Skip to content
Part 19 of 25 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

Abinda aka yi da wanda ba’a yi ba duk sai da ta faɗa masa, baba-alhaji kuwa ransa in yayi dubu to ya ɓaci nan yasa aka qira masa Muhammadu. 

Alhaji bayan fitan sa a gida, Companyn sa da suke aikin fata ya nufa dan yaga yanda ayyukan ke tafiya.

Yana zaune tare da wani abokinsa sai qira ya shigo wayansa, ganin mai qiransa yana murmushi ya ɗauka dan yasan ba zai wuce baba-alhaji yakeso su gaisa ba “Assalamualaikum stoho mai ran ƙarfe”

Baba-alhaji a ɗaya ɓangaren cikin masifa ko amsa sallaman bai yi ba shima ya fara zazzago nasa surutun daga qarshe ya ce “ka tabbatar yaron nan ya gyara kamun na sako qafana a cikin Gombe dan in yaga yayi auren nan to bayan rai na ne” yana gama magana kittt ya kashe waya, Alhaji ajiyan zuciya ya sauqe ya ajiye wayan yana auna rashin hankali irin na Mustapha da yarintan da ke damunsa, abokinsa ne ya dubesa yace “Alhaji Muhammadu lafiya kuwa?

“Ina lafiya kuwa Alhaji Ahmed kana gani yaron nan mustapha na ƙoƙarin jazamun magana”.

Abokin nasa ya ce “haba dai Mustapha kuma, yaro mai hankalin nan”.

Murmushi Alhaji yayi, nan take ya kwashe komai a taqaice ya faɗawa abokin sa ya ɗaura da cewa “in ba yarinta dake ɗawainiya da Mustapha ba ina shi ina ‘yar wata can qasa indiya bama anan Nigeria ba”.

Abokin Alhajin ma murmushin yayi yace “amma dai stoffi akwai rigima Alhaji in ba haka ba ai kai ne jikan sa ba yaranka ba kuma ko kai ai bai kamata ya hanaka abinda kake so ba balle kuma yaronka, gaskiya ba’a kyautawa Mustapha ba dan soyayya ba abun wasa ba, kawai ku barsa ya auro wacce yake so inyaso sai ya haɗa su biyu duka, kaga dai gaskiyan matar nan rabo yana kisa gwanda tun wuri ku qyale yara suyi auren su”.

Alhaji jin zancen abokin nasa sai ya sauqe ajiyan zuciya yana faɗin “nima dai tun da stohuwar nan tayi magana ina tunani amma kuma kaji yanzunnan shi baba-alhajin yake cewa in dai Mustapha ya auri bare to sai bayan ranshi ni kuma ban isa na musa ba, amma kuma ba komai Insha Allahu zan shiga Maidugurin da kaina na gwada tausan shi baba-alhajin ko zai sauqo ya amince”.

“To Allah kyauta ya tabbatar da alkhaeryh” faɗin abokin Alhajin yana miqewa ya bawa Alhaji hannu suka yi musabaha ya fice a office ɗin.

Alhaji ko da ya dawo gida surutu ya dinga yiwa Hajja akan tasan abinda ke faruwa tayi shiru, ita dai Hajja ido ta zuba masa har ya gama ya ciro waya ya qira Mustapha yana ɗauka ya ce masa “duk abinda kake yi ka tabbatar ka zo bayan sallahn isha’i” yana gama magana ya kashe wayan sa ya miqe yana kan mita.

Hajja da kallo kawai ta bisa, tana mamakin wani abun dan tasan ba’a yi ba amma ba komai Allah shige ma kowa gaba a al’amuran sa.

Mustapha shine bai zo qiran Alhaji ba sai wajan qarfe takwas, nan Alhaji ya dinga masa faɗa sannan ya ce “ka tabbatar ka kula da yarinyar mutane kar na kuma jin wani abun balle na gani”.

Shi dai kansa a qasa bai ce komai ba har Alhaji ya gama maganan sa ya sallamesa, kamun ya miqe ya nufi sashin sa, a palourn ya same ta zaune tana cin abinci, sanye take da kayan bacci riga da wando masu kauri da duhu ta tufke gashin kanta mai tsayi dai-dai gwargwado, kallo ya qare mata a taqaice yana taɓe baki ya ce “wannan ina ta kai Maimoon tawa” haka dai ya basar yayi sallama wanda a gefen Asma’u kaman sauqan aradu haka ta ji sallaman ba zato ba tsammani dan har ta storita, amsawa tayi tana masa sannu da zuwa shima ya amsa ya qarisa ya zauna.

