Innai na komawa gida ta wuce gidan baabaarta inda ta tarar da Baabaa tare da Baffai a zaune suna hira.
Tana shiga ta gaida Baabaa sannan ta gaishe da Baffai.
Kallonta Baffai yayi yace “Uwata inkin cire kayan makarantar akwai inda za muje ki raka ni”.
Innai ta buɗe baki zata amsa sai Baabaa Mero ta rigata tace “amma baka storon Allah mai sunan Malam ace dan tsabar tsagwaran rashin tausayi balle ta-ido a gabana ba bayan raina ba kai ma zaka fara nunawa takwara baqin hali irin na uwatta Indo, ace yarinya daga dawowa ba ko hutawa ka hau ta da jarabar stiya, to in kayi wasa ba inda takwara za taje kai ɗin daa ubanwa ya hana ka iya yaren masu jan kunnen, jimun jaraba fa, ai sai ka bari baiwar Allah tayi sallah taci tuwo ta huta, ku kama ku tura yarinya jarababben boko sannan baza’a barta ta hutawa rayuwanta ba dan cikan rashin imani balle tausayi”.
Baffai yace “ayi haquri Baabaa”.
Innai ta miqe ta shiga ciki ta cire uniform nata sannan ta ɗau kwanon abinci da ta gani a rufe da kuma madaran shanu mai ɗumi, ta ci ta sha sannan ta fito ta watsa ruwa tayi alwala tayi sallah.
Fitowa tayi a ɗakin taje gefen baabaa ta zauna tace “baabaalle ta ina Baffai na?”
Harara Baabaa ta aika mata da shi tace “ja’ira, ubanki ya tafi koyan yiwa mutane sannu da gida, kullum na ajiye madara ta sai ki daqarqare ki shanye yo to ke da za kiyi bokoko a wuta ina ruwan ki da madara ai da aure kika ce za kiyi sai na daqarqare nima na dinga ɗirka miki madara dai-dai gwargwado da duk wani abun da nasan zai sa ki kece reni a wajan ƴan iskan mazan yanzu”.
Innai da bata fahimci me baabaa ke nufi ba tace “yanzu dai ina Baffai ba?
“Dan ubale ubanki ya tafi gidansa tashimun a gefe kamun na zaune ki ƴar ƙwal uba” .
Tura baki Innai tayi ta miqe ta sanya hijab ta fice a gidan.
Tana qoqarin shiga gidan Baffai ya fito, ganinsa sai ta masta gefe ta durqusa tace “Baffai dama zanzo qiran naka ne”.
Murmushi Baffai yayi yace “to uwata tashi mu tafi kar dare ya mana a hanya ko.
Taso wa tayi suka kama hanyam rugan su Arɗo, suna tafiya suna hira har suka isa.
Cikin gidan ta shige shi kuma Baffai ya tsaya wajan su Arɗo suka yi sallar Magrib sannan suka shigo gidan tare.
Innai tayi sallah tana zaune a gefe su Baffai suka shigo nan ya umurce ta da ta biyo su, suka shiga ɗakin suka tarar matar ta idar da sallah.
Innai tsayawa tayi kallon matar duk da duhu ya fara amma hasken ɗakin yana haska su, matar fara ce kyakkyawa in ka ganta ba zaka ce babbar mata bace, kama take da larabawa.
Gaisawa da matar Arɗo da Baffai suka yi sannan Innai ma tace “ina wuni”.
Matar fuskanta da murmushi dan yarinyar ta shiga ranta tace “how are’u doing baby? Innai tace “am doing good”…
Bayan sun gama gaisawa cikin harshen turanci da Innai wacce ba wani sosai-sosai ta iya ba, nan matar ta faɗa mata komai dalla- dalla yacce zata gane dan tawa su Arɗo bayani.
Innai ajiyan zuciya tayi tace “Baffai wai ita a cikin Gombe take amma hastarin ya faru da ita ne tana dawowa daga Jigawa state dan acan suke zaune da yaranta, yanzu tana so zata koma Gombe ne saboda yaranta tasan hankalinsu a tashe yake amma in Allah ya yarda zata zo baza’a jima ba” Matar murmushi take dan tasan Innai ta fahimci zancen ta kuma yarinyar ta qara burgeta.
Arɗo duk da ba sosai yake jin hausa ba amma kasancewar Innai tayi wani maganan da fillanci shima ya fahimta nan dai yace ba komai Allah kaimu.
Bayan sun fito Baffai ya yi sallama da Arɗo suka kamo hanyan komawa gida ga dare yayi ga duhu, tafiya suke suna hira na ɗa da Uba.
