Skip to content
Part 23 of 24 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

DMD bai nufi Gombe ba direct Abuja ya wuce dan ankammala komai na shopping-mall ɗin, wata arniyar hotel ya kama ta manyan masu kuɗi wanda daga masu mulki da manyan ‘yan siyasa sai manyan masu kuɗi ke zuwa hotel ɗin, kwanansa ɗaya washegari ya fito daga mall ɗin wanda ake shirye-shiryen buɗewa gobe ya dawo hotel ɗin, bayan yayi parking ya fito a motan ya kulle, tafiya yake hankalinsa na kan wayansa da aka turo masa saqo daga Canada yana dubawa, ba tare da ya kula ba ya ji ya yasar da key na motan sa, har ya shiga ɗakin da ya kama bai kula da ya yasar da abu ba, ruwa ya wasta sannan ya yi ordern coffee aka kawo masa.

Yana kurɓan coffee nasa yana ayyukan sa a waya sai ya ji knocking.

Wata haɗaɗɗiyar mota ne ta shigo hotel ɗin da mugun gudu, ana gama parking aka buɗe duka qofofin kusan a tare, wasu ƴammataye ne suka fito guda uku sai gefen da yake na driver ne kawai a buɗe ba’a fito ba, ɗayar da ta fito daga gefen zaman driver ne ta ce “reeysah me kike kallo ne ba zaki fito mu tafi ba?

Wacce aka qira da reeysah ce ta jefo qafafuwanta waje, wasu arnun hill’s ne a qafanta wanda daga takalmin qafan zaka tabbatar mai qafan ta haɗu, a hankali ta qarisa fitowa, sanye take da riga da wando iri ɗaya wanda ake qira da Up&down wanda a qalla kuɗin kayan zai kai 300k, inda take kallo duk ƴammatan suka bi da kallo, ganin guy ɗin sai duk suka shagala da kallonsa suma, ɗayar ce ta ce “reeysah amma guy ɗin nan ya haɗu fa”.

“Hmmn! Zee ba kaɗan ba, ai ni naga mijin aure dama excellency ya fara magana miji kamun ya bar villah” tana gama magana ta taka a hankali ta ɗau abinda ya faɗi a hannun guy ɗin da ta gani sannan ta bi bayansa, sai da ta ga ɗakin da ya shiga sannan ta juyo wajan freind’s nata tana faɗin “let’s go guy’s”.

Ɗakin da suka kama suka shiga sai da suka huta sannan ta ɗau key ɗin ta fito bayan tawa qawayen nata sai ta dawo, tana isa qofan tayi knocking.

Tashuwa yayi ya buɗe dan duk a tunaninsa ko waiter ne yazo amsan cup na coffee ɗin, kallo ɗaya ya mata ya ce “lafiya?

Cike da qwarqwasa ta ce “zan iya shigowa?

Ba tare da DMD ya ce komai ba ya juya ya shige ciki sai ta biyo bayansa, zama tayi a ɗaya daga kujerun palourn tana gaishesa cikin harshen turanci, har ta yi ta gama bai ce mata ko qala ba kuma bai kalleta ba, gajiya tayi ta ciro car key nasa ta ce “am dama key na motanka ka yasar shine nace bara na kawo maka”.

Hankalinsa da idanuwansa na kan waya ya ce “okay thanks! You can kept it”.

Yana gama faɗan haka ya juya ya shige bedroom.

Reeysah kaman za tayi kuka ta ajiye ta tashi ta fice, amma tana ayyana wa a ranta itafa taga mijin aure, ko da ta koma cewa qawayenta tayi ya amshi soyayyanta.

Fareesah(reeysah) kyakkyawan budurwa wacce a qallah za ta kau shekara 26 da haihuwa, yarinya ta uku ga present president na Nigeria, wacce tayi karatu a America bata jima da dawowa ba aka fara mata maganan aure, da farko ta nuna taurin kai tana yawon ajenan-ajenan da qawayenta sakamakon yarinyace da bata ji an sangartata, yayyunta biyu duka sun yi aure sai qannenta maza biyu da suke karatu a outside, yaran manya ministoci da ‘yan kasuwa na sonta amma ba maganan aure a gabanta, amma ganin DMD sai taji za tayi auren.

Yana jin qaran fitan ta ya ja guntun tsaki, ya rage hasken wutan ɗakin ya kwanta.

