Skip to content
Part 10 of 17 in the Series Jawaheer by Fatima Dan Borno

Rufe idanunsa ya yi, a lokacin da yake jingine a jikin windon yana jin wani irin ɓacin rai yana shigarsa wanda ba zai iya cewa ga dalilin ɓacin ran ba. Yana jin kamar hucin mutum, a bakin windon hakan yasa ya juya tare da zura idanunsa a cikin windon yana duban komai ta hasken ƙwan lantarkin da ke waje.

Sanye take da ‘yar riga iya guiwarta me ɗauke da hannun vest. Kanta babu ɗankwali hakan ya ƙara bashi daman zurawa dogon gashinta idanu. Ƙafafunta farare tas! Kamar bata taɓa taka datti da su ba. Ƙirjinta ya kaiwa duba, tana da cikar ƙirji wanda har ya ɗara na Nayla. Haka tana da yalwan ƙugu, wanda suke a ɓoye, sanya irin wa’innan kayan kaɗai zai baka daman ganin su. Shi kansa ba zai iya yanke wa kansa hukunci a irin halin da yake ciki ba. Ƙinta ko haushinta, ko kuma tausayinta. Duk da zuciyar da ke ɗauke da tausayinta ɗin bata da wani tasiri agurinsa. Wuyanta ya kaiwa duba, wani sarƙa ne, wanda duk rintsi bata cire sarƙar nan kamar na maita. Haka kawai idanunsa ke yi masa gizo da sarƙar marigayiya. Don haka ya fara takowa cike da isa, kamar ba zai iya isa inda yake son zuwa ba. Haka ya sake ɗaure fuskarsa kamar wani basarake.

Abin mamaki tafiya kawai take yi a tsakar gidan, a cikin kuma irin wannan daren. Jin motsi yasa ta waiwayo. Idanunsa sun firgita ta, musamman yadda suke kafe akanta, haka kuma ita yake tunkarowa. Da baya da baya take ja, tana jin tsoron yanayin da yake. Ji tayi ta ci karo da bango, hakan ke nuna mata takun tafiyarta ta kai ƙarshe dole ta ja ta tsaya. Ido ta zuba masa a lokacin da yake ƙoƙarin yi mata rumfa. Kwarjininsa ya bugeta. Lokaci guda tunanin zai yi mata kiss ya firgitata, hakan yasa ta ja numfashi ta rintse idanunta, musamman yadda taga idanunsa tsaye akan ƙirjinta. Shurun da ta ji ne yasa ta buɗe idon a hankali. Sarƙar da ke hannunsa ta bi da kallo tare da sauke ajiyar zuciya. Dubanta ya yi, wani irin duba da ke nuna tsanarta a fili,

“Kina tunanin zan yi maki wani abu ne? Kin yi kuskure babba.”

Juyawa ya yi, yana jin idan har ya kama Alhaji Musa ɓacin ransa zai ragu. Haka gobe yake da shirin isowa har gidan Mai nasara. Sai ya gaya masa dalilin da yasa zai amshi zuciyar Nayla ya sawa ‘yarsa.

Shigewa ɗakinsa ya yi, ya jawo bargon da Nayla kullum take rufe shi da shi, ya rufe kansa yana jin ina ma zata dawo su dauwama a tare.

A hankali yake jin ɗumin mutum, hakan yasa ya jawo ta jikinsa yana jin dadɗan ƙamshi masu sanyi da sa natsuwa. Yanayin sanyin garin da kuma yadda daren ya tsala, sun taimaka wajen ganin Mujaheed ya ƙarasa ficewa daga tunaninsa.

