Da asussuba Baabaa Mero ta tashi Innai tana mita “Ke takwara tashi ki shirya da wuri kamun Magaji yace nice ban tashe ki ba kin sansa da fiska kaman na uwarsa Habiba, Ni Mero wannan jarabar karatun yaren ƴan wutan da kuka ɗaurawa kanku kam ai kunga ta kanku da tambaɗar stiya babu ku babu hutu ba qanin ubanku da yaja muku da kuɗin ku kuka nemawa kanku tangaɗi a hanya” Baabaa Mero ta faɗa tana shumfiɗa darduman ta.
Taso wa Innai tayi da salati ɗauke a bakinta da kuma addu’an tashuwa bacci, fita tayi a ɗakin ta samu buta cike da ruwa Baabaa Mero ta aje mata.
Ɗauka tayi ta zaga bayi ta fito tai alwala ta koma cikin ɗakin nanma ta samu darduma a shumfiɗe sai ta tada sallah ta idar ta ɗau carɓi tayi lazumin ta da azkar nata sannan ta miqe ta gyara ɗakin.
Ta fita ta share tsakar gidan tana qoqarin haɗa kwanukan da suka ci abinci jiya ta wanke sai Baabaa Mero ta fito ɗaki tana cewa “ke takwara wai me kike shukawa ne tun……..”
Maganan bakin Baabaa Mero ne ya maqale ganin abinda Innai ke yi sai ta zuba salati ta ɗaura hannu a kai tace “Aradun Allah takwara in baki tashi ba zan zaune ki kinji na ranste har Aradu, yanzu dan tsabar neman fitina da bala’i ana zaune lafiya zaki nema min jarabar tamɓadan Magaji ni Mero na shiga ɗaka na kasa fitowa”.
Miqewa Innai tayi tana tura baki ta ɗau bokati tana ɗiban ruwan wanka, Baabaa Mero kaman zata kifu a qasa haka ta nufo ta tana cewa “dan ubanki Isa ina magana kina abu kaman wata hawainiya ko wacce ƙwai ya fashewa a cikin hanjayenta ko, to zaki zaunu kuwa”.
Innai ganin da gaske Baabaa Mero ta tunkaro ta da gudu ta ɗau bokatin tayi banɗaki, Baabaa Mero ta tsaya tana qwafa “Hmmn! Da kin tsaya na nuna miki iya qarfi na ai ja’irar yarinyar mai nemawa mutane jaraba kuma saura karki fito a bayin nan da wuri ki zauna kaman wacce aka aiki bawa garinsu ko aka bawa mace filo da tabarma tana naquda”.
Baabaa ta lelashe kwanuka ta ɗuma mata madara, cikin mintuna kaɗan ta gama wankan ta fito sumui-sumui ta wuce ɗakin ganin hararan da Baabaa Mero ke binta da shi don tasan halin stohuwar yanzu sai ta zaune ta ba ruwanta da maganan jika ko kaka.
Ko minti biyar bata yi ba ta shirya staff cikin uniform nata da yayi matuqar amsan ta kai kace dan ita aka fitar da colorn uniform ɗin, fitowa tayi stakar gidan Baabaa Mero ta ɗago kai ta kalle ta sai lokacin ta sake fuska tayi murmushi tace “takawarar arziqi kar kice zaki tafi ba ki karya ba, dan haka tsaya kisha madaran da na ɗuma miki ga wannan naira ɗari ne ki sayi abu a makaranta ko”.
Miqa hannu Innai tayi ta karɓa ta sanya a aljihun ta kamun tace “baabaata zan sha amma ba naje na gaishe da su Baffai kamun sai nazo na karya na tafi kar na ɓata lokaci na haɗu da Hamma ya buge ni”.
Baabaa Mero tace “shikkenan ki dawo lafiya kuma kiyi sauri tunda dai kuma kinsan baqin halin jarababben Hamman naku, saura kuma ki tsaya ɓata lokaci dan ita uwar taki ba ta amsa gaisuwanki ba kinji ai”.
Innai na murmushin ta ce “Baabaa ta yanzun nan zan dawo” ta faɗa tana fita a gidan baabaa Mero ta nufi gidansu.
Da sallama ta shiga gidan, Hassu ta samu a madafin nasu sai tace mata “sannu da aiki surbajo am kiyi haquri na barki da aiki” tana gama magana ta wuce ɗakin Innar su sallama tayi, Baffai ya amsa mata yace “shigo uwata”.
