Skip to content
Part 7 of 22 in the Series Jahilci Ko Al'ada by Harira Salihu Isah

Tana shiga gidan baabaa tun daga bakin qofa ta cire hijab tana kwalawa tsohuwar qira “Baaabaaallle taaaaaa!!.

Baabaa Mero dake stugunne tana gyara akurkin kajin ta juyowa tayi tana faɗin “yau ni Mero naga cikakken carɓin jaraba da stiya, ke dai takwara makaho ma ya ganki ya sara miki a iya qwalawa mutum qira kaman yaci bashin ki da hanci kaman stinken balangun kwaɗi”.

Tura baki tayi tace “Baabaata ko kice mun sannu da dawowa mana kin hau ni da surutu, to ni nayi fushi ma gidanmu zan tafi” ta faɗa tana juyawa cikin burga.

Baabaa Mero qaramin stoki taja ta sunkuya ta ci-gaba da abinda take yi ko ta kanta bata bi ba. Innai ganin haka tana tura baki ta juyo ta shige ɗakin ta cire uniform nata ta sanya na gida ta ɗau kwanon abincin da ta gani da madaran shanu a gefe ta hau ci.

“Ke dan rawanin mai anguwan garinku banson kwarzaɓa, ni na baki abincin ne ko uwaki mara zuciya Indo? Daga ganin abinci kika hau ci kaman wata almajirar garin munafukai, yo Allah na tuba dama uban wa ya baki wannan mugun shawara ta ki tafi boko ba tare da kinci komai ba sai kace mai zuwa neman aljanna ko kuwa ance Annabi ake gani acan, ni Allah na tuba inba Annabi zanje gani ba bance akwai abinda zai sa na stallake ɗumammen madara mai amfani da qara lafiya jikin mutum na ɗibi jiki suɓutun-suɓutun kamar shanuwar huɗa wai na tafi wata wajan jarabar ba, inbanda gayyan jaraba ba komai a boko mutane su ta fama da biro da farar fefa kaman masu aikin Allah” cewar baabaa Mero da ta shigo ɗakin yanzu.

Sai da ta gama ci ta ɗau madaran da sanyin sa kaman ansa a firiji(fridge) ta kwankwaɗa tayi hamdala sannan ta kalli baabaa tace “nifa ba da son raina na tafi ba Hamma na ne ya sani a gaba wai mu tafi lokaci na qurewa kuma a hakanma na kusa yin letti”, harara Baabaa ta aika mata tace “shi Magajin ai shine hanjayen cikinki dole ya sa ki gaba ke kuma ki bisa jagwab-jagwab kamar tinkiyar sa za’a kai kasuwa, to Insha Allah zai zo har gidan nan ya sameni zanci mutuncin sa ba qidaye ɗan bani na iya da wuyansa kaman lagwanin risho, ke kuma tunda ya zamo mala’ikin mutuwa gare ki dole ki biye masa ki tafi haka, in nice tun yaushe na bostare nace ban karya ba amma ke shegen storon kin nan kar ki daina sai an rainaki ai sha-sha-sha kawai”.

Innai tashuwa tayi tace “nikam ba nayi sallah na tafi islamiyya gwanda ke kinyi naki”.

tashuwa tayi tayo alwala tayi sallah sannan ta wuce makaranta, Baabaa Mero sai sababi take “ja’irar yarinyar wataran tayi abu uwa babbar mata uwar gardaye”.

Baabaa ta haɗa uniform na Innai ta wanke mata, yana bushewa ta naɗo mata ta ajiye tana faɗin “na miki mai wuyan ƴar gwafan uba kyazo ki goge abunki.

Yau watanta curr tana zuwa makaranta inda cikin watan wani shaqiqin shaquwa ya shiga tsakanin ta da Afrah duk inda kaga qafan Innai a cikin makarantar to za kaga na Afrah, a wata gudan nan duk ajin ba wanda baisan qawancen su ba. Malamin English nasu kuwa wanda Afrah da sauran ƴan aji suka sawa suna “Malam ba-wasa” sam basa jituwa da Innai wanda karan-zuqan da ya sawa Innai itama Afrah ta sa mishi, sai dai duk yin su basu rena shi ba dan bai bawa ko wacce ɗaliba fiskan hakan ba.

Kaman kullum yau ma an tashe su breakfast kowa da ke cikin ajin ya fita sai ɗai-ɗai ku sai kuma Afrah da Innai da suke zaune suna hira Afrah na copyn note.

