi tare har da ita, sannan ta kuma yiwa iyayen Maimoon faɗa “shi aure da kuke gani nufi ne na Allah, in Allah yaso kuma rabo ya ranste sai ku mutu ayi, ko ayi ba yanda kuka iya kunya ta kasheku daga baya”.

Sallaman Mustapha Papa yayi, sannan ya sanya aka maida kakar Maimoon (Aliyah) Bangalore.

Bayan wata biyu su Mustapha sun gama exam’s, nan aka dinga shirin graduation nasu wanda kowa iyayensa zasu halarta, mutanen Nigeria sun samu isowa suma, Nura, Hajja, Maryam(matar Nura) sai Alhaji.

Tunda suka zo Hajja ke qara jaddada masa jan kunne akan kar ya kuskura yayi wannan magana balle mahaifin sa yaji, Nura da yasan duk abinda ake ciki har da maganar da yayi da Papa nan shima yake kaffa-kaffa yake addu’an Allah kawo wa ɗan uwansa komai da sauqi.

Ranar graduation akayi hidindimu, kama daga yaye ɗalibai da wasanni da al’adun makarantu yayin sallaman ɗaliban su.

Mustapha da familyn sa suna zaune a qayataccen wajen zaman da yake nasu shi da iyayensa, Alhaji ke magana “yanzu tunda an kammala komai yau gobe zamu wuce kai kuma yaushe zaka biyo mu?

Qasa yayi da kai yace “Alhaji sai nan da wata guda zamu gama kammala komai”.

“To Allah ya kaimu, ka tabbatar ka gama komai akan lokaci ka dawo tunda kana sane da batun baba-alhaji kuma so ake a hada bikin naka da na ƴan uwanka acan Bornon…”

Maganan da Alhaji yake yi ya dakatar ganin wata yarinya da tazo ta tsaya gefen Mustapha.

Ba iya Mustapha ba, hatta Nura da Hajja sai da suka sha jinin jikinsu domin kana ganin yarinyar kasan ita Mustapha ke so, Maryam matar Nura tayi qasa da muryanta tace “mijin habibty wannan baiwar Allahn tamun kyau Allah sa budurwan Mustapha ce”.

Nura dai ya kasa bata amsa dan dukan su idanuwan su na kan Alhaji da jin abinda zai faɗa.

Maimoon da ta tsaya gefen Mustapha ganin dukansu su kalleta su kalli babban mutumin da ta bashi matsayin mahaifin Mustapha, sai kawai ta stugunna tana gaida Alhaji, shi kuma ya amsa cike da mamaki yanawa Mustapha kallon neman qarin bayani.

Gaishe da Hajja tayi ta amsa ba yabo ba fallasa, Nura ma suka gaisa fuska a sake, Maryam ma suka gaisa tana mata murmushi dan ita Maryam har zuciyarta Maimoon ta burge ta.

Mustapha yasha jinin jikinsa sosai dan kallon da Alhaji yake masa kaɗai yasan akwai yinta, miqewa yayi ya bar wajan sai Maimoon ta biyo bayansa, su Alhaji kuma binsu da ido suka yi duka.

Kallonsa tayi ta fara magana cikin indiyanci “iyayenka dama sunzo baka gayamun ba?

“Kiyi haquri, yanzu kije gida za muyi magana daga baya”.

Kallon sa tayi sai ta juya tayi tafiyanta, shi kuma ya koma wajan zaman nasu.

Alhaji kallonsa yayi yace “ina sauraranka”.

“Alhaji me ya faru? Faɗin Mustapha da ya waske kaman baisan abinda Alhaji ke nufi ba.

“Mustapha mun fara wasan reni da kai? Inajinka wacece ita?

Hajja kau da kai tayi, Nura kuma yayi qasa da kai ya ciro wayan sa yana dannawa, Alhaji duk yana kallon su kuma ya fahimci sun san komai da ke tafiya “Mustapha ina sauraranka”.

“Alhaji ba komai dama…dama…”.

Cikin qufula Alhaji yace “Mustapha dama me? Ko ba zaka iya magana bane?

“Alhaji wacce zan aura ce, kuma dama babanta ya…”

Cikin ɓacin rai Alhaji ya dakatar da shi “Mustapha dama abinda kake qullawa anan qasan kenan? Dan na baka damar zuwa nan karatu ko? To bari kaji tun wuri ka aje maganan nan a gefe kana komawa kaje borno ka zaɓi mata a haɗa aurenku ayi da ƴan uwanka, karka bari ma baba-alhaji yaji zancen nan”.