Washegari da sassafe ya shirya ya fice gaba-ɗaya a hotel ɗin, reeysah kuwa sai da rana ta fito gastal-gastal suka tashi da qawayenta, sunje ɗakin DMD suka tarar baya nan, kaman za tayi kuka haka suka tafi tana faɗin sai ta nemo shi dan ita ba ta da miji a duniya bayan shi, ko da kuɗi ko da mulki sai ta aure.

(😂 Jama’a kuwa fareesah fatan nasara).

Bayan sun qara kwana biyu suka tattara suka koma Gombe, bayan sun ajiye Hajja a Ashaka.

Maganan aure da aka yi kuma daga Daddy har Abiy ba wanda ya ce wa yaran komai, dan Hajja jira take su haɗu duka ta ja musu kunne kar su kuma jawo mata wani abun.

Ammi zamanta take hankali kwance bata shiga tsabgan Aunty Amarya dan zuwa yanzu Ammi ta fahimce ta amma tabar hakan a mazaunin kishi ba wai munafurci ko kissa ba.

Sai da aka kammala hidiman komai aka buɗe shopping-mall sannan ya kamo hanyan dawowa Gombe, cike da gajiya ya shigo gidan, ba tare da yayi part na Ammi ba ya nufi ɓangaren da yake nasa, yana shiga qamshi ya doki hancinsa sashin staf-tsaf ko ina a gyare sai qamshi, ganin haka sai ya murmusa yana faɗin “Allah barmana ke Ammi” ya shige ɗakin nan muna a a gyare har toilet, ruwa ya wasta ya ɗauro alwala yayi Sallah sannan ya bi lafiyea gado ya kwanta.

Fareesah tayi iya nemanta amma ba alama ko guda da zata samu daman samun ko da phone number na DMD balle sunansa, masu hotel ba abinda suka sani akansa sannan bata da labarin shopping-mall da ya buɗe, duk da haka dai kan nemansa take yi taqi haqura.

Hutu na qarewa suka tattara suka koma Canada, inda suke rayuwa cikin kwanciyan hankali sai Ammi kawai da aka barta da sintiri yau tana Nigeria gobe tana Canada, domin Abiy zuwa yanzu sai dai ya dinga leqosu lokaci-lokaci yakan shafe wata guda bai je ba, Ammi hakan dai bai dameta ba domin ita tana zuwa tayi sati guda ta koma in tayi sati biyu a Canada ta qara zuwa tayi sati guda ta koma.

Jay yana aiki a FMC Gombe sai Afreen da ke final-year semester a GSU tana karantan computer science, Afrah kuwa tana gaban Hajja tana secondary school.

Fitowa DMD yayi da shirin tafiya office amma sai ganin Ammi yayi ta fito da nata shirin ita ma, gaisheta yayi yana faɗin “Ammi sai ina?

Tana murmushi ta ce “sai gidan mijina, tunda ku kunqi gidan ubanku”.

Taɓe baki yayi yana gyara zaman suit nasa ya ce “adawo lafiya a gaishesu, and please Ammi inkin samu lokaci kamun ki dawo ki dubamun Companyn Jigawa”.

“Darling yai shekara nawa rabonka da Nigeria? In banyi qarya ba kafi 2 year’s ba kaje ba, tun last da muka je tare muka je Maiduguri kaqi ka koma, ina ji dai anfita harkanka akan batun auren tunda dama shi ne damuwarka, ka fita idona inba haka ba zan mugun saɓa maka, maza-maza nan da Friday anabawa su sweerie hutu ka tabbatar kun biyo ni dan wannan karon zamu kwana biyu acan tunda hutun su sweedy da yawa”.

“Ammi karki manta da zuwa jigawan please” iya abinda ya faɗa kenan yayi hanyan fita waje.

Girgiza kai kawai Ammi tayi tawa yaran nata bankwana sai sun zo, sweetie har da kukanta za ta bi Ammi ai saura two days a bayar da hutu inyaso sweerie ta karɓo musu hutun, da kuka ta bi Ammi har compound na gidan, kallon da DMD ya mata shi ya sanyata haɗiye kukan, Ammi ta shiga motan da ya shiga suka zauna tare a baya driver yaja su sweedy suna ɗaga mata hannu har motan ya ɓace sannan suka juya suka koma ciki.

