Skip to content
Part 22 of 24 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

Darling fara karanta abinda ke rubuce a takardan yayi kaman haka “𝗠𝘆 𝗠𝗮𝗶𝗺𝗼𝗼𝗻 𝗶𝗻𝗮 𝘀𝗼𝗻𝗸𝗶 𝗶𝗻𝗮 𝗾𝗮𝘂𝗻𝗮𝗿𝗸𝗶 𝗵𝗮𝗿 𝗮𝗯𝗮𝗱𝗮, 𝗻𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝗮𝗶𝗻𝗮 𝗯𝗮𝗻𝘀𝗮𝗻 𝗱𝗮𝗹𝗶𝗹𝗶𝗻 𝘆𝗮𝘄𝗮𝗻 𝘀𝗮𝗺𝘂𝗻 𝗱𝗮𝗺𝘂𝘄𝗮 𝗱𝗮 𝗺𝘂𝗸𝗲 𝘆𝗶 𝗯𝗮 𝗮𝗺𝗺𝗮 𝗸𝗶 𝘆𝗮𝗳𝗲𝗻𝗶, 𝗻𝗮𝗰𝗲 𝗸𝗶 𝘁𝗮𝗳𝗶 𝗯𝗮𝘄𝗮𝗶 𝗯𝗮𝗻𝗮 𝘀𝗼𝗻𝗸𝗶 𝗯𝗮𝗻𝗲 𝗮𝗮, 𝗻𝗮𝗰𝗲 𝗵𝗮𝗸𝗮𝗻 𝗻𝗲 𝗱𝗮𝗻 𝗸𝗶 𝘀𝗮𝗺𝘂 𝗸𝗶 𝗵𝘂𝘁𝗮 𝗸𝘂𝗺𝗮 𝗸𝗲𝗺𝗮 𝗻𝗮𝘀𝗮𝗻 𝗸𝗶𝗻𝗮 𝗰𝗶𝗸𝗶𝗻 𝗱𝗮𝗺𝘂𝘄𝗮𝗻 𝗿𝗮𝘀𝗵𝗶𝗻 𝘆𝗮𝗿𝗮𝗻 𝗻𝗮𝗻 𝗮 𝗸𝘂𝘀𝗮 𝗱𝗮 𝗸𝗲, 𝗸𝗶 𝘆𝗮𝗳𝗲𝗻𝗶 𝗮𝗸𝗮𝗻 𝗮𝗯𝘂𝗯𝘂𝘄𝗮𝗻 𝗱𝗮 𝗻𝗮𝗸𝗲 𝗮𝗶𝗸𝗮𝘁𝗮 𝗺𝗶𝗸𝗶, 𝗻𝗶 𝗱𝗮 𝗸𝗲 𝗺𝘂𝘁𝘂 𝗸𝗮 𝗿𝗮𝗯𝗮 𝗶𝗻𝗮 𝗾𝗮𝘂𝗻𝗮𝗿𝗸𝗶 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗿𝗮𝗻𝗺𝘂 𝗱𝘂𝗸𝗮

𝗗𝗔𝗚𝗔 𝗡𝗔𝗞𝗜 𝗠𝗔𝗜 𝗦𝗢𝗡𝗞𝗜 𝗠𝗨𝗦𝗧𝗔𝗣𝗔𝗛𝗡 𝗠𝗔𝗜𝗠𝗢𝗢𝗡 (𝗔𝗕𝗨 𝗠𝗨𝗙𝗔𝗗𝗗𝗔𝗟).

𝗦𝗮𝗶 𝘇𝗮𝗻𝗲𝗻 𝗵𝗲𝗮𝗿𝘁 𝗱𝗮 𝗮𝗸𝗮 𝘀𝗮𝗻𝘆𝗮 𝗸𝗮𝗹𝗺𝗮𝗻 𝗜 𝗟𝗢𝗩𝗘 𝗬𝗢𝗨, 𝗱𝗮 𝘆𝗮𝗸𝗲 𝗱𝘂𝗸𝗮 𝗿𝘂𝗯𝘂𝘁𝘂𝗻 𝗱𝗮 𝗶𝗻𝗱𝗶𝗮𝗻𝗰i 𝗮𝗸𝗮 𝘆𝗶 𝘀𝗮. 

Ammi kaman za ta fire, a take ta nemi duka damuwan da ke damunta ta rasa sai wani farinciki take ji mara adadi, amsan takardan tayi ta qara karantawa, hawayen farinciki da kewan Abiy ya zubo mata ta share sannan ta naɗe takardan.

