Cilli tayi da bargon da ta ƙudundune ta rugo falo kamar mahaukaciya. Wayarta ta ɗauka jikinta na kyarma, ta kira mahaifiyarta. “Mom, Mom Mujaaa…hee…d zai zo ya kashe Dad, da Alhaji Musa. Walh kashe su zai yi. Mom lokacin mutuwata tayi, yau na shiga uku.”
Iya gigicewa mahaifiyar ta gigice, ganin Jawaheer ba zata natsu tayi bayanin da ya kamata ba, yasa ta daka mata tsawa, “Ke! Jawaheer ki natsu pls! Ki gaya min me ya faru?”
“Mom! Zuciyar aro, zuciyar aro na matar Mujaheed ne shiyasa nake sonsa. Mom Mujaheed ya gano Alhaji Musa shi ya kashe masa mata, gayi can ya kama hanyar gidan Alhaji Musa zai kashe shi.”
Ta ƙarasa da wani irin rauni. Hajiya tayi Salati, tayi maganar da ya sa Jawaheer dakatawa daga irin kukan da take yi, “Yau ne ranar nadamar Alhaji Musa da mahaifinki. Duk da mahaifinki bai san mutum Alhaji Musa ya kashe ba, sai daga baya. Amma Mujaheed ba zai taɓa ɗagawa duk me hannu a wannan kisa ƙafa ba . Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi. Ina shawartarki da ki kwaso kayanki ki kamo hanya ki dawo gida.”
Jawaheer ta jawo wani numfashi da ƙyar, ta ajiye ajiyar zuciya ba a yadda ya kamata ba.
“Sai dai Mujaheed ya kashe ni a gidan nan, ba zan iya rabuwa da shi ba. Mom ina jin idan na fito daga gidan nan zan iya mutuwa. Kiyi min addu’a kawai a matsayinki na uwa, zata iso gareni.”
Ajiye wayar tayi tana wani irin shessheƙan kuka. Ganin hakan ba zata fissheta ba, ta miƙe a guje ta ɗauki hijabinta, ta fice zuwa gidan iyayen Mujaheed.
Tana zuwa ta same su zaune a falo, kawai ta durƙushe tana shessheƙa. Gaba ɗaya suka kafe ta da ido, anrasa me ƙarfin halin tambayarta dalilin irin wannan kuka.
“Abba, Umma ku yafe min. Zuciyar Nayla aka dasa min bayan ankasheta.”
Jin maganar suka yi kamar sauƙar wani ƙaton dutse daga sama. Cikin rawar murya Jawaheer ta sanar da su Umma komai akan abinda ta sani.
Umma ta miƙe tana zare idanu, “Kina nufin ku kuka buɗe zuciyar Nayla? Kuna nufin ku kuka wulaƙanta gawar Nayla? Bayan kasheta da akayi, aka rabata da wasu daga cikin sassan jikinta? Kuka raba ni da ita?” Kuka yi mata mutuwar da kullum idan na kwanta sai na ganta a cikin jini?”
Yadda take yi, yasa Abba jawota ya dawo da ita baya. Amma kuma shi kansa ya kasa furta ko da kalma ɗaya.
“Umma nima ban san…” Daka mata tsawa Umma tayi, haka bata san lokacin da ta zabura ta ɗauketa da mahaukacin mari ba. Abba ya sake riƙe ta, ya ce “Jawaheer ta shi ki koma gidanki. Amma bana jin zan iya saurarawa wanda ya kashe min ‘ya.”
Jawaheer ta miƙe tana kuka, tana dafe da ƙuncinta. Tasan lokacin girban abinda suka shuka ne tayi. Ita meye laifinta? Me tayi? Ta tsorata da yadda jikin Umma ke karkarwa, ta fice tana kuka. Gaba ɗaya duniyar tayi mata zafi. Tana jin ko kasheta za ayi ba zata iya rabuwa da Mujaheed ba.