“Darling sam-sam bana son irin wannan halin da kakeyi bai kamata ba”.

Kaman zai yi kuka ya ce “Ammi nifa bansan dalili ba gaskiya banson Nigeria, amma kiyi haquri zan je wani hutun, wannan karon in aka basu hutu dai zasu taho ko Abiy ya zo ya tafi da su”.

“Hmm! Ni Maimoon me zan ce in ba Allah ya shiryamin kai ba Darling, Allah kai mu in aka basu hutun inma Abiynku bai zo ba zan dawo na ɗauke su mu koma amma ba zaka turamun yara su kaɗai a jirgi ba inason yarana”.

Murmushin da ya qara masa kyau yayi ya ce “Allah bar mana ke Amminmu” dai-dai sun iso airport nan Ammi ta sauqa ta samu jirgin ya kusa tashuwa fasinjoji na shiga, ta gama bin step’s na jirgin har ta kusa shigewa ta juyo tana masa murmushi ta ce “ka kulamun da yarana Darling”.

Hannu ya ɗaga mata yana faɗin “Ammi Karki manta da Jigawa”.

Murmushi kawai tayi ta qarisa shigewa dan tasan dalilinsa na jaddada mata bai wuce baya son zuwa Nigerian ba, wajan zamanta ta wuce tana mai karanto addu’an shiriya ga yaran nata a zuciyarta.

Ganin jirgin nasu ya tashi sai ya koma cikin motan, driver ya ja suka wuce katafaren Companyn sa.

Ammi tunda ta zauna a cikin jirgin zuciyarta ke stinkewa, amma bata jin za ta iya haqura ta koma domin tabbas tayi kewan mijin nata, addu’oe ta cigaba da karantowa har jirgin nasu ya ɗaga zuwa Nigeria (ƙasar mu ta gado😂).

A Jigawa jirgin nasu yayi landing, tana sauqa ta wuce Companyn yaron nata dake garin, qiransa tayi ta sheda masa ta isa a Jigawa ta staya za ta duba kamun ta wuce, DMD kaman zai yi kuka haka ya dinga yiwa Ammi magana meyasa bata wuce Gombe.

“Please Ammi ki bari driver ya kai ki”.

“Kaga Darling ƙyaleni in naso driver ya kaini in naso kuma nayi driving da kaina nan da Gombe wani nisa ne?

“Ammi amma kinsan Nigeria ba Canada ba, hanyoyin nasu kaɗai ma ya ishe ki ciwon kai ba sai kin haɗa da driving ba”.

“To ubana! Ni dai ka kulamun da yarana” tana gama faɗa kitt ta kashe wayan ta yi duk abubuwan da ya dace a Companyn sannan ta fito da niyan tafiya amma Managern ya bata haquri ta huta tukunna.

A cikin motocin Companyn Managern yaɗau guda ya bawa Ammi driver akan ya kai ta Gombe, amma sai da yaja masa kunne ya kula sosai da tuƙinsa, sannan suka yi bankwana da Ammi driver ya kamo hanyan tahowa Gombe.

Hankali kwance suke tafiya, inda ta sanya drivern ya tsaya suka yi sallah a Bauchi sannan suka nufo Gombe, har sun fara shiga qauyukan Gombe dan sun kusa isa Kwami, gaban Ammi ne ya tsananta da faɗuwa dan haka sai ta ciro wayanta a haka dan qiran sweedy taji ko suna lafiya, gani tayi babu network dan haka sai ta aje wayan tana ambaton Allah da fatan Allah yasa lafiya.

Kaman daga sama ba zato ba tsammani driver yaji ya yi karo da wani abu kaman an aje akan kwaltan wanda hakan ya sanya shi kasa sarrafa stering motan, ƙwace masa motan yayi hakan ya sanya suka fara gangarawa gefe wanda da qyar drivern ya samu ya tsayar da motan, Ammi da ke bayan motan salati kawai take aikin yi, kamun ta dawo daga duniyan firgicin hastarin da suka kusa yi, kawai ta hangi mutane a gaban motan tasu da makamai, cikin storo ta jawo wayanta ta shiga WhatsApp, ita batama san layin wa ta shiga ba kawai rubutu take jikinta na rawa, tsawan da aka daka mata ne ya sanyata yin saurin kashe wayan ta tura a jakanta ta jefar a qasan motan wajan qasan seat.

