Skip to content

Jawaheer | Babi Na Sha Biyu

5
(1)

<< Previous

Kwance ya sameta, tana kallon sararin samaniya, littafi ne rungume a ƙirjinta. Littafin yake son ya gani don haka yasa hannu zai ɗauka, ya ji hannunsa ya haɗe da ƙirjinta. Ɗayan hannun tasa ta dafe nasa ba tare da ta dube shi ba.

Zura mata idanu ya yi, cikin abinda bai wuce minti ɗaya ba, ya gama nazartar halittarta. Ya ɗan Zame hannun, hakan yasa ta dube shi a firgice. Tana ƙoƙarin tashi ya zabga mata harara.

Can nesa da ita ya zauna a bisa kujera, yana karatunsa. Yana kallonta ta gefen ido yadda take kallonsa. Ya ajiye littafin a natse ya watsa mata wani irin kallo,

“In zo ne?”

Ɗaga kanta tayi alamun eh. Ya ware idanunsa cike da mamaki, sai kuma ya share ya cigaba da karatunsa.

Ganin ba zata daina kallonsa ba, ya miƙe ya fice abinsa. Itama ta bi bayansa tana cewa. “Ni don Allah ka barni kawai inkwana anan gidan.”

Yaso ƙwarai ya bata amsa, sai kuma ga Umma a gabansu. Dubansu tayi tana mamakin yadda akayi har suka shirya haka. Allah kenan. Babu abinda ta ƙosa sama da a haife wannan cikin da ke manne da Jawaheer.

Yau cikin dare yake jin shessheƙan kukanta tana magana, “Waye ya yi min ciki? Meyasa ciki zai bayyana a jikina? A ina na sami ciki? Ya Allah kasa infarka daga mummunar mafarkin da nake yi.”

Jikin Mujaheed ya yi matuƙar sanyi. “Aljanu suna yin ciki ne ya fito a gaske?” Ya tambayi kansa yana waswasi. Zai so ya ga ƙarshen wannan lamarin. Ya Rufe idanunsa yana ambaton Allah, ya aiko masa da mafita.

Kamar a mafarki yake jin takun tafiyar mutum. Ya Buɗe idanunsa yana kallon takun tafiyarsa, har ya fice da gudun gaske. Miƙe ya yi, ya ɗauko bindigarsa ya mara masa baya. Yana kallon yadda ya haura ta katanga, wanda kallo ɗaya zaka yi masa ka gane ƙwararre ne a iya haurawa katanga koda kuwa katangar tafi wannan tsawo. Yaso ya yi harbi, sai dai aikata hakan zai sa maƙota su firgita.

Komawa ciki ya yi hankalinsa a tashe ya buɗe labulen ɗakin Jawaheer. Tana nan kwance rigar barcinta acan gefe. Ya Kauda kansa yana jin yau zai kawo ƙarshen wasan kwaikwayon da yarinyar nan take masa. Ya ji tana kuka tana tambayar wanda ya yi mata ciki, da yake bai da hakkinta sai gashi tun kafin aje ko ina ya gane kwarto take gayyato masa cikin dare, kasancewar bata san yana kwance a falon ba.

Fizgota ya yi, yana huci. A take ɗan zanin ya faɗi ƙasa bai damu ba domin ɓacin rai ya rufe masa idanu. A gigice ta farka tana duban kanta,

“Na shiga uku! Me nayi maka zaka wulaƙanta ni haka? Meyasa zaka yi min tsirara? Duk irin tsanar da kake min ne ya jawo haka? Innalillahi wa…”

Bata kai ga ƙarasawa ba, yasa hannu ya buge mata baki. Hakan yasa ta riƙe bakin tare da fasa kuka mai ƙarfi.

Idanunsa kaɗai da ta duba ta tabbatar da babu lafiya. Haka komai yana iya faruwa.