Duk abinda take yi Papa da Darling suna kallonta, shi Darling ji yake kaman ya rusa ihu dan taqaicin Abiy ganin ya gama wulaqanta masa Amminsa sannan yazo yana faɗin wani abin daban, sai dai ba zaka fahimci hakan daga fiskan Darling ba domin wayansa ya jawo ya ci gaba da dannawa, Dr Mufaddal dai murmushi yayi dan ya sani tabbas yarinyansa soyayyan gaskiya take yiwa Mustapha da wuya ace wai rabuwan ne suka yi, sai kuma ya maida kallonsa kan Darling, ganin abinda yake yi sai ya murmusa kawai bai ce uffan ba, ya dubi Ammi ya fara magana “ina fatan kinji kuma kingani saqon mijin naki ba rabuwa da ke yayi ba?

Ammi na murmushi ta ce “eh Papa”.

“Okay! To Yana da kyau duk lokacin da abu zai haɗaki da mutum ki tabbatar kinyiwa mutum uzuri domin kinga yanzu da ace yayi fushi da ke to zaki tabbata cikin stinuwan Mala’iku ne domin ba rabuwa yayi da ke ba kina da auren sa a kanki amma kikaqi sauraransa balle kiji me zai ce miki, kuma kikaqi duba takardan balle kisan hukuncin da kika yanke dai-dai ne ko akasin hakan, kiyi haquri ako da yaushe shi ne abinda zan faɗa miki domin ke kinsan wani irin aure kuka yi kuma kinsan irin soyayyan da Mustapha yake miki, daga qarshe kuma inaso ki tattara ki koma gidanki daga zaran mijin naki ya buqaci haka, sannan ki kiyaye gaba fatan kina saurare na?

Ammi cikin farinciki ta ce “Insha Allah Papa”.

“Yauwá! Allah muku albarka ya raya zuri’a ya albarkace su, sannan maganan yara sai kisan yanda za kiyi, domin ita Muhseena wataqila ma tare zamu koma maganan makarantan su, sai Munawwara da ita Muheebbah duk yanda kuka yanke sai kuyi, don bana goyon bayan a barsu su kaɗai a gida ba kowa tunda shi Mufaddal ba aure yayi ba”.

Ammi dai komai Papa yace amsawa take yi dan farincinkinta ba misali, sosai tayi kewan Abiy dan a yanzu ba abinda take buqata kaman ta kallesa.

Dr Mufaddal idonsa ya mayar kan Darling da ke danna waya ya ce “my man ka rage zuciyanka akan mahaifinka domin shi ne wanda yayi sanadin zuwanka duniya ba ka da madadinsa, in kuma kanason fushin Allah da rashin albarkan iyaye ta tabbata a kanka sai ka ci-gaba”, Ammi ce ta tari bakin Papa ta hanyar cewa “indai dan ni kake wannan cin ran to ka daina Darling komai ya wuce, komi na duniya mai wucewa ne, sannan tare da kai zamu koma Nigeria wannan karon kuje Maiduguri wajan dangi”.

Darling dai a fiska ba zaka gane me yake ciki ba amma a zuciyansa ji yake kaman ya tashi ya tafi kar ya kuma dawowa, ga abun haushin wai har Borno kuma za suje ba iya Gombe ba, Lumshe ido kawai yayi ya ce “Allah kaimu”.

Nan Dr Mufaddal ya qara yi ma Ammi faɗa sosai sannan ya ce “gobe in Allah ya yarda zan koma”.

Da “Allah ya kaimu” Ammi ta amsa, nan duk suka miqe Ammi tayi sama, Darling ma ya wuce sashinsa, sannan Dr Mufaddal ya wuce ɗakinsa dan ya sanya haqarqarinsa ya huta.

Amma tararwa tayi duk bacci ya ɗauki yaran sun bar TV a kunne, sai da ta kashe komai sannan ta tashesu suka tafi ɗakunan su, sweetie kuma ta ɗauketa ta kaita nata ɗakin itama ta mata addu’a sannan ta fito ta ja mata qofa ta nufi nata ɗakin cikin nishaɗi yau za tayi kwanan farinciki.