Ƙattin maza ne baƙaƙe munana wanda kana ganinsu kasan babu ko ɗigon Imani a tattare da su, bindigu ne a hannun kowannen su kusan su rai bakwai 7, bindiga suka sanya a goshin driver wanda ya sanya shi dole ya fito, Ammi ma fitowan ta yi dalilin stawan da suka daka mata cikin yarensu da batasan me suke nufi ba.

Ammi da hausarta da ba sosai ba ta buɗe baki za ta yi magana amma kamun ta ma fara maganan wani a cikinsu ya buga mata kan bindiga, ai sai kawai Ammi ta faɗi ta sume, wanda drivern ganin haka sai ya fashe da kuka, amma mutanen nan ba imani balle tausayi haka suka dinga jan Ammi.

Jan Ammi suke ba tare da damuwa da gurjewan da take yi da buga kanta ba, kanta ne ya bugu da wani kututturen duste wanda ba shiri ya dawo da ita daga duniyan suman da tayi.

Tafiya mai nisa suka yi, nan kuwa mamaki ya kama Ammi duk da ba ta hayyacinta sosai, wasu mutanen suka tarar tare da waɗansu, munana ƙarfafan maza sun kai goma 10 tare da wasu mutane da suka kai Shida 6 wanda da alama suma kamosu aka yi kaman yanda aka kamo su Ammi.

Mutane biyar a gaba biyar a baya, uku a gefe da gefe suka sanya su Ammi a stakiya suka naushi jeji, tafiya suke iya tafiya ba tare da sun staya ba ko Hutu balle batun shan ruwa.

Abinda su Ammi suka fahimta mutanen basa jin hausa ko kaɗan kuma english ɗin ma sai caping suka iya basu iya brokin ba balle ordinary english.

Tafiya suke sai wata cikin waɗanda mutanen suka ɗauko ta gurgura caping ɗin ta ce “ina jin fitsari”.

Mutanen cikin faɗa da masifa suka yi yare, ganin matan na ƙoƙarin tsayawa suka sanya bindiga suka harbeta nan ta faɗi gawa, suka stalleke suka tusa su Ammi gaba aka cigaba da tafiya.

Wannan lamari ya storata sauran mutane huɗu da su Ammi su biyu, wani a cikinsu da alama tare yake da wacce aka harbe sai kuka ya sanya yana ambaton Allah.

Ammi ce tayi qarfin halin basa haquri da hausanta da bai nuna ba, sannan ta ce suyi ƙoƙari susan yadda za su yi su gudu, duk kallon bakisan me kike yi ba suka wurgawa Ammi domin Waɗannan mutane marassa imani masu fuskan kafuran da ko da kuɗi aka ce ka gudu ba zaka iya ba domin bindigun hannayensu da zubin halittansu kaɗai ya ishe ka shiga storo da tashin hankali.

Tafiya suke har yamma ta yi, Ammi abinka da ba sabonba har qafafuwanta sun kumbura kana ganinta kasan bata hayyacinta, ba abinda suke sai ambaton Allah ya kawo musu ɗauki domin su ba su ma san ko kidnapping nasu mutanen suka yi ko wani nufin daban.

Su Ammi su huɗu mata sai maza biyu, drivern Ammi da kuma ɗan uwan wacce aka harbe, mutanen nan ko alaman gajiya babu a tattare da su ko kaɗan tafiyan da suke yi bai dame su ba, su Ammi ne dai tafiyan ta jikkata su, musamman Ammi kana ganinta kasan duk tafi sauran kalan hutu bata saba da wahala ba.

Ammi kanta ciwo yake ga qirjinta na haka, jiri take gani qafafuwanta sun sunduma ga bugun da suka mata ɗazu ga kuma buguwan da tayi da suke janta, jinin da ya zuba a jikin Ammi shi ya haddasa mata wannan jiri da ciwon kai domin sosai tayi raunuka kuma ta zubar da jini, bibbiyu ta fara gani wanda kamun tayi wani yunquri tuni ta faɗa a jikin wani murɗeɗen qato a cikin waɗanda suka ɗauko su.

Wanda ta faɗa jikinsa cikin faɗa yasa qasan bindiga ya bugeta da shi wanda ya yi sanadin qarisawanta qasa babu numfashi.