 Jawaheer ta kwanta tana duban sama, daga ita sai ɗan wani abu me kama da gyale da ta rufe ƙirjinta da shi. Sannu a hankali ta kama hannunsa ta cusa a cikin gashin kanta, da take matuƙar so ta ji ana sosa mata. Cikin Sa’a ta sami Mujaheed jan gwarzo ne wajen iya sarrafa mace ko ta wani hanya. Haka yatsunsa da ya ware ya tura su a cikin gashin kanta yana sosawa a hankali, ya taimaka ƙwarai wajen sa mata wata kasala wanda bata taɓa jin irinsa ba. Iska me sanyi, ya ratso ta cikin windonsa ya ɗaga labulen ya isko su har kan gado tare da ɗauke ɗan mayafin da tasa ta kare ƙirjinta da shi. A lokacin ne kuma ruwan sama me ƙarfi ya kece kamar da bakin ƙwarya. Irin wannan yanayin yana sanya ma’aurata a cikin wata irin natsuwa, yana ƙara masu wata shaƙuwa musamman idan suna rungume da junansu.

Haƙiƙa babu abinda ya kai aure daɗi da natsuwa, a zuciyoyi irin wa’inda suka ɗauke shi a hanyar samun natsuwar.

Garin ya kaucewa hannunsa ya ji sun sauka a bisa wani abu, da ya yi matuƙar ɗimauta shi. Haka ya kasa tantance a duniyar nan tamu yake ko kuwa? Shuru suka yi na wasu lokutan, kafin kuma ta mirgino da kanta ta dawo ɓarin jikinsa. Tsigar jikinta ya tashi, kawai juya kanta take yi. Sannu a hankali ya gama haukatata da kalolin soyayyarsa, daga bisani ta tsinci muryarsa yana addu’ar saduwa da iyali.

Allahumma jaanibnii Shaiɗa a, wa janibniy shaiɗanu marazaqtana…

Ji tayi wani irin zafi ya ratsata ta ɗinga sauke numfashi, ba yadda ya kamata ba. Daga ƙarshe ta riƙe shi tsam tana faman hawaye tare da girgiza masa kai. Sannu a hankali ya rabata da duk wani abinda take taƙama da shi. A wannan lokacin ne kuma tunani ya dawo masa kai. Ya miƙe yana dubanta.

“Jawaheer kin cuceni kin cuceni…”

Kuka take yi kamar ranta zai fita, tana jin ɗaci a ranta. Adaren farkon da ya kamata ace mijinta yana sa mata albarka, sai gashi ya tashi yana tsine mata. Hawaye shar shar ta rufe ƙirjinta da bargo tana dubansa.

“Mujaheed… Wani irin cin mutunci ne a daren farkona ka wulaƙanta ni haka? Meyasa ba zaka yarda cewa ni ƙaddararka ba ce?”

“Ba zan taɓa ɗaukarki a matsayin ƙaddarata ba, zan ɗaukeki ne a matsayin mace me son zuciyarta. Wacce ta zama sanadin rabani da farin cikina. Jawaheer ki tashi ki bar min ɗakina tun kafin zuciya ta jawo innakasaki.”

Girgiza kai take yi tana hawaye. Haka bata da alamun tashi. Wannan dare ya zame mata dare mafi muni a rayuwarta. Da ace bawa yana iya goge ƙaddararsa da babu shakka daren nan zata goge.

Mujaheed da zuciya ta gama kai shi ƙarshe, tsanar kansa ya gama isarsa, ya miƙe kawai ya zaro belt daga cikin kayansa ya shiga lafta mata. Ihu take tana neman hanyar guduwa amma babu hanya. Abinka da farar mace tuni jini ya ɗinga taruwa a dukkan inda ya shimfiɗe mata belt.

Ƙafafunsa ta kama jikinta na rawa tana kuka, “Don matsayin Nayla a zuciyarka kayi haƙuri.”

Cak! Yaja ya tsaya yana dubanta. Jikinsa ya yi sanyi. Hannayensa ya duba, yana mamakin lokacin da ya fara mugun halin nan. Watsar da bulalan ya yi ya kama hanya ya ɗauko giyan da kullum sai ya kwatanta shanta amma sai ya kasa. Fincike murfin ya yi yana shirin kaiwa baki, ya ji muryarta cikin damuwa da kuka, “Aboki yaushe ka fara karya alƙawari? Ba kayi min alƙawarin ba zaka sake shan giya ba?”

