Nura ya ce “Hajja wai hastari su baffa suka samu a hanyar shigowa Gombe yanzu suna asibiti amma Allah yayi wa baba-alhaji cikawa”.
Innalillahi wa inna ilaihirraji’un! Shine abinda su Hajja duka suka furta dan sunsan baba-alhaji, Hajja hawaye ta fara tana maimaita sunan Allah a zuciyan ta da bakinta dan tasan wannan babban rashi ne, Alhaji kuwa har yanzu bai farfaɗo ba, nan Nura ya barsu shi kuma ya nufi asibitin da su baffansa suke yana qiran layin Mustapha baya shiga.
Ɓangare su Maimoon kuwa su Dr Mufaddal na fita Hindu taja hannun ta sai dai su tafi, ta tirje ta tirje amma tace zata saɓa mata ganin haka sai ta bita amma tana qiran layin Mustapha baya shiga kaman za tayi kuka haka suka fice a gidan, ba tare da sanin ina suka nufa ba kawai suka hau hanya.
“Mustapha ya kamata kaje gidan kaji ya za’a yi tunda ka ce baba-alhaji na hanya ya kamata kaje komai ayi ya wuce ko” faɗin wani matashi wanda da kaɗan ya girmi Mustapha a shekaru.
Cikin yanayin gajiya da kuma damuwa da yake ciki ya ce “Yusuf ba za ka gane ba, wannan stohon fitinan sa ya wuce duk tunaninka kuma Alhaji jin maganansa yake kaman shi ne babansa ba kakansa ba, nasan zai iya sanya Alhaji ya stinemin akan Maimoon ni kuma Allah ya gani ina qaunarta ba zan iya rabuwa da ita ba ko za’a stinemin, aurena da Maimoon har mutuwa ba saki Insha Allahu sai dai duk iya gwagwarmayan rayuwa a yita a jure, don baiwar Allahn nan qauna take mini bilhaqqi wanda a wannan zamani da muke ciki samun mace ta maka irin soyayyan nan ko a film albarka, domin su mata da kake ganinsu in suka ce suna son abu tsakani da Allah to hakan suke nufi har iya ransu, mata basa karya zuciyan namiji sai dai shi ya karya nasu, in har kaga namiji na zancen mace ta karya masa zuciya to kayi bincike da kyau zaka tabbatar da gaskiyar lamari ba hakan bane, mata daga kan ciwon da suke na al’ada zuwa ɗaukan ciki da renon ciki da kuma haifan ciki to daganan zaka fahimci suna da ƙawa-zucin da duk iya sheɗancin wasun su to tabbas wasun su imaninsu da tausayinsu da soyayyansu ba abu ne da za’a ɗauka a wasa ba balle ace zasu iya karya waɗannan abubuwa, Maimoon na qaunata kuma nima ina qaunarta, ina fatan zama da ita kaɗai amma tun kamun ayi nisa qaddara ta sanya nayi wata matar kamun ita, to wannan qaddaran ba ni da ikon guje mata inta tashi aiki a gaba, ni dai fatana Allah sanya duk wata qaddara da zata shigo rayuwarmu ta zama ta alkairi”.
Murmushi Yusuf yayi kamun ya ce “wato kai irin ga ka alaramma ko? Ba za ka mata ko da ɗan daɗin bakinmu na maza ba, ai dai kasan zaka sanyata farin ciki ko taji daɗi ta sake tayi maka qauna dai-dai gwargwado, domin su mata da kake ganinsu sai ana haɗa musu da ƙarya inba haka ba lamarin ba zai tafi dai-dai yanda ake so ba, ” ke kaɗai ce babu qari” sai kaga wannan kalmomi da basu wuce biyar ba su sanya mace haukacewa a kanka ta yarda daga ita babu watan, amma kai a gefenka kana samun hali da kuma wacce kake so sai ka auro abarka ai Allah ne ya halasta shikkenan tayi haukanta ta gama dole ta zauna da kai domin tana sonka”.