“Kince baki san wanda ya yi maki ciki ba, uban waye ya fito daga ɗakinki kuma ya cire dukkan kayan da ke jikinki? Idan baki gaya min ba sai nayi ajalinki.”

Kan Jawaheer ya kulle. Bata da buƙatan kare kanta tunda zarginta yake yi. Bata taɓa jin ɓacin rai irin na yau ba.

“Kishina kake yi? Yaushe ka fara kishina? Kai da ba sona kake yi ba, baka damu da damuwata ba, bare lafiyata me zai dameka idan ma kwarton na kawo?”

Ji ya ke kamar ta watsa masa ruwan zafi. “Ke kin yi kaɗan inyi kishinki. Ina dai tausayinki ne kawai kina gidan aurenki kina bin maza! Maganar so kuwa kinsan baki isa insoki ba, haka ba a gidana zaki ɗinga kawo min dattin zina ba. Kuna iya neman wani wurin amma ba nan gidan ba.”

Sa hannunta tayi ta toshe kunnenta tana cigaba da kuka mai ratsa zuciya. Haka ya zare hannunsa daga wuyanta yana mai kauda idanunsa daga barin kallon sassan jikinta.

Ficewa ya yi, a sakamakon ambaton sunan kishin da tayi, shi kaɗai ya ƙwaceta a hannunsa. Da babu abinda zai hana shi lallasata.

Sai dai ko alama Mujaheed ya kasa daina jin zafin da ke narkewa kamar dalma a cikin zuciyarsa. Haka zuciyarsa ta kasa samo masa mafita a ɗan ƙaramin lokacin da ke gudu a zuciyarsa.

“Jabir.” Zuciyarsa ta ambata da ƙarfin tsiya. A gaggauce ya ɗauki wayarsa ba tare da ya yi la’akari da lokaci, ko nisan daren ba. Ya yi masa kira ɗaya, ta tsinke, ana biyun ne ya samu ya ɗauka muryarsa da barci.

“Mujaheed lafiya? Ka duba agogo kuwa? Meke faruwa?”

“Komai suna sake lalacewa Jabir. Ka tashi ka buɗe idanunka zamu yi magana.”

Jabir ya tashi zaune yana jin duk wani barci ya rabu da idanunsa.

“Innalillahi wa inna ilahirraji un. Ina sauraronka Mujaheed.”

Sai yanzu ya tuna bai yi ta ambaton Allah ba, shiyasa ya kasa samun rangwamen damuwarsa.

“Jabir Jawaheer maza take kawo min cikin gida a cikin dare. Yau na ganshi da idanuna, ba zargi nake ba.”

Shuru Jabir ya ɗan yi, kafin ya ce, “Ka kwantar da hankalinka, haka kada ka kwanta zaka yi ta tunani ne, yanzu ƙarfe huɗu har yanzu kana da daman yin Nafilfili kafin mu ga abinda gobe zai yi. Zan zo insha Allahu. Ga Qur’ani nan, maganin dukkan wani masifa ne, zuciyarka zata huta irin wannan zafin.”

Mujaheed ya sauke wayar ya shige banɗaki. Akan dadduma ya zauna har aka kira Sallah. Daman babu alamun barci a idanunsa. Ya fito zai je Masallaci ya ji kukanta. Yadda take rera kukan zai taɓa zuciyar mai sauraro, amma ko duban hanyar ɗakinta bai yi ba.

Bayan ya dawo Masallaci ya shirya kawai ya fice zuwa Office. Allah-Allah yake yi ya haɗu da Jabir, domin yana cikin ɗimuwa.

Jawaheer ta ɗaga waya ta kira ƙawarta Suhaima tana kuka, “Suhaima, Suhaima na gaji da abinda Mujaheed yake yi min. Sun ce ina da ciki, yanzu kuma ya dawo yana cewa wai ina kawo kwarto a gidana. Meyasa zai jefeni da aikata zina? Meyasa?”

Suhaima ta ware idanunta, kamar Jawaheer tana ganinta.

