Skip to content
Part 21 of 24 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

Tun da Abiy ya auro Aunty Amarya nan fa suka fara samun damuwa da Ammi, duk iya qoqari da haƙurin Ammi da kawar da kai amma sai Aunty Amarya ta kimsta mata munafurci.

A wannan lokacin ne kuma Hajja ta buqaci komawa Ashaka wai zaman Gombe ya ishe ta tunda babu mijinta, Abiy da Daddy sun-yi-sun-yi amma firr Hajja taqi zaman cikin Gombe, ganin haka ba yanda suka iya suka amince kawai aka gyara gidan su dake can Ashakan ya koma ginin zamani da komai da komai, suka nemo mata ‘yan aiki da driver da mai gadi, sai da aka zuba komai sannan aka sanya ranar komawanta. 

Abiy zuwa wannan lokaci gaba-ɗaya ya sanjawa Ammi daga Mustaphan da ta sanshi ya koma wani Mustapha daban, a da dai ta san yana sonta amma a yanzu ba ta da bakin faɗan yana sonta amma kuma bata isa ta ce baya sonta ba, abubuwa ƙara kacamewa suke, akwai ranar da Hajja ta ga abinda Aunty Amarya ke yi na mugunta ga su Munawwara, faɗa ta mata sosai sannan ta stawatar wa Abiy da ya kwaɓi matar sa akan jikokinta ko su samu matsala, Abiy yama Aunty Amarya faɗa ita kuwa ganin haka sai ta nuna ta amshi laifinta duk da ba mugunta tayi ba amma kuma a gefe guda kistawa Hajja munafurci take yi, ba’a jima ba Hajja abun ya isheta ta koma Ashaka da zama, bayan Daddy ya bata Afrah su zauna tare.

Ammi dai komai aka yi sai ido take binsu da shi daga Abiy har Aunty Amarya ba um ba umn’umn, abu ɗaya ya isheta rashin zuwan Mufaddal, daga qarshe dai ta buqaci zuwa India amma Abiy da qyar ya amince bayan ya ce sai dai tabar masa yaransa ta tafi ita ɗaya, Ammi dai bata son ja’inja dan haka ta ɗauki Muheebbah kawai suka tafi, sun isa lafiya Dr Mufaddal da ya manyanta zuwa yanzu sosai yaji daɗin ganinsu, amma ganin yanayin yarinyar sa kaman tana cikin damuwa nan dai ya masta mata da tambaya amma ta ce ba komai daga qarshe fita harkanta yayi yana bin ta da addu’a, damuwan ta na rashin zuwan Darling gida kawai ta faɗa masa amma shima ya ce ba yanda baya yi da Mufaddal yaje Nigeria sai yaqi shiyasa ya fita harkan sa dan gaba kaɗan in ya mallaki hankalin kansa to zai je.

Cike da damuwa Ammi ta fara magana cikin Indianci dan sosai abun ke mata ciwo, Allah ya gani tana qaunar Mufaddal fin tunani “Papa yanzu Darling bai girma ba? Shekara ishirin da ɗori fa, yaro gaba-ɗaya baya son mu baya son zuwa wajan mu, ni abun na damuna dan kaman abun maita kullum qannensa cikin maganan sa suke yi, ni inaga qarshenta tattara su zan yi na kai masa su fama, ace yaro bazai waiwayi iyaye ba, gaba ɗaya yaja ana ganin laifi na, yaron nan ga mahaifinsa ga kakansa amma ba wanda yake tunanin zuwa dubawa sai ya dinga sanya ni damuwa kawai shi a barshi da iya qiran mutane kaman ance masa lokutan mu duka nasa ne ko da yaushe qira kawai..” cikin ɓacin rai Ammi ta dinga faɗa daga qarshe Dr Mufaddal da qyar ya danne zuciyarta bayan ya qira Mufaddal a wajan ya ce masa lallai-lallai nan da kwana biyu ko me yake yi yayi squeezing na sa ya zo, ganin yaron ya amsa zai zo ne nan hankalinta ya kwanta, suka dinga hira da mahaifinta har yake faɗa mata hukuncin da ya yanke na damqawa Mufaddal dukiyar sa, ba tare da taja ba ta ce “Allah ba shi ikon kula da dukiyan” da “Ameen” Dr Mufaddal ya amsa yana zolayan sweetie da ke kwance a jikinsa.