Ruwa ta kawo masa da abun sha sai abincin da take ci ta kawo gabansa tana faɗin “kayi haquri bansan zaka shigo ba”.

Shi dai Mustapha bai ce komai ba ya taɓa kaɗan yana satan kallonta, daga qarshe ya umurce ta tazo suci tare ba musu ta dawo gefensa suna ci tare yana kallonta.

A wannan dare dai ya mai da Asma’u cikakkiyar mace sannan suka fahimci juna ya mata faɗa na haɗa sa da gida ita kuma ta nemi yafiyar sa.

Zuwa yanzu Mustapha da Asma’u suna zaune lafiya duk da dai Mustapha ba sonta yake ba kuma itama tasan da hakan amma tana son shi kuma a ɓangarenta ta amince ya auri Maimoon dan tana ganin za ta fi samun nistuwa itama.

Ana haka dai ciwo ya kama baba-alhaji ba ji ba gani, ciwo yayi tsanani wanda ganin hakan sai Alhaji da iyalansa suka tattara suka nufi Maiduguri, sunje lafiya sun duba shi, duk da dai baba-alhaji ya ga Mustapha da Asma’u lafiya kuma shima yana cikin zafin ciwo amma hakan bai hanasa yiwa Mustapha faɗa ba dan shi a ganin sa yana son ɓata masa tsarin rayuwan familyn sa ne, in da ya kuma jaddada musu ko bayan ransa bai yarda wani ya auro bare ba.

Shi dai Mustapha duk abinda baba-alhaji ke faɗa jinsa kawai yake yi.

Basu fi sati biyu ba suka tattaro suka dawo Gombe, Maryam matar Nura dai addu’a take Allah ya qaddara auren Mustapha da Maimoon duk da kuwa Asma’u ‘yar uwatta ce amma tan son Maimoon da Mustapha.

Basu fi wata guda da dawowa ba Maryam ta fara laulayi, wannan laulayin ba qaramin faranta ran iyalan Alhaji yayi ba kowa ɗauki yake yi barinma Mustapha duk da shima a kullum hango Maimoon da cikinsa yake yi.

Kwatsam Alhaji ya samu qira daga Maiduguri kan jikin baba-alhaji ya tsananta kuma yana buqatan kallon su shi da Hajja, ba tare da ɓata lokaci ba suka shirya suka tafi Maiduguri su biyu.

Bayan tafiyansu Mustapha da Nura suka shirya jirgi ya lula da su qasar India, suna isa suka nufi asibitin da aka kwantar da Maimoon, ganin yanda ta koma ba iya Mustapha ba har Nura sai da yayi ƙwalla ya tausaya masa, kaka-Aliyah taji daɗin zuwansu kuma jikin Maimoon har yayi dama-dama a kwana 2 da suka yi, nan dai Nura ya buqaci da a ɗaura auren Maimoon da Mustapha amma Dr Mufaddal ya nuna qin amincewar sa dan tunda dangi basa sonta kar aje yarinyar sa kuma ta qarisa mutuwa.

Anyi juyin duniya amma Papa da Ammaa sunqi, Mustapha har da kukan sa amma sunqi dan kowa a cikin su yasan sharrin qiyayya balle ma da suka ji yanzu Mustapha na da mata, har sai da kaka-Aliyah ta sa baki sannan Dr Mufaddal ya aminta dan sosai yake jin maganan surkuwar ta shi, ba tare da ɓata lokaci ba Nura ya biya sadakin Maimoon rufi dubu hamsin a kuɗin indiya, a kuɗin Nigeria kuma dubu ɗari kenan.

An ɗaura aure lafiya-lafiya ba tare da sun sanarwa kowa ba a gida, Maimoon kuma tun da aka ɗaura aure shikkenan sauqi ya fara samuwa gadan-gadan, ganin sun kwashe sati guda sai Nura ya buqaci da zasu ɗauke ta su dawo Nigeria tare amma kaka-Aliyah tace a’a su zasu kawo ta daga baya in ta gama samun sauqi, Mustapha ba don yaso ba suka baro India yana cike da farin ciki da kewar sahibar sa Maimoon wanda a gefenta itama hakan take.