Innai tace “ni banga amfanin note da kike ta aikin yi ɗin nan ba, mu da zamu dage da karatu tunda za’a fara test ina muke ta copyn note”, Afrah barin rubutun da take yi tayi tace “habibty ke ba zaki gane ba fa, bakisan note ma da kansa C.A bane kuma kinsan na Malam ba-wasa ne dama yaqi jininmu rashin note sai ya sanya shi mana repeat tunda dai kinga yanzu shine sabon formmastern mu” faɗin Afrah tana ci-gaba da rubutun ta.

“Uhmn ni dai ba wani note da zanyi in yaga dama ya maidani Nursery” faɗin Innai tana ɗan tura baki.

Afrah abun ma sai ya bata dariya “habibty kin ganki kuwa kaman baby-doll dama aka ce su Maryam sun iya shagwaɓa to naga ɗaya yau, amma maganan note ko baza kiyi ba ni zan miki dan banson sa mana ido da yake ɗin nan especially ke..” qaran bell da suka ji wanda ke nuni da break-time ya qare shi ya sanya su gyara zaman su Afrah ta rufe littafin gabanta tana cewa “Alhamdulillahi saura naki in na koma gida na miki”.

Malamin P.H.E ne ya shigo musu (physical and health education) ya koyar na tsawon mintuna arba’in ya gama ya fita, malamin Arabic 1 ya shigo shima yaci lokacin sa ya fita.

Classes aka dinga musu har qarfe biyu ya buga kamun aka tashe su dan yin Sallahn azahar.

Tafiya suke ita da Afrah dan zuwa masallaci suyi sallah. “me kike sauri haka kaman zamu tashi sama?” Afrah girgiza kai tayi tace “kefa habibty zan miki na yarenku wai a ɗonmari problem(kina da damuwa) kinsan muka koma lokacin Qur’an ne kuma kinsan Ustaz na uzuri amma banda na latti gwanda ke nasan kin iya haddan da ya bayar ni ko ban iya ba dole nayi sauri”.

Suka qarisa masallacin suka yi alwala suka gabatar da sallahnsu sannan Innai ta ji wa Afrah haddan ta har sanda uku saura yayi kamun suka tashi suka koma aji.

Suna shiga ustaz ya shigo, Afrah lumshe ido tayi tana hamdala a zuciyarta, nan aka fara karɓan hadda. Duka layin benci biyu dake gabansu mutum kusan takwas kwata-kwata mutum uku ne suka ba da haddan dai-dai duk wanda ba suyi dai-dai ba Ustaz ya tsayar da su, aka iso kan Innai ta miqe cikin nistuwa ta fara karanto Suratul-Maryam wanda aka basu shafi guda.

Tana kammala karatun cikin yabawa da haddan nata Ustaz yace “attakbir” ƴan aji suka amsa da “Allahu Akbar!” Ustaz yace “jamil-jiddan barakhallahu feeki, ijlis” Innai zama tayi tana hamdala dan bata zaci zata iya kawo haddan dai-dai ba duk da dai tayi nacin karatu har sai da Baabaa ta qwace Qur’anin tace ta kwanta dare tayi.

Afrah miqewa tayi jikinta na ɗan rawa, ganin haka sai Innai ta kama hannunta tana magana qasa-qasa “Qawa fell comfortable okay” ajiyan zuciya Afrah ta sauqe nan ta fara rera nata karatun cikin nistuwa har ta kammala ko gyara ɗaya ba’a mata ba, itama kabbara Ustaz yasa aka mata sannan ya umurce ta da ta zauna.

“Habibty jazakhilla bikhair ta shiga aljanna Nagode” Afrah ta faɗa qasa-qasa dan kar Ustaz ya jiyo ta.

Duka ajin sanda aka karɓi haddan su sannan waɗanda basu iya ba aka bisu da bulala goma-goma kuma ustaz yace ranar Monday su tabbatar sun kawo masa haddansu, ganin rabi da kwatan ajin basu iya ba sai bai musu qari ba kawai aka yi muraja’a ya gama ya fita qarfe 3:20.

Yana fita Afrah ta rungume Innai tace “habibty ba dan ke ba da wallahi yau na tabbata sai nasha bulala kuma anamun bulala nasan sai ciwo dan ni tun ina yarinya ana duka na sai nayi rashin lafiya, Allah saka miki”.

Lokacin tashi nayi suka fito suka tarar masu ɗaukan su duk sun zo nan suka yi sallama kowa aka yi gida da shi.

Arɗo ya kalli matar nan cikin hausansa da bai nuna sosai ba yace “yanzu kai bawan Allah maimunatu ka she ja ka tahi to ya ja kayi ka gane jida ɓandu wala jam ko saɗɗa, ka bari idan ka walke duka hai ka koma gidanka”.