Ɓangaren Abiy da Aunty Amarya soyayya suke sha, dan Ammi na tafiya Aunty Amarya ta ji kaman ansarara mata an bata iska, ganin wannan sakewan ta qudurin aniyan koran Ammi a gidan, gefe guda kuma tana gallazawa Munawwara da Muhseena duk da dai ita Muhseena kusan halin Darling gare ta amma duk da haka Auntya Amarya sai da ta sanya mata karan zuqa.

Habibty (mummy) tana kallon duk abinda ke faruwa, amma ba ta da bakin magana dan akwai ranan da ta sanya baki amma abun ya zama magana har Daddy ya mata faɗa, ganin haka sai dai ta bar su a ɓangaren ta inkuma Aunty Amarya ta qira su to bata hanasu zuwa dan har dukan yaran tana yi kuma ta hanasu faɗawa kowa.

Sai da Ammi ta kwashe sati guda a India amma Darling bai zo ba, fushi tayi ta daina ɗaukan wayansa, ga hankalinta ya koma kan yaranta da mijinta da kullum sai ya qira yaushe za ta dawo, abun na bawa Ammi mamaki in dai tana gida kullum suna faɗan da babu dalili dan watarana haka kawai zai shigo ya dinga mata masifa batasan hawa ba balle sauqa, amma indai za’a ce yau ta ɗaga ƙafa ta fita to fa ko anguwa ne ya dinga qira kenan ta dawo, to abun na bata mamaki qarshe dai ta bar hakan akan yanayin rayuwa dan bata taɓa ɗaura alhaqin komai akan abokiyar zamanta ba.

Dr Mufaddal da dawowansu kenan daga zaga gari da yarinyar tasa da jikar sa, da mamaki yake kallon Abiy da ke tsaye cikin gidan kaman wanda aka ce wani nasa ya mutu, bayan sun shiga ciki sun gaisa Dr Mufaddal ya ja jikarsa suka basu waje, suna tafiya Abiy ya rungume Ammi wai yayi kewanta, qarshe ɗaki suka qarisa suka baza soyayyan su sannan ya fito ya sallami Dr Mufaddal ya koma Nigeria yana mata magiyan ta dawo, Ammi ko dan yaranta tasan ya kamata ta koma dan haka ta shiga shirin komawa duk da bata cika wata gudan da taso tayi ko dan ta hutawa rayuwanta, bayan tafiyan Abiy da mako guda ya kuma dawowa dan wannan karon da qyar ya yarda ya koma ba tare da ita ba, bayan kwana biyu da komawansa suka gama shiri zasu tafi har driver yasa kayansu a mota za su tafi kaman daga sama suka ji muryan Darling, sweetie wajansa taje da gudu ta maqale masa, Ammi dai fushi tayi zata tafi da qyar Dr Mufaddal ya rarrasheta suka zauna, nan kuma ta saki jiki da ɗan nata ya dinga zuba shagwaɓan sa kaman shi ne sweetie, tambayanta yayi “Ammi ina kika baro su sweedy?

Hararansa tayi a wasa ta ce “su kam suna gidan ubansu dan ba su da inda ya fi shi”.

Murmushi kawai Darling ya yi dan yasan nufin ta amma bai ce mata komai ba dan shi yasan dalilinsa na qin zuwa domin tun da Allah yasa Abiy ya auro figaggiyar matar sa shikkenan ya tsani gidan da kuma ganin cin kashin da akewa Ammi kuma bai isa yayi magana ba ita ta ce ba komai dan tana son mijinta, shagwaɓe fiska yayi kaman yaron goye ya ce “Ammi ku dawo wajena a Canada muyi rayuwanmu”.