Sauran duk stayuwa suka yi suna yare cikin fushi da stawa-stawa kaman za su kaure da faɗa a junansu, cikin yaren nasu wanda da alama shi ne babba stakaninsu ya ce “cap me de legit, oh she wan for her bodi woto-woto?(me ya faru ko bugu take buƙata?)

“Oga Pwade faɗuwa tayi a jikina kuma kaman bata numfashi”.

Wanda aka qira da Oga Pwaden ne ta masto ya sanya jibgegen qafansa yayi ball da Ammi amma ko mostawa bata yi ba dan kaman ta sandare ma da alama bata numfashi, qara naushinta yayi jin shiru sai ya stugunna ya sanya hannunsa a hancinta ya ji shiru ba numfashi, haka wuyanta da zuciyanta, jin shiru sai ya miqe yana masifa “kunsan dalilin ɗauko su, abinda za suyi baya buqatan kasancewan su da yunwa ko ciwo me yasa baku tambayi ne take so ba yanzu ga shi kunmana asaran mutum biyu kuma mata ga shi wannan kana ganinta kasan za ta fi burge Oga-kwata-kwata”.

“Sorry Oga pwade, to Ojonjo ya ɗauke ta mu tafi mana” sauran suka haɗa baki wajan faɗan hakan.

“Ku baku da hankali ne? Inmuka tafi da deathbody(gawa) muyi me da ita inba Oga-kwata-kwata ya kashemu ba, mu bar gawan mu tafi amma mu kula da sauran kar asaran tayi yawa ga shi ba mutane da yawa muka samo ba”.

“To Oga Pwade” suka haɗa baki suka faɗa, duk sai da suka naushi Ammi sannan suka tsallake gawanta suka tusa qeyar sauran a gaba suka cigaba da tafiya.

Tunda drivern Ammi ya ga haka sai shima ya kama salati yana kuka, dan duk stiya gwanda ace da ranta akan yanda suka mata ga shi ta mutu, baiwar Allah da gatanta amma dabbobin daji ne za su ci gawanta, kuka ya dinga yi wanda mutanen da suka ɗauko su sun zaci wani abu ne nan suka ciro biscuits suka raba musu, ai da gudu duk suka amsa kowa na korawa a cikinsa hannu baka hannu qwarya.

Ammi yanda suka barta a yashe kaman gawa ko mosti bata yi har can stakiyan dare wajajan qarfe biyun dare sai ga hadari da walkiya ba jimawa aka fara ruwa kaman da bakin qwarya, ruwa ake me qarfi kuma duka a jikin Ammi yake sauqa, kaman wacce aka stikara haka taja dogon numfashi tare da buɗe idanuwanta, jikinta ba inda baya mata ciwo ga kanta da ke sara mata kuma yana mata kaman jiri-jira, abu ta gani a hannunta kaman kwali, ba tare da ta tsaya duba menene ba ta sa a bakin zaninta ta tashi tanajin jirin haka ta sanja hanya ta kwasa a guje dan tabbas ta tuno abinda ya sa ta ganta a tsakiyan daji.

Gudu Ammi take yi ba ko waiwaye dan ji take kaman zasu biyota, ba tare da ta damu da kumburan qafan nata ba ko raunukan jikinta haka take kwasan gudu tana taka qayoyi jefa qafa kawai take yi bata san inda take nufa ba, jirin ne ya ci-gaba da damunta tana kan gudun amma abun fin qarfinta yayi tana gudu tana layi kaman wacce ta sha wani abu, ba zato ba tsammani lokaci guda ta taka wani mugun qaya da kuma kwalba, garin waywaye taci karo da wani ɗan bishiya tayi baya ta buga kanta akan wani qaton kututturen bishiya mai stini, shikkenan Ammi a gurin ta kuma mugun faɗuwa ba ta ko mosti dan ta bugu, qafafuwanta na jini kanta na jini.

Belloji ɗa ɗaya tilo ga Arɗo wanda Allah bai bashi haihuwa ba sai yayansa da ya haifa ya basa kyauta kuma ba jimawa Allah yawa iyayen belloji rasuwa, nan Arɗo ya riqesa gam-gam tunda shi baya haihuwa kuma ɗan yayansa sannan yayan nasa ya basa kyauta tun da ran sa, belloji na da shanyensa da mahaifinsa ya bar masa, Arɗo ma yana da nasa, sai belloji ya haɗa yana zuwar musu kiwo, tun yana yaro har ya girma.