Ihu Innai ta sanya “Wayyooo! Allah naaaaa, hande kam mi boni! Baffai qaya ya soke ni, Wayyo zafi!” cewar ta tana yarfe hannu dan azaba.
Da sauri Baffai ya laluɓo touchin da ya kunna yana haska qafan nata, wuff kaman walqiya yaga gimawan bindin abu, cikin sauri Baffai ya haska qafan Innai.
Salati yayi ganin abinda yayi tunanin ne ya faru, maciji ne ya cije ta ba qaya ba, tana yarfe hannu har ta fara kuka dan ciwon da take ji.
Abinda ya rataya a wuyan sa kaman ɗan-kwali ya jawo ya kama qafan nata ya ɗaure mata cinyan ta sannan ya ɗaga ta cikin sauri suka qarisa rugan nasu yana mata sannu.
Innai ba abinda take sai hawaye, suna shiga cikin gida Baffai yace “A’ishatu kawo mun tabarma”.
Inna ta fito da tabarma ta shumfiɗa masa ya ajiye Innai yace “zo ki mata fifita ba naje na qira Baabaa”.
Inna tana tsaye daga gefe har Baffai ya juya zai fice bata mosta ba.
Baffai juyowa yayi ganin ta tsaye bata mosta ba ransa a ɓace yace “A’isha ba dake nake magana ba?”
Inna sunne kai tayi qasa ta juya ta shige ɗakin ta.
Baffai har zai bita ɗaki sai kuma tuna yarinyar sa kar dafi ya haura mata sai ya fice da sauri ya je gidan Baabaa Mero, da sallama ya shiga Baabaa na kallonsa tace “kai mai sunan Malam lafiya na ganka haka ragaja-ragaja kaman an biyo ka? Ina ita takwarar tawa take?”
Baffai yace “Baabaa mun gamu da stautsayi ne ki taimaka mana da gadalin dafin maciji”.
Cikin sauri Baabaa ta miqe daga zaunen da take ta ɗaura hannu a kai tace “kar ka ce mun takwara ta maciji ya ciza?”
Baffai yace “baabaa ita ce”.
Baffai bai ida rufe baki ba Baabaa Mero ta wawuri hijab tayi hanyan waje sai kuma ta juyo ta shige ɗakin ko minti guda bata yi ba ta fito da wani qulli a hannunta tayi waje ko takan Baffai bata bi ba.
Shigowa gidan tayi ba sallama dan ta manta da Sallaman ma, inda ta jiyo nishin Innai tayi ta same ta kan taburman sai zufa take yi numfashi sama-sama kaman zata sume.
Cikin hanzari Baabaa Mero ta riqo qafan da taga an ɗaure ganin babu haske ta ɗaga kai za tayi magana sai taga Baffai a gefenta, qaramin tsaki taja tace “kai Isa ka sanya ni gaba kaman mai neman tubarraqi ba zaka kawo mun haske ba dan tambaɗewa tunda ciwon ba’a jikinka yake ba ko?”
Touchi ya kunna ya haska mata qafan, nan ta murza gadalin ta manna mata a wajan ciwon.
“Miqo mun ruwa a kofi” cewar Baabaa tana duban Baffai, miqewa yayi ya wuce madafin gidan ya ɗu kofi ya ɗiba ruwa ya kawo wa baabaa, jiqa maganin tayi tana tallafo kan Innai sai gani tayi Innai ta sume.
Magaji ne ya shigo gidan da sallama ganin su Baffai sai yayi wajansu “me ya same ta Baffai?” Cewar Magaji ganin Innai a kwance a sume kuma baabaa na sharar qwalla kaman anyi mata mutuwa. Cikin masifa Baabaa tace “Ubanka Musa ne ya same ta dan rashin tausayi ko sannu ba zaka mata ba”.
Kallon Baabaa kawai yake yi tana bam-bami tana sawa Innai ruwan maganin da ta jiqa a baki amma yana zubewa ne kawai baya shiga bakin ta.
Ganin haka sai Magaji ya amshi kofin maganin ya riqe kan Innai ya ɗan buɗe bakinta yana stiyaya mata ruwan maganin.
Ruwan maganin na isa maqoshi ta ta buɗe ido tana haɗiyan ruwa, sai da ta shanye tass sannan ta rufe idonta ta koma tayi luff da kanta a cinyan Magaji.