Kanta a qasa tana sauraran sa duk da ba duka abinda yake faɗa take ganewa ba amma tasan akan tafiyanta ne, cikin sanyi da yake yanayin ta tace “Baba na gode sosai but an apologizing because I have children’s and I know they’re in serious need of me two months is not easy” ta faɗa da harcenta da kusan turanci ya cinye sa don kanaji kasan wannan ba cikakkiyar bahaushiya ba.

Matan fara ce sosai kuma kyakkyawa wanda kana ganinta kasan ba ‘yar Nigeria bace domin turancin nata ma pure one ne ba irin broken ko pidgin ko capin na Nigerian ba, ciwon da take ciki da raunukan jikinta bai hana kyawunta fitowa ba duk da kuwa shekarunta sunja dan zata kai arba’in da ɗori.

Arɗo da ba abunda ya fahimta a maganan ta sake baki kawai yayi yana kallon ta har ta gama tayi shiru sai yace “aradun Allah maimunatu ban gane duka abinda ka she ba wannan yare ta mashu janjayen kunnuwa ni muntala(Murtala) ina jan gane kawai ka bari ita malam isa in ta Jo hai ka mata inta iya to in bata iya ba hai ta nemo mai ji”, ba yanda ta iya haka tayi shiru kawai tana addu’a Allah ya kawo wannan bawan Allah lafiya.

Washe-gari Baffai yaje rugan, suka gaisa daɗi-daɗi da hausa duk da wani abun bata ganewa, ta masa maganan komawanta da Hausa da turanci, Baffai haquri ya bata kan shima ba yaji amma in Allah ya yarda in zai zo zai taho da yaronsa mai ji sai suyi magana.

Matan nan tunda taga Baffai taji hankalinta ya kwanta da shi kuma fahimtar da tayi shi yake mata magani sannan ba biyan sa ake ba sai abun ya matuqar burgeta har take tambayar kanta “dama har yanzu akwai masu irin halin nan? Ko da yake yanda nakan ji labarin waɗan nan yaren akan ce wasun su na da mutunci sai dai wasunsu AL’ADAR su ta sai su ya su basu mutunci wa bare” shigowan matar Arɗo ne ya dakatar da ita daga tunanin da take yi, kasko ta kawo mata da garwashi nan ta lulluɓeta tayi hayaqi sannan taje ta kawo mata abincin su wanda zuwa yanzu ta saba da shi barinma madaran shanu wanda yake dama ita masoyiyar sa ne.

Duk magungunan da zata yi aiki dashi matar Arɗo ta haɗa mata sannan ta fita, kaɗan ta stakuri miyan shima sabo da maganinta da ke ciki sai gasashshen naman rago da ta ci kaɗan shima, madaran ne ta sha sosai dan sanda taji kaman cikinta zai fashe kamun ta aje ƙwaryan.

Arɗo yace “malam Isha Allah ya biya ki hi kawai jamu she maki don kuwa kema kin taimaka, haka fa daga fita kiwo kawai hai ga belloji da gudu wai shun ga gawa hai na gama storita gawa kuma ana jaune hai lafiya, to muna juwa muka ga bawan Allahn nan maimunatu jina-jina Allah dai ya kare ahe bai mutu ba da ransa kaɗo kam hai muka qira ki”, “ba komi Arɗo ai yiwa kai ne fatan dai Allah daɗa karewa ya bata lafiya yanzu dai zamu zo da yaron waje na Insha Allah gobe inyaso sai suyi magana ya faɗa mana in ma komawan ne in Allah ya yarda ba zai gagara ba sai mu shirya mata tafiya” cewar baffai.

“Ke dai takwara Allah aiko miki da Manzon shiriya domin kuwa kina buqatan shiriya wai kullum na miki wanki goga kayan naki ya gagareki kindai san gobe ranar da kuke storo har shi mai jan kunnen da ya qirqiro muku jarabar karatun yaren ƴan wutan ko, in ba za kiyi ba shikkenan kiyi zamanki ni dama banso zuwanki makaranta ba naso kawai kiyi aurenki ki haifaman ‘yan yara kyawawa masu kama da ke, to Allah na tuba ai gwanda ma kiyi bokon wani shawaragin ne zai yarda ya aure ki yarinya shekara sha huɗu kike nema kin balaga ba ko alaman nunu (nono) a qirjinki ni bantaɓa ganin budurci irin naki ba ma takwara, ba sakaran da zai aureki ba ki da komai yo yanzu mazan duk sun zama ‘yan iska masu satifiket mu a zamanin mu saima mun kusa haihuwan fari muke fara nunu wata ma sai ta haihu nunun ke fitowa kuma haka muke zauna lafiya da mazajenmu ba ruwansu da iskancinku na yaran zamani, nasan Hansai ma ta kusa fara wa amma ke shiru qirji kaman an daɓe kwalta, Allah na tuba maka da wannan jarabar yarinya mutum yaqi yin nunu bare ace ya fara jini su dole na Samari suqi ki, kin wani rantaɓo tankin kashi (ɗuwawu) kaman babbar mata gaki dau ba jiki ba nunu amma sai tulin ɗuwaiwaya” cewar baabaa tana stefewa Innai kai.

