Skip to content

Jawaheer | Babi Na Bakwai

5
(1)

<< Previous

Yau garin an tashi da sanyi, don haka dukkan su suna sanye da kayan sanyi, suka kama hanya domin shiga ƙaton kanti domin siyan abubuwan da basu da shi.

Sun yi nisa wajen siyayya, Mujaheed ya ji muryar wata tana cewa, “MD idonka kenan?”

Waiwayowa ya yi, tare da murmushi. Nayla tana gefensa tana dubansu. Hannu ta miƙa masa, alamun su gaisa. Abin mamaki Nayla ta yi saurin janye hannunsa da suka kusa haɗewa, ta miƙa mata nata. “Da ni ya kamata mu gaisa, shi kuma sai kuyi magana da baki, ko Aboki?”

Mamaki yasa ya kasa magana, haka tayi matuƙar ƙoƙari wajen ɓoye abubuwa da yawa da ya hana ta fallasa abinda ke cikin zuciyarta. Sai ma murmushi kawai da take yi. Mujaheed ya yi murmushi, ko yau ya mutu ya ga wata alama da zata iya gamsar da shi Nayla ta fara kishinsa.

Matar bata wani damu ba, suka gaisa kawai suna hirar yaushe rabo. Suna fitowa Nayla ta sunkuya kamar zata ɗauki abu sai kuma ta hau murza idanu. Cikin sauri ya ɗagota yana ƙoƙarin ganin sun haɗa ido, amma ta kasa. Hawayen da ya gani ne yasa ya gigice ya kama kafaɗunta yana tambayar dalilin hawayen.

“Wani ƙwaro ne ya faɗa min a ido, amma ya fita.” Shuru ya yi, kamar zai sake magana sai kuma ya yi shuru.

Kai tsaye suka wuce gidan iyayensa. Ganin Abba yasa ta ware suna ta hira ana dariya. Gaba ɗaya ta hana kowa sakat a gidan. Kamar daga sama suka ji ta ce,

“Abbana su waye iyayena?”

Mujaheed da ke shan zobon da Umma ta kawo masu, ya hau tari da ƙarfi. A gigice ta tashi ta ɗinga buga bayansa tana yi masa sannu. Sai da ta tabbatar ya daina tarin kafin ta sake duban Abba cikin ido, “Abba su waye iyayena?”

Abba ya gyara zama ya miƙo mata hannunsa ta kama. “Mamana meyasa kika yi wannan maganar?”

“Ina hanyar dawowa ne daga Islamiyya Aboki bai zo da wuri ba, wannan malamin da ya taɓa riƙe ni a office dinsa, har aboki ya yi masa duka, shine ya ke gaya min wai ni tsinto ni akayi bani da dangi.”

Nayla tana magana idanunta fes akan Abba. Tunda mutanen gidan suke basu taɓa ganin mace me zurfin cikin Nayla ba. Yarinya ce ƙarama amma da wahala kaji cikinta.

“Nayla tun yaushe ya gaya maki hakan?”

Ɗaga kanta tayi alamun tunani, sai kuma ta ce, “Ankwana biyu. Abba da gaske ne, ku ba iyayena bane, idan ku iyayena ne meyasa kuka yi min aure da Aboki?”

Abba ya yi shuru, daga bisani ya ce, “Nayla ke ce muka haifa Mujaheed ne muka tsince shi. Kuma yasan hakan. Haka ya yi tawakkali.”

Nan da nan hawaye ya tsinke mata, “Abba na barwa aboki iyayena, ku cigaba da ɓoyewa gara duniya ta ce ni aka tsinta. Bana son a taɓa min aboki.”

A hankali ta tashi ta dawo gaban Mujaheed da ya yi nisa a cikin tunani. “Aboki na baka Iyayena kyauta kaji?”

Gyaɗa kansa kawai ya yi, ya miƙe yana jin zuciya tana cinsa. Lalle zai koyawa mutumin nan hankali. Kai tsaye ya kira yaran aikinsa yasa a ɗauko malam Musa akai shi police station kafin ya ƙaraso.

A karo na biyu Mujaheed ya yi wa Malam Musa dukan da aka kasa gane kamanninsa, sannan ya ja masa layi da Nayla. Ya kuma rantse ko kallonta ya sake yi, sai ya tsiyaye masa idanu. Malam Musa ya yi matuƙar tsorata da lamarin Mujaheed haka ya ga wani irin ƙaunar Nayla a cikin ƙwayar idanunsa.

