Skip to content
Part 5 of 25 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

“Takwara ke ko kiji tsoron Allah da shegen son jikin dake damun ki ɗaga ni kar ki karya stohuwa”. Cunno baki Innai tayi ta ce “Baabaata ba kiga fa aikin da nayi ba duk na gaji”.

Baabaa Mero ta ce “ni tashi mun a jiki kamun ma takaici yasa na surfa ki na kirɓa ki, shagiri-girbau kawai dama can uban wa ya sanya ki aikin da zaki faɗo man a ka kaman gini, mutum banda gulma da kini-bibi ba abinda ya iya wai baka gama samun sauqi ba sai shegen son aiki kaman ba jini ne ajikinki ba, to kyaji dashi stunstun da yaja ruwa shi ruwa ke duka dan haka ɗagani banson jaraban sakalci”.

Hassu tana dariya ta ce “Baabaa kuma fa tare muka yi aikin bama ita kaɗai tayi ba”.

Baabaa ta ce “Allah dai ya miki albarka Hansai dube ki da kwarinki kaman ba kiyi komai ba”. 

Tura baki itama Hassu tayi tace “nifa Baabaa ki dena cemun Hansai ɗin nan, duk kun ɓatamun suna wai Hassu wai Hansai ni fa gwanda ku dinga cemun Hafsatu na yafi daɗi aradu”. 

Dankwalo ta mata tace “nace dan matar ubanki Lami baza’a ce ba Hansai zance, wato kema kin renani kamar qannan mai zubin kajin mayun nan ko?” 

Hira suke da raha abunsu kaka da jikokinta.

Tashuwa suka yi suka ce “Baabaa kici tuwo ba muje gidan baba mu dawo”. 

“To ku dawo lafiya ku gaidamun su Shatu da halimatu” cewar Baabaa Mero tana jawo Radion ta. 

“Zasu ji baabaarmu”. Sai tace “ƴan kwal uba iyayen kalen dangi tunda kashe taku uwar kuka yi zaku qwacewa ubanku nasa, ni baabaar iyayenku ce ba ku ba”. 

Fita suka yi suna dariya sanin halin ta “Allah ja kwana ya bar mana baabaar iyayenmu” faɗin su. Murmusawa tayi tace “Allah maku albarka kuma”. 

Tafiya suke abinsu suna hira sai Hassu tace “Addah gaskiya yau nikam muje dandali in anjuma yayi”

Waro manyan idanunta tayi tace “Hassu ki rufa mana asiri mu mutu a gida maza su mana sutura, Hamma Magaji ya ganmu acan ko ya samu labarin munje kashinmu ya bushe dan haka ni ba ruwana kinsan gobe monday kuna da school ko?”

Hassu kaman za tayi kuka tace “Kai de Addah nikam muje dan Allah please” To ki dawo lafiyah ni dai Innai ba ruwana ba dani ba gaɗa a kotu, kuma in an ganni a lahira kaini aka yi” Innai ta faɗa suna qarisa shigewa gidan baban nasu.

“Assalamu’alaikummm⁴ Maamaaa³” suka haɗa baki suka yi sallama, mama da ke fitowa banɗaki tace “ai tun da naji anata kwala sallama da qiran nan nasan sai ke aikin ki ne Innai Allah shiryamana ke”. 

Innai na dariya tace “Mamata nayi kewanki ne fa”. 

“A’a kam ba wani kewa yanzuma nasan wajan su Shatu kukazo ba waje na ba” mama ta faɗa tana ajiye butan hannun ta. Dariya Hassu tayi tace “laa Mama kaman kinsani nice kawai nazo gaishe ki”. 

Mama tace “au wai ke ɗin Hassu ai gwanda Innai ma akan ki, dukan ku dai kunsan wajan su wa kuka zo”. 

Suna dariya suka durqusa suka gaishe da mama ta amsa ta tambayesu ya su Innansu da lami? Duk suna lafiya suna gaidaki har da Baabaa ma. 