Kallon yaro man kaza ba ka san me kake yi ba Ammi ta masa, sannan ta ce “in na bika wa zai zauna min a gidan miji na? Ko ka fara raba aljanna ba ni da labari?

“Please dai Ammi Allah hankalinmu kwance mu koma kinji, sweetie ai kina son zama a Canada ko? Ya faɗa yana kallon sweetie da ke cinyan Dr Mufaddal.

Sweetie washe baki ta yi ta ce “eh Darling ina so”.

“Please Ammi mu koma dan na tabbata su sweedy ma suna so”.

Hararansa tayi ta ce “tashi min a jiki nikam tunda aure na kakeso ka kashemun, in qannenka na so sai ka tattara su ba wanda ya hanaka kai ne babban yaya uba kuje can ku fama ni dai ina gidan mijina sai mutuwa kuma Insha Allah, hankalina a kwance a gidana ba inda zan je, kuma kai ma in kayi wasa ka gama zama a qasar waje kenan mu koma kayi aure muga jikoki”.

Tun da Ammi tayi maganan aure sai ya ɓata fiska ya miqe ya shige ɗakin sa, Dr Mufaddal dai yana kallonsu aikin murmushi kawai yake yi yana ƙara jin qaunar tilon yarinyar tasa da jikokinsa, haquri ya bawa Ammi akan ta qyale Darling a can ɗin da sannu a hankali zai fahimta, kuma batun aure in lokaci yayi zai yi.

Abiy ganin an kwana biyu ba idon Ammi nan ya qira ya dinga masifa sai ta dawo ko kuwa ya hanata qara zuwa Indiya, haquri ta basa kan cewa Mufaddal ne ya zo amma sam yaqi sai dai ta dawo shi kam tun da yaron baya qaunar su kar yazo yayi zamansa, abinka da uwa duk da haka sai da ta qara sati guda, Darling na komawa itama ta tattaro suka dawo, amma ganin yanda yaranta suka koma a zamanta na wata guda ma bai cika ba sai da ta tausaya musu, ga shi Abiy ya ce rashin lafiya suka yi, sai kawai ta yanke hukuncin da ta tafi ta barsu gwanda ta haƙura da tafiya kawai.

Rayuwa haka ta dinga tafiya ba daɗi da daɗi sai godiya ga Allah, zuwa yanzu kuwa Daddy ya koma sabon gidan sa da ke Tunfure kuma shi ma Abiy na ƙoƙarin komawa nasa sabon estate ɗin da ke anguwan manya GRA kusa da gidan abokin sa da ke takaran gomnan Gombe, Ammi dai tana ganin rayuwa amma duk da haka bata taɓa bari zuciyarta ta amince sharrin kishiya ne, komai barinsa take yi akan jarabawan rayuwa, tsakaninta da Abiy kuwa ya wuce misali kullum faɗa ba dare ba rana amma kaman kuran ƙarfe ko da ba ranar da yake ɗakinta bane za kaga ya shigo yayi masifa yayi soyayya, kuma duk abinda ke faruwa itama a ɓangaren ta baya damunta sai ma ƙara jin ƙaunar Abiy da take yi.

Hajja dai kullum cikin qiran Ammi take yi ta sauqe mata kondon masifa akan ta hana jikanta zuwa balle ya zo ya ganta, Ammi ta rasa ya zata yi dan ko da ta samu Abiy da maganan ya tsawatar masa ko zai dawo amma qarshe akanta masifan ya ƙaru domin Darling ko wayan Abiy da ya ɗauka bai ce qala ba har Abiy ya gama ya kashe, sai abun ya koma kanta ita ce ta sanya yaron ya rena kowa bata bawa yaransa tarbiyya ba, wannan rana Ammi tayi kuka domin Hajja ta goranta mata an aurota bare kuma Abiy ma ya goranta mata akan tarbiyya, dan haka qiran Darling tayi tana hawaye ta fara magana da Indianci “Mufaddal! Mufaddal! Mufaddal! Ka ji na qira sunanka sau uku ko, to wallahi na ranste in baka zo Nigeria ba babu ni babu kai, me yasa kake so a kanka adinga gayamun magana ne, ko haihuwanka da nayi shi ne laifin da na maka kai kuma, to tun raina bai ɓaci ba ka dawo dan baka isa na haifeka kuma kai ɗaya ka hanani zaman lafiya da mijina ba, in baka zo ba sai na saɓa maka kuma dolenka kayi aure kaji na faɗa maka” qitt tana gama magana ta kashe wayan ya share hawaye dan kar qannensa su shigo su gani, zama tayi tana mai bin yaran nata da addu’an shiriya da alkairi.