Darling yan haurawa sashinsa ya jawo system nasa ya ci-gaba da aikinsa dan bayajin bacci ma, Burinsa ya kammala ayyukan kamun ace za su tafi Nigeria, sai dai gefe ɗaya na zuciyansa tunanin Abiy yake yi na irin yanda ya mayar da Ammi dan yaga tana sonsa.

Washegari da sassafe Dr Mufaddal ya shirya dan ya dage Darling ne zai kai sa airport ba driver ba, ba yanda ya iya yana gama shirin zuwa office suka kama hanyan airport Dr Mufaddal nakan masa faɗa cikin sigan rarrashi har suka isa, ya shiga jirgi zuwa India shi kuma Darling ya juyo driver yayi office da shi.

Abiy yana tashuwa da sassafe ya fara shirye-shiryen zuwa wajan masoyiyar sa, Aunty Amarya dai tana ganin ikon Allah sai dai sanin halin sa bai cika son yawan tambaya ba sai tayi shiru, sai da zai tafi ya ce mata “sweetheart na tafi Canada zan kai week sai na dawo”, Aunty Amarya da kallon taqaici da haushi take binsa, cike da kishi ta ce “me za kaje yi a Canada? Ina ka sake ta to me zaka je yi? In yaran ka kakeson kallo ba sai ka sanya shi ya kawo su ba tunda kai ka haifesa ba shi ya haifeka ba” surutu take yi ido rufe wanda kanaji kasan kishi ki azalzalanta.

Abiy kallonta kawai yayi bai ce komai ba, dan yana rasa dalili shi bayason ɗagawa mace murya amma duk da haka Maimuna da yake so yakan iya ɗaga mata murya, ba tare da ya damu da yanayin magananta ba ya ce “wanda ya faɗa miki na saki Maimoon to ki koma ki qara tambayansa, sai na dawo” yana gama magana ya fice.

Aunty Amarya bin bayan Abiy tayi tana surfa masifa, qarshe ganin driver ya fita da shi sai itama ta koma ta ɗau waya ta qira Hajj, “assalamualaikum Hajja anwuni lafiya?

“Lafiya Alhamdulillahi Rabi’atu ya gidan? Ya mijinku?

“Ba lafiya ba Hajja, gashinan ya kama hanya wai zai tafi Canada kuma bayan ta sake ta, nace in yaran yakeson gani ai sai ya ce a kawo su”.

“Rabi’atu wa aka saka? Ba dai kicemun Mustapha ya saki Maimunatu ba, INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI’UN! Wai yaran nan ina kukeson duniya ta kai ku ne? Mutum ya auri mace da wahala amma cikin sauqi ya rabu da ita, to dan ubansa zai dawo da ita dan wannan cin amana ba da Fatuma ba”.

Auntu Amarya jin ba abinda take so Hajja ke faɗi ba sai ta kaste waya tana faɗin “mstwwww! Duk bakinsu ɗaya wallahi Maiduguri zan je, ba ta isa ta dawo ba” tana gama magana ta shige ɗaki ta hau shirya kaya a akwati.

Abiy driver ya kaisa har airport jirgi ya ɗaga da su sai Canada republic, taxi ya hau har qofan gidan yaron nasa sannan ya sallami taxi ɗin, da sallama ya shiga palourn inda ya tarar shiru ba kowa kaman basa gidan, sama ya haura nan ya samu yaran suna aikin karatun Alkur’ani wanda ganin Abiy ya sanya su miqewa da gudu kowa ya je yayi hugging nasa har Afreen suna masa sannu da zuwa, amsawa yayi yana tambayan su ina Amminsu? Hanyan ɗakinta suka nuna mishi alaman tana ciki, cikin zumuɗi da son ganin matar tasa ya lallaɓi sweetie da daraba ya zille ya nufi palourn da zai sada shi da ɗakin Ammi.

Fitowanta wanka kenan ta gama shafe jikinta da turaruka masu daɗin qamshi, kayan da suke matuqar amsanta ta fitar ta sanya, Pakistan dress tana staye gaban madubi taji anbuɗe qofan ɗakin nata, duk ɗaukanta yaran ne sai bata juya ba ta cigaba da rolling nata tana faɗin “wai sweetie ban hanaki shiga ɗaki ba sallama ba…” Maganan bakinta ne ya kaste jin ta jikin mutum wanda ta tabbatar ba kowa bane face Abiy, shi kuwa cikin farin ciki ya rungumeta ta baya yanajin kaman yau ya fara raɓarta, Ammi farinciki ne da wani irin nishaɗi ya lulluɓeta amma sai ta waske ta ja aji taqi yin mosti balle ta ce qala, sai qoqarin tashuwa da take yi amma Abiy bai bata wannan daman ba.