Taɓe baki Mustapha yayi ya ce “tabbas a JAHILALLEN AL’ADA tamu ta maza da muka ɗauka ba laifi ne faɗawa mace haka ba, amma ina so ace ba iya ni da kai ba so nake mazan duniya duka su fahimci wani abu guda ɗaya shi yiwa mace ƙarya akan daga ita ba qari bai da fa’ida domin wani daga nan yake jawa kansa reni a wajan matarsa tunda alqawari ya ce, kaga kuma duk wanda bai cika alqawari ba shi da Ubangiji kuma kimarsa da ƙwar-jinin sa ga al’umma disashewa take yi, sannan ka zama ba abun yarda ba ga mace wanda kuma in ana zaune tare to fa tabbas ana so a yarda da juna zama tafi inganci, sannan ka sani a addinance da ka yiwa mutum qarya ka sanya shi farinciki gwanda ka faɗa masa gaskiya ka sanyasa baqin-ciki ko da kuwa yaya abun yake domin ita ƙarya raminta ƙurarre ne kuma fure take bata ‘ya’ya, amma ita gaskiya komin daren daɗewa sai farinciki ya maye gurbin baqin-cikin da mutum ya shiga na ɗan wani lokaci, sannan da kake cewa dole mace ta zauna da kai domin tana sonka, amma ba ka san cewa soyayya na komawa qiyayya ba? Kuma gwanda qiyayya tun ranar farko akan qiyayyan da ya samo asali daga soyayya, akwai tashin hankali a ciki da rashin kwanciyan hankali wanda muke ganin laifin matan mu akan suna aikatawa dan mun ƙara aure amma a baɗinance mu munsani mune muka ja komai kuma mune muka haddasa komai amma sai muke maidawa kansu, tabbas Allah ne ya halasta amma karya zuciyar mace ta hanyan mata ƙarya mara amfanu wannan Allah bai halasta ba, ana so ne duk lokacin da kake neman mace da niyar aure to ku gina komai kan gaskiya duk da akwai wajaje da ɓoye wani abun ya halasta dan ka auri mace amma wannan abu baya ciki, sai dai kuma a wannan duniya tamu mun ɗauke sa AL’ADA wanda ni a gani na JAHILCI KO AL’ADA za’a qira sa oho, amma dai tabbas ba AL’ADA mai kyau bane, munsan wani abu qaddara ne da kuma jarrabawa amma tun ranar farko sai ka nunawa mace iya gaskiyanka sai kaga daga baya ko da menene zata fahimce ka Insha Allahu duk iya wuyan sha’anin mace a wajan kishi sai kaga Allah ya wanke ka ya fahimtar da ita, Allah kawai ya kyauta mana amma a gaskiya ni ba zan yi daɗin baki ko ƙarya a inda nasan in abun ya wuce za’a iya shiga tashin hankali ba”.
Yusuf na dariya ya bugi kafaɗan Mustapha cikin wasa ya ce “to shugaban masu faɗan gaskiya sai aje aji da baba-alhaji ko aji da Maimoon Allah kawo ciki da goyo, yau-yau ɗin nan Allah kawo rabo”, Mustapha na dariya ya miqe yawa abokin nasa sallama ya hau motan sa ya kama hanyan gida.
Yana tsaka da tuqi kaman ance masa kalli gefen can, kawai ya hangi Maimoon da mahaifiyarta, yana mamaki ya sauya aqalar motar sa zuwa side da suke yayi parking a gabansu, fitowa yayi a motan amma kamun yayi magana tuni Maimoon ta shige jikinsa, Hindu ta dinga surutu wanda daga qarshe Hajja ya qira ta haɗa su da Dr Mufaddal kamun Hindu ta haqura ta shiga mota suka koma gida, suna isa Hindu ta sauqa ta shige ciki, shi kuma ya kama hannun Maimoon suka nufi sashin sa.