Juyawa yayi yana qarewa Nura da Hajja kallo, ƙwafa yayi yace “duk abinda Mustapha yake qullawa da saninku da kuma goyon bayanku da ɗaurin gindi da kuka masa, kai Nura ka fita idona ka kama kanka, Hajiya karki bari labari yaje kunnen baba-alhaji da ba zaku kwashe ta daɗi ba kema kin sani” yana gama magana ya miqe yabar wajan.

Sai sannan Hajja ta samu daman yin magana “kaga abinda nake gudu ko? Ni na sani kome zaku aikata za’a ce nice na ɗaure muku wajan zama barin ma dai kai Mustapha amma babu komai”.

“Hajiya kiyi haquri ki bimu da addu’an alkairi” faɗin Nura da ke cike da tausayin ɗan uwansa.

“Nura in banyi haquri ba ya zanyi da ku? ‘ya’ya ne Allah ya bani duk kuma sun tafi sai ku biyu kawai kuka tsaya Allah ya nufa, to ai haquri da ku ya zamamun dole Allah dai ya jiɓanci lamuranku ya tabbatar da alkairi a rayuwanku, amma Nura ka dinga yiwa Mustapha faɗa, dan hanyar da ya ɗauko ba mai ɓullewa bane”.

Washegari su Hajja suka tattara suka koma Nigeria inda suka baro Mustapha akan zai taho daga baya amma da qyar Alhaji ya yarda bayan ya kuma ja masa kunne.

Sai da ya ɗiba sati basu yi magana da Maimoon ba tana fushi akan bai faɗa mata iyayensa sun zo ba, da qyar dai yaje har gidan su ya lallaɓa ta sannan ya mata bayanin halin da ake ciki ba tare da storo ko fargaba ba tace bákomi ita dai tana son shi.

Mahaifinta ta faɗa wa abinda ke faruwa amma kasancewar sonta da yake yi shima ya amsa ba komai zasu tafi Nigerian tare da Mustapha.

Bayan ya kammala komai da komai da zai yi suka kamo hanyar Nigeria da Mahaifin Maimoon da kuma kakarta.

Bai ma tunkari garin Gombe da su ba dan ya tabbata ba za su shirya da Alhaji ba dan haka sai suka yi Borno state, sun isa lafiya inda baba-alhaji yaji daɗin ganin sa amma yana mamakin mutanen da yazo tare da su.

Tarba mai kyau akawa kaka-Aliyah da Dr. Mufaddal duk da ba wanda yasan me ke tafe da su, sai bayan sun huta sannan washegari suka nemi yin magana da baba-alhaji.

Bayan sun gaisa Dr. Mufaddal ya fara zayyano abun da ya kawo su, cike da haquri yake magana dan Mustapha ya faɗa masa komai daga wajan stohon ne.

Baba-alhaji da ya zauna turus kaman an shuka dusa kallo kawai yake bin Dr. Mufaddal da shi na jin zancen da yake yi.

Baba-alhaji, farin dattijo stoho wanda ya stufa cukuf amma kana ganinsa zaka san da sauran qwarin sa, buɗe baki yayi ya fara magana “To to madallah naji zancen ku da kuma buqatanku amma ina mai baku haquri anriga an masa mata”.

kaka-Aliyah ce tayi saurin taran numfashin Dr. Mufaddal dake qoqarin magana ta hanyar cewa “ai kuwa sai dai a haɗa masa biyu dan kuwa jikata ta gani tana so, mu nan da ka ganmu ma da shirin mu muka zo”.

Baba-alhaji cike da masifa yace “sai inga mai aurawa yaro na wata can ƴar garin kafurai”.

“Yanda kake musulmi a wajan Allah haka muke duk ɗaya wataqila ma mun fiku imani dan haka in Allah yasa za’a yi bikin nan sai ka mutu anyi ni da ka ganni nan ba ruwana da shiga tsabgan abinda Allah ya qaddara dan in yazo da qarar kwana sai mutum ya mutu kuma qudurar Allah ta tabbatu” kaka-Aliyah ta faɗa itama cike da masifa dan kana ganinta kaga masifaffun tsofaffin indiyawa”.