Haka kwana biyu Mujaheed ya shiga tunani me girma, akan zurfin ciki irin na Nayla, hakan ke nuna masa akwai abubuwa da yawa da take dannewa ta kasa fitowa ta gaya masa.

Nayla tana kwance a ƙirjinsa yana chatting, yana gaya mata abubuwan da ke faruwa a duniya. Har ya gangaro kan wani labari da ƙawa ta je kai ƙawarta gidan boka daga ƙarshe aka sako ta. Nayla ta ware ido ta ce, “Aboki, shiyasa naji daɗi bani da ƙawa, kaine ƙawata, kaine komai nawa. Idan ƙawa ta ce zata raba ni da kai, zan iya mutuwa Aboki.”

Ta ƙarashe kamar zata yi kuka. Ya ce, “Wayyo har na hango friend na maidota ƙaramin ɗaki ina wulaƙantata, indaina yi mata magana.”

Hannu ta kai, ta ɗinga dukansa yana karewa, daga ƙarshe ya kamota gaba ɗaya ya maidota ƙasansa. ‘Yan yatsun kafafunta yasa harshe yana lasa a hanakali. Hakan yasa komai ya tsaya mata cak! Tana jin wani abu yana sauyawa a jikinta. A kullum tana tambayar kanta wannan wani irin yanayi ne? Tana son ta tambaye shi dalilin da yasa da zarar ya taɓa ta, shikenan ta dosa fama da mutuwar jiki kenan. Batasan ya akayi ba, har ya dawo saitin kunnenta yana mata magana, cikin wata murya da bata taɓa jin Abokinta da irinsa ba. Hakan yasa ta fara fitar da wani irin sauti, wanda ya sake taimaka masa ya ƙarasa fita hayyacinsa.

A kunne ya raɗa mata irin abinda yake son tayi masa. Babu musu ta kai bakinta inda yake buƙata. Ji tayi yana fidda sauti, a shirmanta ko mutuwa zai yi tayi saurin miƙewa tana jijjiga shi. “Aboki mene ne? Bari inkira Umma.”

Tsura mata ido ya yi, sannan ya jawo ta cikin wani irin kasala yasa hannunsa yana shafa gashin gaban goshinta. Ya ce “Idan kika kira Umma me zaki ce mata? Zaki iya gaya mata ke kika sa ɗanta ya fita hayyacinsa, saboda tsabar sha’awar ‘yarta?”

Sai yanzu ta ankare ta yi saurin rufe fuska. Sai kuma ta buɗe, “Aboki wani abu nake ji idan kana taɓa ni.”

“Wannan shi ne auren friend. Da zaki daure da na nuna maki yadda duk ma’aurata suke yi. Kin cika tsoro da raki ne. Kin amince inyi? Ta haka ne zaki sami Muhibbat muyi ta nuna mata ƙauna.”

Riƙe hannunsa tayi ta ce, “Ka bari sai jibi.” Murmushi ya yi, yana son ganin yaushe ne jibin nan. Yana binta a hankali ne, kasancewar akwai yarinta a tare da ita.

Da sassafe yana barci, ya ji tana tashinsa jikinta na rawa. A hankali ya buɗe idanunsa, “Aboki nayi mugun mafarki zo muje ka rakani muyi sadaƙa.”

Babu musu ya ware idanunsa ya miƙe yasa jallabiya, suka fice. A hanya ya tsaya suka siya waina, suka fito, yana kallonta tana rabawa almajiran har suka gama. Ta juyo ya yi mata murmushi suka shiga mota.

A hanya ne take ce masa ya biya da ita wajen kutare. Haka suka biya ya ciro kudi ya bata, ta ɗinga raba masu. Ta juyo ta rungume shi, “Aboki haka zamu ɗinga yi muyi koyi da Abbana da Ummana ko?”

Kai kawai ya ɗaga mata, suka juyo yana shiri zai je office tana firfita masa shayi.

“Kin ga kinsa na makara ko?

“Sorry Aboki, mafarki nayi wai ansace min kai.”

“Ansace ni sai kace buhun shinkafa?”

“A’a buhun mutum ne fa kai.”

Murmushi ya yi mata sannan ya karɓi kofin ya haɗa da ita ya jawota jikinsa. “Bani a baki, daga yau kin fara aikin lada.”