“Ciki? To ke ina kika sami ciki Jawaheer?”

Jawaheer ta sauke wayarta kawai tana shessheƙa. Sai yanzu tayi danasanin tonawa kanta asiri. Amma kuma tana ganin Suhaima mai iya rufa mata asiri ne. Abinda ta sani, idan damuwa tayi wa mutum yawa baya sanin lokacin da yake fitarwa,domin kuwa a lokacin mafita kawai zuciya take nema.

Abinda bata sani ba, tana ajiye waya sharrin ƙawaye, Suhaima ta dannawa Rahama ƙawarsu kira.

“Ke Rahama kin ji wai Jawaheer tana ɗauke da ciki? Kuma miji bai taɓa kusantarta ba.”

Gaba ɗaya suka yi dariya. Rahama ta ce, “Oh yau kuma ina ƙaryar da ake raina mana hankali ba a taɓa sanin ɗa namiji ba? Wacce bata taɓa sanin namiji ba ne, zata iya abubuwan wayewan da Jawaheer take yi? Ni dama kawai kallonta nake yi. Yanzu ya ake ciki?”

Suhaima ta taɓe baki, “Ni ko da take ‘yar uwata kuma ƙawata ba burgeni take ba. Kawai ina biye mata ne da bata shawarwari, amma Walh ban ƙi ta mutu ba. Ga miji mai tsada ɗan gidan babban gida. Ai ina tabbatar maki ba zai taɓa sonta ba. Ke ƙawata neman lambarsa nake yi in aika masa saƙo in ce dama bin maza take yi. Ke har da mata zan ce tana bi domin inƙarawa miyata zaƙi.”

Rahama ta buga shewa, ta ce “Shiyasa nake son ki ƙawata. Daga nan tana ficewa sai incusa kaina kawai ya aureni.”

Anan ma suka sake shewa. Suhaima ta bata amsa cikin dariyar mugunta, “Ƙawata baki da kyau sam! Bari zan sake kiranta inyi mata kalar tausayi domin jin ƙarin bayani.”

A haka suka yi Sallama Suhaima ta ɗinga kiran Jawaheer sai a kira na huɗun ne ta ɗauka sai dai ta daina kukan.

“Kiyi haƙuri Jawaheer kowani tsanani yana tare da sauƙi. Ki gaya min yadda abin yake sai insan hanyar da zamu ɓullowa abin.”

Abinka da wacce take cikin damuwa kuma tana neman mafita? Kawai sai ta buɗa baki da ninyar bata labari. Daga can ta ji muryar mijin Suhaima yana magana da ƙarfi.

“Amma Suhaima kin ji kunya! Jawaheer ɗin kike son cin amanarta? Ina tsaye ina jikin kina gayawa Rahama matsalar da Jawaheer take ciki har kina dariya…”

Ƙit! Ta ji ankashe wayar, wanda hakan yasa ta ɗan firgita. Hawaye ɗaya bayan ɗaya ke sauka a fuskarta. Ɗabas! Ta koma ta zauna.

“Suhaima?” Ta maimaita kiran sunanta a karo na babu adadi. A take ta fara tuna irin taimakon da tayi wa Suhaima tun bata da ko sisi, da irin gwagwarmayar da tayi akanta. Hatta mijinta Aliyu ita ce ta yi tsaye akansa. Daga baya ne ma ta ɗan janye. Yau sakayyar da zata samu kenan?

Abinda bata taɓa tunani ba, haka bata taɓa zato ba. Kuka take yi da iya ƙarfinta. Mahaifiyarta ta kira ta gaya mata komai. Shuru Mom ɗin tayi daga bisani ta ce,

“Kin yi kuskure. Samunki kaɗai zaki gayawa maƙiyi shima saboda ya mutu ne, ba wai rashin nasararki ba. A duk lokacin da kika cewa ƙawa kina cikin matsala, kina rabuwa da ita zata yi maki dariya tayi tunanin ke banza ce mara sirri. Amma idan kika bayyana mata samunki, zata kasa barci zata je tana gayawa duniya ashe haka kike samu? Daga nan zata ɗaukaka darajarki ba tare da tasan hakan take yi ba. Mahaifiyarki ita ce wacce zaki gaya mata matsalarki, ta share maki hawaye ba tare da ta bari kowa yaji ba, bare har kuma wataran tayi maki gori. Ina fatan yanzu kin sami darasi?”