Shi kuwa Abba kiran Mujaheed ya yi a waya ya ɗauka muryarsa a shaƙe, kamar wanda ya yi kuka. Abba ya ce,
“Duk inda kake ka dawo gida. Nasan kai hukuma ne, amma kada ka ɗauki wata doka a hannunka. Jawaheer ta sanar da mu komai.”
Girgiza kansa ya yi, “Abba ka gafarceni ba zan iya dawowa ba. Ban taɓa yi maka musu ba, amma yau numfashina kaɗai za a zare ya gagareni isowa ga Alhaji Musa.”
Abba ya bi wayar da kallo a lokacin da ya fahimci Mujaheed ya kashe wayar. Umma ta goce da sabon kuka ta ce, “Shikenan mun shiga uku. Ashe masifa muka aurawa Mujaheed da hannun mu? Yaron nan ya ce mana baya so, muka nace. Abban Nayla ka barni inje nima inshaƙe yarinyar can kowa ya huta.”
Abba ya riƙe kansa kawai yana Salati. Ya zubawa sarautar Allah idanu, haka ya miƙa komai gun Allah shi zai aiko masa da mafita.
Hawaye suka zubowa Abba, yana jin mutuwar Nayla ta dawo masa sabo fil. Miƙewa ya yi, ya shiga kaiwa da komowa. Babban burinsa yaga wanda ya aikata hakan ya ji menene dalilinsa. Me kuma Nayla tayi masa da har ta cancanci irin wannan kisan wulaƙancin?
A can ɓangaren Mujaheed kuwa, gudu yake shararawa, yana dukan sitiyarin motar da iya ƙarfinsa. Gani yake yi ba zai iso ga Alhaji Musa ba.
“Aboki meyasa kake sa ni a bayan mota?”
Tana maganar ne bayan ta rungume shi ta baya, ta saƙalo hannayenta a wuyansa tana taɓa ƙirjinsa. Ji ya yi gabansa ya faɗi, cikin lokaci ƙalilan kwanyarsa ta birkice. Hannu ɗaya ya kai ya riƙe hannun, ya bata amsa cikin sanyi,
“Saboda kin cika ɓarna shiyasa na kai ki baya. Amma kuma yanzu na fahimci sabon ɓarnar da kike ƙoƙarin fara yi, ya fi na farkon muni dole dai ki cigaba da zama a gaba Friend.”
Yana jin dariyarta har tsakar kansa. Yana jin wannan dariyar ta tafi kenan har abada. A lokacin da yake karya kan motarsa gidan Alhaji Musa a lokacin ne ya furta, “Allah ya jiƙanki Friend.”
Parking motar ya yi, tare da ciro bindigarsa. Hakan yasa Jabir saurin fitowa ya mara masa baya. Sai dai kuma, tuni Alhaji Mainasara ya kira Alhaji Musa ya gaya masa komai, hakan yasa Alhaji Musa ya tattara ya gudu.
Mujaheed ya tokari ƙofar da ƙarfi kamar sau uku zuwa huɗu, ƙofa ta faɗi kawai ya kutsa kansa, yana faɗin.
“Ko a cikin ƙabari ka ɓuya sai na ciroka nayi maka hukunci. Ka raba ni da Nayla, kake tunanin kayi rayuwa cikin jin daɗi? Ka gama zaman duniyar nan, dole ne ka bi Nayla inda ta tafi.”
Jabir ya dafa kafaɗansa, “Mujaheed kayi haƙuri don Allah. Nayla ta riga ta tafi.”
Dubansa ya yi, kafin ya fizge kansa yana tafiya da baya da baya. Gaba ɗaya ya fice hayyacinsa.
“Jabir baka da amfani a cikin rayuwata. Zai fi kyau ka koma ka ɗauki Jawaheer ka mayar da ita gidanku. Kana ɗaya daga cikin maƙiyana ba zan taɓa ganin farinka ba.”