Duk yanda ta so mostawa Abiy ya hanata wannan qoqarin ita kuma ga shi tabbas tayi kewansa dan bata qi su qare rayuwansu a haka ba, cikin danne abinda take ji ta ce “sake ni kar yara su shigo su ganmu haka”.

Abiy murmushi yayi dan yasan aji ake ja masa, kuma yasan me zai yi a wuce wajan amma sai ya nemi jan maganan dan so yake yau ta taɓa rigiman nata, muryanta ya kwaikwaya ya ce “babu ɗan albarkan yaron da zai shigo duk sun san Amminsu na kewan Abiynsu, sannan kuma nima ba sake ki zan yi ba dan da shiri na nazo wannan karon ya kamata a samawa Muheebbah qani tunda ta haura shekara biyar ɗin, kuma dama starin na shekara biyar-biyar ake yi”.

Ammi qara ɓata rai tayi jin abinda ya ce “hmmn! Wato ma planning nake yi kenan? Good inma shi ne ai magana ta wuce yanzu ba komai tsakanina da kai sake ni”.

“Aiko ni da ke muke da abu babba ma stakaninmu, yanzu dai fatan an buɗe takardan an ga me na rubuta kuma an yafe mini an karɓi tubana?

“Uhmñ! Na buɗe kuma naga saki uku, so na jima da yafe maka jeka wajan matar ka inma yaranka kazo ɗauka ka ɗaukesu Allah tsare hanya”.

Murmushi Abiy yayi jin rigiman nata da gaske take yi, sai kawai ya haɗe bakinsu cike da son nuna mata irin kewanta da yayi da kuma soyayyanta da neman afuwanta haka yake sarrafa ta, wanda a take Ammi ta amshi tuban nasa ta kuma yaba soyayyan sannan itama ta miqa nata qoqon neman yafiyan ta hanya maida masa martani mai nuni da tayi matuqar kewan sa.

Cike da soyayya da qauna suka sarrafa juna wanda na tabbata ko wasu matasan ma’auratan ba lallai su shumfiɗa irin wannan soyayya ba (shi yasa ake son in za kayi aure kayi dan Allah, domin in kayi dan wani abu daga lokacin da abun ya gushe to fa ba zaman lafiya balle soyayya sai a ta ɗaukan alhaqin juna).

Bayan komai ya lafa sun yi wanka tare, Abiy na zaune kan Ammi a qafansa nan ya dinga qara bata haquri da lallashi, wanda Ammi ba ɓata lokaci ta ce “na yafe maka, komai ya wuce ina fatan hakan kar ya sake faruwa, kuma za ka yafemun Nima?

“Ai na jima da yafe miki Maimoon, Allah miki albarka ya barmu tare, sannan ina so ki sani har abada kibar tunanin rabuwa tsakaninmu, domin ban taɓa son wata mace kaman ke ba kuma bana tunanin akwai wacce zan so nan gaba kaman ke, abubuwan da suke faruwa tsakaninmu kuma in Allah ya yarda zan ɗau mataki kinji..”

Kaste Abiy tayi ta hanyar cewa “komai ya wuce ka daina dawo da shi, sannan in dai ni ce Maimoon za ka ɗau mataki dan ni to na yafe duniya da lahira kar kayi wani abun dan in kayi ma ba zan yafe ba”.

Abiy na murmushi cike da son matar tasa ya ce “shikkenan angama ranki ya daɗe nustuwar Mustapha”.

Ammi ma murmusawan tayi ta ce “to ranka ya daɗe yallaɓoi ina neman wata alfarma”.

“Maimoon faɗi ko ma menene Insha Allah zan yi miki da yardan Allah in har bai fi qarfina ba”.

“Yallaɓoi dan Allah maganan Mufaddal, ka daina biye masa kaga dai yaro ne kuma komai zai wuce in ya girma, dan Allah kai mahaifinsa ne ka yafe masa, sannan maganan komawa Nigeria ina neman alfarman zama a Canada tare da yaran nan tunda ya sanya su a makaranta inyaso sai mu dinga zuwa Nigerian in sun samu hutu”.