Asma’u na zaune tana jiran isowan su baba-alhaji su Mustapha suka buɗe qofa suka shigo, ɗago kai tayi amma ganinsa da Maimoon ba ƙaramin ɓata mata rai yayi ba dan haka sai ta fara habaici “anyi ba’a yi ba wai anraka baƙo kuma baƙo ya dawo, domin yanda aka sake ni haka za’a saki mutum, kuma Allah na tuba wani dare ne jemage bai gani ba, ai sai dai daren mutuwarsa, da ɗi da ƙari ko a jikina wai an mari kakkausa..” hausa ta dinga yi wanda ita dai Maimoon ba hausan take ji sosai ba balle a kai ga baqaqen magana, shi kuma Mustapha ko a jikinsa sai ma rungumota da yayi suka shige ciki, ganin shigansu kaman za tayi kuka haka ta miqe ta shige ta ɗauko wayanta tayi ta aikin qiran layin fanne amma baya shiga balle a ɗauka har ta ajiye wayan sai ta tuno da kawunta da suka taho tare nan ta qira shi ta samu layinsa busy, sai can kamun ya ɗauka suka gaida sama-sama nan yake faɗa mata abunda ya faru da asibitin da suke, kuka ta sanya tayi jifa da wayan ta sanya mayafi ko ta kan su Mustapha bata bi ba ta fice ta nufi aisbiti.
A ɓangaren Mustapha kuwa fitowa yayi kitchen na sashin Asma’u ya sama musu abinda za su ci sannan ya koma ya lallaɓa Maimoon ta ci suka shiga farantawa junansu dan kusan sun manta da meke faruwa ma, suka lula duniyar su ta ma’aurata.
Hindu tunda ta shiga take ta surfa masifa qarshe ganin Maimoon bata shigo ba sai ta kishingiɗa zaman jiranta har dai bacci ya ɗauke ta, ɓangaren Asma’u kuwa asibiti ta nufa, nan ta tarar da Nura da kawunanta biyu da kuma jikinsu da sauqi suna zaune, amma fanne da yayanta da kuma kawunta dake jan motar duk sun samu rauni, kawunta ya karye a ƙafa, yayanta kuma kansa ne ya bugu sai fanne da ƙashin guiwanta ya goce hannunta ya samu karaya biyu sannan kanta ya bugu shima sosai, sai baba-alhaji da Allah yayiwa cikawa tun kamun a iso asibitin.
“Innalillahi wa inna ilaihirraji’un! Shi ne abinda itama Asma’u ke maimaitawa wacce tun ba’a je ko ina ba har nadama ta fara shiganta domin a ganinta ita ce taja komai sanadinta ne suka kamo hanya.
Anan Gombe aka wa baba-alhaji sutura aka kai shi hanyan bajoga (maƙabarta) aka zauna zaman makoki, da kuma jinyan su fanne dan Alhaji yaji sauqi shi kam, ɓangaren Maimoon da Mustapha soyayyar su suke sha duk da kuwa rashin da aka yi dan tun ranar da Mustapha ya kai ta sashin sa to kullum tana can sai in ta shigo gaishe da su Hajja da su kaka-Aliyah, Dr Mufaddal da Hindu tun da aka yi sadakam bakwai suka koma suka bar kaka-Aliyah.
Fanne ma zuwa yanzu taji sauqin jikinta, wanda ganin haka sai Alhaji yasa duka aka tattaru aka tafi Maiduguri dan saura kwana biyu ayi sadakan arba’in, sun isa lafiya da kwana biyu aka yi sadaka jama’a saura aka waste, family meeting aka haɗa wanda anan aka qara jajantawa juna na rashin babban bango tsayayye da aka yi, yayansu babba wanda yake ɗa a wajan baba-alhaji ba jika ba shi ya fara jawabi “da farko dai ina mai bamu haquri duka akan wannan rashi, kuma muna masa fatan samun rahama da gafarar Ubangiji, Allah haɗa shi da Annabin Rahama SAW, tun da abubuwan nan ke faruwa ban so sanya baki ba dan gudun mastala da yawan ka-ce-na-ce amma duk da haka a yanzu Allah ya sanya ni a matsayin da dole nayi magana, kai Mustapha ta kanka zan fara domin kuwa iyayenka basu da laifi sai dai abinda baza’a rasa ba, Mustapha tunda ka tashi iya rayuwarka kana zuwa cikin ƴan uwa kai kasan irin aure da muke ta AL’ADA wanda har shi mahaifin naka wannan AL’ADA tayi aiki a kansa, ya fara neman yarinya ƴar yare amma ba ƴar dangi ba an taka masa birki kuma ba tare da ja’inja ba ya amince ya auri mahaifiyarku gata nan Fatima ƴar albarka, wan ka shima ganin tsarin family sai ya nemi ya auri ƴar dangi dan aka ce ” zaman lafiya yafi zaman ɗan Sarki ” sannan tunda muke a zuria’an mu ba wanda ya taɓa gigin ko gangancin karya wannan AL’ADA tamu ta tun iyaye da kakanni sai kai Mustapha, tabbatas ba kayi dai-dai ba wanda garin rashin jinka ya jawo mutuwar hatsari ga mahaifinmu duk da dama mu munsani kowa da irin hanyar da tasa mutuwar zata ɓullo amma baka kyauta ba, ina fatan za ka gyara dan kai ma zuwa gaba ka samu ‘ya’ya masu jin maganar ka da kiyaye dokar ka?