Shiga ɗakin tayi kanta a qasa tana murmushi ta stugunna tace “Baffai jam ɓandu na”
“Jam dada Baffai mako noi sare? noi baabaa am?
“Jam Baffai am noi shungullajo noi fewel?
“Fewal alhamdulillahi shungullajo ɗon miyetti Allah daadaa Baffai mako” murmushi ta yiwa Baffai bayan sun gama gaisawa cikin fillanci yana ce mata har an shirya kenan.
Ta juya wajan Innar su dake gyaran gado tace “jam ɓandu na Inna”.
“Jam” a taqaice Inna tace haka bata kuma cewa komai ba kuma bata ko kalli inda Innai take ba taci gaba da aikinta.
Baffai ya kalle ta ya girgiza kai dan baima san menene zaice ba tunda dai ko kunyar idon sa bata ji.
Innai tace “Baffai yau ne dama zan fara zuwa makaranta”
Baffai da murmushi yace “to-to yaune shiyasa naga uwata ta shirya tayi kyau sosai to ki maida hankali sosai kinji, a dage sosai Allah miki albarka ya albarkaci karatun ku yasa al’umman Annabi SAW mu amfana da shi”.
“Ameen Baffai na” ta faɗa tana murmushi.
“Inna na tafi sai na dawo” ko juyowa Innar tasu ba tayi ba balle ta mata wata addu’ar.
Haka ta tashi ta fice, bayan Baffai yace taje wajan Hammansu kamun ta tafi.
Tana fita a ɗakin ta shiga ɗakin mama lami da sallama, amsawa mama lami tayi fuskanta a sake tace “ƴar ɗaki na sai yanzu aka shigo?
Gaishe da ita tayi tana murmushi haka itama ta amsa, sannan tace “Mama lami na yau zan fara zuwa makarantan da aka nema mun a Ashaka”.
“To yau ne dama, amma dai za kike dawo wa ko? mama Lami ta tambaye ta sai tace mata “eh mama lami zan ke dawowa Insha Allah amun addu’a”.
“To Allah bada sa’a ya albarkaci karatu tashi kije kar kiyi latti ko, ta ɗau murtala ta miqa mata gashi ki sayi abu”.
Murmushi tayi ta amsa tace “Nagode Mama Lami sai na dawo”.
fita tayi a ɗakin ta wuce ɗakin Hamma Magaji.
Tsayawa tayi a bakin qofan tayi sallama, amsawa yayi yace “wacece?” sai tace “nice Hamma”.
ya qara cewa “ke wa?
turo baki tayi kaman yana ganinta tace “Innai ce fa Hamma”.
yana daga ciki ya murmusa yace “ok come in”.
Shiga tayi ɗakin ta same shi daga shi sai vest da threequater, ganin sa haka sai ta sunkuyar da kanta qasa ta gaishe sa ya amsa yana cewa “sai yanzu kika shirya kenan kin tsaya biyewa stohuwar nan ko, to gwanda ita taci zamanin ta karki dage kanki za kiwa ita ba ruwanta, yanzu ba’a auran matan da basu yi karatu ba ko basu waye ba gwanda ki dage in kinason samun miji kaman yacce kullum take faɗa”.
Kanta a qasa, ba tace komi ba sai wasa take da bakin hijab nata dan maganan sa ya bata kunya ita ina ma take ta aure.
Miqewa yayi yace “kin sani a gaba ba zaki fita na sa kaya ba ko so kike ki kalli jikina ne kam? Maza Je waje ki jirani gani nan zuwa muje ki hau abin hawa ya kaiki na riga nawa Rabe (rabiu) magana zai ke kaiki yake dawo dake har makarantan”.
Tana tura baki ta rufe fuska tace “to Hamma Nagode Allah saka” bai qara cewa komi ba ta tashi ta tafita.
Hassu ta samu ta fito wanka itama ta shirya zuwa makaranta, ganin Addan nata sai tace “Adda a dawo lafiya Allah bada sa’a ko, muma muna zuwa soon” murmushi Innai tayi tace “to Ameen ya Allah kuma Allah taimaka hassu a dage ayi karatu ayi exams lafiya”.
“Ameen Adda”.
Wucewa waje tayi tana fita sai ga Magaji tace “Hamma zamu bi gidan Baabaa ko?
Wani kallon da ya mata shi ya sanya ta zuge bakinta bata qara cewa komi ba, Allah yaso already kominta na tare da ita madaran ne kawai kuma tasan akwai buga match da Baabaa Mero in ta dawo.