Dogon ajiyan zuciya Abiy ya sauqe domin Allah ya gani baya jin akwai abinda yake qauna a duniya sama da yaran nasa amma kuma dan qara samun nistuwansu da faranta musu zai yarje da hakan, cikin murmushi mai nuni da gamsuwa da batun ta ya ce “kaman yanda na ce koma menene zan amince miki kuma zan miki, to na amince inyaso zan dinga zuwa akai-akai fatan zaki kula mana da su? Kuma ko ba’a yi hutu ba wani lokacin kema ki dinga leqowa tunda kinsan wani zubin muna busy sosai kuma ba zan jure har fin sati ba tare da na ganki ba”.

Cikin jin daɗi Ammi ta amince tare da qara rungume mijin nata, nan suka ci-gaba da farantawa junansu.

Aunty Amarya shiryawa tayi ta kama hanyan Maiduguri, inda tana isa ta sami mahaifiyarta ta sanar mata, amma da yake mahaifiyar nata ba ruwanta sai ta tsawatar mata akan ta koma gidan mijinta, Aunty Amarya dai hakan bai gamsar da ita ba, sai ta samu fanne, itama fannen cewa ta yi “amma tabbas Rabi’atu baki da hankali, ki godewa Allah Mustapha ya aureki shi ne har kike kawo wani maganan? Wannan auren su Mustaphan fa kaman an bisa da baki wallahi kana mastawa a lamarin ka baqonci lahira, yanzu ina baba-alhaji? Ina Alhaji surkinki? Ina Asma’u? Ko yarinyan da Asma’u ta haifa bata zauna ba dan haka ya isa kisan wannan auren nasu Allah ne ya haɗa, amma kuma tunda kince sakinta yayi ba mastala kya iya samun Alhaji babba amma dai ni fanne naga ayar Allah ba ruwana da lamarin Mustapha da ƴar qasar can”.

Aunty Amarya kaman za ta haɗiye zuciya haka ta yi kwana biyu a daddafe ta dawo bayan ta gama ɗaura aniya da sabon shirin shiryawa Ammi manakisa wanda sai ya rabasu na gasken-gaske.

Ɓangaren Hajja kuwa Daddy (Nura) ya qira ta dinga masa faɗa akan ya tabbatar Mustapha ya dawo da maimuna inba haka ba zata saɓa musu, shi dai Daddy haquri ya dinga bawa Hajja sannan suka yi sallama ya qira layukan Abiy baya tafiya sai ya bari akan zai qira daga baya.

Yau aiki ya sha ba kaɗan ba dan da qyar ya samu kayakinsa da aka riqe su suka fito, companyn Jigawa kuma ya seta komai dan shi ne dama dalilin aikin da ya hanasa bacci da wuri jiya, sai dai duk da haka akwai buqatan ya je dan duba sauran abubuwan ga kuma maganan meeting da ake jiran approval nasa, sai can yamma kamun ya fito ya dawo gida.

Da sallama ya shigo palourn wanda tun daga bakin qofa ya gama kallon farincikin da ke kwance a fiskan Ammi kuma yasan tabbas Abiy ne ya zo, ba tare da ya ce qala ba ya qarisa shigowa yana faɗin “sannu da gida Ammi” yana gama faɗa ya wuce haurawa sama.

Ammi dai amsawa tayi tana murmushi ta masa sannu.

Abiy ne ya sauqo ɗauke da sweetie tana ta aikin shagwaɓa, domin su ma yaran karan kansu sunsan yau Ammi na fatinciki kuma suma zuwan Abiy ya sanya su farinciki domin kewan mahaifin nasu suke.

Wasta ruwa yayi sannan ya jawo wayansa yana laluɓo Numbern Jay yau kusan kwana biyu bai qira sa ba, “hello dude yau ka tuna da ni ne? Cewar Jay da yayi picking call ɗin.

“Mtsw! Za ka fara surutun naka ko?

“Hhh ba dole nayi surutu ba Allah ya stagomin baki, ai kaikam sai tsagun bakinka ya manne tunda baka buɗewa kayi magana da kyau, salatin ma a zuciya ake yi, yanzu dai ya su Ammi? Ya kuma labarin Abiy? Ina su sweetie ina Afreen?

DMD dafe kai yayi yana faɗin “ko me kayi ba laifinka ba nine na qiraka, amma kaji wallahi ko ɗaya ba zan amsa ba, ka gaida gida” kitt ya kashe wayan yana jan guntun tsaki.

Jay na kan qiransa amma ko kallon wayan bai yi ba, ya shige toilet.