Nura dai komai yake yi shahada ne dan zuciyar sa na cike da storon me zasu tarar a gida tunda ba wanda yasan zancen kuma gashi shine ya jagoranci komai, amma a gefen Mustapha ko wannan tunanin baya yi illa farinciki da yake ciki, sun sauqa lafiya sun tarar su Alhaji ma basu dawo ba.

Nura ya faɗawa Maryam abinda ake ciki, itama ba tare da ta damu da cakwakiyar da zai faru ba ta dinga farinciki har da murna, ɓangaren Asma’u ma Mustapha bai ɓoye mata komai ba ya faɗa mata, ko ba komai ta ji kishi tunda ita dai Allah yana gani tana qaunar sa amma sai ta danne zuciya. Bayan mako guda da dawowan su Mustapha su Alhaji ma suka dawo sun baro jikin baba-alhaji sai a hankali kawai.

Har aka kwana biyu da dawowan su tsakanin Nura da Mustapha ba wanda yayi qarfin halin tunkarar iyayen nasu ya faɗa musu abinda ake ciki, daga qarshe dai Nura ne yayi qarfin halin zuwa wajan Hajja ya faɗa mata komai da ya faru, cikin tashin hankali ta kalli Nura tace “ashe Nura baka da hankali? Har za kuje ku ɗaura aure wa kanku ba tare da sanya albarkan iyaye ba wato kun girma ko? To ba ruwa na dole mahaifinku yaji maganan nan tun da wuri asan yanda za’a yi kamun baba-alhaji ya ji tunda dai ku kunnen qashi gare ku, gaku marassa iyaye marassa manya kune iyayen kanku har za kuyi gaban kanku kuje ku ɗaura aure ba saninmu to maza-maza ku shedawa mahaifinku kamun na faɗa masa da kaina dan ba zai yiwu dan na haifeku sai ku dinga jamun magana ba, ni kuka raina komai ku ka yi ni za ku tinkara ku faɗawa tunda ni mareniyar wayo ce ba abinda na isa nayi to ku faɗawa mahaifinku shi da ta isa kuma kukejin storon sa dan baza’a ce nice na ɗaure muku wajan zama ba wannan karon”.

Nura kaman zai yi kuka ya ce “shikkenan Hajja Allah huci zuciyanki Insha Allahu zamu faɗawa Alhaji amma so kuke ki sanya mana albarka da addu’oenki, Wallahi Hajja ko kece kikaga halin da baiwar Allahn nan ke ciki sai kin tausaya mata amma ba komai kiyi haquri ki yafe mana”.

Harara Hajja ta aika masa “to ban tausaya mata ba a rufeni da duka, nidai na faɗa maka maza-maza kuyi gaggawan faɗawa mahaifinku, shi kuma Mustaphan tunda fitsarar sa har takai haka to ya tabbata ya rubuta wa yarinya sakinta kamun ya tunkaro mahaifin naku kuma kan magana take garin Borno, maza tashi ka ficemun daga gani “.

Nura haquri ya dinga bawa Hajja amma ganin ta bawa banza ajiyarsa sai ta miqe ya fice yana hamdala ko ba komai sun rage wani aikin saura na tunkaran Alhaji dan baba-alhaji basa ta shi tunda shi ba ubansu ba ba kuma uban iyayensu ba.

Hajja ajiyan zuciya ta sauqe Nura na fita ta ɗaga hannu sama tana faɗin “Allah ka sanya albarka a wannan auren, Allah ka musu albarka duka ka basu ikon haqurin zama da juna, Allah ka shiryamun su ka basu zuria’a masu albarka, Allah ka jiɓanci lamuran su ka kawo musu komai da sauqi” sannan ta miqe, haka kawai itama Hajja taji tana farincikin wannan auren duk da tasan akwai ƙura dan ko wannan zuwan nasu kan su dawo sai da baba-alhajin ya jaddada musu akan Mustapha ya kiyaye shi.

