Skip to content
Part 4 of 15 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

 اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله

Sai nan gaba za ka san gaskiya nake faɗa maka kuma ni mai sonka ce, in ka girma ka tsofe ka rasa mai yarda ta aure ka, ka ci-gaba da biyewa Baffan ka wai baka girma ba gaka shagiri-girbau ko? To dan ma ka sani shi Baffan naka ma auren wuri ya yi dan dai kawai Allah bai kawo haihuwar da wuri ba ne amma ai da yana da yaro kusan sa’an ka, yo ni Meramu Allah Na tuba maka ba don kar na karta saɓo ba ai Magaji da cewa zan yi da ma bai haihun ba kaga fa tsakani da Allah ya ce Allah Ya dube su yai musu kyautan da ba kowa ke samu ba, yarinya nutsattsiya kuma kyakkyawa gata da sunan manya, ni fa wannan ɗan banzan AL’ADAN ba dani ba in faɗa maka ji nake kaman in kama Indo in shaketa kowa ya huta, dan cin fuska irin na Baffanku ya ɗauki sunana ya sawa yarinya sannan a nuna kiri-kiri ana son kashe yarinya dan hassada da bakin ciki, shi kuma shashashan gashi solo-ɓiyo ya kasa tsawatar mata wai ita kunyan ƴar fari to Allah wadaran wannan kunya da jahilallen al’ada, kalla fa hankali irin na takwarata da tausayi da sanin ya kamata, tana taso wa ita gata mai son uwarta yarinyar nan fa bata warke ba ta tashi ta tafi gidan can ina mata magana ko ta saurare ni kuma nasan aiki za taje tai ta yi kaman jaka dan abinda suka ɗauke ta kenan ita ma ƴar buhun uba, amma Allah wadaran naka ya lalace wannan rashin zuciya na Innai na sani jin watarana kaman na zaune ta gata ba auki ba sai kuma naji tausayinta ƴar ƙaniya kawai”.

Goro ta gutsura kamun ta ci-gaba da surutun ta “kaga fa Magaji wallahi ina jiyewa mutanen nan hisabin Ubangiji, sunan ta Maryam fa suke mata wannan ɗanyen jaraba su basu san lukutin al’haqi suke ɗauka wa kansu ba Kuma kwaran-kwatsa duk in suka yarda suka yi sanadin mutuwan takwara ta sai nayi shari’a da su har shi uban nata isa sai hukuma sun shiga tsakanina da su, dukan su jarababbu tambaɗaɗɗu ƴan buhun uba”.

Dariya ya so kwace wa Magaji ganin yacce take yi kaman suna gabanta, danne dariyan yayi yace “yanzu dai stohuwa naji magananki amma dan Allah kar kice mun in kayi wa mai suna Maryam abu zunubin ka dabanne kuma lukuti ne?”

Gyara zama Baabaa Mero tayi, dan kuwa abun nema ya samu an sosawa Baabaa Meramu inda yake mata ƙaiƙayi, ta ce “Yauwa Magaji kaga kuwa gwanda da kayi tambayar nan dan nasan duk karatun muhammadiyan ka da bokoko awuta baka sani ba dan ba mai sani wannan sai wanda Allah ya nufa da arziqin rahaman sani, NANA MARYAMA, Maryama daban ce a cikin mata ka duba fa irin girma da darajan Qur’ani amma ba wata mace da Allah ya ambaci sunanta kai staye a ciki sai Nana Maryam Uwar isah”.

Murmushi tsohuwa tayi dan in tana wannan labari daɗi take ji “ita Maryama komai nata daban ne, hankali gareta, ga haƙuri, ga nutsuwa, ga iya zama da mutane, ga addini, ga kyau, ga ilimi, ga tarbiyya, ga tausayi, ga iya soyayya, uwa uba baiwa gare ta wanda ba kowa ke sani ba sai wanda Allah ya nufa da ikon sani barin ma dai wanda ya auri mai wannan suna Allah dai ya yiwa duk wata mai suna Maryam albarka a duk inda take” ( na ce ba Baabaa Mero mu kuma da ba maryam sunan mu ba sai ki tsine mana na ce a tsine mana).

Magaji sauraran Baabaa Mero kawai yake yi yana cewa a ransa “kaga aku gidan surutu daman ke kullum a yabon sunanki kike” amma a zahiri sai yace “aikuwa Maryam ta wuce haka ma Baabaa”.

Washe haƙora ta yi tace “kaga ɗan albarka shiyasa nake sonka nake faɗa maka gaskiya ka yi aure, ai ni duk wanda zai yaba mun takwara tom banda kamarsa sonsa nake da ƙaunarsa, Allah Dai Ya muku albarka ya nuna mun auranku da yaranku”. Murmushi Magaji ya yi bai ce komai ba.

“Kunga ja’irin yaro ba za ka amsa da Ameen ba wato ance maka bansan murmushin na son aure ba ne kayi” cewar Baabaa Mero tana washe baki.

Magaji yace “haba ni me zanyi da wata bayan ina da ke yar tsohuwata ta, kinsan fa da tsohon zuma ake magani”.