Baba-alhaji masifa ya dinga yi, daga qarshe dai kwana kawai suka yi suka yi shirin tafiya, Mustapha ko haɗuwa da baba-alhaji yaqi yi tare suka fito da su kaka-Aliyah suka nufo Gombe kuma, kaka-Aliyah sai sababi take a mota tana bawa Mustapha haquri ya kwantar da hankalinsa in dai da ranta sai ya auri Maimoon, Dr Mufaddal da ido kawai yake binsu dan ba shi da ta cewa.

Suna isa cikin Gombe suka yi gidan Alhaji cikin rashin sa’a kuwa suka tarar Alhaji na gida, Hajja ta karɓe su hannu bibbiyu, Maryam matar Nura da take ji kaman Amaryan aka kawo dan daɗi sai nan-nan da su kaka-Aliyah take yi.

Alhaji dai da ido yake binsu bai ce komai ba dan yasan kwanan zancen amma bai da labarin zuwan su Maiduguri.

Bayan sun huta da dare nan ma kaka-Aliyah ce ta fara magana, tunda ta fara bayanin ta mai kama da masifa dan haushin baba-alhaji da take ji, kowa a palourn ido ya zuba mata, Nura kuwa sai raba ido yake ya kalli wannan ya kalli wannan.

Sai da ta gama jawabin ta sannan Alhaji ya numfasa yace “ina mai baki haquri maama amma tunda har yaron yayi dabaran kai ku can Maiduguri amma baba-alhaji yaqi aminta to banda yanda zan yi dan dukkanmu masu biyayya gare sa ne kuma wannan AL’ADA tamu tun kakanni ban isa nace a’a ba”.

Cikin taqaici kaka-Aliyah da idanuwanta ke kan Alhaji tace “aikam dama gado ba karambani ba dole dai kace haka amma ko kunqi ko kunso in Allah ya nufa auran nan za’a yi sa kuma sai duk ku mutu, amma jikata inda alkairi to sai ta auri wanda take so”.

Sai yanzu Hajja ta buɗe baki tayi magana “kuyi haquri Allah ya bata miji nagari” wani kallo Alhaji ya wasta ma Hajja wanda ya hanata qarisa maganan dan tasan cike yake fam da haushinta, duk a ganinsa itace ta ƙulla komai ko kuwa da saninta yaran suke komai.

Dr. Mufaddal da kansa ke gefe ba abinda yake tunani sai yarinyarsa ɗaya tilo da irin soyayyan da take wa Mustapha, numfasawa yayi kamun ya fara magana “Alhaji ina mai baka haquri dan Allah dai a dubi lamarin nan, yarinyar mu tanada ilimi dai-dai gwargwado boko da addini duk da kasantuwar mu ɗin indiyawa ne amma ba inda muka gaza ta neman sanin addinin Musulunci, yaro na sonta itama tana son shi dan Allah a duba lamarin, inma kuɗin aure ne ko wani abu mu mun yarda zamu biya sadaki kaman yanda ake yi a al’adance a qasar mu”.

Kamun Alhaji yace wani abu kaka-Aliyah ta tari numfashin sa nan ma, ta hanyar cewa “a’a kaga Mufaddal karka wani roqesa duk ka qyale su, in Allah yace za’a yi auren nan to in Allah yaso ya yarda za’a yi kuma su mutu, to dama rabo kam wa ya bari? Ai in Allah yaso sai kaga su da kansu sun ladabtu sun ɗaura”.

Alhaji da zuwa yanzu ya fara qufula sai yace “na baku haquri Allah ya mai da ku lafiya” yana gama magana ya miqe ya fice a palourn.

Hajja ce ta basu baki ta basu haquri sannan ta qirawo Mustapha yawa Dr Mufaddal jagoranci har zuwa ɗakin da aka ware masa masauqin sa, itama kaka-Aliyah aka kaita nata masauqin.