Sai da aka kwana ɗaya, biyu ana ƙoƙarin na uku Hajja ta dinga surutu in basu faɗawa Alhaji ba to yau zata faɗa masa, ganin haka a ranan da dare Alhaji na zaune palourn sa yana kallon labarai suka shigo, bayan sun gaishe sa sai duk suka yi shiru aka rasa mai fara magana, Alhaji kallon su yayi kamun ta tambaye su “akwai mastala ne?

Mustapha ya buɗe baki da niyan yin magana sai Nura yayi ya maza ya fara korowa Alhaji bayani kansu a ƙasa duka, Alhaji kuwa tun da Nura ya fara magana ya zuba musu ido ko kiftawa ba yayi.

Hajja da ta sako kai zata shigo palourn, jin abinda suke faɗa sumui-sumui ta juya ta koma ɗakinta tana musu addu’a kawai Allah kawo musu komai cikin sauqi.

Sai da Nura ya gama koro bayani kamun Mustapha ya buɗe baki ya ce “kayi haquri Alhaji”. wannan magana ta Mustapha shi ya bawa Alhaji daman iya haɗa laɓɓunsa ba tare da dogon zance ba ya ce “kun kyauta, ku tashi ku bani waje shashashshu kawai”.

Da mamakin iya abinda Alhaji ya furta suka kalli juna suka miqe suka fice a palourn tare, sai da suka gama magana sannan kowa ya wuce sashin sa.

Alhaji sai da ya gama nazari da tunani sannan ya nufi ɗaki inda ya samu Hajja har ta kwanta, qyaleta yayi ganin kaman tayi bacci ya kwanta shima, Hajja kuwa likimau tayi ba bacci ba dan har dai da taji sauyawan numfashinsa alaman bacci ya ɗauke sa sannan ta miqe ta ɗauro alwala ta tada nafila mai cike da addu’a ga yaranta rayayyu da matattun duka ( to Hajja Allah ya amsa).

Sai da aka shafe sati guda Alhaji bai ce musu komai ba, gefen Mustapha kuwa soyayya da Maimoon ruwa-ruwa kullum suna maqale da waya dan zuwa yanzu jikinta yayi sauqi sai abinda ba za’a rasa ba, dama shigan ciwo ne mai sauqi amma fitansa sai a hankali.

Asma’u tun tana dannewa tana haquri har abun ya fara isar ta, dan yanzu kullum Mustapha raba dare yake yana soyayya da Maimoon, magana Asma’u ta masa amma sai ya bata haƙuri shi gaskiya yana son Maimoon ba zai iya dannewa ba, sai kuma Asma’u ta fara ɗaga hankali tana masifa daga qarshe qiran fanne tayi ta faɗa mata komai, ita kuma fanne ta samu baba-alhaji ta faɗa masa qarya da gaskiya, duk da zafin ciwon da baba-alhaji ke ciki bai hanasa qiran Alhaji ba, sai aka yi rashin sa’a layinsa baya shiga, nan dai suka dinga gwadawa shiru, baba-alhaji dan masifa har jikinsa tashuwa yayi.

Alhaji kuwa har zuwa yanzu bai ce komai ba sannan bai tunkari Hajja da maganan na yayi shiru tunda yaran sun nuna masa bata sani ba itama kuma ya yarda.

Maimoon zuwa yanzu ta warke rass kaka-Aliyah ta gyarata dai-dai gwargwado nasu indiyawa, jikinta dai bai koma normal ba dan kana ganinta kasan tayi jinya amma duk da haka ta murmure tayi kyau abunta abinka da kyakkyawan mutum kuma ‘yar indiya, kaka-Aliyah tayi maganan tarewan ta amma Hindu ta tirje sam sai sunga ana son ‘yar su kamun ta tare, kusan samun damuwa suka yi da Dr Mufaddal amma sam taqi yarda, kaka-Aliyah tayi-tayi amma Hindu taqi ganin haka sai suka fita harkanta suka yi shiru maganan tarewan, ganin an kwashe wata amma shiru sai kaka-Aliyah ta dinga masifa sai yarinya ta tare in taso ta stine mata ai itama zaman gidan mijinta take, qarshe dai suka tsayar da ranar tarewan bayan sun tuntuɓi Mustapha shima ya faɗawa Hajja, nan aka dinga shiri Mustapha na gyaran sa amma duk shirin su da suke yi Alhaji bai sani ba.