Su bororaye ne na usul masu kiwon shanu, da ikon Allah dai suka ya da zango a wannan jejin har suka gina gidajensu na kara suka hayayyafa, amma sunqi shiga cikin mutane balle batun yin wani karatun zamani, sai ta muhammadiya kawai itama ba wai har can ba kawai na yin salla ɗan fatiha, Nasi da Falaqi.

“Hai belloji kam wei hai me shisheyi a shikin uwar ɗaka ba jaki hito hai ki tai kiwo ba, ko hai sho kike shaniyata ya mace da yunwa ce? Arɗo ke magana cikin harshen shi da fillanci ya cinye.

Yaron da ya qira da belloji ne ya fito daga wani ɗan madaidaicin bukka sanye da wando wanda suke ɗinkawa sama ya ɗame qasa ya buɗu da riga burgujeje da takalminsa wanda akewa laqabi da “tashi ka bi shanu”.

Belloji ɗan mastashin saurayi da ba zai haura shekara 17 ba siririne fari yana da ɗan tsayi sannan kyakkyawa ne dai-dai gwargwado, sandarsa ya ɗauka ya saqala a bayan wuyansa yana faɗin “yanju jan tai kiwon fa Arɗo, aradun Allah shaniyaki ya qi yin shauri aradu buge hegiya jan yi, na tai hai na dawo” ya faɗa yana ficewa a gidan.

Arɗo cikin fillanci ya zagi bellojin yana faɗin “cegiya belloji hai ki dawo da shanuwai na lahiya”.

Belloji yana fita ya kaɗa kan shanaye fin ɗari biyu suka yi jeji, yana tafiya yana ɗan waqar sa da fillanci.

Tafiya suka yi sosai shanaye na kiwo yanda ya kamata domin yanayin garin anfara ruwa ciyayi sun fito yanda dabbobi za su ci su qoshi, qasan wani bishiya belloji ya samu ya zauna yana ɓare gyaɗansa da ya taho da shi yana ci dabbobi na cin ciyayinsu su ma.

Har yamma ta yi sannan belloji ya fara kaɗo kan shanayen, wasu biyu ne suka yi kwana nan ya bisu yana taro kansu, da qyar ya samu ya haɗe su ya gangara da su rafi suka sha ruwa sannan suka nufi hanyan dawowa gida, belloji yana tafiya dai ya hangi bishiyan gwandan jeji yayi ‘ya’ya sun nuna, rasta wajan yayi yana faɗin “cege Arɗo jai washe matauni (haƙora), wanga gwandan da ta nune hai ka she kana taɓa hi kai fahe na shan jaqi jai yi”.

Kamun belloji ya qarisa wajan yayi tuntuɓe da abu, da yake kansa na sama miqawa kawai yayi zuwa bishiyan bai lura da me yayi tuntuɓe ba sai da ya gama ciki aljihunansa da gwandan jejin ya juyo kawai ya ga mutum jina-jina a kwance a qasa kaman gawa, cikin rashin storo ya masto kusa da ita yana faɗin “hai belloji ta shiga shaba’in Aradun Allah, wannan mutum ko aljan? Aradu ji cegen da cau dole na ɗauke sa hai muje na nunawa Arɗo me cau na shan Arɗo bata taɓa ganin mai cau ba aradun Allah”.

Belloji ɗago ta yayi ya saɓa a kafaɗa, qarshe akan shanu ya ɗaurata suka koma gida.

Suna shigowa gida ya bar shanayen a garekensu sannan ya ɗago matar da ta ɗauko yayo gidan Arɗo da ita yana shiga ya ce “Arɗo jo kiga aljana na shamo Aradun Allah yau, ai ni naga aljana mai cau Aradu”.

Matar Arɗo ce ta fito cikin fillanci tana faɗin “ke belloji ina kinka shamo wanga mutum?

Belloji ya buɗe baki zai yi magana sai ga Arɗo ya shigo “belloji kin higa uku kin lalashe, ina kika shamo aljana mai kyau? Cewar Arɗo yana qarisowa cikin gidan.

Matar Arɗo ce ta ce “haba Arɗo kur kuyi irin ta belloji mana, wanga ba aljani bane mutum she Aradu”.