Mama tace “ashe kuce mun daga gidan Baabaa kuke, to fatan tana lafiya?” suka bata amsa da “tana lafiya lau”. 

“Masha Allah to ga can su Shatun suna sallah a ɗaki” mama ta faɗa. 

Wucewa ɗakin su shatu suka yi, Innai tace “uwata sannu da ibada”. 

Shatu na murmushi tace “sannu Adda Innai”. 

Hassu tace “Shatu ba magana ne ina hali take? 

“Ke dai Hassu aiki ya ganki sunan Inna gareni amma baki ko sakayawa sai dai kice Shatu gastau-bajau” yarinyan da ta kusa sa’an Innai ta faɗa. 

Hararanta Hassu tayi tace “na sakaya akan me? Ai Inna daban ke daban ah to dan sunanku iri ɗaya ba wai ke ce Innan tawa ba ai”. 

“Za ki ji dashi dai” Shatu ta faɗa. 

Alwala Hassu da Innai suka yi suma suka yi sallahn.Abinci shatu ta ɗauko musu dukan su ukun suka zauna suka ci suka cika cikin su, bayan sun gama ci sai kuma hira har hali ta dawo aike ta jona su. Har sai can bayan la’asar sannan Innai tace “Hassu kinga tashi mu tafi naje nai wa mama lami sanwan dare”. 

“Kai Adda ke dai bakya gajiya Allah to ni ba inda zani yanzu ehe ai bamu gama hira ba ko Shatu? Hassu ta faɗa tana kallon Shatu. Shatu tace “eh Addah Innai please ki tsaya sai anjuma kaɗan sai mu tafi duka ai dai mama lamin lafiyan ta lau zata iya yin aiki ta”. 

Innai tace “Nikam ku rabani da jaraban surutun mama Lami dan sai ta kusa cinye ni ɗanya, kuma kunsan gobe dukan ku zaku school dan haka maza-maza tashi mu tafi Hassu”. Hassu ba yanda ta iya haka ta tashi tana aikin turo baki, Sallama suka yi wa mama tana Allah musu albarka suka wuce gidan Baabaa Mero. 

Kwanuka suka ɗauka kawai suka nufi kofan dan komawa gida. Baabaa Mero ke magana muryanta a ɗage “wato dai takwara ke de baki gaaji kirki ba ko kaɗan, Haka zaki barni nai ta zama ni ɗaya agida kaman mayya to ban yarda ba”. 

Innai tana dariya ta juyo tace “Kai de baaballe ta kefa jaruma ce”. 

Baabaa Mero tace “nabi jarumtan da gudu dan buhun ubanki Isa”. 

Turo baki tayi tace “ni banson zagi baabaa” 

Baabaa Mero tace “na zage ki zo ki ɗau mataki shi uban naki ba nice nan na tsugunna na haifesa ba har ya haife ki ƴar ƙwal uba” kara turo baki Innai tayi, sai baabaa tace “ki tura in kinga dama yakai gidanku” .Cikin lallashi Innai tace “tom baabaata kiyi haquri zan dawo nima fa kinsan bazan iya kwana ba’a kusa dake ba”. Washe baki baabaa tayi tace “shiyasa nake sonki takwara ta, tunda kin zama ƴar aiki aje ayi aiki lafiya Allah muku albarka Allah qara miki lafiya ko”. “Ameen baabaata” ta faɗa a taqaice suka juya suka fice a gidan. 

Sun isa sun samu har Mama lami ta ɗaura sanwan dare, tana hangan ta a madafi tace “naga ta kaina yau kuma da surutun mama lami, kinga Hassu je kiyi wanke-wanke da wuri ki gama ki kama shara ni kuma zan karɓi girkin” Zuwa madafin tayi tace “sannu da aiki mama lami”. 