Alhaji na zaune tare da Hajja suna fira sai qira ya shigo wayansa, ganin mai qiran sai da gabansa ya faɗi amma haka ya ɗauka, ai kaman yanda ya tsammani haka ya ji dan da masifa baba-alhaji ya fara ba ko sallama, muryansa ba fita yake ba sosai amma inda yake shiga ba nan yake fita ba “wallahi Muhammadu ka tabbatar yaron nan ya bawa ‘yar mutane talardan ta dan in ba haka ba wannan karon da kaina zan zo har Gombe daga kai har shi ba za kuji daɗi ba, kuma kar naji labarin wasu sunzo gidan ko shi ɗin yaje can qasar kafuran..” haka baba-alhaji ya dinga surfa tijara yana ganawa yasa fanne ta kashe masa wayan, nan kuma yasa ta qira Asma’u ya shaida mata ana kawo mata gidan ta faɗa masa, Asma’u bata so abun ya kai har haka ba amma ta amsa kuma dolenta dan tasan halin fanne, baba-alhaji tari ne ya sarqafe sa da qyar dai ya lafa.

Alhaji bayan baba-alhaji ya kashe waya dafe kai yayi yace “Fatima yaranki za su kashe ni lokacin mutuwana bai yi ba, yanzu ya aka yi magana yaje kunnen baba-alhaji?

Hajja itama da mamakin ta ce “Alhaji ni kuwa ina zan sani, nima mamakin ya aka yi ya ji nake”.

“Ni gaba-ɗaya yaran nan sun ɗaure ni da jijiyoyin jiki na, na rasa yaya zan yi, wallahi har naji da ban tura yaron nan wannan qasar ba, amma dai ya zan yi qaddara ta riga fata Allah ya sanya alkairi, amma maganan tarewan yarinyar nan dole a dakatar ba yanzu ba”.

Hajja dai shiru tayi bata ce qala ba tunda tasan sun riga sun gama magana.

Mustapha bai bi ta kan kowa ba ya tattara ya tafi India, ganin sa kuwa ba qaramin qwarin guiwa ya qarawa Dr Mufaddal da kaka-Aliyah sun san ko ba komai yana sonta kuma zai riqe ta, sai da ya kwana 2 suna soyayyan su sannan ya tattaro ya dawo yana jin kaman ta dawo da matar sa, Asma’u tunda ya dawo ta fahimci India yaje, nan ta qara saro sabon tijara itama wanda basu fi sati ba Mustapha abun na isar sa ya sake ta saki guda, Hajja ta masa faɗa tun Alhaji bai ji ba ya mayar da ita, amma da qyar ya yarda ya mayar da ita.

Mustapha ya kammala komai sai zaman jiran zuwan Amarya sati mai kamawa, yayi ordern kayan akwati ba wanda ya sani ya kawo gefenta ya ajiye, dama starin part na Mustapha da Nura main palour ne babba sai kuma gefe 2 bedroom da palourn ɗayan gefen ma 2 bedroom da palourn, to gefen da Mustapha yake akan nasa shi ya shiryawa Maimoon komai.

Ranar Alhamis mutan India suka tattaro da Amarya sai Nigeria, Dr Mufaddal, Hindu, kaka-Aliyah, Maimoon Amarya.

Sun sauqa lafiya lumui, Nura ne da kansa yaje ya ɗauko su, direct sashin Hajja aka yi da Amarya kuma anci sa’a Alhaji baya gida, nan Hajja ta musu tarba mai kyau wanda ya farantawa kaka-Aliyah, ita kuma Hindu taji dama-dama a ranta, Maryam mai fama da cikinta da zuwa yanzu ya tasa kusan wata 6 sai nan-nan take da Amarya wanda a take suka zama kaman ƙawaye.

Asma’u tunda ta gifta taga shigowan mutane, a sace ta shigo taga Amaryan, tunda Asma’u taga kyawun Maimoon hankalinta ya tashi ba shiri ta juya ta daqa waya ta qira fanne ta faɗa mata, itama ta sanar da baba-alhaji, ba ɓata lokaci shima ya qira Alhaji yana surfa masifa inda yake shiga ba nan yake fita ba kuma yau-yau ɗin nan zai zo Gomben sai Mustapha ya sake yarinyar kuma sun koma, Alhaji da baisan da wannan magana ba shima ransa ne ya ɓaci ya kamo hanyar gida.