Ita dai ko qala bata cewa Baabaa Mero ba sai ma karatunta da take kaman waqa.

Suna gama stifan ta bata ɗari da hamsin tace “gashi maza kaiwa maman lado ta miki tunda uwarki makistiya baqin ciki take da ke na tabbata watarana ma zata aske miki kai tunda taga kinfi ta gaban goshinta gashi, kema da kika wani yo wannan uban kayan nauyi da zafin bansan ina za ki kai ba, gashi kaman hauka”.

Tura baki Innai tayi tace “ni dai a daina zagarmun uwa ta” ta faɗa tana ficewa a gidan.

Ɗaukan buta baabaa tayi ta bita da shi da gudu zata wurgeta sai ta ga har tasha kwana, cikin gidan ta dawo tana cewa “ja’irar yarinya mai zubin aljanu yaushe kika fita har kin ɓace to zaki dawo ki same ni ko aljanar ce ke ma bai dame ni ba nice nan uwar aljanu Maryam shugabar su in muguntar inma kirkin duk masu suna Maryam na Aljanu halinsu ne to ma wa ya isa ya nuna musu mugunta, ooh ni Mero bakina dawo Allah shiga tsakanin mu da jinnu ai wasa nake muku Aradu” ta faɗa tana waige-waige can kuma taci gaba “har ni za ki nunawa halin ‘yan duniya ɗan wani bushashshen kashi, da ace uwar taki kaman ta kowa ce ai sai ya dame ni yo shawaragiyar uwa sha-tara sha-bakwai wacce bata san zafin haihuwa ba bata san Annabi ya kafu ba, inkin sake kin dawo gidan nan mai rabamu sai Allah jeki wajan tambaɗaɗɗiyar uwar taki jarababbu”.

Taje ta samu ba layi Allah ya taimake ta nan aka mata kiston da aka basu a makaranta na “flower in the garden” anayi tana raki har da hawayen ta, ana gamawa ta wuce gidan su dan tasan tabbas taje gidan baabaa to kashinta ya bushe.

Tana shiga taci sa’a ba kowa a cikin gidan sai ta wuce ɗakin su kai tsaye, samun Hassu tayi tana goge nata uniform ɗin nan ta lallaɓata taje ta ɗauko mata nata a gidan Baabaa zata musu gugan.

Da sallama Hassu ta shiga gidan tana cewa “Baabaarmu wai inji Adda Innai a bani kayan makarantar ta”, “tunda ke ce fitsararriya fitsaratun carɓin rashin ta idonki a fistare yake kin fitsare qafafuwanki har da qwaqwalwanki dole ta aiko ki, to gasu can ba kwaɗa su zanyi ba kuma tazo ta tattare komai nata a gidan nan ta kaiwa uwarta tunda dai halin ɗan wani zata nuna mun,kuma ni baabaar iyayenku ce ba ku ba, yara sai tulin kalen dangi tunda baku sai da taku uwar ba ku riqe ta ni ban haifi ja’irai ba, kukam sai Isa da Indo” cewar baabaa mero da ke kulle kajin ta ganin magrib yayi.

Hassu ɗaukan kayan Innai tayi tawa baabaa sai anjuma tayi tafiyan ta dan tasan tana stoma baki cikin rigimar su ita ce za taji kunya sun saba in da sabo.

*****

“Fatu Allah Ubangiji yasa yau wani ɗan albarkan Malami ya daka mun ke tunda dai bakya ganin lokaci mutum sai shegen son bacci kaman man konti” cewar wata farar stohuwa da har gashin girar ta furfura ne.

Yarinya da ake tashi a baccin ne tayi miqa sannan ta tashi ta zauna idonta a rufe tana addu’an tashuwa bacci, sauqa tayi a kan gadon ta gama tsalle-stallen ta sannan ta tura qofan bayin ta dake cikin ɗakin ta shiga tayi wanka cikin minti biyu ta fito ɗaure da qaton towel.