Baabaa ido ta zaro tana salati tace “na shiga arba’in da uku ni Meramu yau me ya samu takwarata tasha maganin kuma ansa mata gadali sannan ba tayi amai ba sai faman lumshe ido take kamar mai shirin mutuwa, don Allah takwara bar wannan lumshe ido kamar wacce ke mashashshara ki buɗe idonki kiyi amai son ranki kinji”.
Ba ita Baabaa ba har Baffai da Magaji hankalinsu ya tashi ganin taqi yin amai sai ma lumshe ido da tayi tana bacci da ya ɗauke ta yanzu”.
“Wai nikam mai sunan Malam babu mutane a gidannan ne? Ko wata sabon salon baqin halin aka qutto gida shiru kaman ba halittan mutane ga yarinya bagatantan kaman wacce zata mutu amma ace ko ɗan stunstu bai fito dubamu ba kaman wanɗanda muka musu kashi akan gado jarababbu tambaɗaɗɗu marassa imani da tausayi” faɗin Baabaa Mero da ta miqe tayi hanyan ɗakin Inna A’i tana cewa “uwar jaraba mai sharɓa-sharɓan baqin hali kina gani yarinya ba lafiya cizon maciji na faman kashe ta kina zaune a ɗaki da hijab kamar mai takaba, wuce muje kiwa jikata tofin cizon maciji nikam”.
Inna dake zaune akan sallaya da carbi a hannun ta sai qasa kawai tayi da kanta tana jin maganganun Baabaa har ta gama bata mosta ba bata ce uffan ba.
Baabaa tace “Indo wai har halin naki ya balaga ya kai haka? Indo rashin storon Allahn ma ya girmama ya wuce misali? Ina magana kina zaune wato ta mutu? Kai subhanallahi tirr da wannan tambaɗewan rayuwa wai AL’ADA, Indo Sallahn ki ma ba karɓuwa zai yi ba dan alhaqin baiwar Allah dake kanki, ni Meramu wannan JAHILCI KO AL’ADAH za’a qira sa? To koma me yake Aradu nayi Allah wadai da shi, Mutum na da iliminsa amma ya cika carbin burbushin tunaninsa tsaɓ da JAHILCI” Baabaa na gama magana ta fice rai a ɓace.
“Kai Magaji ɗauka mun yarinyar nan mu tafi gida na dan in tana gidan nan tun ranar mutuwanta bai yi ba zasu qarisa kashe ta dukansu gaba suke da Allah da ya qaddara zuwan takwara duniya”.
Magaji miqewa yayi ya ɗauke ta a kafaɗa suka fice tare da Baffai sai gidan Baabaa Mero.
Suna shiga gidan tasa Magaji ya ajeta akan tabarman da dama take zaune a kai kamun Baffai yazo qiranta, mafifici ta shiga ɗaki ta dauko Baffai ya karɓa yana fifita Innai Magaji kuwa kanta na cinyansa.
Baabaa tagumi kawai ta zuba tana ganin ikon Allah dan duk iya sanin ta ko wani irin maciji ne ya ciji mutum muddin ta basa wannan magani ta manna masa gadalin shikkenan sai ya amar da dafin, dan a wajan mijinta ta gaji duka magungunan.
Miqewa Baabaa tayi ta shiga ɗaki can ta fito da wani qullin magani da qwai da kofi, tana zama ta fasa qwan sannan ta sanya maganin ta kaɗa, Magaji ta miqawa ya karɓa ya buɗe bakin Innai yana sa mata, sai ta kuma buɗe ido tana haɗiya kaɗan-kaɗan, yana gama bata ta wara ido tana ya tsine fiska sai lokacin ta fara jin tashin zuciya, in tayi kaman zata rufe ido sai taji amai na taso mata tana buɗe ido ya kwanta.
Baabaa tace “kai Magaji yanzukam ɗago ta kar ta ɓata maka jiki” sai ya ɗago kanta ya zaunar da ita amma yana riqe da ita. Sai lokacin Baffai ya tuna da maganan tofi nan take ya ɗau kofi da ruwa ya fara addu’a yana tofawa sannan ya sa mata a bakin ta sha, tana gama sha ko kofin bai gama barin bakinta ba sai amai, sosai take amai kaman zata harar da kayan cikin ta, ganin haka sai duk suka yi hamdala suna aikin jera mata sannu.