Hararansa tayi tace “kaga ɗan ƙwal uba da yaudara, zai cuceni tom ni bana sonka kaje ka kawo man kishiya kawai shi nake so, in ka yi sa’a ka samo Maryama dan ina faɗa maka Magaji samun Maryama sai me rabo da sa’a irin rantsanstar rabon nan dan ko kana sallan dare da bada sadaka kai har ma da raba zakka kuma qarshenta ko makka kake zuwa duk juma’a sai da rabon ka samun mesuna Maryam ko da kuwa da kuɗin ka”.

Na ce ba Baba Mero ma tsohuwa ta yaba Maryam bare mu tom muma dai ba mu gwada Waƙan umar m shariff Maryama.

Nayi soyayya kala-kala amma banga ya naki ba

Naga yammata iri-iri a kyawu ba zasu kai ki ba

Kalamun so kashi-kashi banji salo irin naki ba

Kyawun halinki ba’a faɗa na baki hanya wuce gaba

Gata nan tafe masoyoyiyata gata nan tafe tana zuwa

Maryama zooo maryama zooo maryama zooo masoyiya…

Amincin Allah ya tabbata a gareku masu suna Maryam

Zan juya kenan na fice kamun Magaji ya ganni ba sai aka yi sa a muka haɗa ido da Baabaa Mero ba ni ko na ƙara tamke al’ƙalami na, Baabaa Mero cewa ta yi “Allah dai ya miki albarka Hariratu ourmmarhn batooler Allah kawo Batoolerh lafiya mu kwaso shoki mu zuba qara’i, tattaro kayanki a inda kika sauqa a qauyen nan daga yau kin dawo gidan nan da zama tunda kika waqe Maryama, inga uban da zai takura miki ko ya koraki” ta faɗa tana hararan Magaji

Godiya nake Baabaa Mero.

Fan’s ɗin baabaa Mero azo a taya ni Godiya jama’a dan kuwa labari yanzu aka fara, Baabaa Mero har da ɗaki ta ba ni muje zuwa.

 *****

Hiransu suka ci-gaba da yi da Magaji anan yake ce mata zai nemowa Innai makaranta a cikin Ashaka kuma suna son na taje ta dawo.

“Na shiga arba’in da uku ni Meramu yanzu sabi da Allah wannan jarabar bokon har da takwara ta, Magaji yanzu ina laifin kace zaku mata aure amma wai boko, wanne kalan boko ne haka nikam gaskiya bason bokon nan naku nake ba dan so nake takwarata tayi aure ta haihu tunda raina naga yaranta inyaso kai ka stofe ma a gida bai dame ni ba”.

Taɓe baki Magaji yayi yace “ke kika jiyo ni dai makaranta zan turata”.

Cikin masifa Baabaa Mero tace “tunda duk kunnenku a hure yake baku ɗauke ni a bakin komai ba kun cike carɓin mun fistara tsaff to shikkenan ba komai, sai abinda kuke so za kuyi ko? to billahillzi bari shi uban nata Isa yazo ya same ni kowa ya shaida kuma ya ji in dai takwara ta taje makaranta ta dawo ta rasa mijin aure ko zaka mutu kai zaka aure ta”.

Haɗe fuska ya yi ya miqe yana cewa “kamun a ji mu ba na yi tafiya ta”.

Taɓe baki ta yi ta ce “kaima kai ka jiyo tambaɗaɗɗen yaro kawai ko itama bata sonka takwarar tawa sai me sallan dare kai ko farillahn ma nasan da ƙyar kake miƙawa balle nafila”

Dariya ta basa ya ce “ni dai ƴar tsohuwa byee”

Cikin masifa ta ce “na boye maka ƙafan ubanka Musa ɗan buhun uba ni zaka wa wannan banzan yaren da kuke zagi dashi yaren ƴan wuta yaren jarababbu tambaɗaɗɗu, to to ni Meramu me ya haɗani da wuta ina masoyiyar Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam, Allah mana tsari da wuta ban da nima da shirme na Magaji ina da suna Maryam kam ai ma mune farkon shiga aljnna”.

Murmusawa ya yi ya ce “ai kuwa dai ga ki sunanki Maryam ga ɗanki Isah Annabi guda ai kece ma a gaba”.

Washe haƙora ta yi tace “Allah dai ya maka albarka Allah qara mana son Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam”.

Murmushi yayi dan ko ba komai yawan ambatan Annabi da take yi yana sanya sa jin dama-daman surutun ta “ƴar stohuwata Malama Maryama mai kama da hurul-eyn na tafi” ya faɗa yana ficewa a gidan, Allah tsare ta yi masa.

Ganin ana neman ƙarfe sha-ɗaya 11 taso wa Baabaa Mero ta yi dan tayi sallan walha.