Harara ta mata tace “wato dai ɓaro-ɓaro a gidan nan kike nunamun ba nice uwarki ba Innai, kinsan ba uwarki ce da aiki ba kika kama figaggun qafanki kika tafi yawo to yana da kyau bari kiji ko uwarki bata miki riqon da na miki ba dan ni nan da kika rena ɗin to nono ne kawai ban baki ba da kuma haifan ki amma duk wahalanki nice nan na shanye su tass nice komi naki, ko mutuwa za kiyi kuka ko kallo baki isa uwarki ba bare har ta baki nono”. Kanta a kasa tace “ki yi Haquri mama” dan in da sabo ta saba duk randa ta mata laifi wannan gorin kam sai tasha shi har da wanda yafi wannan.

Tsaki mama Lami taja ta wuce a wajan, duk abun nan da suke yi har da maganganun mama Lami Inna dake waje kusa da madafin tana gyaran ɗan akurkin dabbobi tana jinsu amma ko juyowa ta takallesu ba tayi ba kuma ko a fuska baa alaman maganganun da akayi ya dame ta. 

Hassu ke kunkuni tana wanke-wanken tana cewa “ai de wallahi Inna kece kika jawa Adda” a haka Hassu ta gama wanke-wanken ta kama sharan gidan. Innai ta qarisa girkin ta raba ta sawa kowa nasa, ta kai na Baffai ɗakin mama lami sannan ta kai na Hamman su ɗakinsa.

Hassu ta ɗau nasu ta kai musu ɗakin nasu, Innai ta kaiwa su Inna nasu qofan ɗakin mama lami. 

Bayan sun kammala komi Magrib yayi dukansu alwala suka yi kowa ya shige ɗaki dan yin sallah. Bayan sun idar ita da Hassu duka suka ɗauki Qur’ani suna karatu kamun a qira isha’i.

Masha Allah! shine kawai abun furtawa saboda daɗin muryansu sannan karatun na fita zar-zar, a haka har aka qira isha’i sannan suka rufe Qur’anin suka tashi suka gabatar da sallahn.

Tuwonsu suka ja suna ci suna fira, can suka jiyo muryan baffansu alaman ya dawo kenan. 

Bayahn sun gama cin tuwon kowa ya wanke hannunsa, sun tabbatar Baffai ya gama cin nasa tuwon yana zaune a taburman saqa a tsakar gidan.

Zuwa wajansa suka yi suka stugunna gefensa, kallon su Baffai yayi yace “Mamana ku zauna ko”. 

Zama suka yi a tabarman baffan nasu.

Gaishe sa suka yi ya amsa yana sa masu albarka.

Kallonsu yayi yace “yaran Baffai ko akwai wani abun ne?

Kan Innai a qasa ta girgiza kai, Hassu kuma tace “bakomi baffanmu”

Baffai yace “To Allah muku albarka, yauwa mamana munyi magana da yayanki za’a kaiki makaranta gobe in Allah ya kaimu tunda naga kinji sauqi sosai”

Kanta a qasa tace “Allah kaimu Baffai”

Sai Yace “Ameeñ ƴar Baffai, sannan na kwana kike so ko na aje a dawo?”

Haryanzu kanta a qasan tace cikin nistuwa “ko wanne Baffai zaɓinku shine nawa”.  

Murmusawa yayi aransa yace “dattakuwa yarinya mai halin manya Allah rayamun ke yai maki albarka Maryam uwata” a fili kuwa yace “to shikkenan dama dan naji ta bakinki ne amma tuni Hamman ku yace za kike zuwa ki dawo”. 

Hassu tace “ai yafi Baffai dan nikam bazan iya kwana ni kaɗai ba”

Murmushi yayi yace “Allah muku albarka”

Suka amsa “Ameen”.

 

Ya ce “To kowacce taje ta kawo Qur’anin ta naji haddanta kamun Hamman ku ya dawo”.

Hassu ta tashi taje ta ɗauko musu.