Babu musu ta karɓa tana bashi ta kwarar masa a jikin kayansa. Salati ya yi da ƙarfi ya miƙe. Nayla kuwa ko a jikinta ta ce, “Ayyah sorry, ka samo tsumma ka goge.”

Bai ce mata komai ba ya koma ciki ya sauya wasu kayan. Ya miƙa mata hannu ta kama, suka fito. Yana shiga mota ta tsaga ƙafafunta ta haye jikinsa tana fuskantarsa.

“Idan ka tafi ko? Kai gaida Ozumba.”

Ido ya ware, yana dubanta, “Wace ce kuma Ozumba?”

“Wannan arniyar.”

Hancinta ya jawo da ƙarfi, wanda yasa tayi ƙara, “Me nayi maka zaka gutsure min hancina?”

“Zan gaya maki abinda kika yi bari indawo.”

“To ka dawo lafiya. Malamin mu ya ce idan miji zai fita muyi masa addu’a, idan ya dawo ma mu godewa Allah. Haka mu ɗinga tuna masu da addu’o’i idan sun mance. Kuma daga yau zamu ɗinga kwana da alwala kariya ce me girma inji malamin mu. Allah yasa ka nemo halas, haramun kuma Allah ya toshe maka idanun ganinsa Sai mene ma?”

Murmushi ya sakar mata ya riƙe yatsunta yana ƙare masu kallo, “Sai kuma yadda zaki bani haƙƙina. Ki tambaye shi banda wa’innan sai mene kuma? Kada ki tambaye shi a gaban ɗalibai za su yi maki dariya. Duk abinda ya gaya maki sai ki gaya min kin ji?”

“Yauwa na tuna wani kuma. Ya ce mu ɗinga tunatar da mazajenmu haƙƙin zumunci. Sai na tuna daga kai har su Abba baku zuwa gidan Baba Ma’aruf. Don haka duk dangi da suke kusa da nesa zan gayawa Abbana, mu shirya muje ko?”

“Haka za ayi Gwanata. Sai a shirya Weekend aje ayi kwana biyu. Maza shiga ki shirya zuwa anjima zan dawo inkai ki makaranta. I love you.”

Rungume shi tayi, ta lumshe idanunta, ita kaɗai tasan meke damunta, “I love you too Aboki.”

Haka ta fito tana ɗaga masa hannu yana ɗaga mata. Ɗaki ta koma tana dubawa me zata yi masa ta burge shi? Ɗakin girki ta shiga tayi masa abinci me rai da motsi, ta haɗa masa zoɓo, kasancewar tasan yafi son zoɓo fiye da komai. Ta shiga wanka tayi ado da ‘yan ƙananun kaya. Zama tayi ta caccaɓa kwalliyar da ita kanta mamakin kanta take yi. Haka ta gyara gashinta ta tubke a tsakiyar kai. Turaren ƙamshi tasa ta turara ɗakin. Hatta zanen gado sai da ta sauya masa. Tana buɗe kaya ta ciro su lafayarta, da kayayyakin da Umma ta haɗa mata wanda turarukan ta ce mata jikinta zata ɗinga turarawa. Ta fito da komai. Itama tana son shiga sahun manyan mata. Tana son mijinta ya ƙara sonta, hakan baya yuwuwa kuwa sai da gyara.

A matuƙar gajiye ya dawo kasancewar wani bincike da suke yi, yana neman ya hargitsa su. Kafe tv tayi da ido, hakan yasa har ya shigo bata sani ba. Mamaki ya hana shi magana, komai ya sauya a cikin gidan. A gabanta ya zube hannayensa. Juyowa tayi tana dubansa, sai kuma kunya ya kamata, tasa tafukan hannayenta ta rufe fuskarta. “Iyye Friend ce ta koma kamar ‘yar turawa? Lalle wannan malami Allah ya saka masa. Abu ɗaya ya rage masa, ya koya mata yadda zata yi babban aiki.”

Tana dariya ta buɗe fuskar ta zuba masa. “Wata a makarantarmu ta ce min tana sonka wai kana da kyau.”

“Sai kika ce mata mene?”

Zaro ido tayi, “Ashe ban ce maka sannu da zuwa ba. Ya su ozumba?”