Sosai tayi amai ta galabaita, tayi luuuu! zata faɗi Magaji yayi saurin taro ta, nan Baabaa ta miqe ta ɗauko roba da ruwa sannan ta sanya Magaji ya gogewa Innai jikinta ta kawo wani riga tace ya sanya mata, kallon Baabaa yayi jin abinda tace na ya sawa Innai riga, duk da dai qanwar sa ce kuma yarinya ce tunda shekarunta sha-huɗu 14 kuma ba komai qirjinta amma baya jin zai iya sa mata rigan dan gudun mastala shi shaiɗan ba’a iya masa.
Ganin ya tsaya da riga a hannu sai ta harare sa ta karɓa zata sa mata shi kuma Magaji kau da idonsa yayi sai da ta gama da mata ya juyo, baabaa ta sanya shi ɗaukan Innai ya kaita ɗaki, ya ɗauke ta ya kaita ɗaki ya kwantar da ita akan gadon ta ya juyo ya fito.
Duk suna zaune zugum-zugum kowa yayi shiru ko wannensu da abinda yake tunawa a ransa yayinda shi kuma Magaji tunani yake wannan yarinya ko kaɗan bata da nauyi kullum ka ɗaga ta kaman ka ɗaga stinke.
Baabaa Mero tace “mai sunan Malam kana ji na?”
Baffai ɗaga kai yayi alaman yana sauraranra, sai ta numfasa tace “mai sunan Malam abun ya isa haka yau shekara ɗai-ɗai shekaru sha-huɗu kenan da haihuwan takwara sannan tun randa aka haifeta har yau ba abinda ya sanja na daga AL’ADAN da uwarta ta ɗaura wa kanta, abun ya isheni yau an qureni na tabbata nan gaba ko ba rai aka kawo takwara indo ba zata kalli gawanta ba balle batun ta mata addu’a ko ta wanke ta dan haka zan ɗau mummunan mataki a kanku duka abun ya ishe ni, ku tashi ku bani waje” ta faɗa tana kallon Baffai da Magaji.
Magaji kallon Baabaa yayi yace “baabaa kiyi haquri amma ni na tabbata Inna na son Innai irin matsanancin soyayyan nan ma, dan Allah kuyi haquri ku mata uzuri”.
harara baabaa Mero ta aika masa da shi tace “kai dan ubanka Musa tunda ba kai ake azabtarwa ba dole kace haka, bayan AL’ADA ta kunyan ɗan fari kasan akwai AL’ADAH ta SHA’DI kamun aure ko? To tunda kace haka ka tabbatar sai an maka za’a baka mata jarababben mara tausayi har za kayi magana ni da nasan ba dan an daina sha’di ba sai dai ka mutu ba aure, to ciwon da ake ji a shaɗi na ɗan awanni ko mintuna ka isa ka haɗa shi da irin ciwon da ake ji na rashin kulawa daga mahaifiya? Anbar duk waɗan nan AL’ADUN saboda zamani yayi kowa ya fahimci yawancin AL’ADU ba komai bane face JAHILCI da kuma ɗaukan alhaqin bayin Allah a banza da wofi abu ba aya ba bare hadisi kuma dai ba Mustahabbi ba ko sunna balle a qira sa farilla kaman yacce mutane ke jahiltan kan su suka aza a gaban goshi, ciwon da takwara ke ji ba ko wanne mai laga-lagan zuciya bane zai iya ɗauka ka godewa Allah uwarka Habiba ba ruwanta da wannan JAHILALLEN AL’ADA dan da kai ne na tabbata sai ka shiga duniya dan jaraba”.
Baffai kansa a qasa ya kasa cewa komai shi kaɗai yasan me yake kissinawa a ransa, dan sosai yau A’isha ta quresa.
Baabaa masifa take kaman zata ari baki barin dai in ta tuno rashin kunyan da Inna ta mata, cewa su Baffai tayi su tafi dare nayi tunda qarfe ɗaya na dare har ya gota, ficewa suka yi suka tafi gida, Magaji yawa Baffai sai da safe ya wuce ɗakin sa.
Baffai yana shiga ɗakin ya samu Inna a kwance da alama tayi bacci ma, qaramin tsaki yaja ya shumfiɗa sallaya ya kwanta a nan qasa.
Baabaa ɗaki ta shiga, cike da tausayi ta kalli Innai tace “takwara Inshà Allahu damuwanki ya kusa qarewa nasan me zan yi” nan ta kwanta a nata gadon bayan tayi addu’a ta shafawa Innai itama ta shafa nata.
Ina mai matuƙar baku haquri na rashin ji daga gareni jiya Monday sakamakon wani uzuri da ya riqe ni, amma Insha Allahu yau page’s 2 zan turo, amma fa ya danganta da sharhinku, dan in kukayi yamun to da yamma ma