Arɗo ne ya ce “Allah sarki bawan Allah dubi jikinshi hai duk shiwo, kai Maman belloji kawo tabarma”.

Matar Arɗo taburman ta ɗauko aka shumfiɗe Ammi, ruwan zafi ta ɗaura bayan ya ɗumu ciwokan fiskan Ammi da qafanta aka goge aka manna mata wani ganye da Arɗo yasa belloji ya daka.

Anan rugan tasu Arɗo ya aika aka qira wani mai magani, amma har aka kwana biyu ba alaman sauqi dan ga duk alama matar dogon suma ta yi, inka kalleta ma ba lallai ka gane da ranta ba.

Daga qarshe Arɗo ya aika rugan hamman aka masa magana da Baffai saboda dama kowa yasan Baffai a harkan magani dan ya gaji mahaifinsa ne mijin Baabaa Mero, anci sa’a Baffai ya amsa zai zo, inda ba ɓata lokaci ya je ganin matar sai ta basa tausayi kuma ya dage zai taimaka dan shi ma ya samu lada ba sai anbiya sa komai ba, kuma cikin ikon Allah ya mata magani ta warke.

 *****

Cigaban Labari.

Baabaa Mero ke rafka salati tana faɗin “ai nikam tunda Allah yasa Isa da Indo suka haifoki shikkenan sun haifomin jaraba, jarababbun iyaye koɗaɗɗu suna ganin na stofe sun turoki ki qarisa ni, da basa sonki suka haifeki ni Meramu naga rayuwa, Allah na tuba badan-badan ba ai sai nace da basu ma haiho ki ba, yarinya kullum abu guda jaraba akan bokon ‘yan wuta, to Aradu aure za’a miki a haka kije can ki fama in aka miki gori baki da ko nunu kece kika ja, shawaragiya shiyasa kullum ba ki da auki kaman hastin-bana”.

Innai tura baki tayi ta ce “ni fa ba iya zuwa zan yi ba baabaata”.

“Don yayan ubanki Musa ni baabaar ubanki ce ba taki ba, ja’irar yarinya kawai, Aradu in baki shirya ba kinfito yau sai nayi qasa-qasa da ke a garin nan, ko ma kija na ɗauke ki mu tafi masallaci naje can na bada sadakarki, ai ni Meramu aiki kuma ya qara samu na tunda jarababben hamman naku ya tattara komastansa wai ya tafi shima tasa karatun can wata uwa duniya ai ni aka bari da dogon baki akanki dan dama shi kaɗai kike storo kaman azara’ilunki,to bari kiji ubanki Isa zan sanya a nemomin salula duk randa kika buga min tijara nima na kamosa a salula na sanar masa yana miki adashe a littafi duk randa ya dawo ya ɓarzamin ke ‘yar buhun uba”.

Innai tura qaramin bakinta tayi tana qunquni ita qafanta na ciwo ba inda za taje, qarshe kuka ta sanya tana shura qafa “ni bazanje ba yau kuma ni na gaji da bokonma kuma Allah ba zan yi aure ba yiiiiiiiiiii yiiiiiiiiiii Wayyooo! Uwataa”.

Baabaa Mero wangale baki tayi tana ganin ikon Allah dan taqaici ta ma rasa me za ta yi wa jikartata ta huta, sai kawai ta rarumi daron kwano da yake gefenta tayi kan innai, ita kuwa ganin haka sai ta ruga a guje ta shige ɗakin ta turo ƙofa tana ihu ta rarumi kayan makaranta ta sanya ta fito ko mai bata shafa ba balle kwalli a ido, Baabaa ganin ta fito a shirye taɓe baki tayi ta ce dan uban mutum inyaga dama ya tafi tunɓur nidai abarmin gida a tafi koyo yaren ‘yan wuta, Allah yasa wancan qawar taki fatuma ta miki dariya”.

Innai tura baki tayi ta qi ko cin komai ta fice, gidansu taje ta iske Baffai ya fita, kaman za tayi kuka haka ta gaishe da mama Lami ta gaishe da Innarsu duk da ba amsawa take ba, Allah yaso ta Mama Lami ta bata Naira ɗari sannan ta fito ta samu Rabe na jiranta kawai ta ɗale mashine suka ɗau hanyan makaranta.

<< Jahilci Ko Al’ada 22Jahilci Ko Al’ada 24 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×