Sauke kwalban ya yi, yana dubanta. Naylaa ce ta fito daga cikin jikin Jawaheer ta ƙaraso har gabansa kawai ta rungume shi. Sannan ta jawo hannunsa ta kai shi har bakin gado, ta koma ta kamo Jawaheer ta zauna a gefensa. Ita kuma tayiwa kanta mazauni a cinyarsa. Hannu tasa tana shafar ƙirjinsa daga bisani ta haɗe bakinsu wuri guda, hakan yasa Jawaheer ta sunkuyar da kanta tana jin wani irin kishi.

Nayla ta tallabo fuskarsa tana murmushi. “Abokiii kaima ka fara ko? Aboki babu kyau babu kyau… Ka hanani inkwanta lafiya a makwancina, kullum da irin damuwar da nake shiga. Na taɓa gaya maka mata biyu zaka aura. Aboki zuciyata kake so, ni na roƙa kafin inmutu da naji Alhaji Musa ya rantse zai kashe ni, kuma zai sawa wata zuciyata, nace masa na amince ya sawa wata zuciyata. Kasan dalilina? Saboda bana son inbarka a cikin ƙunci zuciyata zata taimaka maka. Dama zuciyata kake so, kuma gata nan Allah ya bar maka. Ka daure aboki zaka iya, zaka so ta fiye da yadda ka soni. Idan kuka haihu sunan ‘yar Muhibbat, ba Nayla ba kaji? Idan Muhibbat ta haihu sai ta sa Nayla.”

Tana gamawa ta manna masa sumba. Riƙe hannunta ya yi da ƙarfi kamar zai rabata da su, ƙara tasa tayi magana cikin shagwaɓa, “Aboki… Zaka karya ni fa.”

Bai damu ba, ya cigaba da magana cikin zafi, “Kada ki sake cewa wata zata fiki a zuciyata. Har abada babu macen da zata iya fin ki. Nayla ankashe ni tunda aka tafi min da ke. Babu wani wayo da za ayi min ko dabara.”

Bubbuga ƙafa tayi tana magana kamar zata yi kuka,

“Ni dai sai anjima tunda abun haka ne. Allah ya raya abinda ke cikin Jawaheer. Ku maza idan mace ta haihu sai ku rage sonta, kada ka wulaƙanta Jawaheer kaji? Kada wata mummunar ƙaddara ta sameta ka ce zaka gujeta. Ina sonka aboki.”

Hannu yasa yana ƙwala mata kira, amma sai tafiya take tana ɗaga masa hannu cikin dariyarta.

Firgigit ya tashi, tare da addu’a a bakinsa. Kansa ya yi masa wani irin nauyi. Haka duk ya ɓata gadonsa. Ba wannan ne damuwarsa ba. Tashin hankalinsa da gaske ya yi saduwar aure da Jawaheer? Da sauri ya miƙe ya shiga ɗakinta. Tana nan zaune ta haɗa kai da gadonta. Ƙarasowa gabanta ya yi ya ɗagota tsaye yana dubata. Mamaki yasa ta kafe shi da ido tana jin sonsa yana wani irin fizgarta.

“Ke kinzo ɗakina cikin dare? Mun kwanta gado ɗaya?”

Girgiza kai take yi, tana jin tsoronsa yana ƙara kamata. Tsawa ya daka mata, “Ki natsu kiyi min magana. Ku mata tunaninku iri ɗaya ne, da zarar namiji ya matso kusa da ku, babu abinda zai aikata maku sai iskanci. Saboda jaraba shi ne aranku shiyasa kullum tunaninku iri ɗaya. Ki bani amsa ina tambayarki ina zare min idanu.”

“A’a ban je ko ina ba.”