Mustapha da kansa ke ƙasa haquri ya bayar bazai qara ba, numfasawa dattijon da ke magana yayi ya ɗaura da faɗin “madallah da mai babban suna, to Allah maka albarka ya albarkaci zuria’an ka, yauwá dai magana ta biyu duka wa kai, abinda ka aikata na saki bai kamata ba sam-sam, eh tabbas munsani Allah ne ya halarta saki amma fa shi ma Allah da kansa baya son sakin dan duk sa’ilin da aka furta saki ga mace to al’arshin Ubangiji sai ya girgiza, Mustapha baka kyauta ba ko ba komai ita ‘yar uwarka ce sannan kuma mu da ka ganmu bamu saki don yaranmu maza da mata masu biyayya ne da jin magana na magabatansu da mazajensu tun da nake a zuria’an mu na taso ban taɓa jin ga wani yayi saki ba a’a sai dai wance ta rasu sai mijinta ya auro wata qanwarta ko ‘yayarta, akan batun saki baka kyauta ba ko da me ta maka amma ba komai Allah sa haka ne alkairi gare ku da mu duka, sannan sai magana ta ƙarshe akan matsayin aurenka da Maimuna, ni na amince maka sannan ina binku da addu’an alkairi kuma ina fata kowa da ke nan wajan ya aminta da batun kuma ya sanya muku albarka” da idanuwa yake binsu dan jin ko akwai mai ja da batun auren.
Fanne da take ji kaman ta shaqe baffan nasu da ke magana ita ce ta fara buɗe baki tayi magana “gaskiya ni dai ban amince da maganan auren nan ba tunda har zai iya wulaqanta ‘yar uwansa akan bare tun ba’a je ko ina ba, inaga in abu yayi stamari? Ai muma sai ya wulaqanta mu akanta duk da yanzun ma ya wulaqanta mu ɗin”.
Murmushin manya dattijon yayi kamun ya ce “bayan ita babu wani mai magana?
A cikin mutane talatin da ɗauri da ke cikin babban palourn kwata-kwata mutum 2 ne suka yi magana da fanne da wata yarinyar baba-alhaji Mama-kumboji, ganin haka murmushi dattijon ya kuma yi sannan yace “to Alhamdulillahi! na ɗauka rabinmu basu yarda ba ashe kusan dukanmu za’a ce sun amince, to Masha Allah! Ke kumboji ke babbace ina so ne kiyi tunani da hankalinki ki yanke abinda ya kamata kamun kice wani abu kuma karki kawo son zuciya a cikin tunaninki, ke kuma fanne zan miki uzuri ke yarinya ce kuma kina tunanin duka mu bamu qaunar ‘yar wajan yayarki Asma’u, amma karki manta nine mahaifin baban Asma’u sannan ga Gambo ga Baana sune iyayen mahaifiyar Asma’u abun nufi iyayenki kenan kema ko, to duk da ke yarinya ce inaso ki duba me yasa su basu ce komai ba inkin dubo abun na tabbata kema za ki aminta, wannan aure na Mustapha da yarinyar nan maimunatu ina so ku sani duk mu ɗauke sa a Allah ya qaddaro ne ba yanda aka iya, kuma ina mai kyautata zaton akwai alkairi da kuma rabo wanda Allah ya ɓoye a auren dan haka ina umurtanmu duka da mu bisu da addu’an zaman lafiya, sannan ina so nayi magana ta ƙarshe wanda ba iya Mustapha ba dukkanmu da yaran da zamu haifa gaba ina so a kiyaye aikata irin wannan laifin, a stayar iya kan Mustapha ga dai yara nan Masha Allah kowa na haifa sannan ko mace guda ko mata 4 mutum yake buqata akwai su a dangi Allah ya hore mana haihuwa dai-dai dai-dai duk da dai yaranmu basa wuce uku biyu, to Allah musu albarka, Allah albarkaci zuria’an mu gaba-ɗaya Allah qara haɗa kawunanmu, Allah yajiqan magabatanmu ya rahamce su, to sai duk wani mai abun faɗa a shawara ko abinda ya kamata muna sauraro”.