Bayan wasu kwanaki Ammi ta fita ta tafi gidan Daddy yara suna makaranta, hiransu suka sha da habibty tana faɗa mata yanda suka yi da Darling ta tabbata suna hanya, mummy murmushi tayi ta ce “amma Ammi kin kyauta dan kuwa wannan yaran zasu ja mana magana su kashe mana aure da girmanmu, na gaya miki jiyannan Hajja ta qira ta dinga surutu wai mun ɗaurewa yaranmu wajan zama basu son aure”.

“Ai Habibty yaran namu sai addu’an shiriya da stawatarwa irin nawa kam abun yayi yawa dan na rasa wani irin zuciya da hali ga Darling ko kaɗan baya storon kowa balle shakkan kowa, ko ni baya jin maganata”.

“To Allah dai ya shirya mana su ya kawo su lafiya” faɗin mummy.

Sai da suka gama shan hiran su har Afreen ta dawo ta mannewa Ammi kamun daga baya Ammi ta musu sallama ta shiga motan ta nufo gida, Afreen sai kuka take aikin yi za ta bi Ammi da qyar aka lallasheta sai weekend.

Ammi na isowa gida tun daga compound na gidan take jiyo muryan ihun Munawwara dan dama sun dawo makaranta ta sani, da sauri har tana tuntuɓe ta shiga gidan, abun ba qaramin mamaki ya bata ba ganin Aunty Amarya na aikin zane Munawwara, ko mostawa Ammi ta kasa sai muryan Darling da taji kaman daga sama ne ya dawo da ita daga hayyacinta, da mamaki take kallon sa yaushe ma ya zo har ya shigo gidan? Ganin abinda yake ƙoƙarin yi tayi saurin dakatar da shi tana faɗin “Darling Maman naka kake nunawa da yatsa tarbiyan da na maka kenan?

Ammi na rufe baki ta jiyo muryan Abiy yana faɗin “tabbas tarbiyan da kika musu kenan ba musawa dan haka kika nuna musu su tayaki kishi, in banda yaro ya zama fistararre matar tawa zai nuna da yasta to tabbas kuwa ka jawa uwarka”.

Da mamaki Ammi da sauran yaran ke kallon Abiy dan Darling ko ido bai ɗaura akan Abiy ba balle wani abun, kallon jan kunne kawai yake bin Aunty Amarya da shi, ita kuma kuka ta fashe da shi har da sheshsheqa tana faɗin “kayi haquri baby dan na hukunta yarinya akan tayi laifi shine laifi na amma ba zan qara ba komai ya wuce kuyi haƙuri” ta faɗa tana kukan kirsa ta wuce cikin ɗakinta.

Abiy da kallon za mu haɗu ya bi Ammi sannan ya juya ya bi matar sa, ita kuwa Ammi Darling ta zubawa ido, ta rasa me zata ce kawai ta shige ɗakinta ita ma.