Ajiyar zuciya ya ƙwace masa kawai ya juya. Har ya kai bakin ƙofa kalaman Nayla suka ɗinga yi masa yawo. Girgiza kai ya yi, ko alama ba zai iya ba. Cikin sauri ya fice ya yi wanka ya gabatar da Sallah, sannan ya fice ya kama hanyar gidan Ummansa. A tsaye ya karya, ya ce zai je wani aiki Kaduna. Kai tsaye maƙabarta ya wuce ya ƙaraso gaban ƙabarinta ya sunkuya. Addu’a ya yi me tsawo, sannan ya duƙar da kai. “Allah ka gajarta min zamana a gidan duniya. Allah ka ƙara haɗa ni da baiwarka. Nayla Allah ya jiƙanki da sauran al’ummar musulmi baki ɗaya. Kada ki manta ina sonki.”

Da ficewarsa kai tsaye ya ɗauki mota ya wuce Kaduna. Da isowarsa bai nemi Jabir ba, don baya buƙata, kai tsaye ya wuce Office ɗin Mai nasara da ke Waffroad anan ‘yan kaji. Bai jira anbashi izini ba ya kutsa kansa, yana jin Secretary ɗinsa yana dakatar da shi, amma ko kallonsa bai yi ba.

Alhaji Musa da shigarsa Toilet ɗin cikin Office ɗin Mai nasara kenan Mujaheed ya faɗo babu ko sallama. Mainasara da ya gama kaɗuwa ya ɗaga murya, ta yadda Alhaji Musa zai ji,

“A’a MD ne a tafe? Kai wuce ka barshi wannan ai surukina ne, bai da buƙatar iso.”

Mutumin ya juya da girmamawa ya fice. Mai nasara ya cigaba da magana, “Haba Mujaheed ai sai kayi sallama ko?”

“Me kyakkyawar zuciya ake yiwa sallama, haka idan akayi sallama aminci ake nemawa mutum, baka daga cikin amintattun da zanyi maka sallama. Ina Alhaji Musa? Ko ka fito da Alhaji Musa ko kuma inɗauki fansa akan ‘yarka. Zan banƙareta da ranta inciro zuciyar Nayla inkai mata kayanta. Kasan kuma zan iya.”

Yau ake yinta, Alhaji Musa da ya gama jin komai ya ɗinga salati yana sa hannu akai, fitsari ya biyo wandonsa. Tabbas yasan lokacin tonuwar asirinsa ne yazo, domin kuwa Mainasara ba zai taɓa rufa masa asiri ba, akan dai a taɓa masa tilon ‘yarsa.

Mainasara ya dafa Mujaheed ya ce, “Shiyasa naso mu zauna mu fahimci juna. Ni ina zanga Alhaji Musa? Wannan lamarin mu ba mu san ɓarnar da ya aikata kenan ba. Jawaheer me ta sani don Allah don Annabi? Idan ka hukuntata zaka ɗauki alhakinta ne.”

Mujaheed ya ɗago a fusace, “Ni meyasa kuka ɗauki alhakina? Meyasa? Kunsan illar da kuka yi min ne? Aikina ne bincike, haka ban taɓa yi na faɗi ba. Zan zaƙulo duk wani mai laifi akan kisan Nayla. Alhaji Musa kuma ni kaɗai nasan irin horon da zanyi masa kafin mutuwarsa. Idan kuma kuna taƙama kuna da kuɗin da zaku iya kashe Case ɗinnan, na shirya fito da duk wani abu da na mallaka domin ganin na hana masu son zuciya aikata hakan a yayin hukuncin su. Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! Ko babu ko sisina, zan sa bakin bindiga inharbe Alhaji Musa, muddin aka ce za a iya juya case ɗinnan. Sunana MUJAHEED MUH’D Jami’in da bai san tsoro ba. Ka gaya masa wannan saƙon don nasan kuna tare. A yau idan na tsananta bincike na gadama sai inbaka mamaki. Domin tun daga cikin Toilet ɗinka zan fara har izuwa ƙarƙashin kujerarka. Idan na gadama zan bar shaidar da anjima zan dawo inɗauka. Amma zan bi komai a hankali har ya gama guje-gujensa. Ni sai na kawo ƙarshen zaluncin Musa. Daga ƙarshe kaje ka kwashi ‘yarka da ke zaune a gidana na sake ta.”