Tunda Hajja ta shigo ɗakin Alhaji ya haɗe fiska ya juya mata baya,ganin haka tasan dama za’a rina wai kwando da zubar da ruwa, zama tayi ta fara basa baki akan batasan abinda ke faruwa ba, Alhaji tashuwa yayi ya dinga mata masifa da faɗa ita ta ɗaure wa yaran wajan zama “Fatima kece kika basu wannan fiskan, tunda baba-alhaji ya nemi ayi auren Mustapha ya koma da matar sa amma yaron nan yaqi to nasan akwai abinda yake shiryawa, kema kika zo kika sanya baki har aka barsa ya tafi haka nan kinga kuwa da saninki yake aikata komai dan kece kikama nuna masa hanyar tunda mastayinki na uwa kamata yayi ki sanya ayi bawai a bari ba, to ki buɗe kunnuwanki kinjini da kyau dan in anyi duniya dan Manzon Allah SAW to Mustapha bashi da mata sai Asma’u dan tunda ya nuna nashi yarintan da rashin hankalin to ya daƙilewa kansa damar zaɓar mata kenan, baba-alhaji ya zaɓa masa kuma in Allah ya amince aure nan da sati Uku masu zuwa ko ya shirya ko bai shirya ba, ina fatan kin fahimta?”

Ajiyan zuciya Hajja ta sauqe sannan ta miqe ta haura gadon ta kwanta abunta ba tare da tace komai ba “dan wannan inda sabo to tabbas an saba wai karuwa da cutan qanjamau, indai muddin mace zata tsugunna ta haihu to fa sai dai ta toshe kunnenta kuma ta kau da ido dan akan yara ba abinda ba za taji ba wai ɗan kuka mai jawa uwarsa jifa, wani uban daga randa kika ɗauki ciki shikkenan halayya daban-daban za ki dinga gani, salo iri-iri kama daga hantara, wani rashin kulawa, wani daga ranar an qaurace miki kai wani ma ya dinga jin haushin ki kamar kece kikawa kanki cikin dan wannan AL’ADA ce mai kama da JAHILCI ta maza, a yayin da kika haihu kuma shikkenan duk laifin duniya ke za’a ɗaurawa in yaro yayi ba dai-dai ba dan babu mai miki uzurin cewa ba halinki bane koko ke kina naki ƙoƙorin, amma a haka in Allah bai shirya maka ba sai kaga wani ɗan ya tashi amma kuma ba shi da abin renawa irin mahaifiyar sa, to Allah ka kyauta mana ka bamu shiryayyu, dan mazajenmu sai a hankali kawai sai addu’a ko kaɗan ba ko wanni namijin ne yasan wannan zafi da ciwo na ɗaukan ciki da haihuwar ciki ba, su yara kawai suke gani basu san ita uwa tasan mai ta ɗan-ɗana ba, mu mata sai dai godiya ga Allah da yayo mu kuma ya mana wannan baiwa ta ɗaukan ciki, haihuwa da kuma ciwon al’ada(period) sannan ya jarabce mu da mazaje daban-daban wanda wasu daga cikin su basa duba wannan raunin namu, Allah ka qara mana haquri sannan ka ci-gaba da bamu dama da ikon cinye waɗannan jarabtar tamu ta hallayar wasu mazan..” muryan Alhaji ne ya katsar mata da zancen-zuci da take kan yi.

“Fatima nayi magana kin mini shiru, wato ga mahaukaci na zance ko? Cewar Alhaji da zuwa yanzu ya sake fiska ya kuma tashi ya zauna.

Miqewa Hajja tayi tace “kai ne mahaifin sa sannan kuma ka yanke hukunci, ko so kake na ja da hukuncinka na kuma yin wani laifin? Ai magana ta ƙare Allah kaimu nan da sati uku ya kuma tabbatar da alkhaeryh ya basu zaman lafiya da zuri’a masu albarka shine kawai”.

“To su kuma mutanen da ya yayuɓo yazo da su ya za’a yi dasu?

Murmushi Hajja tayi tace “to ai kuma aikin gama ya riga ya gama wai karuwa da cikin shege, ba wani sauran magana tunda ka sallame su kuma ka basu haquri”.

Kallonta yayi yace “yanzu dai wani shawara za ki bada? Ga lamari ya isa gaban baba-alhaji, gaskiya yaran nan akwai rashin hankali yanzu sunsan mutum da stufa Allah kaɗai yasan me baba-alhaji zai yanke”.

Wannan karon ma murmushin Hajja tayi tana faɗi a ranta”sai da lamari ya lalace sannan za’a nemi shawarata maza, maza kenan to Allah ya kyauta” a fili kuwa cewa tayi “Alhaji banda abun cewa sai dai fatan alkairi Allah rufa asiri”.