Kumboji ce ta bada haquri sannan ta sanyawa auren albarka wanda hakan yayiwa kowa daɗi musamman iyayen Mustapha, nan dai aka tattauna abubuwan da suka kamata sannan taro ya waste, a ranan Alhaji, Nura, Mustapha, Hajja, Maryam mai stohon ciki da Maimoon da kaka-Aliyah suka tattaro suka dawo Gombe inda aka baro Asma’u acan tunda ba wanda yayi maganan komawanta.
Bayan kwana biyu da dawowan su kowa ya huta nan Alhaji ya zauna da dukka iyalan nasa, ya maimaita musu a kiyaye sannan ya sanya albarka wa auren wanda shi dama da jimawa ya sanya musu albarka, daga qarshe ya maida dubansa kan kaka-Aliyah ya ce “mama ina mai matuƙar baku haquri na abubuwan da suka faru ayi haquri a yafe mana”.
Murmushin manya kaka-Aliyah tayi sannan ta ce “bakomai Allah ya yafe mu duka, Allah basu zaman lafiya da zuri’a masu albarka sannan ina fatan kunga abinda nake guje muku na qoqarin ja da abinda Allah yake nufin qaddarawa, daga qarshe nima zan baku shawara guda, duk da dai munsani AL’ADA wani abu ne da mu mutane muka riqesa gam-gam kaman addini ko Farilla ko Sunna, eh tabbas akwai wasu AL’ADUN mu da suke zama halas a addinance daganan sai ya zama addini ba al’ada ba kaman ace a al’adanmu mace sai ta sanya hijab ta rufe jiki, babu yin zina, babu shan giya da dai sauransu to Masha Allah wannan ne AL’ADA da addini ma ta yarda da shi amma kaman hana aure da sauran su muma munsan me muke yi amma ba al’ada ba, to shawarata ita ce ko nan gaba wani abun ya ɓullo kar ku nemi jaa da hukuncin Ubangiji ku dai komai za kuyi kubisa da addu’a dan kaman yanda na faɗa tun farko in Allah ya qaddara abu barinma aure kuma ace da rabo ciki to fa s kiyayi Allah domin sai ya ɗauke mutum kuma ayi abun ba wanda ya isa ya hana, Allah ya kyauta to, da farko nace zan zauna da jikata amma yanzu dai ina buqatan komawa”.
Alhaji dai bai ce komai ba, Hajja ma kusan hakan sai rufe taro da addu’a da aka yi.
Bayan sati guda kaka-Aliyah ta koma India, inda Dr Mufaddal yaji daɗin abinda ya faru na amincewa da aka yi da auren yarinyar da haka a ɓangaren Hindu ma, bayan wani lokaci Maryam ta haiho yaranta tagwaye mace da namiji ranar suna yara suka ci sunan kaka-Aliyah da kuma mahaifin Maryam, wannan abu yayiwa Maimoon daɗi nan suka ci-gaba da zamansu cikin aminci.