Tunda Mujaheed yake magana, Mai nasara yake haɗiye kakkauran miyo da ƙyar, jin ya ce zai bincika har toilet yasa ‘yan hanjinsa kaɗawa. Zufa ya shiga keto masa. Daga ƙarshe ya kashe shi a tsaye, da ya sakar masa ‘yarsa a dai-dai lokacin da Jawaheer zata iya mutuwa indai ta ji wannan maganar. Jikinsa na rawa ya kira mahaifiyar Jawaheer ya gaya mata, haka ya kasa sukuni sai kaiwa yake yana komowa. Alhaji Musa da ya gama tsurewa ya ce, “Rankashidaɗe ka kira mahaifinsa, ka tsara shi tunda yana jin maganar iyayensa.”

Sai yanzu ya ɗan sami natsuwa, ya ɗaga waya ya kira Abbansa ya tanƙwashe murya ya gaya masa komai. Hankalin Abba ya yi matuƙar tashi da jin Mujaheed ya saki Jawaheer. Ita kanta Umma ta sakko, tana jin tausayin Jawaheer. Haka sakin ya girgiza su ƙwarai da gaske. Haka idan suka barshi haka zai yi ta aure yana sakin matan.

Mahaifiyar Jawaheer ta Kirata ta gaya mata ta kwaso kayanta ta dawo gida. Jawaheer da ta ji zuciyarta ta tsinke tasa kuka, “Mom babu inda zanje, zan zauna inyi Idda a ɗakina kamar yadda Allah ya yi magana a cikin Alƙur’ani me girma akan Idda. Zan bi abinda addinina ya ce inzauna inyi idda a ɗakin mijina. Amma na tabbata kafin zuwan kammalawan zan iya mutuwa Mom. Mom aboki shi ne rayuwata gaba ɗaya.”

Sauke wayar tayi tana cigaba da kuka. Ganin hakan ba zai yi mata bane ta ɗauki Hijabinta ta shiga gidan su, tana kuka ta zube a gaban Abba. Sai dai ta kasa magana. Abba ya ɗagota yana bata baki, Umma ta jawo ta ɗaki ta tasa ta gaba sai ta ci abinci, amma ina abincin ya ƙi ciwuwa. Suna nan zaune kowa zuciyarsa babu daɗi, Mujaheed ya dawo da sallama. Ganin Abbansa yana kaiwa da komowa ne yasa ya kafe shi da ido, daga bisani Ummansa ta fito tare da Jawaheer.

“Abba kayi haƙuri na yanke shawarar rabuwa da…”

Bai kai ga ƙarasawa Abbansa ya iso gabansa gadan gadan ya ɗauke shi da mari jikinsa na rawa ya nuna shi da yatsa,

“Mutumin banza mutumin wofi. Yaushe ka fara yanke hukunci ba tare da sanin mu ba? Allah ya halasta saki, amma baya son sa. Al’arshin Allah saki ke girgizawa. Haka kaf cikin zuri’armu babu wanda ya taɓa yin saki sai kai? Sai kai Mujaheed? Da zaka furta sakin ‘ya a gaban mahaifinta baka ji kunya ba? Ko kana nufin har kunyarka ta ƙare ne? Mahaifin Jawaheer ya fi ƙarfin cin mutuncinka, ko da kuwa mahaukaci ne me kwana a bola. Ya zama dole ka girmama shi tunda har ya wanke ‘ya ya miƙa maka. Na kula kana son ka zama mahaukaci! Domin marabanka da mahaukaci bin bola! Ka dawo hayyacinka tun kafin fushin Allah ya kama ka Mujaheedu. Kana son ka zama jahili. Jahili ne kaɗai baya taɓa yarda da ƙaddara! Addinin musulunci ya zo mana da abubuwa cikin sauƙi ya kuma sa mana tauhidi a zuciya, kai ina naka tauhidin? Ka gaggauta mayar da matarka ɗakinta tun kafin ka gamu da fushina. Ruwanka ne ka kyautata mata wannan ba zan sa ka dole ba, kamun Allah kaɗai ya isheka akan yarinyar nan ba sai na jaddada maka ba. Haka na fita haƙƙinka Mujaheedu tunda har na kaika islamiyya ka iya bambance tsakanin ɓaki da fari.”

