A lokacin da Mujaheed ya yi hatsari, a wannan lokacin zuciyar Jawaheer ya buga da ƙarfi, ta dafe wurin tana Salati. Mom ɗinta ta riƙeta tana tambayarta lafiya? Cikin rikicewa ta dubi mahaifiyarta, ta ce “Na shiga uku Mom, wani abu ya sami Mujaheed, Mujaheed yana cikin matsala. Walh akwai abinda ya same shi, ki taimake ni Mom inje gare shi.”
Kwantar da ita tayi a jikinta tana shafa bayanta. “Ki natsu kiyi masa addu’a, duka-duka yaushe ya rage ki zama mallakinsa? Ya kamata Jawaheer ki rage irin wannan zazzafar soyayyar da kike gwada wa akan Mujaheed, shi ɗa namiji sakarai ne, da zarar yaga ana sonsa, shikenan sai ya riƙa wulakanta ‘ya mace. Ita kuma ‘ya mace tana da girma da ƙimar da ta fi ƙarfin wulakancin ɗa namiji.”
Jawaheer ta ɗago tana duban mahaifiyarta, “Mom ko zai ɗinga yanka naman jikina ne, na amince zan zauna da shi. Ni ba zan iya boye soyayyar da ke zuciyata ba, ba zan iya ba. Mom na gaya maki Mujaheed yana cikin wani hali ki taimakeni inje inganshi.”
Hankalin Hajiya Zakiyya ya kai matuƙa a tashi, don haka ta ɗinga lallaɓa ‘yarta har barci ya kwashe ta.Wanda ya yi dai-dai da shigowar Dad ɗinta. Ya dubi Hajiya da damuwa ya ce, “Na ƙosa a ɗaura auren nan, tun kafin matsalar da muke ta birnewa ta haƙo kanta. Ina tsoron Allah ina tsoron yaron nan Mujaheed. Ki kalli yadda ya datsewa Alhaji Musa ɗan yatsa? Na gayawa Alhaji Musa ya yi nesa da ni, har sai ‘yata ta sami muradin zuciyarta.
Hajiya ta jinjina kai kawai, tana ji a jikinta lokacin matsalar ‘yar su ne ya tsaya.
Mujaheed yana farfaɗowa ya duba ko ina, yana mamakin abinda ya kawo shi asibiti. Sai da ya ji azaba a ƙafafunsa ne kafin ya tuna da komai. Da ƙarfi ya riƙe kansa yana jin muryarta a kunnensa, “Aboki kaina zai cire, aboki ni zafi nake ji ka cire min ciwon nan.”
Lumshe idanunsa ya yi, ya sani da son Nayla Zai koma ga Allah. Yana yi mata soyayyar da baya fatan ko sau ɗaya ne ya kwanta ba tare da ya tuna da ita ba. Muryar Ummansa ya ji tana magana kamar da faɗa,
“Ko dai kana son ka gaya mana kafi mu damuwa da Nayla ne? Gara kai ayyukanka sun rabaku, na wasu lokuta, mu da muke kwana da ita mu tashi da ita fa? Kana jayayya da hukuncin Allah, kuma Walh zaka sa kanka a uku.”
Bai ce komai ba ya kawar da kansa gefe guda.
Cikin hukuncin Allah Mujaheed ya sami sauƙi, haka aka sallamo shi, yana kallon kowa ana ta shirin biki, shi dai bai ce komai ba, haka bai da alamun tofa wata magana a bakinsa.
Jabir ya shigo yana nemansa, kai tsaye ya wuce Garden ɗin. Zaune ya same shi ya tasa sarƙan a hannunsa yana kallo. A hankali ya dafa shi, “MD ba zaka yi haƙuri da ƙaddararka ba?”
“Wacce ƙaddara daga ciki? Ƙaddarar rashin Nayla, ko kuma ƙaddarar shigowar masifa cikin rayuwata?”
“Jawaheer ba masifa ba ce, ka ɗauka Jawaheer ita ce Nayla.”
Ƙura masa idanu ya yi, kafin ya girgiza kai,
“Jawaheer ba zata taɓa zama Nayla ba, har abada. Nayla ta daban ce, dan ita aka halicceni haka dan ni aka halicceta. Ka daina haɗa Nayla da Jawaheer.”
Miƙewa tsaye ya yi, dai-dai da zubewan hotunan Nayla. Dukkansu suka bi hotunan da kallo.
“Jawaheer ta ɗauko ruwan dafa kanta. Zata yi danasanin zaɓo ni a matsayin mijin aure. Babu macen da zata iya haƙurin zama da ni, kamar matata Nayla. Ita ce komai nayi dai-dai ne a wurinta ko da kuwa kuskure ne. Ita ce bata iya fushi da ni, ita ce ke tsoron iyayena suga aibuna. Nayla ce Umma zata yi min faɗa ta kwana kuka, ta ƙi ci ta ƙi sha, sai mun taru muna lallashinta. Jabir ina tausayawa rayuwar macen da zata iya haƙurin zama da ni.”
Jabir ya duƙar da kai, tuni hawaye suka gangaro masa. Haƙiƙa rashin Nayla a cikin wannan zuri’ar babban tabo ne, da ba zai taɓa gogewa ba
Mujaheed ya koma gidan jiya, baya magana da kowa, baya shiga lamarin duk wata halitta da ke cikin gidansu. Ya mayar da Garden wajen zamansa, kuma abokin hirarsa.