Da sauri ya juya da nufin ficewa, sai idanunsa suka hasko masa hoton Nayla. Dawowa ya yi gaban hoton mamaki ya ɗaure masa kai.
“Ba dai Alhaji Musa yana son Nayla bane? Idan yana sonta meyasa ya kashe ta?”
A take wani irin kishi ya turnuƙe shi, ya kaiwa hoton duka, “Ƙarya ne! Ni kaɗai nake son Nayla, saboda zuciyata aka halicci zuciyar Nayla. Babu wanda ya isa ya shigo cikinta.”
“Shigasa Allah ya bar maka zuciyarta a raye.”
Mujaheed ya juyo cikin wani irin zafi ya kaiwa Jabir duka, wanda Jabir ya yi matuƙar takan Sa’a ya kauce masa. Tabbas da dukan nan ya sami Jabir da babu abinda zai hana bakinsa fashewa. Wannan karon Jabir ya yi matuƙar tsorata da lamarin Mujaheed, hakan yasa tunda ya samu ya kauce bai sake gigin furta komai ba.
Mujaheed yana ficewa ya kama hanyar maƙabarta.
“Aboki ba zaka mutu ba gaskiya sai na haifi Muhibbat, ita kuma Muhiabbat ta haihu sai ka…”
“Aboki kada ka tafi ka barni.
“Wayyo jini, jini, jini.. Aboki jini.
“Aboki goya min ‘yar babyn nan.”
“Zuciyata ce take min zafi”
“Ina kishinka aboki sai dai ina son dukkan abinda kake so.
“Mata biyu zaka aura a duniya aboki.”
“Abbana ka ba aboki fili kaji?”
“Abbana ka ba aboki haƙuri idan ba haka ba, ba zan ci abinci ba.”
Manyan kalaman Nayla, suka ɗinga bin iska suna fitowa da ƙarfi, ta dai-dai saitin kunnensa suna bayar da wani irin sauti, kamar saukan ƙarar aradu. Tartsatsin da suke badawa me haɗe da haske, su suka taimaka wajen sakin sitiyarin tare da riƙe kansa da ƙarfi yana faɗin,
“Nayla kada kiyi min haka, ki tashe ni daga barcin da nake yi, ki hanani yin mafarkin nan…”
Wani irin hatsari ya yi, wanda ba ƙaramin me sauran kwana ne, zai yi hatsarin nan kuma ya fita ba.
Jawaheer tana zaune ta yi firgigit ta tashi, jikinta yana rawa, tana jan numfashinta da ƙyar. Sake fitowa tayi tana tafe tana tangaɗi kamar wacce tasha wani abu. A ƙofar falon su Mujaheed taja ta tsaya, tana kallon tsanarta a fuskar iyayen Mujaheed.
Hakinta na rawa ta haɗa kalmomin, ta watsa masu,
“Aboki, yana cikin matsala. Wani abu ya same shi.”
“Abbana ina aboki? Abbana ka kira aboki jikina yana bani aboki baida lafiya, don Allah Abba ka kira min aboki. Wayyooo..”
“Dakata kada ki tara min jama’a bari inkira shi. Gaskiya Nayla kina damuna da ke da abokin nan naki, kun isheni sosai.
Firgigit Abban ya yi, tare da ɗauko wayarsa ya na ƙoƙarin neman Mujaheed. Sai dai kiran wayar Jabir, ya riga turo kai, don haka ya ɗauka jikinsa a sanyaye.
“Abba ku taya Mujaheed da addu’a ya yi mummunar hatsari, irin hatsarin da idan har ya rayu, sai ikon Allah.”
Jabir da ke, kuka kamar ransa zai fita, ya sauke wayar yana duban jama’a cikin jajayen idanunsa,
“Ku taimakeni ku sa min shi a mota, kada inrasa ɗan uwana.”