Wayan ta ne ya ɗau qara tana dubawa taga “Dad” ɗan tura baki tayi dan tasan duk aikin kakarta ce, sanda wayan ya kusa yankewa ta ɗauka a hankali tace “Daddy good morning”

Morning too Afrah, mai kike yi har yanzu baki shirya zuwa makaranta ba? Kinaso na turo miki yayanki ko?

Cikin shagwaɓa tace “daddy Allah sharri take mun yanzu haka na saka uniform karyawa zanyi na tafi kuma yanzu 6:30 ne”

Afrah ungo naki, dan gidanku uwar tawa ke miki sharri maza-maza ki shirya yanzun nan kar qarfe 7 ya sameki a gida hope am communicating?

“Yes Daddy a gaishe da habibty” ta faɗa tana murmushi

Kitt ya kashe wayan.

Taso wa tayi tana ƴar rawanta cikin mintuna biyar ta gama shiri komai da komai yau ma a hannu ta riqe takardun ta, qofan ɗakinta taja ta rufe.

Hango tsohuwar nan tayi a palourn hakimce akan kujera da ƴar rakani kashinta a gefenta (Old Nokia), gaishetaa tayi tace “Hajja na tafi” harara stohuwan ta aika mata da shi tace “Fatu yanzu dan na fadawa ubanki gaskiya shine zaki gaisheni a tsaye kuma kiqi karyawa to baki isa ki fita gidan nan baki karya ba”.

Gudun ɓata lokaci kuma tasan time ya tafi bakin Hajja ya kamata a daka ta sai ta zauna ta karya sama-sama tace “kuma ni a daina cemun fatu in ba za’a ce Afrah ba ace Fatima kar mutum yaga kaman sunansa gare ni ba ruwa na da wata takwara” Afrah ta faɗa ta fice tana dariya dan tasan ta cokalo stuliyan dodo.

Hajja tana zaune tace “duk abinda kika ce kincewa uwarki Mairamu rasai akuyan jauro”.

Masu aikin gidan ne suka tattare inda Afrah ta ɓata suka gyara komi kaman ba’a taɓa ba dan duk sunsan halin Hajja akan tsafta.

Yau kusan tare suka iso makarantar dan drivern Afrah na juyawa Rabe ya iso da Innai, cikin farin ciki Afrah ta rungume Innai tace “habibty jaɓɓama” murmushi Innai tayi tace “kinfara koyan fillanci kenan halan bafulatani zamu bawa ke”.

Wucewa suka yi filin assembly inda aka yi inspection waɗanda ba suyi style na kiston da aka bada ba aka fitar da su, Allah ya taimaki Afrah da Innai sunyi nan Afrah ta dinga hamdala a zuciyarta ta godewa Hajja dan ita ce ta masta mata akan sai tayi kiston.

Sun gabatar da karatun yau inda wa’danda basu bada haddan sati uku da suka wuce ba suka bada kuma Alhmdlh kowa ya iya nan aka musu qari sannan wani sati ran labara za suyi C.A na Qur’an kowa ya tabbatar ya iya.

Ana tashin su suka fito tare har bakin gate amma yau ba wanda mai ɗaukan sa ya iso a cikin su sakamakon antashe su da wuri, Afrah tace “habibty yaushe za kizo gidanmu kiga hajjata? Innai na murmushi tace “nima yaushe za kizo kiga baabaa ta”.

Afrah ta buɗe baki za tayi magana sai ga drivern ta nan, tura baki tayi tace “baba driver zai kaste mana hiranmu dama kullum karatu na hanamu yi dan haka sai anzo ɗaukan ki zan tafi nima”.

Innai kawai murmushi ta mata dan tasan ko tace ta tafi ba yarda za tayi ba tunda ba yau ta fara yin hakan ba inda ba ita Innai aka fara zuwa ɗauka ba Afrah bata yarda ta tafi ta barta.

Suna staye har qarfe huɗu ya cika nan fa Afrah ta dage Innai ta bita gidansu, suna cikin ja’injan sai ga Rabe ya iso nan Innai tayi hamdala tace “case closed gashi ya zo”.

Hararanta Afrah tayi a wasa tace “dama nasan ba zaki je gidanmu ba ai tunda muna yanka mutane dole kice case closed” nan kowa ya hau abun ɗaukan sa aka yi da kowa gida, Afrah dai har suka rabu taqi yiwa Innai dariya, abun ya damu Innai.

<< Jahilci Ko Al’ada 6Jahilci Ko Al’ada 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×