Mujaheed da yake jin zuciyarsa yana suya ya rage tsawonsa a gaban mahaifinsa. “Kayi haƙuri Abba na mayar da ita. Kayi haƙuri. Ka yafe min, nayi kuskure Abba.”

A zuciyarsa kuwa ji yake kamar ana rura masa wutan tsanar Jawaheer. Jin muryarta suka yi cikin kuka tana magana, “Abba shi ne zaka yi wa aboki faɗa har ya yi fushi?”

Fuu tayi waje ta zauna a can bakin gate fuskar nan a ɗaure. Umma da Abba suka shiga kallon kallo. Mujaheed kuma ya bi ta da kallo har ts fice. Dukkan su suka yi ajiyar zuciya.

Lallaɓawan duniyar nan Jawaheer ta ƙi kallon iyayen Mujaheed, sai ma kuka da ta sa masu. Hakan yasa Abba ya dawo yana duban Mujaheed fuska a ɗaure.

“Kaji ka lallaɓata.”

“Amma Abb…”

“Ya isa haka. Umarni na baka.”

Jiki a sanyaye ya fice.  A gabanta ya tsaya yana dubanta. Daga bisani zuciyarsa ta ɗinga gaya masa ya juya kawai. “Ke! Tashi ki bar nan.”

Ya ɗaga mata tsawa. Ga mamakinsa sai ta noƙe kafaɗa, “Ni dai ba zan tashi ba sai Abba ya baka haƙuri.”

Abba ya ƙaraso yana duban Mujaheed ba tare da ya ce masa ƙala ba, ya dubi Jawaheer, “Yi haƙuri ki tashi mu tafi, na bashi haƙuri.”

Kai tsaye ta miƙe tana dariya.

Wayarsa kira ya shigo, aka tabbatar masa da anga Alhaji Musa ya shiga wani hotel. Ajiyar zuciya ya ƙwace masa. Da gaggawa ya fice daga gidan su.

Ƙarewa hotel ɗin kallo ya yi, kafin ya dubi yaron aikinsa da ke cikin kayan gida ya tambaye shi Room number ɗin? Ya gaya masa.

Kai tsaye ya ƙwanƙwasa yana tsaye fuskar nan babu walwala. Babu wani tunani ya buɗe ƙofar, sai dai irin naushin da ya ji a fuskarsa yasa gaba ɗaya ya kasa gane a wacce duniyar yake.

Budurwar tayi maza ta mayar da kayanta jikinta na rawa ta fice. Rufe ƙofar ya yi ya koma ya zauna yana duban yadda har yanzu bai dawo daga duniyar ruɗun da ya shiga ba. Mujaheed ya ware idanunsa da suka yi masa nauyi, yana kallon gawan Nayla kwance a ƙofar gate ɗin gidan su. Yana kallon lokacin da ya yi bankwana da ita, irin bankwanan da har abada ba za su sake haɗuwa ba.

“Gaya min yadda akayi ka kashe min matata. Haka tun wani lokaci ka ɗauka kana bibiyar rayuwarta? Bana son inkai ka Office sai na sami wa’innan amsoshin da kullum nake neman su ido rufe. Gaya min da irin laifin da tayi maka.”

Shuru Alhaji Musa ya yi, daga bisani yasa guiwowinsa a ƙasa jikinsa yana rawa. Yana roƙon Mujaheed.

“Ka taimakeni kada ka kashe ni don Allah. Idan ka kashe ni zaka bar marayu a cikin wani yanayi. Matata bata da kowa sai ni, ni kaɗai ne gatanta, yarona zai taso cikin maraici.”