Ɓangaren Jay kuwa dariya ya dinga yi yana faɗin “Allah ka shiryi dude ka gwadamun ranan da zai sauya, ai wannan mace me zama da kai ta shiga uku”.

Sai da Ammi ta tura aka qirasa kamun ya fito, sama-sama ya gaishe da Abiy sannan ya zauna Ammi tayi saving nasa ta cika cikinsa.

Washegari DMD bai je office ba, Managern sa ya qira ya tura masa abubuwan da ya kamata, dan so yake ya huta aikin da yayi kwana biyu ko ishashshen bacci ba ya yi, inda ɓangaren Abiy da Ammi kuwa soyayyan su suke yi kaman sabbin aure, a ranan kuma Abiy ya sa duka suka shirya har Darling suka tafi shopping, kaya niqi-niqi kowa ya jida, aka wa sweedy sayayyan tafiya school Afreen ma aka mata na dawowa Nigeria, Abiy ma ya jida kayaki, shi dai DMD ba abinda ya ɗauka illa iyaka wani headband na mata da ya gani ya masa kyau, Abiy ne ya biya kuɗin komai suka kuma wucewa suka yi sayayyan kayan ƙwamulashe, yawo suka yi sosai sannan suka dawo gida, kowa ya jida nasa yayi ɗakinsa da shi, Darling a Waldrop ya jefa headband ɗin ba tare da yasan ma me zai yi da shi ba.

Washegari da sassafe sweedy ta kama hanyan India bayan Abiy da Ammi sun mata faɗa ta kula sosai, Afreen kuma sai da aka kwashe sati guda kamun suka juyo tare da Abiy da ke cike da kewan matar sa.

Abiy na dawowa Aunty Amarya cikin kirsa ta lallaɓasa ta basa haquri akan ba tayi dai-dai ba kuma ba zata qara ba, abinka da mata da miji nan suka shirya suna soyewansu, da farko sai yayi kwana biyar ko sati a Nigeria sai ya je Canada yayi kwana biyar ya dawo, ana rayuwa ana tafiya haka har dai Aunty Amarya ta fara kasa hali, sai yayi sati bai je Canada ba kuma in yaje baya wuce kwana biyu zai dawo, qarshenta kwana ɗaya yake yi ya dawo, daga baya kuma zai fi sati biyu bai je ba kuma a ranan da yaje a ranan zai dawo, ita dai Ammi duk haka bai dameta ba, ga yaranta na makaranta tana kallonsu suna kallonta hankalinta yafi kwanciya, a cikin wannan halin DMD yayi approval na meeting nasa a Zamfara inda yana shigowa ya gabatar da komai ya juya ya koma ko sauran companies ɗin bai leqa ba balle Gombe, Abiy da sai da ya raba hali domin faɗa ya dinga yiwa Ammi kaman ita ce ta yi hakan, qarshe sai da ya kwashe wata bai je Canada ba, Ammi kuwa duk tabi ta damu a wannan lokacin ne kuma yara suka samu Hutu har da sweedy da ta kwashe shekara a makaranta ta dawo dan haka sai Ammi ta sako su gaba har DMD duka diro Nigeria.

Aunty Amarya a fiska kuma a gaban Abiy nunawa take duk duniya ba wanda take so irin yaransa kuma bata kishi da Ammi, amma a bayan fage rashin kunya takewa Ammi ta ke kuma zuba mata munafurci, sai da suka kwashe sati biyu da zuwa sannan suka je Ashaka, Hajja farincikin rasa inda zata sanya kanta ta yi ganin jikokin nata, nan ta dinga zubawa Abiy faɗa kaman za ta ari-baki ” Maimoon kiyi haquri naji abinda ya faru, wato tunda shi Mustapha yanzu ya butulu ɗa namiji hankaka gabansa fari bayansa baqi shi ne har da saki nan Rabi’atu ta qiran tana faɗamun”.

Ammi da tayi qasa da kai cewa tayi “Hajja bakomai ba saki bane nice naje Canada”.

“A’a ‘yar nan karki wani rufa masa asiri ai na sani, shi Mustapha dan staɓar ya zama ciki ba Godiyan Allah balle tuna alheri ya mance yanda ya sha gwagwarmaya ya aureki har zai iya daukan hannu ya baki takarda tunda shi sha-sha-sha ne, to ya taimaki kansa dan da mun haɗu tabbas sai na saɓa masa”.