Sunje sun sami Rabe dama yana niyan zuwa ɗaukanta har gida ganin shiru bata zo ba har lokacin sai kuma gata, gaisawa ya yi da Magaji yana cewa “Magaji dama yanzu nake niyan zuwa na jiku shiru”, “Ba komi kai kam inba matsala in shida da rabi tayi 6:30 ka dinga zuwa har gida” faɗin Magaji fiska a sake, sai Rabe yace “to Magaji”.
“Innai hau mu tafi” cewan Rabe yana qoqarin ta da mashine, hawa tayi kanta a qasa.
Kallon ta yayi yace “ke kuma ki kula sosai kar naji kar na gani in ba haka ba kinsan sauran, sannan ya ciro kuɗi ɗari biyu ya miqa mata yace a dawo lafiya” Rabe yaja mashine suka kama hanyan Ashaka, Feeeeee haka suke tafiya gudu yake sosai ganin lokaci yaja gudun kar tayi latti farkon zuwanta.
Magaji ganin sun ɓace wa ganinsa juyawa yayi ya koma, gidan babansa ya wuce.
Da sallama ya shiga gidan dede baban nasa ya fito zai fice dan tafiya kasuwa, ganin Magajin sai yace “A’a yaron Baffan sa ne a gidan mu da sassafen nan?”
Murmushi yayi ya tsugunna har qasa yace “baba antashi lafiya? Gaisawa suka yi sai ga Mama ta fito suka gaisa itama.
Baba yace “Magaji kai de kam ina ga yanzu ma wataqila baka jin yaren ka daga hausa sai yaren yahudawan nan to Allah shiryaku ya maku albarka kawai”.
Shatu da hali suka fito a ɗaki da shirin makaran ta, ganin Hamman su duk sai suka stugunna har qasa suka gaishe sa, amma sai yayi fiska a haɗe yace “me kuke yi a gida har yanzu baku tafi makaran ta ba? Zan fa ɓalla ku akan maganan karatu” da sauri suka wa Mama da baba sallama suka fice a gidan, suna fitowa suka haɗu da Hassu nan suka kama hanya sai makaranta.
Baba yayi murmushi yace “ai gwanda ka dinga tsawatar musu yaran nan ko kaɗan basa ji sai a hankali” sallama baba yawa mama suka fice tare da Magaji yana rakasa suna tattauna wa.
Baba yace “Magaji kai kuma ya ake ciki ne ka ji fa maganan Baabaa ko?
Sosa qeya yayi yace “baba a ɗaga mun qafa a ɗan qyale stohuwan nan tukun nikam ma na kusa komawa zamfara maganan karatun kuma in dai naje zan iya kai shekara huɗu 4, kaga in na dawo sai nayi auren”.
Murmushi baba yayi yace “Magaji shekara huɗu 4 akan shekarunka shekara 30 kenan fa, so kake ka stofe ka rasa matar aure ko ta maganan Baabaa?”
Magaji kansa a qasa yana murmushi yace “Baba a dai sa mana albarka Allah tabbatar ma na da alkhaeri nan da lokacin”, “To Ameen ya Rabbi Magaji” faɗin baba.
Raka baba yayi har wajan da motor ke ɗaukansu da dabbobinsu zuwa cin kasuwa sanda suka tafi ya juyo ya koma gida dan shiryawa shima yau yana son shiga cikin Gombe.
Best Way International School Ashaka.
Rabe ya kawota sun iso lafiya ya ajiyeta ya juya akan sai yazo ɗaukan ta in an tashi.
“Bismillahirrah manirraheem
يا رب انى اسعلك كل ما خير فى هذل بلد و هذل مدرسة، و اعوذ بك من كل ما فيه شر،بجح رسو لله صلى الله عليه و سلم
يارب ارزقن بل علم نفع….”
Addu’oee tayi sosai kamun nan tayi stepping qafanta a cikin makarantar.
Makaranta ce babba sosai ɗalibai ne ko ta ina kowa ka gani sauri yake da alama assembly za’a fara.
Ba tare da ta ankara ba tayi karo da mutum, Littatafan dake hannun wannan yarinya suka zube.
Haquri ta shiga bata suka stugunna tare suna kwashewa, yarinya ce ƴar kimanin shekara sha uku 14 dan bata wuce sa’ar Innai ba.