Mujaheed yasa hannu ya ɗauke shi da mari, kala-kala masu gigita mutum. Sannan yasa hannu ya damƙi doguwar jallabiyarsa jikinsa yana ya rawa.

“Ka ce mene? Maimaita abinda ka ce min. Ka maimaita!”

Ya daka masa tsawan da ko ina ya amsa a cikin ɗakin. Mujaheed ya sake ɗauke shi da mari yana faɗin sai ya maimaita abinda ya ce. Dukansa yake yi da iya ƙarfinsa. Daga bisani ya shaƙe wuyan rigarsa, idanun nan kamar jan gauta.

“Sakarai! Kai ƙaton sakarai ne!! Wawa shi yake aikata mugunta ya koma yana dariyar samun nasara. Mahaukaci shike zuwa duniya yana wulaƙanci ba tare da ya tuna akwai irin wannan ranar ba. Ranar nadamar dole! Ka kashe rayuwata kana son inraya taka? Marayun da kake gudun kada a barsu a duniya, irinta ne ka kashe! Halin da kake gudun barin su a duniya, irin halin nima ka barni a ciki. Yadda ka kassara rayuwata ko danginka zan ƙarar bana jin zaka fanshe abinda kayi min. Zaka gaya min dalilan da na tambaya ko sai na fara azabtar da kai?”

“Tottto… Zan gaya maka..”

Mujaheed ya sassauta riƙon da ya yi masa, ya sake shi ya koma kujera ya zauna yana mayar da numfashi. Idanunsa a rintse, baya son haɗa ido da Alhaji Musa, idan ba haka ba, zai iya sa bindiga ya ɗauke numfashinsa.

“Tun lokacin da ka datse min yatsa na ci burin sai na rama abinda kayi…”

Bai kai ga ƙarasawa ba, Mujaheed ya sake miƙewa ys damƙi wuyar rigarsa jikinsa yana wani irin rawa. Ya shaƙe wuyansa da iya ƙarfinsa, “Ɗan iskan banza! Shiyasa ka yanke shawarar ɗaukar fansa ta hanyar kasheta? Ita ta datse maka ɗan yatsa ko kuwa ni? Ashe baka da jarumtar tunkarata sai dai ka tunkari mace! Macen ma yarinya ƙarama kamar Nayla? Shine zaka kashe min ita? Dalilin nan ya yi kaɗan idan baka gaya min dalilin da zan gamsu ba, sai na yayyanka naman jikinka da ranka har ka mutu!”

Buga kansa ya yi, da bango wanda ya haddasa sumewan Alhaji Musa. Mujaheed ya saki murmushin takaici yana dubansa, “Idan ka mutu ban wulaƙantaka ba, zan hana da gawanka, zan ɗauki gawanka da kaina inmiƙawa tsuntsaye.”

Ruwa ya ɗauko ya kwara masa, ya saki ajiyar zuciya tare da maganganun sumbatu. Mujaheed ya fizgo shi yana masa wani duba, “Ba lokacin sumbatu bane, gaya min dalilin da yasa ka kashe min matata.”

“To. Tun lokacin nake bin bayanta, idan zata je makaranta. Naso Nayla, naci burin insace ta in ajiyeta kawai a gidana ta zama karuwana.”

Ɗau! Ya dunƙule hannu ya auna masa naushi a baki, tuni bakin ya rine da jini. Alhaji Musa ya ce, “Wayyyooo Allah, kayi haƙuri kayi haƙuri.”

Mujaheed bai ce komai ba yana nan yana duban wani gefe. Hakan yasa ya cigaba,

“Kullum idan mun so saceta sai mu sameta tare da kai. Ana hakane Mai nasara ya bada cigiyar ana neman zuciya za a siya da kuɗi me tsoka. Kawai sai Nayla ta zo min a rai. Nayi masa alƙawarin zan kawo zuciya, na wata da ta kusan mutuwa, amma sai dai Doctor ɗinsa da Jawaheer su zo nan Abuja daga nan sai ya sami Private Hospital ayi ciniki da su. Cikin ƙanƙanin lokaci aka haɗa komai. A wannan daren aka sato Nayla, bayan anga fitarka. Kasancewar masu kula da dukkan motsinta suna kwana a unguwarku.

