Umma, ta jima tana lallaɓa Jawaheer, sannan tayi mata sallama ta fice. Wanda ya yi dai-dai da shigowar Jabir. Sai da ya karya, sannan ya miƙe tsaye yana duban Jawaheer.
"Ya kamata ki daina zama a cikin duhu, ke kaɗai ce a yanzu nake sa ran zaki dawo min da farin cikin ɗan uwana. Haka idan kika ji labarin Jawaheer zaki hana kanki damuwa da kuma jin haushin Mujaheed, na tabbata zaki yi masa uzuri. Nasan ba zaki so kanki ba, zaki gane Nayla har abada ba zata bar rayuwar Mujaheed ba. A yanzu kuma idan. . .