Baba-alhaji da qyar aka dannesa akan ya bari gobe su taho kamun ya haqura.

Alhaji yana isowa gida, ya hau Hajja da Mustapha da masifa dan ko kula su Dr Mufaddal bai yi ba, qarshe ma saqon baba-alhaji ya basu sannan ya ce Mustapha ya tabbatar ya bawa yarinya takardan ta kamun gobe, wannan masifa har kunnen su kaka-Aliyah wacce ita kuwa tace jikarta taga gidan zama, Hindu kuwa an sosa mata inda yake mata qaiqayi ta dinga mita za’a rena yarinyarta za’a maida yarinya bazawara dan haka su yau zasu koma amma kaka-Aliyah ta hana tace sai sun jira zuwan baba-alhaji taga ta inda zai raba abinda Allah ya qulla, Dr Mufaddal dai nasa iso ya kasa cewa komai, domin shi mutum ne mara son hayaniya komai aka yi dai-dai ne, ba abinda yake ji sai yarinyar sa amma yana binsu duka da addu’an alkairi.

Mustapha da Maimoon a gefensu kuwa duk abinda ake yi bai dame su ba, su damuwan su ma su haɗu da juna amma an hanasu wannan daman Hindu ta kasa ta stare daga sashin Hajja sai India ba inda yarinyarta zata je salon a maida ta bazawara, shi ma Mustapha Alhaji ya kasa ya stare in har ya keɓe da ƴar mutane to bai yafe masa ba kuma sai ya sake ta, Hajja dai tausan Mustapha tayi sannan ta dinga bawa su kaka-Aliyah haƙuri amma kaka-Aliyah ta nuna ba komai dama duk wani aure wanda zai yi qargo ya gaji haka, yawan qalubale yawan qwari da qargon aure.

Maryam ma duk abinda ake tana maqale gefen Maimoon har dare kamun ta tafi sashinta.

Tunda ya shiga palourn Asma’u ke ruwan masifa da bala’i sai ya sake ta cin amana ai an ɗaura auren ma bai sanar mata ba sai daga baya, nan dai Mustapha yaji ita ce takai zance kunnen baba-alhaji, ba ɓata lokaci ya kuwa rubuta mata sakin da ta buqata, saki guda ya mata ya zama biyu da wanda aka yi kwanaki.

Nura dai ba shi da ta cewa sai zubawa sarautar Allah ido, dan yasan gobe baba-alhaji na dirowa Gombe to ta kansa za’a fara shine yayi wa komai jagora, amma Maryam ta dinga kwantar masa da hankali ta rarràshi mijinta suka lula duniyar masoya ta ma’aurata zuciyanta cike fal da addu’an Allah yasa kar a saki Maimoon.

Washe-gari baba-alhaji ya dinga fitina ba yanda aka iya haka aka sako shi a motan gida shi da jikokinsa 3 da fanne da kuma yayan Asma’u da suke uwa ɗaya uba ɗaya, suna hanya Asma’u ta qira ta shaida musu sakin da Mustapha ya mata da dare da kuma na kwanaki nan fa masifa ya ninku baba-alhaji ji yake babagana baya sauri a tuqin, dan ciwon dake damunsa ma neman sa yayi ya rasa ba abinda yake cinsa sai masifa da burin ya gansa a gidan Muhammad “in banda jarabar yara basu sa maka ciwon kai ba haka jikoki basu sanya maka ciwon baki ba dai yaran jikoki ne zasu sanya ka hawan jini, ni in ba azalzala da rashin ji irin na yaran zamani ba me zai kai ni wata gari can Gombe, banje sun samartaka ba sai da stufa kucuf-kucuf ina ƙoƙarin mutuwa, Allah kyautawa yaran zamani da kafiyar stiya wai soyayya” cewar baba-alhaji da yake magana da qyar.