Qannensa rungumesa suka yi suna kuka, haka ya ja su suka bi Ammi amma tayi fushi taqi sauraransa, suna zaune shiru can sai ga Abiy ya shigo a fusace ko me Aunty Amarya ta kista masa oho, yana shigowa ya kama faɗa ganin haka yaran suka fice a ɗakin, Darling dai yana zaune jikinsa sai rawa yake yana da-na-sanin shigowa Nigeria, bai gama dawowa daga duniyar tunanin da ya faɗa ba ya ji sauqar mari yana ɗagowa ya ga Abiy ne ya mari Ammi, idanunsa jawur ya miqe yayi kan Abiy amma Ammi sai ta riqe sa idonta ba ko ɗigon hawaye tana masa surutu “Mufaddal ba ka da hankali ne me za ka yi? Mahaifinka ne fa ko bayan wanda ka yi ɗazu wani abun za ka kuma yanzun? Da qyar da suɗin goshi ta riqesa qarshe dai kan gadonta ya faɗa a sume,hankalinta ne ya tashi tana jijjagasa, Abiy da ya storita yayi baya ko qala bai ce ba, ya ja staki ya fice, amma fa kana ganinsa kasan a storace ya ke da yanayin yaron nasa dan yasan da an barsa to fa akwai mastala.

Ammi ruwa ta yayyafa masa amma shiru, sai kawai ta sanya shi gaba ta dinga kuka, kaman wanda aka jefo haka Jay ya shigo ɗakin yana tambayanta me ya faru? Ganin Darling a wannan yanayin a take ya fara ba shi taimakon gaggawa wanda da ikon Allah da qyar ya dawo hayyacinsa amma yana riqe da kansa, qarshe sai da Jay ya ɗaura masa ruwa da allurori.

Ammi ta ga tashin hankali dan sai da ya ɗiba kwanki biyu kamun ya koma dai-dai, yana warkewa kuma ya tattara suka tafi Ashaka, sai da ya kwashe sati guda kamun ya dawo a ranan da ya dawo a ranan ya ce zai koma in yaso daga baya Jay ya bisa, Ammi kaman za tayi kuka haka ta lallashesa amma ya ai, daga qarshe dai barinsa tayi ya tafi tana jin kaman ta bi sa, sai kuma daga nan zuciyanta ya fara saqa mata zama da yaranta yafi wannan zaman tashin hankalin dan indai cutan Darling kenan akan ɓacin rai to tabbas yana buqatan mahaifiya ko mata a kusa da shi, amma kuma soyayyan Abiy sai ya danne wannan waswasin son bin yaron nata, haka ta dinga zama Abiy na fushi baya ko shiga harkanta.

Aunty Amarya buri ya cika nan ta dinga baza shagalinta, mummy dai komai aka yi sai dai ta bada haquri amma bata da bakin yin magana kar ace munafurci, Afreen da ke ɗawainiyan son Darling wannan abu da ya faru ya ja bata gansa ba sai ta yanke hukuncin qullawa Aunty Amarya gadar zare tunda taƙamanta takurawa mutane ga shi ta hanata kallon masoyinta, a gefen Hajja dai bata san me ke faruwa a Gombe ba dan yanzu a irin kirsan Aunty Amarya to ita ce ta gaban goshin Hajja sai dai abinka da soyayya da mai kula da kai na gaskiya, har lokacin tana jin Ammi daban a zuciyanta yanda tayi haquri ta dage har ta auri yaronta ta haifa musu kyawawan jikoki.

Sai da aka shekara biyu amma Darling ko ƙofa ta kashin Nigeria bai leqo ba, duk da tunanin qannensa da Ammi na azalzalansa amma da ɓacin ran da zai tarar gwanda masa zama anan yana kewansu, a gefe guda kuwa yana qara lallaɓa Ammi ta dawo Canada dan har kakansa sai da ya sanya a maganan amma Ammi dai ta ce gidan mijinta za ta zauna.

Ana haka Sweedy ta nemi da ta tafi India itama karatun ta amma sam-sam Abiy yaqi sai dai su yi a nan Nigeria, wannan abu ba ƙaramin ciwo yayiwa Ammi ba amma ta shanye tunda dai yaransa ne ba yanda ta iya, Sweedy na qiran Darling ta sanar da shi ba second thought ya shirya komai yanda ya dace, Abiy yayi tafiya zuwa China dan shigo da wasu kayaki na Companynsa masu yin hanya (kwalta) sai kawai Darling ya shigo Nigeria a ranan ya shirya sweerie da sweedy ba tare da ko Ammi ta sani ba ya tattara su suka koma Canada, ba karɓan transfer ba komai da yake kuɗi na aiki nan ya sanya sweerie a makaranta ita kuma sweedy ya fara mata duk wasu shirye-shirye da zata tafi India tayi karatunta bayan sunyi magana da kakansa.