Mutane da yawa sun tausayawa Mujaheed. Shi kuwa Abba da ƙarfi ya ɗinga faɗin, “Innalillahi wa inna ilaihirraji un! Ya Allah na bar komai a hannunka, kayi min maganin wannan masifa da ke tunkaro mu. Ɗauko hijabinki mu je Mujaheed ya yi mummunar hatsari.”
Umma ta ɗinga gyaɗa kai, hawaye suna zuba har cikin bakinta. Ita kuwa Jawaheer tana jin hakan, ta faɗi ƙasa a sume. Gaba ɗaya suka kafe ta da idanu. Idan har da gaske zuciyar Nayla ce a jikinta babu shakka Jawaheer zata iya haɗiyar zuciyarta ma ta mutu. Tausayinta ya karyowa Abba, ya ƙaraso wurinta da sauri yana faɗin a yayyafa mata ruwa.
Tana farfaɗowa ta ja sunansa, “Abokiiii…. Kada ka tafi don Allah aboki. Ka tsaya ka jirani in haifi Muhibbat, itama Muhibbat ta haihu ka ka aurar da ‘yarta. Abba ka cewa aboki ba zai mutu ba.”
Umma ta rushe da kuka, tana kallon zuciyar ‘yarta a jikin wata. Abba ya ɗinga lallashinta yana gaya mata babu abinda ya sami Mujaheed.
Dukkansu suka kama hanyar asibitin da Jabir ya sanar da su suna wurin. Ko da suka iso babu wanda aka barshi ya shiga gurinsa. Likitoci kuwa sun kai biyar akansa, kowanne da irin taimakon da yake badawa.
Ɗaya daga cikin su ne ya gayyaci Abba Office ɗinsa, Jabir ya biyo baya. “Ku kwantar da hankalinku insha Allahu zai ji sauƙi, ba wani ciwo ya ji ba, jinin da ya zubar ne ya gigitaku kuke tunanin kamar abin ya yi tsanani. Sai dai abu me wahala ne Mujaheed bai rasa tunaninsa gaba ɗaya ba. Saboda gaba ɗaya matsalar akansa ne. Don haka zamu jira mu ga farfaɗowarsa. Sai kuma jini da muke buƙata da gaggawa don asa masa.”
Jabir ya miƙe ya fice yana maimaita Losing Memory? Hakan yana nufin zai iya mance kaf abubuwan da suka faru da shi a rayuwarsa? Har soyayyar da ke mayar da shi zararre? Ƙwaƙwalwarsa zata sami hutu kenan?
“Idan hakan zai sa Mujaheed ya sami natsuwa Allah ka mantar da shi komai.” Ya tsinci bakinsa da furta addu’ar nan cikin ƙwarin guiwa.
Jawaheer kuwa ta ƙi ci ta ƙi sha, tana nan zaune idanun nan sun kumbura saboda kuka. Fakar idanun su Umma tayi, ta shige gun Mujaheed.
A ƙirjinsa tayi makwancin tana shessheƙan kuka, “Aboki, aboki ka tashi. Ka ce min zaka tsaya har sai na haifi Muhibbat ɗina, ita kuma ta haifi ‘yarta ko aboki? Idan baka tashi ba zan iya mutuwa aboki.”
A hankali yake jin maganganunta a tsakiyar ƙwaƙwalwarsa, a hankali yake magana yana juya kansa da ke tsananin sarawa , “Naylaaa, Naylaaa!!”
Ya faɗa da ɗan ƙarfi, hakan ya jawo hankalun mutane da dama zuwa ɗakin. Dakta ɗin suka shiga dudduba shi, a yayin da Jawaheer ta koma gefe ta raɓe tana jin sanyi yana sake shigarta. Doctor ya ɗago cikin farin ciki. Ya kira sunansa.
“Mujaheed ɗaga idanunka ka gani su waye wa’innan?”