“Ameen Fatima, nikam ma maganan stohuwar nan nake qara juyawa da kyau fa”.

Kallonsa tayi da alaman tambaya “wacce stohuwa?.

“Haba Fatima kema kinsan wa nake nufi fa, akwai wata wacce ta wuce baqin da Mustapha ya yayuɓo, amma fa kinsan gaskiyar matar nan na cewa rabo na iya kisa, yanzu in Allah ya qaddara sai mu mutu kuma ayi su zauna, yanzu dai sai mun saurari baba-alhaji”.

“To Allah ya kyauta” faɗin Hajja da ta kwanta cike da alhinin abinda ke faruwa.

Washegari sassafe Dr. Mufaddal ya fito a shirye akan kaka-Aliyah ta fito su tafi amma tace bata san zancen ba, ai gidan surakanen jikarta ce ba ita ba tafiya da sassafe haka kaman an korata, Papan Maimoon ba don yaso ba ya tsaya suka karya har sai da hansti tayi kamun suka yi sallama da su Hajiya da Alhaji inda kaka-Aliyah ke kan maimaita ma Alhaji sai jikarta ta auri wanda take so, har airport Mustapha ya kai su, gaba ɗaya kunyan su yake ji amma Dr. Mufaddal ya nuna bakomai haka Allah ya qaddara dama.

kaka-Aliyah kallon Mustapha tayi tace “jikana kar ka damu in Allah yayi duniya dan Manzon sa to ba mai hanaka auran jikata sai shi Allah da kansa, dan haka ko ma sunqi yarda ni nan zan sanya a ɗaura maka aure da jikata in yaso su kashe auren in sun isa”.

Cikin girmamawa da aminta da maganan stohuwar yace “to kaka Allah ya mayar da ku lafiya”.

Jirginsu na tashuwa mustapha ya juya gida, yana shiga Alhaji na qoqarin fita shi kuma, kallo ɗaya ya yiwa Mustapha ya kau da kai ya shige motar sa aka buɗe masa gate ya fice, sai da Mustapha yaga fitan mahaifin nasa kamun ya shige cikin gidan.

A palour ya tarar da Hajja sai qarasawa yayi gefenta ya zauna kansa a qasa, Hajja kallonsa kawai tayi ta girgiza kai ta miqe ta bar palourn, mustapha kuma ganin haka sai shima ya miqe ya wuce ɗakin sa zuciyansa cike fal da damuwa ga kuma shawari da zuciyarsa ke kista masa.

Su kaka-Aliyah sun koma India lafiya inda guard’s na Papa suka zo ɗaukan su tare da Maimoon, tun a mota Maimoon ke ta ɗaukin jin ya su Papanta suka qare da dangin Mustapha, kaka-Aliyah cikin tausayin jikar nata da soyayyan da take wa Mustapha ta dubeta cikin harshen su ta ce “Maimoon na raba ki da ɗaurawa ‘da namiji soyayyan duniya, ba wai na hanaki soyayya ba a’a amma dai ki sassauta dan kaman yanda kika ga network ba shi da tabbas to gwanda network akan namiji ki tsagaita Maimoon”.

Kallon kaka-Aliyah tayi idonta cike da ƙwallah ta ce “nima so nake na rage amma na kasa kullum cikin qara jin sonsa nake a zuciyata, in Mustaphan bai aure ni ba zan iya mutuwa”.

Tausayin Maimoon ne ya cika zuciyan kaka-Aliyah da kuma Papa dake mazaunin gefen driver, duk addu’a suka bita da shi a zuciyansu dan abun sai dai addu’a.

Sun isa gida, Hindu ta tare su da ya ake ciki? Amma daga kaka-Aliyah har Papa ba wanda ya bata amsa, ganin haka sai taja baki tayi shiru, har aka kwana biyu kaka-Aliyah ta tattara ta koma Bangalore tana mai addu’an Allah ya kawo wa yaran ɗauki cikin lamuran su.

Tsakanin Alhaji da Mustapha kuwa ko gaisuwan sa baya amsawa kuma yanzu haka auren sa da Asma’u saura sati da kwanaki, Maimoon kuma suna waya sannan tasan halin da ake ciki dan ita auren sa bai dame ta ba damuwanta ya aureta itama ko da mata uku zai qaro.