Ammi dai tun fita yara shiru ba su ba labarinsu har dare, qarshe ta qira Darling amma layinsa baya shiga wanda hakan ke mata nuni da baya Nigeria, mamaki ne ya kamata ƙarara ta rasa ya zata yi, dan ko da ta qira layin Canada nan su sweerie suka ce su dai da Darling za su zauna, abun ya dameta ga shi bata san me zata faɗawa Abiy ba in ya dawo kuma ga shi yana dawowa za su koma sabon gidan sa na GRA.

Duk abinda ke faruwa Aunty Amarya na gani dan haka ta gama ƙulle-ƙullenta jira kawai take Abiy ya dawo ta juye masa dan ta ranste ba za’a koma sabon gida da Ammi ba, a gefen Ammi kuwa damuwa ya mata yawa ga kewan yaran ya qaru yanzu ba shi kaɗai ba har su uku, ga damuwan sweetie kullum ita dai yayyunta, ga kuma tunanin abinda Abiy zai yanke, duk abun Aunty Amarya dai Ammi kam baya gabanta dan har lokacin bata jin hausa sosai barta da English ko Indianci kuma yaren kanuri ko ka zo bata ji.

Abiy ba sanarwa kawai ya diro Nigeria, kallonsa ba ƙaramin girgiza Ammi yayi ba amma ta danne, kasancewan a ɗakinta yake nan ta tarbi mijinta, ba tare da ya lura da rashin yaransa ba suka sha soyayyan su, daga yanda Abiy ke tafiyar da Ammi insun haɗe zaka fahimci zallan soyayyan da yake mata amma sai ta rasa me yasa sukeeyawan faɗa.

Washe gari ya tambayi yara nan ta faɗa masa sunje hutu wai Canada, da mamaki yake kallon ta yana maimaita abinda ta ce “hutu a Canada! Yanzu lokacin hutu ne ko menene?

Ammi dai ta rasa ta faɗa daga qarshe dai ɓata mata rai yayi kamun ya koma ɗakin Aunty Amarya, nan kuma ya sanya su shirya za’a yi waliman buɗe gidan nan da two days sai a koma washe-gari in an gama waliman, ba tare da ɓata lokaci ba kowa ya fara shiri duk da dai komai na buqata an zuba a sabon gidan komai na zamani fin na wanda suke ciki, ba buqatan su ɗauki komai.

A ranar da aka yi walima, aka buɗe gida da addu’a da jama’a, sweetie ce ta yanka qyallen da aka sanya na buɗe gidan bayan ta sha kyaututtuka daga abokanan Abiy nan taro ya waste mutane kowa ya koma da takeaway banda wanda aka ci har aka bari.

A ranar da dare bayan dawowan Abiy yana zaune ɗakinsa, Aunty Amarya ta shiga ta kista masa ƙarya da gaskiya, aikam Abiy ya cika yayi fam, paper ya ɗauka yayi rubutu ya kai wa Ammi a daren kuma ya umurce ta da ta bar masa gida kuma kar ta tafi masa da yarinya, Ammi ta shiga tashin hankali a daren ta haɗa komai nata ba tare da ɓata lokaci ba da sassafe ta fito zata tafi, sweetie ta dinga kuka amma Ammi ta tsallake ta yi tafiyanta, Aunty Amarya daɗi ta dinga ji Abiy ya saki Ammi dan haka ta baje, washegari aka koma sabon gida.

Aunty Amarya taji daɗin sabon gida dan komai yayi sai dai baqin ciki take yi duk tulin wannan dukiya bata da ko kakkauran kashi balle ɗa ɗaya mai gada, nan ta fara damuwa ganin koma mene Ammi ce da riba.