Karatun suka yi, ya qara musu yace “a dage yaran Baffai Allah maku albarka Allah taimaka ko”

Suka amsa da “Ameen baffanmu”

Sallamansu yayi sannan suka tashi suka bar wajan. 

Innai tace “nikam zan koma wajan Baabaata”

Hassu tace “to Adda sai da safe”. 

Innai sai da safe tawa su Baffai da su Inna, Hassu ta raka ta amma basu isa gidan ba ta dawo ita kuma ta qarisa. 

Ɗakin Innar su Hassu ta shige ta ɗale gado, Kallonta kawai Inna tayi ta murmusa tace “Uwata tashi maza kije kiyi alwala kizo kiyi adduan bacci”.

“To Innanmu” alwala taje tayo tazo tayi addu’a takwanta saboda gobe zuwa makaranta monday. 

Da sallama ta shiga gidan ta samu Baabaa na zaune akan ƴar tabarmar ta da abun goron ta a gefen ta.

Amsa mata sallaman baabaa tayi tana washe baki tace “Sannu takwara ƴar albarka”.

“Sannu baabaalle ta” cewar Innai da ta kwanta ta ɗaura kanta a cinyar tsohuwan.

 

“Yauwa Baabaata in tambaye ki” cewar Innai. 

Baabaa Mero tace “tambayeni ƴar nan ina jinki”. 

Baabaa ta nikam me yasa ba ki cika son a kawo miki tuwon dare bane?

Murmushi baabaa Mero tayi tace “yo ina za ki gane ke yarinyace takwara”. 

Turo baki Innai tayi tana cewa “ni dai faɗamun”. 

Tom takwara tuwo da dare cinsa sosai ai bai kamata ba balle ga mu stofaffi, saboda ba’a son mutum na cin abu mai nauyi in zai kwanta sannan kuma gani tsohuwa kinga bakina sai da kayan maƙwalashe.

Dariya Innai tayi tace “ga gaskiyan nan ya fito baabaata kawai kice kwaɗayi gare ki”

Make mata baki baabaa tayi tana cewa “wato ma nice ke kwaɗayi, to ba dole nayi kwaɗayi ba na stufa shekaru nawa ni Meramu”. 

“Uhmn” kawai Innai tace.

kallonta baabaa tayi tace “takwarata ya aka yi?

Cunno baki tayi tace “ni fa Allah nagaji da karatun nan baabaa kice abarni nayi zama na haka”.

Make mata baki Baabaa Mero ta kuma yi tace “dan ubanki Isa kin gaji da karatu dan gidan ku uban wa zai miki? Ki godewa Allah ma zaki dinga nesa da uwarki ko taqaicin ta zai ragu miki, ko so kike ki zauna ba ki zuwa makarantar baqin cikin halin Indon ya kashemun ke dan buhun ubanki, ai ko ni nan ba qaunar maganan bokon nan nake ba amma tunda wannan balagaggen mai jarabar taurin kan yace zaki to ko baki na zai kai cikin Gombe tsayi sai kinje gwanda na haqura na biki da addu’a dan zuwan naki yafimun, ke ba saurayi ba balle ayi maganan aure gwanda kawai kije ko hankalina ya kwanta, domin Indo na tabbatar gaba(haushi) take yi da ni da gan-gan take laɓewa dake, amma dai ni take nufi tunda ta ga ba sunan uwarta gare ki ba shiyasa take mun wannan cin fiskan, Allah de ya saka miki takwarata”. 

Murmushi Innai tayi ba tare da tace komi ba domin ta saba da irin wannan magana, kuma yana qara mata zafin da take ji a zuciyan ta, duk da zuwa yanzu yaci ace ya zama soso da sabulun ta.