Labari ne ya samu Maimoon na rasuwar kaka-Aliyah, tayi kuka har ta godewa Allah sannan suka tattara suka tafi ta’aziya amma acan suka baro ta sai an yi bakwai ita zata dawo, a wannan lokaci ne kuma Asma’u tazo har Gombe ta bawa Mustapha haquri sannan ta roqi su Hajja tafiya da kuma qoqon baran su roƙa mata Mustapha ya mayar da ita, ba tare da musu ba yace shi bai da matsala amma sai Maimoon ta dawo, bayan kwana biyu Asma’u ta koma Maiduguri.
Maimoon anyi bakwai ta dawo cike da kewan iyayenta, bayan dawowanta da kwanaki Hajja ta mata maganar Asma’u nan ta amince bakomai, ba ɓata lokaci aka qara ɗaura auren Asma’u da kuma Mustapha, rayuwa suke cikin kwanciyan hankali wanda a lokacin kuma aka gane Maimoon nada juna biyu kusan na watanni huɗu, kowa yayi farinciki, Mustapha ya dinga kula da ita da abun cikin ta, Asma’u ta sani Mustapha Maimoon yake so amma ganin itama tana sonsa sai ta kawar da kai tunda tasan Maimoon mai kirki ce kuma tana ƙoƙarin ganin sun zauna lafiya.
A lokacin da cikin Maimoon ke da wata 7 yaran Maryam na da watanni biyar a duniya kwastam aka wayi gari duk babu su, rashin yaran ya taɓa Maimoon sosai dan inka gansu tare kai kace ita ce ta haife su ba Maryam ba, abinda ke haɗa su da Maryam shan nono, cikin Maimoon na cika wata tara ta haifo santalelen ɗan ta namijin inda ya ci sunan kakansa MUFADDAL, sai Maimoon ta yiwa sunan alkunya da Darling. Maryam ta qara haihuwa yaro namiji ya koma ta qara haifo namiji lokacin Mufaddal na da shekara biyu sai akan wannan yaron mai suna Jabeer ya tsaya, tun Daga kan Mufaddal Maimoon bata qara haihuwa ba, har ya kai shekara biyar inda a lokacin Asma’u ta samu juna biyu ciki nakai haihuwa kuma a wajan naquda ita da yarinyar nata Allah ya amshi ransu, Maimoon tayi kukan rashin Asma’u sosai domin zaman lafiya suke yi.
Sai da Mufaddal ya cika shekara goma ciff a duniya sannan Allah ya azurta Maimoon da samun wani cikin wanda a lokacin kuma Maryam matar Nura ta haifi yara kusan 6 amma duk sun koma saura biyu, Jabeer mai shekara 8 sai Afreen mai shekara 2.
Maimoon ta haifo yarinyarta mace inda taci suna MUHSEENAN amma suna qiranta da sweedy daganan kuma bata qara haihuwa ba sai da yarinyar ta shekara biyar, nan ma mace ta haifa MUNAWWARA suna qiranta sweerie, wanda a lokacin bayan shekara guda Maryam itama ta haifo mace nan taci sunan Hajja suna qiranta Afrah, takwarar Hajja na da wata guda a duniya Allah yayiwa Alhaji rasuwa, wannan mutuwa ta girgiza alhalin Alhaji da ma ƴan Maiduguri dan kowa ya sanshi mutum ne mai haquri da kuma biyayya, bai kai mako guda ba tsakani mahaifiyar Maimoon itama Allah ya mata rasuwa, a lokacin Mufaddal na da shekara 16 kuma zuwa lokacin ya sauqe Qur’ani mai girma yana karantan business a India dan kusan acan ya tashi, Mufaddal yaro mai kyawu na wuce misali, ga haquri ga kuma zuciya sannan baya ɗaukan raini, tunda ya taso cikin soyayyan iyaye da kakanni duka ɓangare biyu sai dai Hajja da kawai suke kaman ‘yar stama kullum, ga shi dai tana sonshi sosai amma kullum cikin masa stiya take, shi kuma Allah ya wadata shi da saurin fushi ga zuciya sai dai yana da haquri da sauqa da wuri.
