A can gidan su Jabir kuwa, Jawaheer ta haɗu da Zara, sai ya zamana tunaninta kaɗan ne, domin Zara akwai suturu, don hakane zaman ya ɗan yi mata daɗi.
Haka garin Allah ya waye Mujaheed ya kasa sanya komai a cikinsa. Da gaske yake jin wata zazzafar ƙaunar Jawaheer a zuciyarsa. Wannan shi ake kira da lamarin Allah. Baka isa ka gane me zai faru da kai gobe ba.
A cikin kwanaki biyu kacal ya sauya kamanninsa, haka ya rasa ina zai dosa? Har Jabir ya kira ya gaya wa, amma sai ya bi shi da addu. . .