“Eh Mom. Abinda yasa ban gaya maki ba, saboda bana son ku raba ni da shi.”

Mom ta jinjina kai, sannan ta ce, “Kada ki damu, ki cigaba da addu’a. Akwai shawarar da zan baki zaki ɗauka?”

“Insha Allahu.”

“Ki dage da addu’a nima zan cigaba da yi, ya fi na da. Haka kuma ki daure ki fita hanyar Mujaheed. Ki daina shige masa, ki daina nuna damuwa akansa. Ki daure nasan akwai wahala amma ki dage kin ji?”

“To mom zan dage insha Allahu.”

A ƙalla Jawaheer ta sami sauƙin abubuwan da take ciki. Haka ta bar mahaifiyarta a cikin tunani mai zurfi. Lamarin Jawaheer yana cigaba da bata tsoro.

A can ɓangaren kuma Suhaima da mijinta, tana kashe wayar ta haɗa rai ba tare da ta iya cewa komai ba.

“Ki ji tsoron Allah Suhaima. Idan kika ce tukunyar wani ba zata yi tausa ba ina tabbatar maki naki ko ɗumi ba zata yi ba. Ki ji tsoron ranar da sharrin da kike ƙoƙarin aikawa wani ya dawo kanki. Kafin auren Jawaheer ya mutu ƙila naki ne zai fara mutuwa. Ke duk abubuwan da kike yi baki gani? Zaki kwashe sirrin Jawaheer kina gayawa wacce babu alaƙar fari a tsakaninku bare na baƙi? Tsabar iya gulma ko? To ki jira ranar da naki asirin zai fasu.”

Ya ja tsaki ya fice. Ta murguɗa baki, ko a jikinta haka babu nadama a tare da ita. Babban burinta ta wulaƙanta Jawaheer.

Wannan kenan.

Mujaheed ya kasa zaune ya kasa tsaye. Da ya ji Sallama sai ya yi tunanin Jabir ne. A wannan lokacin ogansa ya shigo yana tambayarsa wasu file, da tuntuni suke gurin Mujaheed, a lokacin anbar case ɗin, yanzu kuma ansake tada case ɗin. Yana gama bayaninsa ya fice abinsa yana roƙonsa ya kawo su. Ya zama dole ya koma gida, ya tambayi Jawaheer tunda zuciyar Naylaa yake tare da ita, yasan zata iya sanin inda suke. A gaggauce ya bar Office ɗin ya kama hanyar gida cike da saƙe-saƙe.

A ƙofar ɗakinta ya ji kamar alamun motsin mutum, hakan ya tashi hankalinsa, haka kuma idan tunanin da yake yi gaske ne, a yau zai iya kama ko waye kenan.

Abin takaici ko kafin Mujaheed ya shiga, har mutumin ya bi ta windo ya fice a gujen gaske. A lokacin kuma Jawaheer ta fito tana goge jikinta da tawul ɗin da ta fito wanka da shi.

Mujaheed ya kafe kanta da rinannun idanunsa, yana duban yadda ta jiƙa gashin kanta. Kauda kanta tayi a karo na farko, ta danne zuciyarta daga barin yi masa shisshigi.

Zuciyarsa ke gaya masa kawai ya rabu da jawaheer ko zai ji sauƙi a cikin zuciyarsa. Dole yana da buƙatar lallaɓata ta bashi files ɗin da yake da tabbacin tasan inda yake. Kusa da ita ya matso, hakan yasa ta fara zazzare idanu gabanta yana cigaba da faɗiwa. Rintse idanu tayi da iya ƙarfinta ƙafafunta suna rawa.