Baba-alhaji gaba ɗaya ya sanya a hau shiri tunda yaran da za’a haɗa bikin nasu tare komai sun kammala sai aka bar watannin aka ce duka a sati mai kamawa za’a yi, duk shirin da ake yi Mustapha ko a jikin sa kuma zuwa yanzu ya gama yanke shawaran abinda zai yi, Hajja dai ta zubawa sarautar Allah ido tana binsu da addu’a.

A can India Maimoon wasa gaske ta fara rashin lafiya wanda ya kai su har asibiti, Papa ya rasa yanda zai yi haka kaka-Aliyah ma, mahaifiyar ta kuwa zuwa yanzu itama ta saduda so take yarinyarta ta auri wanda take so.

Anshiga satin biki, ana hidima ba kama hannun yaro, su Alhaji duka sun tattaro sun dawo Maiduguri har da Mustapha da aka sha daru da shi kamun ya biyo su dan sai da Alhaji ya nuna ɓacin rai sosai, anyi hidima an gama an ɗaura aure ya kai 6 duka na jikokin baba-alhaji, an kai ko wacce Amarya ɗakinta.

Sai da suka kwashe sati guda a Maiduguri kamun suka tattaro suka dawo garin Gombe, duk kwanakin nan da aka ɗiba Mustapha ko kallo Asma’u bata ishe sa ba balle maganan ya shiga ɗakinta, sai da suka kwashe wata guda da dawowa Gombe amma bai bi ta kan Asma’u ba, ko da Hajja ta fahimci hakan sai ta qira sa.

Zaune yake a gaban Hajja wacce ke zaune a bakin gadon ta, kansa a qasa ya ce “Hajja ganinan”.

Kallonsa tayi da kyau kamun ta buɗe baki ta fara magana “Mustapha meyasa ba ka ji? in har kasan ba za ka iya kula da yarinyar mutane ba meyasa ka aure ta, su fa mata da kake gani ƴan lallashi ne kuma masu buqatan kulawa ne ba wai ka ajiye mace ka fita harkanta ba, haquri shine naka a matsayinka na mijinta, duk abinda kake yi ina sane ina kallonka ne kawai na maka shiru, dan haka tun kamun mahaifinku ya sa baki kayi ƙoƙarin gyarawa ka kula da matarka, ƴar uwanka kuma ƙanwarka fatan kana ji na?

Mustapha da yake ji kaman ya saka kuka ko magana ya kasa sai kawai gyaɗa kai da yayi yana ƙoƙarin miqewa, Hajja ce ta kama haɓa a ranta kuwa cewa tayi “nasan za’a rina wai an saci zanin mahaukaciya” da kallo kawai ta bisa har ya fice a ɗakin, yana fita a sashin su Hajiya ya wuce sashin yayansa Nura.

Da sallama ya shiga, Maryam dake zaune tana kallo ta amsa tana murmushi “sannu da shigowa Ango”, Mustapha taɓe baki yayi bayan ya qariso ya zauna.

Murmushi ta kuma yi tace “Angon Maimoon mijin Asma’u ya aka yi?

“Habibty ina mijinki?

Ta buɗe baki zata bashi amsa sai maganan Nura ya dakatar da ita, Nura da ke qarasowa palourn yana murmushi yace “ganinan Mustapha Autan Alhaji da Hajja” ya zauna gefen qanin nasa, suka gaisa Habibty ta kawo musu abun karyawa suka karya sannan ta miqe ta koma ciki ta basu waje dan ta ga qanin mijin nata so yake su zanta da yayansa.

Mustapha juyowa yayi a yanayi na damuwa yace “yaya Maimoon fa zuwa yanzu ko abu bata iya sawa a bakin ta wallahi storo nake kar soyayyata ta kashewa mutane yarinyar su kuma ita kaɗai suka haifa”, dafa kafaɗansa Nura yayi ya ce “Mustapha nima abun na damuna kuma bansan ta inda zamu ɓullo masa ba, kaga dai Hajja bata goyon bayanmu sannan Alhaji baya sauraran kowa, shi baba-alhaji kuma ya dage akan wannan al’adan, kai kam dai inaji Alhaji yana batun zai yi tafiya so sai muje mu dubo ta da jikin amma kuma ka fara bai wa Asma’u kulawan da ya kamata in har kanaso nasa hannu a lamarin nan”.