Ammi na fita ba ta nufi Indiya ba dan kar ta ɗagawa Dr Mufaddal mahaifinta hankali, sai ta nufi Canada.

Su sweedy kaman daga sama suka ga Ammi, sunji daɗi amma rashin ganin sweetie abun ya dame su, Darling dai ya mastawa Ammi sai da ta faɗa masa komai yanda aka yi nan ya dinga farinciki Abiy ya sake Ammi sun huta, washegari ya shirya ya ɗauko sweetie ko ta kan Abiy bai bi ba.

Ammi taji daɗin ganin autar tata nan tayi murna ta rungumi yaranta suna rayuwa hankali kwance, bata kai wata guda da dawowa ba kawai suka ga Abiy wai ya zo su koma da Ammi da yaransa, ita dai Ammi ko sauraransa ba ta yi ba amma yaran kam abu da uba da ‘ya’ya sai Allah sunji daɗin ganin mahaifinsu, har Abiy ya tafi Ammi taqi kula shi.

Nan fa Abiy ya mai da Canada wajan sintirin sa duk bayan kwana biyu sai yazo kuma sai yayi kwana 2 ya koma, amma duk da haka Ammi ko kulasa ba ta yi duk da duk ranar da ya tafi sai ta ci kukanta a ɓoye, Allah ya gani tana qaunar mijinta kuma tasan shi ma yana sonta, a gefen Darling duk abunnan da ke faruwa yana gani kawai yaqi shiga harkan Abiy ne dan gudun ɓacin rana, kuma bai wa Ammi magana ba tunda yasan sun riga sun rabu to iya ƙoƙarin sa zai yi kar ma a mayar da auren.

Ko da mummy taji labarin nan ba ƙaramin mamaki tayi ba duk da tasan kaɗan kenan daga sharrin Aunty Amarya, kuma dama su kanuri zama da su a kishiya sai in Allah ya staga dan wasunsu basa zama banza, Daddy ma yayi bala’in shi sannan ya ce da Ammi kar ta yadda ta kula Abiy ta barsa ya gama haukansa tunda da girmansa yake biyewa munafurcin mace.

Hajja dai labari bai kai kunnenta ba, a lokacin kuma jay ya fara aikin asibitin sa, Afreen da suka samu huta ta dage sai ta je Canada dan haka ba wanda aya hanata tayi tafiyanta tunda kowa yasan soyayyan dake tsakanin Ammi da Afreen da yake Afreen takwarar Ammi ce.

Abiy fa tun yana ɗaukan abu wasa har ya zama gaske, Ammi taqi ba shi dama ya mata bayani balle yayi yunqurin bata umarni ta yarda ta bi, ɓangaren Aunty Amarya ba abinda ya dameta tana farantawa Abiy tana rayuwanta qalau, dan babbar damuwarta dama Ammi da yaranta ne kuma ga shi cikin ruwan sanyi sun tafi sun bar mata gidan.

Abiy Darling ya sama akan yawa Ammi magana ta sauraresa duk abun bai kai haka ba, amma ko kallon kirki Darling bai yiwa Abiy ba domin duk sanda ya ɗaga ido ya kalli Abiy ba abinda ke faɗo masa sai marin da ya yiwa Amminsa da kuma wulaqanci wai a sunan soyayya.

Wasa-gaske Ammi watanta 2 a Canada kuma Abiy bai bar sintiri ba, sannan ita kuma bata kulashi ba, ganin abun yaqi ci kuma yaqi cinye wa sai Abiy ya niqa garinsa ya kama hanyar India domin yasan in ba tanan ya biyo ba ba zata sauraresa ba.

Abinda Abiy bai sani ba kuwa ashe Aunty Amarya ta gama shafawa mutanen Maiduguri kan cewa ya saki Ammi, suna can suna ta farinciki har da ita ba wanda yasan sintirin da Abiy yake na ganin Ammi ta dawo gare sa.

<< Jahilci Ko Al’ada 20Jahilci Ko Al’ada 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×