Mujaheed ya ɗaga kai ya dubi kowa, a hankali ya mayar da idanun ya rufe. Shi kaɗai yasan irin azabar da yake ciki.
Sai da Mujaheed ya yi kwanaki biyu baya um bare um um, kuma yana ji yana iya magana, tsabar tsanar Jawaheer yake sa shi cikin wani irin ƙunci. Ya tsaneta baya sonta baya kuma jin zai iya sonta.
Kusa da shi ta matso, a lokacin da bata san yana ji ba, “Aboki… Ka ce min ba zaka tafi ka barni ba ko? Idan baka tashi ba zan damu, zuciyata tana yi min ciwo.”
Kalamanta sun ƙi daina yi masa kama da na Naylaa. A hankali ya buɗe idanunsa,
“Ke mayya ce? Uban waye abokin naki? Nace ki nesanceni, amma rabon wahala yana ƙara sanyaki kusanto ni. Ki tafi ki bar kaina idan ba haka ba ni zan bar maki asibitin.”
Miƙewa tayi tana girgiza kai tare da ja da baya, “Kada ka tafi, lafiyarka ta fiye min komai a duniyata. Zan nesanceka ka yafe min.”
Haka ta ɗinga ja da baya tana girgiza kanta. Tana fitowa ta ci karo da Abba saura kaɗan ta zube ƙasa, Abba ya kamo ta. Kafeta ya yi da ido yana jin tausayin yarinyar yana ratsa shi.
“Kiyi hakuri Jawaheer. Ki dage zaki iya insha Allahu.”
Abba ya ƙarasa yana duban Mujaheed. Tun bayan da Doctor ya gaya masu Mujaheed ya sami sauƙi sosai, haka lafiyarsa ƙalau Abba ya sami natsuwa.
Abba yana son ya yi masa magana akan Jawaheer, sai dai yana son yaga iya gudun ruwansa don haka ya share kawai ya cigaba da dubansa.
“Mujaheed nima fushi kake yi da ni? Ina kula da kai baka son haɗa idanu da ni. Me nayi ni kuma?”
Mujaheed ya buɗe jajayen idanunsa ya watsa su akan mahaifinsa. Sai dai ya kasa bari su haɗa idanu da shi, “Abbana bana fushi da kai. Abba Nayla tana yawan zuwar min. Abba na kasa mance Nayla dai-dai da minti ɗaya. Don Allah Abba ko bayan babu raina, ka ɗauki fansa akan mutanen da suka kashe min Nayla. Ina son naji dalilin da yasa suka aikata min hakan. Nayla bata cancanta ba.”
Abba ya kamo hannayensa yana dubansa cike da tausayi irin na ɗa da mahaifi. “Babana kayiwa Nayla addu’a tafi buƙatar hakan. Kayi tawakkali da haka akasan musulmin ƙwarai. Dubi can wurin ka gani.”
Mujaheed ya bi hannun mahaifinsa har izuwa wajen windon da yake nuna masa. Bishiyar Gwaiba ce, wata yarinya ke tsunkowa. Dukkansu suka yi murmushi, domin Nayla ce ta faɗo masu a rai. Daga haka ya rufe idanunsa.
*****
Suhaima ce zaune kusa da Jawaheer ta rasa ma da kalmar da zata yi mata amfani da ita. Duk wanda yasan Jawaheer a lokutan baya a yanzu idan ya ganta da wahala ya ganeta. Bata da aiki sai kuka. Idan ta ga zata yi wa kanta lahani ne, sai ta dafa indomie. Yau kwanaki uku kenan da sallamar Mujaheed amma bata taɓa sa shi a idonta ba.
“Jawaheer anya kina da tawakkali kuwa? Ance wacce aka sa maki zuciyarta mace ce me addini. Meyasa a zuciyar aro ba haka bane?”