Mustapha da yaji sanyi a ransa tunda ɗan uwansa na goyon bayan sa sai ya amince ba komai zai kula Asma’u, bayan sun kammala magana sun yanke shawarar yanda zasu ɓullo wa lamarin sai Mustapha ya sallami yayansa ya bar sashin, amma bai wuce sashin sa ba ya ɗau mota ya fice a gidan gaba-ɗaya.

Asma’u yarinya kyakkyawa Masha Allah, a shekaru ba zata wuce sa’ar Maimoon ba, sanye take da dogon rigan zani wanda ya amshi jikinta, tana hakimce kan 1seater ta zuba tagumi wanda a zahirance TV dake maqale a bangon palourn take kallo amma a baɗinan ce hankalinta da tunaninta baya duniyar Gombe, ringing da wayanta ke yi ne ya kaste mata tunanin da take aikin yi, jawo wayan tayi ganin mai qiranta sai da ta share guntun ƙwallah kamun ta ɗauka ta kara a kunnenta “Assalamu’alaikum fanne an tashi lafiya?

Lafiya Alhamdulillahi Asma’u ya gidan naku? Ya maigidanki da iyayenku?

Asma’u jin an ambaci maigida wanda ita a zaman da take yau kusan wata 2 da aure amma bata ga ko giftawan ƙeyarsa ba sai Kawai ta fashe da kuka, cikin tashin hankali a ɗaya ɓangaren matar tace “ke Asma’u lafiya kuwa daga tambaya sai kuka waye ya mutu?

Cikin sheshsheqa ta ce “lafiya fanne ba wanda ya mutu”.

“Asma’u lafiya shine kike kuka? Faɗamun meke faruwa, me mijin yake miki yanzu na faɗawa baba-alhaji shine dai-dai kowa”.

“Ba komai fanne kawai kewanku nake yi”

Matar dai bata yarda da abun da Asma’u ta faɗa ba, nan ta sauya harshe ta fara magana mai kama da faɗa da yaren nasu, Asma’u dai tayi shiru tana sauraran matar tana kuma kan share hawayen dake sintiri a kumatun nata, jin matar ta tsagaita tana kuma tambayanta sai tayi ƙasa da kai ta fara faɗa mata komai duk abinda ke faruwa daga farko har qarshe, nan matar ta dinga surutu daga qarshe dai ta kashe wayan, Asma’u ganin matar ta kashe sai ta kifa kanta a cinya tana sakin wani marayan kukan.

Surutun da mata dattijuwa mai kama da Asma’u ke yi shi ya tashi mijin matar daga bacci yana faɗin “fanne lafiya ke da waye?

Cikin masifa ta fara magana “wai yanzu saboda tsabar muhammadu yaransa sunfi qarfinsa ace daga biki har yau wata har 2 amma yaron nan Asma’u bata taɓa sanya shi a ido ba wannan ai lalacewa ne, insun san haka yaron nasu ya gagara me na dagewa a ɗaurawa marainiyar Allah ciwon zuciya tun tana yarinya, gaskiya sashin baba-alhaji zanje in har yaron ba zai iya ba ya sakomun yarinya banson rashin mutunci tunda su iyayensa basu haifi mace ba balle su san zafin hakan..” masifa fanne ta dinga yi da qyar mijinta babagana ya rarrasheta ta haqura amma ta ɗau alwashi a ranta sai baba-alhaji ya ji abunda ke faruwa.

Bayan fitan mijin nata, farau-farau ta haɗa dan tasan baba-alhaji shi ya fi so, ta yafa mayafinta ta fice a sashin.

Gidan baba-alhaji stoho mai ran qarfe, babban gida ne iya ganin ka sashi-sashi shi da iyalansa, wanda a hakan ma wai wasu basa cikin gidan amma gida ne babba sosai, fanne da sallama ta shigo palourn baba-alhaji aka amsa mata sannan ta shige, zaune yake a kan kujeransa na gado da sandar sa gefensa, sai wani jikansa da yake zaune suna fira, gaishe su fanne tayi sannan ta ajiye abinda ta kawo wa baba-alhaji, yana gani ya fara washe baki yana sa mata albarka, ganin bata tashi ba sai yake tambayan ta ko da wani abu? Ba tare da ɓata lokaci ba fanne ta fara zazzagewa baba-alhaji qarya da gaskiya.

<< Jahilci Ko Al’ada 17Jahilci Ko Al’ada 19 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×