Tunda garin Allah ya waye Mustapha ya fice a gidan ya qira Maimoon kawai suna soyayyan su ba ruwansu da fitinan da ake yi sanadin su, Hindu ko abin karyawa taqi masa kallon arziqi ita burinta kawai su tattara su koma yanzu karma rana ta fito ta same su a qasar jama’a, Dr Mufaddal dai ɗakin da aka basa yake ciki yana ayyukan sa da zai yi ta waya bai bi ta kan Hindu ba dan shi ko karan hauka yasha ba zai maida yarinyar sa bazawara da hankalin sa ba.

kaka-Aliyah kuwa fitowa tayi ta wane a palourn Hajja kai kace gidan ta ne tana faɗin ba ita ba barin gidan sai jikarta ta haihu, Hajja dai abun kaka-Aliyah ma dariya yake bata dan haka nan suka dinga hiran su kaman ba komai.

Alhaji dan ɓacin rai ko fitowa bai yi ba yana ciki yana jiran isowan baba-alhaji dan shima zuwa yanzu renin hankalin yaran nasa ya ishe sa tunda har yarinya zata tare ba’a faɗa masa ba, gefen Asma’u kuwa ta gama haɗa kayanta dan su fanne na zuwa suka gama abinda ya kawo su da ita za’a juya ba zata zauna da Mustapha ba a faɗin ta.

Alhaji na zaune a palourn sa idanuwan sa akan TV yaji muryan wayansa, ganin layin ɗan uwansa dai ya ɗauka, abinda aka faɗa masa ne ya sanya shi miqewa yana furta “INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI’UN! Kuna wani asibiti? Okay to ganinan zuwa yanzun nan” ya faɗa yana ficewa a palourn, tarar da Hajja da kaka-Aliyah yayi zaune amma bai bi ko ta kansu ba ya fice, ganin jiran driver zai ɓata masa lokaci sai ya ɗau mota da kansa ya nufi hanyan asibitin da aka ce masa.

Hajja dai tun fitan Alhaji hankalinta bai kwanta ba, nan ta wa kaka-Aliyah magana bari tana zuwa, ta miqe ta shige ciki.

Wayanta t ɗauka ta qira layin Alhaji yafi sau uku amma bai ɗauka ba haqura tayi ta koma palourn ta zauna, sai kuma ga Hindu ta fito riqe da hannun Maimoon, Hajja da kaka-Aliyah idanuwa suka zuba mata ganin ikon Allah, amma ba wanda yace ko ci kanki.

Hindu na jan Maimoon tana tirjewa har da kuka, Dr Mufaddal da muryan Maimoon ya fito da shi ganin abinda ke faruwa da abinda Hindu ke faɗi yana isowa ba ɓata lokaci ya ɗaga hannu ya kwaɗa mata mari yace “sake mun hannun yarinya kiyi tafiyanki”.

Idanuwanta a bushe tace “wallahi sai na tafi da yarinyata ba wanda ya isa ya hana ni” duka maganan da suke cikin harshen Indianci ne dan haka Hajja bata san ma me ke faruwa ba, ganin suna qoqarin yin abinda bai kamata ba Maimoon cikin kuka ta fara magana “shikkenan Papa kayi haquri mu koma na haqura da Mustapha, Ammaa kiyi haquri ki daina na haqura mu koma..”, Nura da ya shigo hankali tashe shi ya kaste maganan Maimoon, cikin damuwa Nura da tashin hankali yace “Hajja Alhaji yayi hastari suna asibiti”.

Dukkan su miqewa suka yi suna salati, Hajja da gudu tayi cikin ɗakinta ɗauko hijab, nan ta tarar da misscall na layin Alhaji.

Hajja, kaka-Aliyah, Nura, Dr Mufaddal duka suka fice za su yi asibiti bayan ya gama jawa Hindu kunne kar ta yarda ta fita da Maimoon a gidan nan.

Suna fita suka ɗau hanyan asibitin da aka kai Alhaji sun isa an shiga da shi accident and emergency dan yayi rauni sosai, nan Hajja ke tambayan Nura dama ina Alhajin zai je? Nura ya buɗe baki zai bawa Hajja amsa sai yaga qiran yayan babansu ya ɗauka, jin abinda baffa babagana ya faɗa sai ya sanya salati yana faɗin “okay gamunan zuwa Alhajin ma ya samu hastari muna asibiti a cikin Gomben”.

Hajja dubansa tayi ta ce “kai da wa?

<< Jahilci Ko Al’ada 18Jahilci Ko Al’ada 20 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×