Kunnenta ya murɗe da ƙarfi har sai da tayi ƙara, “Iyye Friend anfara kishi? Amma naji daɗi sosai.”

“A’a ni bana kishi, naga kuna ta chatting ne.”

“Zaɓe kika fara yi min?”

“Kayi haƙuri idona ne ya gani. “

“To zo muje kiyi min komai yau.”

Binsa tayi tana cewa, “Amma banda wanka. Ni yaushe zan iya ganin babba yana wanka? Walh sai inji tsoro. Masu yin haka ma ina masu addu’a.”

Murmushi kawai ya yi, yana kallonta ta zauna tana jiransa har ya gama kintsawa ya fito. Ƙamshin komai ya sauya a gidan. Ita kanta ƙamshinta ya sauya. Yana fitowa ta kawar da kanta, bai ce mata komai ya zauna yana shafa mai. Ya ce ta ɗan shafa masa a baya. Har zata yi masa musu, ta tuna da wa’azin malamin su, don haka ta karɓa tana shafawa a hankali. Yadda take yi kamar me yi masa waiwayi. Ajiyar zuciya ya ƙwace masa ya miƙe suka nufi dinning. Anan ma ya cika da mamaki bai ce komai ba ya kammala ci, ya ce taje ta shirya ya kaita Makaranta.

Bai san meyasa ba, yana ajiyeta ya kasa tafiya. Yana nan zaune kamar me gadinta. Tana fitowa yaga kamar wata mota tana binta a baya, hakan yasa ya fito ya ƙure motar da idanu. Sai dai me motar yana ganin Mujaheed ya juya ya bar wurin. Da hannu ya nuna mata motar tabi motar da kallo, har sai da ta ɓace masu sannan ta dawo da kallonta kansa, “Waye?”

“Ke zan tambaya idan kin san motar.”

Girgiza kai tayi, “Ni ban taɓa ganin irin motar ba.”

Kai tsaye suka wuce gidan Umma, anan suke gaya masu maganar zuwa zumunci, Abba ya yabawa kaifin hankali irin na Nayla, don haka suka shirya Weekend suka nufi Kaduna. Kwanan su ɗaya suka juya. Dangi na nesa da na kusa duk sai da suka kai masu ziyara.

Ɗabi’un Nayla gaba ɗaya sun sauya, sai ririta Mujaheed take yi kamar ance za a ƙwace mata. Yau suna kwance da misalin ƙarfe biyu na dare, bayan Sallah da suka yi a tare ya ce, “Friend ki gaya min gaskiya. Da gaske baki da kishi?”

“Aboki ina da kishi irin wanda bansan a inda na samo shi ba. Amma kuma ina son farin cikinka fiye da nawa. Na amince inkwana a cikin ƙunci idan har zaka kwana a cikin farin ciki. Ina son duk abinda kace kana so. Ban taɓa ganganci da abubuwanka ba. Ina son duk wanda ya ce yana sonka ko waye. Mata kuma da kake ta gwada ni akan su, nasani, baka kusantar keɓewa da wata mace. A cikin halayyarka nasan wanda zaka iya aikatawa da wanda ba zaka iya ba. Don Allah ka ɗinga yi min addu’a nafi buƙatarsa.”

Murmushi ya yi yana shafa kanta, “Ban taɓa kai goshina ƙasa ba tare da ambato ki a cikin addu’a ta ba. Ada ina jin zafi da naga kamar baki kishina, amma ranar da naga kinyi kuka saboda wata tana son taɓa min hannu na gazgata kina kishina.”

Lumshe idanunta ta ɗingayi barci ya kwashe ta. A kwana biyun nan yana kula da ita, idan suna hira sai barci ya kwashe ta. Ya rasa irin wannan dalilin.

Tare za su fita ta ci lafayarta, ya yi matuƙar yi mata kyau. Zai sa ƙafa ta girgiza masa kai, “Baka yi addu’a ba.”

A tare suka yi addu’ar sannan suka fice fuskokinsu cike da farin ciki.

A yammacin yau ne, ya miƙa mata takardu ya ce ta ɓoye masa, abubuwansa masu mahimmanci duk ya takarta ya bata. Anan ne take ganin komai sunanta ne manne akai, ta ɗago tana dubansa.