Tattarewa suka yi tare yarinyar na murmushi tace “ba komi sister muje assembly ko, wani aji kike?
“SS 1” Innai ta faɗa tana gyara zaman jakan bayanta.
wannan yarinyan tace “Ok ajinmu ɗaya muje layi ko”.
Layin ƴan SS 1 suka je suka tsaya, aka yi conducting assembly for almost 30 minutes before aka sallami students kowa yayi aji.
Da yake yarinyar ɗazu na tsaye bayanta ce mata tayi “muje class our new commer” murmushi Innai tayi suka wuce aji.
Da Bismillah ta shiga, jan ta yarinyar tayi suka zauna a kujera na 3 a layin mata.
Kallonta tayi tace “ke new commer ce ko kaman yacce nace dan ban taɓa kallonki a ajinnan ba? Ta faɗa ta stigar tambaya.
Murmushi Innai ta kuma yi tace “eh yau na fara zuwa”.
yarinyar ta juya za tayi magana sai ga Malami ya shigo, tashi suka yi duka ajin “gud morning Uncle”.
suka haɗa baki wajen cewa.
“Morning”.
ya amsa musu a taqaice ya musu alama da su zauna.
Black board aka goge ya rubuta subject ɗin da ENGLISH LANGUAGE topic
PART OF SPEECH
Juyowa yayi kamun yayi komi yace “class can someone help us tell what he knows about part of speech ,or can someone just explain?
Wani yaro ne ya ɗaga hannu, alamin yayi pointing nasa yana cewa “ehem am getting you”.
Naa naaa nounn is a name of things, objects or…. Tsayawa yayi ya gagara qarisawa yana in-ina, Malamin ya kalle sa yace “can you please sit down, any other person class?
Kowa yayi shiru ganin malamin na da zafi kar wani ya tashi yace ba haka ba.
Hankalinta gaba ɗaya na kan Black board kaman mai tunanin wani abu daban, yarinyar ɗazu ce ta taɓa ta tace “sister malamin nan fa na kallonki”
Sauqar da kan ta qasa tayi jikinta na rawa tace “Hande kam mi boni, nifa ina copyn rubutun da yayi ne”.
“Heeyyyy youu!!!” suka ji ya musu tsawa, a take jikinta ya fara rawa kaman wacce aka wa duka idonta ya tara hawaye.
Malamin yana nuni da su yace “am asking question and you guys are busy making noise right? Oya be on ur fit”.
Yarinyar ta tashi ta kama hannun Innai suka tsaya tare, malamin yace “you should tell class what u’re discussing about or else..”
Haquri yarinyar ta bada amma da qyar malamin yace “ok you get ur sit” yana nuni da yarinyar, sai ya juya kan Innai yace “so you can’t apologize right?
“Sir she’s a new commer” cewar yarinyar.
Tsawa ya daka mata “can you please shut up ur mouth my friend, am talking u’re talking idiot”.
Innai da kaɗan take jira ta fashe da kuka jikin ta har yanzu rawa yake kaman ace firit ta kwasa a guje haka take ji sai kulle idon ta kawai tayi, ƴan aji na kallonta saura na dariya qasa-qasa saura na jin tausayin ta.
Kallonta yayi yaja qaramin tsaki yace “have ur sit” da sauri yarinyar taja hanunta ta zaunar da ita tana hamdala, ita kuwa Innai tana zama sai hawaye da qyar ta seta kanta har ya kammala karantarwan sa ya fita bata gane komai ba. malamin Islamic ya shigo musu
Sosai take gane lectures en ,hankalinta duka na kan malamin har ya basu Home work
Akan su lissafo masa adadin annabawan da aka lissafa a Alqur’ani
Yana fita aka fice musu break.
Yarinyar ɗazu ne har yanzun suke tare, kallonta tayi tace “sister ba ki faɗamun sunanki ba”
Murmushi Innai tayi tace “sunana MARYAM ISAH MUHAMMAD”. Yarinyar tace “Wow! suna mai daɗi sosai nake son sunan Maryam dan sunan mommy na kenan” murmushi kawai Innai ta mata.
“Ni kuma sunana FATIMA NURA MUHAMMAD amma ana cemun Afrah” murmushi Innai ta mata tace “kema sunanki me daɗi”.
Ni ƴar cikin garin Gombe ne iyayena ma na can kawai an baiwa kakata ni ce shiyasa muke zaune anan ni takwarar ta ce, Innai tace “la nima takwarar kaka ta ce ai kuma nima nafi zama a gidan kakata”.