“Suhaima kenan. Zuciyar aro Mujaheed take so fiye da komai, Mujaheed bai taɓa yi wa Nayla laifi da gangar ba, bai taɓa yi mata kallon banza ba, bai taɓa kwanciya ba tare da ita ba. Yana tarairayarta kamar ƙwai. Labarin Mujaheed da Nayla kamar labarin littafan Hausa. Wanda da yawa ake ganin ba gaskiya ba ne, ake ganin wani abin ba zai faru ba, haka labarin su yake. Ta yaya kike tunanin ranar da ya juya mata baya zata iya barci duk tawakkalinta? Ta yaya kike tunanin zata iya natsuwa idan babu Mujaheed a gefenta? Suhaima duk dare bana iya barci, saboda zuciyar aro ta saba kwanciya tare da shi. Don Allah ki taimakeni don Allah.”
“Zaki iya zuwa gidan malaman tsubbu?”
“Suhaima samo wata hanyar amma banda wannan. Ba zan iya cutar da Mujaheed ba. Hasalima shirka bata burgeni, duk wanda ya yi ƙarshensa nadama ce. Zuciyar Mujaheed zalla nake nema ba aron da malam zai bani ba. Ina shan wahala. Suhaima babu yadda za ayi a sake sauya min zuciyar nan?”
Girgiza kai tayi tana duban Jawaheer, “Idan aka sake yi maki aiki irin wannan sai dai ki mutu Jawaheer. Shawara ɗaya zan baki babu wanda ya gagari Allah, ki kai ƙararsa gun Allah. Ki dage da addu’a wataran sai kin yi dariya. Sai kin ga kamar ba ayi ba. Akwai wata addu’a zan karɓo maki ki dage addu’ar tana dauwamar da ƙaunar mace a zuciyar mijinta.”
Kai kawai take gyaɗawa tana share hawaye. Haka suka yi sallama jikin kowa a sanyaye. Tana nan zaune a falon ya shigo har zata tunkare shi ta tuna kalaman da ya yi mata akan ta nesance shi. Jikinta na rawa ta raɓe tana makyarkyata.
Ko kallonta bai yi ba, ya shige ɗakinsa. Ya sake fitowa zai fita ya dubeta kawai ya yi saurin ficewa.
Yau weekend babu inda ya je yana zaune a falo yana sauya tashoshi. Bai ji fitowarta ba, sai ji ya yi an zauna kusa da shi tare da riƙe hannayensa, “Aboki bani da lafiya zazzaɓi.”
Ta manna masa hannunsa a tattausan wuyanta. Shuru ya yi ba tare da ya iya cewa uffan ba, haka bai daina kallonta ba. A hankali ya zame hannunsa ya cigaba da kallon film ɗinsa.
“Abo…”
“Ke! Idan kika sake ce min aboki sai na cire shegen bakin nan. Tashi ki bani waje tun kafin intattakaki, in watsar da ke a juji.”
Jawaheer ta miƙe ta shige ɗaki da gudu. Ko ta ce ba zata je gunsa ba, sai zuciyar aro tayi ta damunta akan dole sai ta je. Ita ya zata yi da irin wannan masifar?”
Cikin dare kamar ance masa ya dubi sashen da take, yaga wucewar abu kamar mutum. Ƙurawa wurin idanu ya yi yana son sanin shin mutum ɗinne?
Hanyar ɗakinta ya bi, a lokacin da ya ga fitan wani abu kamar mutum aguje. Lokaci daya zuciyarsa ta harba da ƙarfi. Ɗakinta ya shiga yana so ganin ko menene. A zaune ya sameta ta haɗa kanta da guiwa. Idanunsa yakai kan bireziyanta da ke yashe a ƙasa. Shuru ya yi, har zai yi mata magana ya juya kawai.
Indai kuwa hakane, akwai wani abu da ke ɓoye wanda Jawaheer take sane da hakan, amma kuma shi bai sani ba.