Nayla tana kuka tana roƙona akan inkaita wurin aboki tayi sallama da shi, amma muka hana. Nace zan kwanta da ita da ƙarfin tsiya, yadda take kuka yasa na fasa. Kai tsaye na gaya mata kashe ta zanyi, ta durƙusa tana roƙona kada injawo ka shiga matsala, amma naƙi dubanta. Na gaya mata wata bata da lafiya kuma zuciyarta za a cire bayan na kasheta. Kawai sai naga tana murmushi. Ta ce min indai zamu yi mata taimakon nan ta amince a ɗauki zuciyarta a baiwa wata, tana da tabbacin zuciyarta tana raye a duniya kamar bata mutu bane. Damuwarta farin cikinka.

A take akayi mata allura, muna kallonta tana shure-shure da taimakon likitocin aka yiwa Jawaheer dashen zuci. Shi ne muka cire wasu sassan jikinta dan kada a gane zuciyar kaɗai muka ɗauka. Yaran aikina suka dawo da ita bayan sun tabbatar babu kowa.

Mujaheed ya rintse ido yana jin kamar yanzu abin ke faruwa. Yana jin kamar zai iya taimakon Nayla.

Miƙewa ya yi, ya buɗe ƙofar ya miƙawa yaransa Alhaji Musa ya ce su wuce da shi gayi nan zuwa.

Kusan a tare suka isa Office ɗin. Duka yasa ayiwa Alhaji Musa, yana sumewa suna kwara masa ruwa. Haka ya dawo kusa da shi ya ɗinga gana masa azaba kala-kala. Haka a take ya haɗa shi da motar ‘yan sanda suka tafi aka kamo likitocin haka aka rufe asibitin. Gobe kuma za aje Kaduna a kamo ɗayan likitan. Alhaji Musa ya dage ya ce shi sam Mai nasara baida masaniyar wannan abun. Bayan gaskiyar zance ɓoyewa ya yi, a lokacin da ‘yarsa take yawan kiran sunan aboki, ya kira shi yana tambayar wacece take da zuciyar? Anan ya gaya masa komai, a lokacin ne yasan labarin Mujaheed. Amma sai bai damu ba, tunda ‘yarsa ta sami lafiya.

Cikin ciwon kai me tsanani ya dawo gida, bayan ya tabbatar duk sun shiga hannu. Sai dai da dawowarsa cikin gidansu ya tarar da wani tashin hankalin. Har zai shiga ɗaki Umma ta ce,

“Ka zo ka ɗauki matarka. Ɗazu bata da lafiya muka kaita asibiti wai tana ɗauke da juna biyu.” A firgice ya dubi Ummansa, ya dawo da dubansa ga Abbansa haka cikin gaggawa ya janye idanunsa zuwa kan fuskar Jawaheer da tunda aka gaya mata zancen cikin take kuka. Su iyayen sam basu gane dalilin koke koken da take yi ba.

Ƙiris ya rage Mujaheed bai kifa ƙasa ba, ya sake duban umman ya ce, “Ciki? Ciki fa kika ce Umma? A ina ta samo cikin? Haba wasa akeyi, idan Jawaheer ta yi ciki zai kasance a ruwa tasha kenan?”

Anan kuma sai aka hau kallon kallo, jikin Umma yana wani irin rawa. Haƙiƙa ba sai anyi masu ƙarin bayani ba, sun fahimci inda zancensa ya dosa. Jawaheeer ta sake rushewa da kuka jikinta yana wani irin rawa. Umma tayo kanta gadan-gadan. Shi kuwa Mujaheed ji ya yi gaba ɗaya duniyar tayi masa zafi. Meke shirin faruwa ne da shi?

<< Jawaheer 9Jawaheer 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×