“Bakomai Hajja ya wuce, am nace ba Hajja dama munason zuwa Maiduguri da yaran nan”.

Washe baki Hajja tayi ta ce ” ‘yar albarka Allah miki albarka ai ya kamata kam zuwa Maiduguri dan za suce tunda Allah ya ɗauki Alhaji shikkenan kuma ni da ku bama zuwa, yanzu dai wannan tafiya duka za’a yi sa kowa da kowa”.

“To Allah ya kai mu”.

Ammi washegari tabar Ashaka su, DMD kuwa sai da yayi kwana biyu kamun ya dawo yabar su sweedy a can, dan sweetie indai gidan Hajja ne to ko babu Ammi za ta zauna.

DMD ya je ya dubo Companyn Jigawa, sannan ya wuce Abuja nan ma ya duba sabon shopping-mall da zai buɗe, komai lafiya sannan ya juyo. a ranar kuma duk suka tattaro da iyalan Daddy da na Abiy suka nufi Maiduguri.

Sosai family suka ji daɗin zuwan su Hajja, nan aka sauqesu a sashi na daban, dan duk da kasancewan basa zuwa amma duk wani dangi yana da masauqi a family house ɗin domin a yanzu yawansu ma ya sa an raba family house ya zama biyu, ɗaya stohon na iyaye da kakanni ɗaya sabon kuma na jikoki da yara, sannan duka gidajen manya ne iya ganin ka wane anguwa guda.

Zuwan su Hajja ya sanya an haɗa qwarya-qwaryar family meeting in da aka buɗe taro da addu’a sannan Alhaji babba da zuwa yanzu shima ya stufa sosai ya fara koyo bayani, sai da yayi ya gama sannan aka buqaci duk wani mai abun faɗa ya faɗa.

‘yar uwan Hajja da suka haɗa uba ne ta fara koro bayani akan abinda suka kista da Aunty Amarya na game da auran yaran kan cewa su Jay da DMD su zaɓi mata su sweedy ma anmusu miji.

Tun shigowan sa babban palourn ya samu waje ya zauna wayansa ya ciro yana laste-lastensa bai ko kalli kowa ba balle ya tofa musu qala har sai da ya ji abinda dattijuwan da Hajja za ta girmeta da kaɗan ta faɗa, ɗagowa yayi ya wasta ma matar da baisan wacece ma ita a wajansa ba wani malalacin kallo, har zai buɗe baki sai kuma me ya tuna oho ya maida hankalinsa kan wayansa, Daddy ne yayi magana “in Allah ya yarda Duk zasu zaɓi mata in yaso ba jima sai ayi auren tunda duk yanzu suna da aikin kansu”.

Jay idanuwansa ya baza a ɗakin ganin yaran mata basa palourn sai ya taɓe baki yana faɗi a ransa “in yaranku suna da kyau kuma sun nuna to ko huɗu ne ni Jabeer zan aura amma in kwailaye ne to tarihi zai maimaita kansa, mata zan nemo zuqeqiya” vibrating na wayansa ne ya kaste masa zancen-zuci da yake yi, ganin mai qiran sai ya miqe ya fice a palourn yana ɗaukan qiran.

Shi ma miqewa yayi yana maida wayansa aljihu tare da sanya ɗaya hannun a aljihun wandon jeans na jiginsa da yayi matuqar amsar sa, gaskiya DMD kyakkyawan qarshe ne dan yanda qananan kayan suka zauna a jikinsa kai kace ba ɗan Nigeria ba ne, ficewa yayi a palourn duk sai suka bi su da kallo Aunty Amarya da dattijuwan da tayi magana taɓe baki suka yi, Ammi kuma qasa tayi da kanta tana addu’an shiriya ga yaran nasu da maganan da suke ja musu, Abiy dai ko qala bai ce ba dan shi komai aka yi dai-dai ne baya qaunan ya kuma yin wani laifin.

Hajja dai tayi supporting na shawaran, Aunty Amarya ranta fari tass har aka yi addu’a aka waste, wasu na ta zancen DMD ya rena mutane ai gado yayi wajan Mustapha.

Jay yana gama wayan yabi bayan DMD da ya nufi ficewa a sashin babban palourn da ake meeting yana faɗin “dude Angon ƴar Maiduguri jirani mu fara shirye-shirye”.