“Baabata kimun tastuniya mai daɗi har nayi bacci kinji” cewar Innai da idanuwan ta ke kan farin-wata tana murmushi. Baabaa tace “dan gidanku tunda ni manguwanku ce(mai aiki) ubanki na biyana duk wata dole kice na miki tastuniya, tashi maza kiyo alwala muyi nafila mu samu mu kwanta ki huta gajiyan ayyukanki”. 

Innai kaman za tayi kuka tace “ayya de baaballe ta ki bari sai anjuma ki tasheni muyi nafila” ta faɗa tana lumshe ido kaman mai jin bacci. 

Washegari Monday, Hassu ta shirya ta wuce makaranta da wuri dan suna daf da fara exam’s na fita a aji biyar 5. Innai ce tayi aikin komi kaman kullum kama daga ɗumame shara wanke-wanke duk, sannan ta shirya ta yiwa Mama Lami da Innan su sallama ta wuce gidan baabaa Mero dan ta jira Hamma magaji acan

Bayan ya karya shima wanka yayi ya shirya dama already sunyi magana da Baffai tun da asuba.

Ɗakin Inna ya nufa “Assalamualaikum” ya furta ya tsaya neman izinin shiga ɗakin. 

“Wa’alaikassalam Magaji burtu on”. 

Innan mu jamɓanduna.

Jam Magaji, noi fewel?

Alhamdulillahi Inna.

Noi shungullajo?

Alhamdulillahi Inna, noi kugal?

Kugal ɗon Magaji sai miyetti Allah….

Magaji yace “Inna ba muje cikin Ashaka sai mun dawo”. “To a dawo lafiya Magaji am Allah ya tsare hanya Allah kaiku lafiya ku kula sosai ko” cewar Inna cikin kulawa. 

Da “Ameen” ya amsa ya fice a ɗakin, ya wuce ɗakin mama lami ya gaishe ta ya fice yayo gidan Baabaa Mero. 

Da sallama ya shiga gidan ya tarar da su a tsakar gida, gaisawa suka yi da Baabaa Mero sannan tace masa “to wallahi Magaji na baka amanan takwarata bana hana ku kaita makaranta inkun so har bangon duniya amma dai karka manta da maganata kaji da kyau, duk da ma dai tafi qarfin irinka”. 

Haɗa fiska yayi yace “Ke fito mu tafi”. 

Baabaa hararan sa tayi tace “kai Magaji zanci buhun ubanka banson jaraban tijara da subahin Ubangiji in ban da tambaɗewa da cin fuska duk kaima bansan yaushe ka koyo baqin hali ba aradu banson cin fuska dan kaji sunanta Meramu ba ke ba ka ji ni ai, fistara kawai sunan Uwar ubanka Musa sai kace ke”.

Ko kallon Baabaa bai yi ba yace da Innai “ina jiranki a waje kika jima kuma ki tafi ke ɗaya” yana faɗan haka ya fice a gidan. 

Baabaa Mero tace “takwara ki kula sosai ko Allah maki albarka ya tsare ku duka”. 

Innai ta ce “Ameen Baabaa ta byeee sai mun dawo”. 

“Oh ni Mero kema yaren ƴan wutan kike son koya na shiga ɗaki na kasa fita to Allah ya staremu da wuta mukam ai masoyan Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam ne ba mu ba wuta da yardan Allah” cewar baabaa tana shigewa ɗakin ta. 

Fita tayi ta samu Hamman su na jiranta, sai lokacin ta gaishe sa ya amsa yana faɗin “mu tafi ko”. 

Sanye take da kayansu na fulani riga da zani fari tass ta sanya milk color hijab iya guiwanta Masha Allah tayi matuqar yin kyau.

Shi kuma Magaji sanye yake da jamfa milk color da hulansa, sun sha kyau ba kaɗan ba kaman ba ya da qanwa ba.

Mashin suka hau ko wanne da nasa ya kaisu bakin hanya dan samun motar da zai kai su cikin Ashaka. 

Baffai ne zaune a fadan rugan da yaje shi da Arɗon wannan rugan suna magana.

