Kwance ya sameta, tana kallon sararin samaniya, littafi ne rungume a ƙirjinta. Littafin yake son ya gani don haka yasa hannu zai ɗauka, ya ji hannunsa ya haɗe da ƙirjinta. Ɗayan hannun tasa ta dafe nasa ba tare da ta dube shi ba.
Zura mata idanu ya yi, cikin abinda bai wuce minti ɗaya ba, ya gama nazartar halittarta. Ya ɗan Zame hannun, hakan yasa ta dube shi a firgice. Tana ƙoƙarin tashi ya zabga mata harara.
Can nesa da ita ya zauna a bisa kujera, yana karatunsa. Yana kallonta ta gefen ido yadda take kallonsa. Ya ajiye. . .