SALLAHN WALHA

 من فضلة الصلاة الضح

 

عن ابي هريرة رضي الله عنه قال ، قال رسول الله صلى الله عليه والسلام ” إن فى جنة بابا يقال له (( الضحى )) فإذا كان يوم القيامة نادى مناد: أين الذين كانوا يداومون على الصلاة الضحى؟ هذا بابكم فادخلوه برحمة الله ” رواه الطبراني

 

و في قول ابي هريرة ايضا أوصاني خليلي بثلاث :

” صيام ثلاثة أيام من كل شهر، ركعتي الضحى ، أن أوتر قلبل ان انام”

Daga falalar sallar walha

FASSARA :

An karɓo daga Abi Huraira Allah Ya ƙara mishi yarda yace, Annabin rahama sallallahu Alaihi was- sallam yace ” a cikin Aljanna akwai wata kofa ana ce mata (( DUHA )) idan Alƙiyama ta kasance mai shila zai yi ƙira, ina waɗanda suka dauwama a sallar walha ? Wannnan kofar kuce ku shigeta da rahamar Ubangiji “

Ɗabarani ne ya rawaito

2: A cikin faɗin Abi huraira kuma,

Masoyina ya min wasiyya da Abubuwa guda uku:

Azumin kwana uku a kowani wata, yin sallar walha, da na ringa yin sallar wuturi kafin nayi Bacci

WALLAHU A’ALAM.

Inna bayan sun gama kukansu da Hassu har bacci ya ɗauke su, farkawa tayi tana mai karanto addu’an tashuwa a bacci, ganin 11 har yayi da sauri ta tashi ta fita a ɗakin.

Da sallama abakinta ta shiga ɗakin Innan su, Amsa sallaman tayi.

Samunta tayi tana naɗin kaya sai ta stugunna tace “Inna kawo in tayaki” ba tace mata qala ba kuma ko kallonta ba tayi ba ta tashi ta zauna a bakin gado.

Kan Innai a qasa tana jin wani iri a haka har ta kammala mata naɗin kayan ta gyara ɗakin sannan ta koma gabanta ta stugunna kaman ɗazu tace “Inna me za’a ɗora na rana? Duk cikin harcen su na fillanci take maganan.

Kau da kai Inna ta yi ba tace komai ba, ganin haka jiki a sanyaye ta tashi ta fita a ɗakin.

Ɗakinsu taje ta tashi Hassu tace “Hassu tashi kije ki tambayi Inna me za’a ɗora na rana sai na ɗaura”.

Kallon Addan nata tayi ta turo baki tace “Adda me yasa ke ba za ki tambaya da kanki ba? In kina qara nisanta kanki da ita ne fa bakwa shaquwa”.

Murmushi ta yi ta zauna gefen gadon nasu na kara(ciyayi) tace “ke dai jeki tambayo kizo muyi tare ko kuwa kiyi wanka ki huta abinki”.

Taso wa Hassu tayi ta fice, ɗakin Innan su ta shiga da sallama.

Amsa mata tayi, ta qarisa ta stugunna gabanta kaman yacce ɗazu Innai tayi (tarbiya ne gare su duka mu kula da tarbiyan yaran mu ko da ba cikin gida ba, ko dan mutanen waje abun ba daɗi ya zama na ana cewa yaranka ba tarbiya dan Allah iyaye mu kula)

“Inna me za’a yi na rana?

Innan su tace “a dafa fara da yaji uwata”

“Uhmn!” Hassu tace kawai.

Inna kallonta ta yi tace “ya aka yi uwata?

“Inna kiyi haƙuri in wani laifi Adda ta maki ki yafe mata kinji” Hassu ta faɗa kaman za tayi kuka

Murmusawa Innan su tayi tace “Yaro Yaro ne! tashi kije kuyi aikin”.

Kasancewan basu kasance masu musu da iyayensu ba tashuwan tayi kaman yacce ta umurceta ta fita a ɗakin.

Aikin suka haɗu da Innai suke cikin qanqanin lokaci suka gama, wanka Hassu ta shiga ta fito itama Innai ta shiga tayi suka shirya.

Duk da tasan ba amsawa Inna za tayi ba amma ta mata sallama tace “Inna zamu tafi gidan baabaa”.

Ɗakin Mama lami suka je dan suce mata sun shiga gidan baabaa kar ta neme su shiru amma suka tarar tana baccin asara (inji kakata baccin mutuwan rai).

Ɗaukan abincin baabaa Mero Hassu tayi suka kama hanyan gidan baabaa bayan sun gama komi a gidan nasu.

Tafiya suke suna hira inda Innai ke cewa “Hassu kar ki damu kinji, ki daina takura Inna kar kema tayi fushi da ke kaman ni da bansan me na mata ba, komai zai wuce zan cigaba da haquri”.

Da sallama suka shiga gidan Baabaa Mero, ta amsa musu tana faɗin “kunga ƴammatan Malam da Inna jikokin Meramu Allah muku albarka ƴammatan aljanna”.

Murmushi suke dukansu Innai ce ta faɗa jikin Baabaa mero tana cewa “washhhh! baabaalle ta na gaji Allah”.

Baabaa Mero kaman mai jiranta ta kalleta tace…

 

<< Jahilci Ko Al’ada 3Jahilci Ko Al’ada 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×