Haka a yau ne ya yi mata albishir da zata cigaba da karatunta. Maƙalƙale shi tayi, kafin ta miƙe ta ce bari ta ɓoye masa. Wani ɓuya tayi me nisa, sannan ta ce yazo ya rakata ta zagaye gidan. Dubanta ya yi ya koma ya kwanta, “Nidai ka zo ka rakani. Inzagata gidana, daga nan kuma muje gun su Abba ingaishe su.”

Ganin da gaske rigima take ji ya miƙe ya raka ta, suka yi ta zagaye. Haka suka kama hanyar gidan Umma a ƙasa. Suna tafe suna hira.

“Ka ga idan muka haifi Muhibbat sai ka sata a makaranta mu ɗinga zuwa muna ɗauko ta ko?”

“Ai baki ɗauko hanyar haifota ba.”

“Tam nayi maka alƙawari idan muka dawo. Amma a aljannah zan haifa maka ka yarda?”

Bai damu da surutanta ba ya ɗinga biye mata, don ba yau ta saba ba. Suna isowa gida ta nufi Umma ta rungumeta. Ta jima a rungume a jikin Umma taƙi ɗagowa. Abba yana mata tsiya yana cewa soyayyar ce yau ta motsa?

“Ɗagowa tayi a sanyaye ta ce, “Ku yi min addu’a ku samin albarka, zanyi tafiya me nisa.”

Gaba ɗaya suka ɗago suna tambayar inda zata je. Ta ce, “Makaranta Aboki ya samo min.” Su Umma suka tuntsure da dariya. Da suka zo tafiya tasa rigima sai Abba da Umma sun rako su har gida. Babu musu suka miƙe suna tafe suna hira. A falo suka zauna ta ɗinga jido masu abubuwan ciye-ciye. A ranar shi kansa Mujaheed ya ji dadin kasancewa da iyayensa. Haka da su Umma za su tafi sai da akayi rakiya. Ta ɗinga ɗaga masu hannu cike da nishaɗi.

Suna dawowa ta gyara kanta tsaf, taje ta kwanta a bayansa. Ji ya yi jikinta ya yi sanyi, ya juyo yana dubanta, “Wani abu yana damunki ne?”

Girgiza kai tayi, hawaye suka wanke mata fuska bata bari ya gani ba ta goge. Yadda take shige masa yasa suka sauya salon wasan. Ga mamakinsa yau bata tirje ba, ta ɗinga biye masa da duk abinda ya ce yana so. Sannu a hankali ya cimma burinsa. Tayi juriyar da bai taɓa tunani ba, haka ya ɗanɗani zuma me matuƙar daɗi. Hakan yasa ya sake komawa ga aikata abinda yake jin kamar bai taɓa jin daɗi irinsa ba. A kunnenta ya ɗinga raɗa mata, *You are so sweet. Allah ya yi maki albarka yasa ki gama da duniya lafiya. Kinsanya ni a cikin farin ciki, ba zan taɓa mance ranar yau ba. Allah yasa yau ɗinnan mu sami Muhibbat ɗin mu.”

Ɗaga kanta kawai tayi, ya kaita banɗaki ya yi mata wanka ya dawo da ita. Sai ji da ita yake yana lallaɓata.

Miƙewa ya yi yana duban agogo, ƙarfe goman dare. “Ki jirani bari inje insiyo maki wani abu. Tukuicin da kika bani ba zan iya barci ba tare da kema na faranta maki ba.”

Ƙura masa ido tayi bayan ta kamo hannunsa, “Kada ka tafi ka barni. Zo kaji wata magana.” Dawowa ya yi da baya, ta manne bakin su wuri guda, hakan yasa suka sake komawa. Sai da ya tabbatar da ya gamsu kafin ya zare jikinsa. A lokacin ta gama galabaita. Wanka ya sake yi mata agurguje sannan ya barta tayi wankan tsarki. Ita kanta tana jin yau kamar ta sauke wani nauyi ne me matuƙar girma.

A hankali ya kamo hannunta, a lokacin sha ɗayan dare har tayi, “Dole infaranta maki. Idan na dawo yau babu barci labari zamu yi ta yi ko?”

“Eh ka dawo da wuri. Ina sonka, na yafe maka Aboki. Ina son cikin nan da ka bani yau, zan haifa maka Muhibbat insha Allahu.”

Jawota ya yi ƙirjinsa ya manna mata kiss a goshi yana ƙara sa mata albarka. Tana nan tsaye har ya fice ya tayar da motar ya kuma kashewa ya dawo da baya. “Zo muje tare.”