Sai da aka shekara biyar kamun Maimoon ta kuma haihuwan mace taci sunanta MUHEEBBAH suna qiranta sweetie, daganan kuma haihuwa ta staya wa Maimoon dan Maryam kam tana kan haihuwan amma tun daga kan Afrah yaran basa stayawa, ganin haka daga qarshe sai suka ɗaure mahaifan kawai, Allah yasa wa waɗanda suke da su albarka.
Tun da aka tura Mufaddal karatu a CANADA nan ya ce yaga wajan zama, ba tare da ansani ba takwaransa Dr Mufaddal ya saya masa gida ya buɗe masa babban Company, rayuwa yake hankali kwance yana Canada yana India in dai ka gansa a Nigeria sai an shekara, amma abun na damun Maimoon wacce suke qira da Ammi.
A ɓangaren familyn Alhaji kuwa rayuwa suke tsaftacciya, musamman Maimoon da Mustapha da yaransu ke qiransu da Ammi da Abiy, soyayya ne suke ma junan su ba na kaɗan ba, Abiy na qaunar yaransa da matar sa, da yaransa da yaran yayansa Nura da suke qira da Daddy inka gansu ba zaka banbance su ba, yaran duka kyawawa ne duk sun ɗauki kyawun kakansu Alhaji amma su sweetie sai nasu ya zama daban da suka haɗa da jinin indiyawa, shi Darling Mufaddal kuwa ya fita daban daga matan har mazan ba mai kyawun sa, Hajja duk tafi sonsa a jikokin ta sai kuma bi da Afrah takwararta, amma son da take wa yaran Mustapha daban ne ta rasa dalili, tun asali son da take wa Mustapha a cikin yaranta daban ne sai ya zama akan jikoki ma haka, amma bata nuna hakan dan gudun kawo rabuwan kai cikin zuria’anta.
Jabeer ma ya bi Mufaddal da abokanayensu ke ce masa DMD(Darling Mufaddal) suna Canada yana karantan likitanci, komai nasu tare suke yi, in ka gansu kace twins ne sai dai banbancin hali kawai, domin Jabeer da shi kuma abokanai ke ce masa Jay (Jabeer) mutum ne shi mai son surutu, ba shi da fushi ko kaɗan, akwai son kyauta ga son raha.
Dr Mufaddal da zuwa yanzu yayi ritaya kuma yake da tulin dukiya, ganin dai Maimoon mace ce sai komai nasa ya ɗaura Mufaddal wanda lokaci ɗaya Mufaddal ya zama babban attajirin mai kuɗi, rayuwarsu suke suna sharholiyan su amma ba ruwansu da harkan mata ko shaye-shaye barsu dai da yau ana nan gobe ana can, shi dai Mufaddal yana binsu ne dan yawanci komai shi yake biya amma ko yawan magana bayayi dan haka ya tashi surutu da yawa sai ya fara ciwon kai, akwai ranar da suka je wani club tun da suka matsa masa yayi rawa ya yanke jiki ya faɗi to tun daga lokacin ma ya daina binsu komai za’a yi yana gefe sai dai ya biya.
Kwastam wani zuwansu Maiduguri sai wata yarinya Rabi’atu ta maqalewa Abiy, duk da dai ba qaramar yarinya bace dan ta manyanta amma kuma bata taɓa aure ba, tun Abiy na basarwa har yaji shima ta masa, domin kuwa Rabi’atu ba qaramar makira ba ce ta kware a iya kirsa, Ammi tun da ta fahimci hakan sai bata nemi jan dogon magana ba da kanta ta samu Abiy ta ce masa gwanda ya aureta tunda tana sonsa kar ta sanya shi aikata abinda bai aikata da samartakan sa ba, Abiy dai yayi borin kunya daga baya ya sanar da Hajja, ita dai bata isa ta ce komai ba, dan abun ba qaramin karɓuwa yayi wajan dangi ba, masu haushin auren sa da Maimoon dama nan suka bada mubaya’a gwanda ya auri ƴar uwar sa tunda Allah yayiwa Asma’u rasuwa, ba jimawa aka ɗaura auren Abiy da Aunty Amarya (Rabi’atu).