Ko nuna alaman ya ji abinda yake faɗa bai yi ba balle batun ya jirasa, sai da Jay ya haɗa da gudu kamun ya iso sa yana faɗin “Allah nuna min randa zanga ƴar Maiduguri ta sanya ka wanke-wanke wallahi sai na sanya ta ramamin wulaqancin nan da kake mun”.

Kallon banza ya bi Jay da shi yana faɗin “ba’a haifi iyayenta ba balle ita, ni banda lokacin mace balle aure amma inaga tabbas zan yi dan waɗannan mutanen su san basu isa su sanya ni auran yaransu ba”.

Jay murmushi yayi ya ce “ashe kai ma ka gama yanke shawara? Ai ina gaya maka dude nikam in har suna da qosasssun yara kyawawa to ko huɗu suka ce zan aura amma aradu indai qwailaye ne to sai dai ayi wanda za’a yi inyaso a yafe ni daga family dama can bai damen ba, bare zan nemo na aura zuqeqiya nunanniya dan ni banson harka da qananun mata, dama muna can Gombe me ya haɗa mu da Maiduguri, Ni fa inaganin ta Abiy zan yi India zan koma na zaɓo mata nustaststiya mai kyau wacce ta iya soyayya kaman Ammi, matan Nigerian nan in ba sa’a kayi ba to duk shiru ne”.

Taɓe baki yayi yace “ɗauko mota ka kaini airport sai ka dawo musu da motan”.

Jay dubansa yayi ya ce “badai yau zaka koma ba dude?

“In na zauna ban koma ba aikin ne zan maka?

“A’a mai da wuqan jirani na ɗauko motan, amma gaskiya ba dan ina buqatan qarewa ƴammatayen kallo ba da na biyo ka mun tafi”.

“Mstww! Ai kai maganan mata shi zai kashe ka, za ka ɗauko ne ko na tafi da kaina kuje ku samu motar a airport?

Jay yana dariya ya juya dan yasan kaɗan daga halin DMD sai ya tafi ta motan ya barota a can yayi tafiyansa.

Motan ya ɗauko DMD ya shiga suka nufi airport, har suka isa Jay shi kaɗai ke surutun sa DMD hankalinsa duka na kan waya kai kace dan kallon waya aka halicci idonsa.

Sai da jirginsu ya tashi sannan Jay ya juyo ya dawo gidan, Ammi na ganinsa ta tambayesa Darling sai ya faɗa mata ya koma Gombe, addu’an a sauqa Lafiya da na Allah shirya ta bisa da shi, Jay kuwa baza idanuwa ya dinga yi yana qarewa ƴammatayen gidan kallo, kyau kam iya kyau Allah ya azurta wannan family da shi don kana ganin ko waccen budurwa za ka tabbatar tabbas Kanuriya ce gaba da baya, Jay yayi kallo iya kallo qarshe dai ya gama rawan idonsa ya rasa ta zaɓa.

Ammi da yaranta suna ɗakinsu a zaune, Jay ya shigo yana faɗin “Ammi gaskiya ni na gama dubawa sama da qasa banga wace ta mun ba kawai na yanke shawara zan jira sweetie ta girma”, ba iya Ammi ba har sweetie da bata cika shekara goma ba sai da tayi dariya duk da rashin wayonta.

Ammi ta ce “son Allah ya shiryaku, ai gwanda ku dage ku nema kamun a nema muku, ka bari kayi ta huɗu da sweetie lokacin ta girma”, tura baki sweetie tayi ta ce “ni Ammi banson ta huɗu ta ɗaya nakeso”.

Duk dariya suka sanya, Jay na faɗin “sweedy ku dage ku zaɓi ku darje duk da nasan ba zaku samu kyawawa irinmu ba”.

Sweedy na murmushi cikin rashin son yawan magana ta ce “big bro kai ma kasan mijina sai ya fika kyau, amma yanzu dai ba ta wannan ake yi ba”.

Hira suka ci-gaba da yi suna dariya, cikin dabara Ammi ke tausarsu tana nusar da su fa’idan bin magana da biyayya ga iyaye, amma sweedy dai ta tuɓure ba wanda ya mata dan abun kaman wanda suke jiran qiris samarin gidan kowa sai faman isar da saqon soyayyansa yake gare su barinma dai Sweedy, domin a duniya sweedy Allah ya hore mata kyau banbancin ta da DMD kaɗan ne dan da ta kaisa shekaru ko ta biyo sa kusa-kusa za’a iya qiransu twin’s.

<< Jahilci Ko Al’ada 21Jahilci Ko Al’ada 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×