Kaman an jefo mutum daga sama haka wani ɗan matashin yaro ya shigo fadan a guje ya zube gaban Arɗo kaman zai faɗi yana haqi yace “Arɗo! Arɗo! Arɗo! aradun Allah mutumin shan ya falka”. 

A tare Baffai da Arɗon suka miqe da sauran jama’an dake fadan.

Arɗo yace “ke belloji mene kike shewa haka?”

Yaron yace “Arɗo aradun Allah kuwa wanshan mutumin ta falka”. 

Da Arɗon da Baffai hanyan da wannan matashin ya fito suka bi da ɗan sauri-sauri, Da sallama suka shiga ɗan madedecin gidan Wanda yake mamallakin Arɗon.

Wani ɗan bukka suka shiga suka tarar da wata dattijuwan mata ana rirriqe ta tana fisgewa. 

Ganin haka sai Baffai yace “su sake ta”

Addu’a yake karantawa yana tofa mata can sai ta daina fisge-fisgen ta yi baya luuuu zata faɗi aka rirriqe ta aka kwantar da ita.

Arɗo dake gefe sai hamdala yake yana cewa “Aradu Malam mun gode maki yau kwana 3 gaci wannan mutumi ta falka mu mun ɗauka ma ya mutu ashe kaɗo kam da ran shi”.

Murmusawa Baffai yayi yace “Arɗo mu dai godewa Allah, Allah kuma ya qara mata lafiya, Allah yasa in ta farka yanzu ta faɗama na daga inda take” da Ameen aka amsa duka mutanen dake cikin bukkan.

Ruwan rubutu Baffai ya bawa matan Arɗo akan a qara shafa mata sannan a bata tasha.

A wannan ruga Baffai suka wuni jikin matan Alhmdlh. 

Sun je Ashaka sunyi komi sun gama zata fara zuwa school Monday mai zuwa,

Suka kamo hanyan komawa gida.

Mota ya kawo su har inda suke sauqa sannan su samu mashine su hau su qarisa gida.

Direct gidan baabaa Mero tace a ajiyeta, haka kuwa aka yi.

Da sallama ta shiga gidan tana kwalawa baabaa Mero qira.

“Baabaata maganin kukana ina kike na dawo”.

Baabaa Mero dake kwance a gadonta na qarfe ta ɗaga kai ta kalleta tace “ke dai Allah shirya ki, mutum sai qira kaman makahon da bashi da sanda Allah ya taro mun ke takwara”.

Zaunawa tayi a kan gadon ta na ɗakin baabaa Mero tana faɗin “washh baabaata na gaji wallahi kaman anmun duka, nifa gaskiya zan fasa karatun nan”.

Baabaa Mero ko kula ta taqi yi sai cewa tayi “sannunku da dawowa ƴan bokoko a wuta”.

Madara me ɗumi baabaa Mero ta bata, ta amsa ta sha ta ɗauro alwala tayi sallah sannan taje ta watsa ruwa ta kwanta sai bacci. 

Hassu sun dawo makaranta da yamma, ganin Addan ta bata nan sai ta kama ayyukan gidan duka cikin qanqanin lokaci ta kammala. 

Bayan kwana uku baiwar Allahn nan da Baffai ke wa magani taji sauqi ta warware sosai dan ta iya tuno sunanta da kuma tana da aure sannan tana da yara amma kuma ta kasa tuna garin da take. Ganin ta tuno waɗan nan abubuwa sai su Baffai suka yi hamdala, ya kuma bayar da wasu maganin da ruwan rubutu a ci-gaba da mata aiki dasu Insha Allahu nan da ƴan kwanki komai zai koma dede.

A kwana a tashi ba wuya a wajan Allah, yau take monday ranar da Innai zata fara zuwa School a cikin Ashaka.

<< Jahilci Ko Al’ada 4Jahilci Ko Al’ada 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×