Ranar da aka tabbatar da Jawaheer a matsayin matarsa, a ranar aka neme shi aka rasa. Har aka kai Jawaheer cikin gidan da Nayla ta zauna, babu Mujaheed. Iyayensa ne zaune a falon suna ta kiran layinsa. Tsalam Jawaheer ta miƙe ta ce, “Nasan inda yake ɓoyewa.”
Gaba ɗaya suka zuba mata idanu. Miƙewa tayi, ta nufi wata hanya sai da tayi tafiya me ɗan nisa, kafin tasa hannu ta buɗe ƙofar. Idanu kawai ya zuba mata har ta ƙaraso tana ninyar taɓa shi, ya watsa mata mugun kallo,
“Mayya! Nafi ƙarfinki. Uban wa ya nuna maki nan wurin?”
“Nima kawai na ganni ne nazo ban sani ba.”
Ta faɗa cikin sanyi. Kafin ya sake magana yaga iyayensa tsaye akansa.
“Mujaheed ka nuna mana iyakarmu, ka nuna mana bamu isa da kai ba. Mun gode.”
Gaba ɗaya suka fice daga gidan, bai yi yunƙurin bin su ba, haka bai ji a zuciyarsa zai iya dawowa cikin hayyacinsa ba. Yana nan kwance ya ɗago yana dubanta,
“Tashi ki bani wuri tun kafin inyi ƙasa-ƙasa da ke.”
Jikinta na rawa ta miƙe ta bar wurin.
Kwananta uku, a gidan bata sa shi a idanunta ba, duk ta koɗe ta lalace kamar ba Jawaheer me ji da kwalliya ba. Tana nan kwance a falon tana fama da zazzaɓi, sai murƙususu take yi a tsakar falon.
Shi gaba ɗaya ma ya mance da akwai wata halitta a cikin gidan, tun bayan da ya rasa Nayla bai sake marmarin shiga gidan ba, sai da aka ɗaura masa aure, don haka komai ya dawo masa sabo fil. Fitowarsa kenan yana sauri ankira su Meeting. Ganinta a kwance tana sanye da vest da wani zani, wanda ba zai taɓa mance da zanin nan, ya sami Nayla kwance a falonta tana kukan ciwo ba. Kawar da kansa ya yi, yana shirin wucewa har ya kai ƙofa ya juyo. Idanu suka haɗa ya dawo da baya ya ɗagota gaba ɗaya ta kwanta a jikinsa. Yatsa yasa ya ɗauke hawayen fuskarta,
“Baki da lafiya ne?”
Kai kawai ta ɗaga masa. Kafin tayi wani abu, amai me ƙarfi ya taho mata, ta ɓata masa kaya. A karo na farko da tausayinta ya tsirga masa, kasancewarsa mutum me tausayin mara lafiya.
“Ya Salam! Sorry bari inkira maki likita ya duba ki.”
Wani irin sanyi ya ratsa Jawaheer har ta fara zaton Allah ya karɓi addu’arta ne. Sai da ya gyara wurin da ta ɓata sannan ya koma ya sake yin wanka ya shirya agurguje. Ya kira likitan gidansa, sannan ya zo saitin fuskarta, “Allah ya ƙara maki lafiya.”
Tana kallo ya fice babu ko waige. Sai dai har likita yazo ya gama dubata, ya tafi babu Mujaheed babu dalilinsa. Har dare ya yi bai dawo ba. Wasa-wasa kwana uku cur babu Mujaheed babu dalilinsa. Tsoro tashin hankali, kuka suka haɗu suka hana ta kwanciyar hankali.
A hankali ta zari wayarta ta gwada kiransa. Bugu ɗaya biyu ya ɗauka muryarsa wani iri. Kuka take yi ta kasa magana, ta rasa me zata ce masa. Daga can ya sha jinin jikinsa, ya ce “Wa ke magana?”
“Aboki ina ka shiga?” Abinda bakinta ya iya furtawa kenan. Sai da ya shaƙi numfashi kafin ya ce, “Ina gun aiki.”
Kafin ta sake magana ya datse wayar, yana mamakin a ina ta samo layin wayar da mutane huɗu kacal suka sani? Riƙe kansa kawai ya yi ba tare da ya iya tuno komai ba.
Jawaheer tana nan kwance bakinta babu daɗi, hawaye kawai ke bin gefen fuskarta. Jabir ya shigo falon yana ƙwala kiran “Amarya! Yau dai na zo inci abincin amare.”
Zuba mata idanu ya yi, cike da tsoro. Anya wannan Jawaheer ɗin da ya sani ne? Cikin sauri ya ƙaraso gabanta ya jero mata tambayoyi a jere, “Jawaheer me ya sameki? Ina Mujaheed ɗin?”
Goge hawayenta tayi ta ce, “Jabir don Allah wacece Nayla? A ina zan iya ganinta?”
“Zan iya kai ki inda zaki ga Nayla, amma sai kin gaya min abinda ke damunki haka.”
Shuru tayi can, ta ce “Ciwon son Mujaheed ke damuna. Kullum zuciyata cikin ƙuna take tana min zafi. Na amince zan yi wa Nayla biyayya idan har zan sami zuciyar Mujaheed. Ka gaya min abubuwan da Nayla take yiwa Mujaheed nima zan ɗinga kwatantawa.”
Jabir ya miƙe kawai yana saƙe-saƙe. Muryar Jawaheer wani lokacin yana rikiɗe masa yana juyawa na Nayla. Zuciyarsa tana sanar da shi kawai ya sanar da ita labarin Nayla, ƙila hakan ya taimaka mata. Tana bashi tausayi, yasan Mujaheed da gaske yake yi babu wata ‘ya mace da zata iya samun zuciyarsa akan Nayla.