Afra tace “ke me ake ce miki a gida?”
“Innai haka ake qira na” ta bata amsa tana murmushi.
“To nidai ba zance Innai ba zan dinga ce miki Habibty tunda sunan mommy gare ki” Murmushin Innai ta kuma yi kawai, sai Afrah tace “habibty ke kam ba dai murmushi ba kam ai sai ki qarar da murmushin naki ki rasa nawa angonmu”.
Dariya Innai tayi tace “Wow! So dama murmushi na qarewa bansani ba?”
Afrah tace “za kiji da shi ni dai yanzu kinga tashi muje wajan break mu sayi abu inason cin awara yau naqi karyawa, muyi sauri kuma an kusa komawa aji”
Murmushi kawai ta mata suka fice a ajin suka yi wajan break ɗin.
Bayan fitan Innai a ɗakin baffai ya dubi Inna yace “A’ishatu zo ki zauna”.
Inna zuwa tayi ta zauna gefen baffai tana murmushi tace Baffan Magaji ganinan”.
Kallon ta Baffai yayi yace inason zan miki magana a matsayina na mijinki kuma uban yaranki indai kin ɗauke ni da muhimmanci kinajin maganata kuma kina ganin mutunci na to inaso na sani”.
“Ina jinka malam” Inna ta faɗa.
“Aisha kinsan ma’anan haihuwa kuwa?
Kinsan bakin uwa kuwa akan ɗanta?
Ko dai wani abun da kike yi ta maganan Baabaa mero ne don na sawa Innai sunan ta shiyasa kike haka?
Ashe mahaifiyata ba mahaifiyar ki bace?
Ko ban sawa Hassu sunan Gwaggo ba? Ki dubi girman Allah kiwa kanki faɗa ko sau ɗaya ne dan ina guje miki aikin ɗan da na sani, makaranta fa yarinyar nan zata tafi amma bakisan tana buqatan addu’an ki da sa albarkanki ba?
Wai duk me yasa kuma akan me kike hakan?
A’ishatu ina guje miki ranan da na sanin abubuwan da kike aikatawa wannan baiwar Allah ranar da wannan nadama bazai haifar miki ɗa mai ido ba, dan wannan ba AL’ADAH bane JAHILCI ne A’ishatu, al’adu da yawa a yanzun an daina su kaman su SHAƊI, AURE DA QANANUN SHEKARU, GUDUN KARATUN ZAMANI, RASHIN AUREN BARE IN BA YARENKA BA KUMA BA ƊAN UWANKA BA, DA KUMA TAKI AL’ADAN TA KUNYAR ƊAN FARI da dai sauran AL’ADUNMU da yawa amma ke me matsalanki A’ishatu?
Kanta a qasa tace “kayi haquri malam dan ko ɗaya ba haka nake nufi ba, Baabaa mero a wajena mahaifiyata ce ko da kuwa ba aure tsakanina da kai balle har da jikoki, kuma ai na mata addu’an Allah ya ba da sa’a”.
“Hmmn! yana da kyau, ni dai ina guje miki ranan nadaman da ba abunda zai haifar miki sai ɗa mara ido don in lokaci ya qure miki alhaqin abinda kikewa yarinyar nan kaɗai ya isheki ba sai da wani abun ba” cewar baffai yana ficewa a ɗakin dan baison qara sauraran ko me zata ce.
Inna bin bayan sa tayi da kallo sai tayi qasa da kanta dan gaba ɗaya ita ma abun na damun ta na rashin wanda zai fahimce ta da kyau.
Ɗakin mama Lami Baffai ya shiga suka gaisa, sai ta kallesa tace “malam ashe uwar masu gida anfara zuwa makaranta?”
“Eh wallahi se dai mu ta musu addu’a kawai” cewar baffai.
Mama Lami tace “to Allah ya basu sa’a yasa a gama lafiya a kuma ci riban karatun”
Da “Ameen” ya amsa ya sallame ta zai fita, tare suka fito tana faɗin “a dawo lafiya”.
ko ɗakin Inna bai koma ba ya fice dan dama ya gama shirin fitan sa.
Sun gama class na yau duka qarfe uku 3:00 aka tashe su, tare suka fito da Afrah ta samu Rabe yazo ɗaukanta. Sallama suka yi da Afrah ta hau mashine ɗin tana ɗaga mata hannu suka kama hanyan gida, Afrah ma drivern ta yazo ya ɗauke ta.