Girgiza kai tayi, “A’a kayi sauri ka dawo.”

Ficewa ya yi, yana son fara siyo mata irin sarƙar da take yawan yi masa magana, daga can zai shiga Office. Baya son barinta ita ɗaya shiyasa ya ɗinga yin komai cikin sauri.

Yana siyan sarƙar yaji gabansa ya faɗi, cikin sauri ya juya kawai ya kama hanyar gida.

Yana shigowa bai tsaya rufe ƙofar motar ba, ya shiga cikin gida. Sai dai babu Nayla babu dalilinta. Mujaheed ya ɗauki waya jikinsa na rawa ya kira Umma yana gaya mata. Saboda gigicewa kawai ya fita daga gidan yana bin hanya. Abba da ya ci karo da shi ya kamo shi, shima jikinsa na rawa, “Mujaheed ina ka tafi  ka bar min Nayla?”

Bakinsa na rawa ya ce, “Naje siyo mata abu…”

Abba ya ɗauke shi da mari, “Kai shashashan ina ne zaka fita ka barta ita ɗaya? Wani abu ne da yau zaka kasa ɗaukarta ku fita tare? Idan wani abu ya sami yarinyar nan kayi kuka da kanka.”

Abba da Mujaheed fa sun haukace sai kaiwa suke suna komowa. Tuni ya kira ‘yan sanda aka baza matakan tsaro. Umma kuwa kuka take yi da iya ƙarfinta tana jin gabanta tana faɗiwa da ƙarfi.

Ƙarfe biyu na dare Mujaheed ya yi kabbara, “Allahu akkbarr. Sai nazo Nayla.”

Tun daga nan bakinsa ya mutu, haka kowa ya kasa gane inda maganar Mujaheed ya nufa. Umma ta sake sa kuka me ƙarfi. Mujaheed yana kallon Abbansa yaje ya yi alwala, bai ce masa komai ba, haka bai yi wani motsi ba.

“Zaka tashi muyi mata addu’ar kuɓuta kokuwa?”

“Ba zan iya ba Abba.”

Abinda bakinsa ya iya furtawa kenan. Abba ma jikinsa ya yi sanyi, tabbas duk yadda suke son Nayla basu kama ƙafar Mujaheed ba.

Washegari da sassafe Mujaheed yana nan zaune tun bayan Sallar da ta zame masa dole bai sake motsi me ƙarfi ba. Lokaci guda ya zabge. Ihun Maigadi da suka ji ne yasa Mujaheed ya riga kowa isowa Gate ɗin.

Gawan Nayla ce kwance a ƙasa, anyi mata kisan wulaƙanci. Irin kisan da har gobe muka kasa mance shi. A gaban gawanta ya durƙusa a lokacin har mutane sun taru. Tunda Umma tayi tozali da gawan ta kurma ihun da sai dai akaji fadiwanta da ƙarfi. Hannun Mujaheed yana rawa ya kai bisa fuskarta da har idanunta anƙwaƙule,

“Sun kashe ki, sun raba ni da farin cikina. Nayla ki buɗe idanunki ki gaya min waye ya yi maki haka? Nayla ta ce a haka? Abba, zo ka ga Nayla sun kashe min ita, Abba Nayla ce kwance cikin jini. *Naylaaaaaaaaaaa….*” Ya ja sunan da ƙarfi.

A wurin nan babu wanda bai yi kuka ba. Yara da manya kuka suke yi. Nayla me son jama’a yau gata a kwance. Rai ba bakin komai yake ba agun Allah. Idan ya gadama cikin ƙanƙanin lokaci zai rabaka da shi. Abba ne ya yi dauriya ya ce, “Allah ya jiƙanki Nayla. Na yafe maki, baki taɓa yi min laifi ba, na yafe maki Nayla na yafe maki.” Sai kuma ya goce da kuka kamar ƙaramin yaro. Yana duban jama’a yana cewa, “Ku zo ku gani Nayla ce aka kashe. Don Allah ku zo ku gani, ankashe min ‘yata.”

Mujaheed ya miƙe kansa yana wani irin sarawa. Tafiya kawai yake yi bai san inda zai sa ƙafafunsa ba. Ji ya yi wani irin duhu ya gilma masa ya zube agun, zubewa me nisan zango.”

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×