Suna hanya tana jin Mujaheed yana cewa babu shi babu Rukayya, ta dube shi, "Aboki meyasa? Naga tana sonka, nima ina sonta. Zan iya yin komai dan ka sameta kaji aboki?"
Hannunta ta miƙa masa, shima ya miƙa mata nasa sai duk suka yi murmushi. Kai tsaye Ice Cream ya siya mata, tana sha tana juya kai alamun daɗi.
Tana isowa gida ta nufi Umma ta sa mata cokali ɗaya a baki, sannan ta nufi Abba ta sa masa cokali biyu ta ce, "Tunda kai ne babba Abbana kai kasha biyu."
Nayla bata da abokai da ya. . .