“Zaki iya tuna inda files ɗina suke?”

Shuru tayi, tana sauke ajiyar zuciya. A hankali kuma ta ji tsoron ya gudu, don haka ta gyaɗa masa kai. Hanya ya bata alamun ta wuce ta ɗauko masa. Bata fita ko ina ba, ta durƙusa wani lungu ta ɗaga wasu kaya sai ga files ɗin. Shi kuma gaba ɗaya ya gama lalacewa a kallon cinyoyinta. Idan har zai cire ƙiyayya yasan Jawaheer ta cika ko ta ina. Zuciyarsa ta cigaba da azalzalarsa akan kwarton da take kawo masa gida. Tana miƙa masa ya dubeta sosai, “Ina sake ja maki kunne ki daina kawo min ɗan iska gida, kina aikata abinda kika gadama. Nan gidana ne, ba dandalin karuwai ba. Ki kuma gaya masa yazo ya ɗaukeki da cikinsa da ke jikinki ku bar min gida.”

Jawaheer ta dafe kanta hawaye ya cigaba da ambaliya a dakalin fuskarta, “Ni ce karuwa? Meyasa kake jifana da dukkan wasu kalaman ɓatanci da suka zo bakinka ne? Meyasa? Allah shi ne shaidata ban taɓa…”

“Ya isa haka don Allah! Cikin jikinki a ruwa kika sha? Waye kuma yake yawan shigowa ɗakinki? Ko wannan ma duk ƙarya ake maki? Yanzu waye ya fice ta windo?”

A gaggauce ta dubi windon, babu ko shakka anbuɗe windon, wanda ita a rufe ta barshi. Haka ta sani sarai Mujaheed ba zai faɗa abinda bai gani ba. Bakinta ne ya mutu, hakan yasa ya sake gazgata abinda zuciyarsa ta hasko masa. Ya Juyawa cikin jin ɗaci haka zuciyarsa kamar zata buga saboda ɓacin rai.

Jawaheer ta durƙushe ta fasa kuka mai ƙarfi, tana jin ɗaci akan abubuwan da suke faruwa da ita. Ta tsani ana dangantata da abinda bata ji ba,bata gani ba. Haƙiƙa babu abinda ya kai sharrin zina ɗaci. A wannan karon bata buƙatar shawarar kowa, ta yankewa kanta samowa kanta mafita tun kafin buɗe sirrinta ya jawo mata aikin danasani.

Da ƙyar ya iya tuƙa kansa har ya iso ofishin, ya miƙawa ogansa files ɗin ya wuce office. Da shigowarsa ya sami Jabir zaune yana karatu. Suka Miƙawa juna hannu, sannan Mujaheed ya zauna yana tambayarsa lafiyar su Umma.

Jabir ya zura masa idanu kawai, ba tare da ɗaya daga cikin su ya sake furta komai ba.

“Mujaheed lafiya kake kuwa?” Jabir ya katse shurun da aiko masa da tambaya.  Sai da ya ɓata lokaci sannan ya dubi Jabir ya ce, “Jabir yarinyar nan kwarto take kawowa gidana. Ni na ga fitarsa har kusan sau uku. Jabir babu mafitan da ya wuce inrabu da yarinyar nan.

Jabir ya sake watsa idanunsa a cikin na Mujaheed yana sake karantar irin tashin hankalin da yake ciki. “Mujaheed idan ranka ya ɓaci ka ɗinga sako addu’a kafin komai, kai kanka zaka fi samun natsuwa. Ina son kafin ka yanke hukunci ka ɗinga tsananta bincike. Binciken nan dai aikinka ne, ba sai Jabir ya koya maka yadda zaka aiwatar ba.”

Mujaheed ya bugi teburinsa da ƙarfi ya ce, “A’a Jabir! Ana bincike ne akan abinda baka gani ba, ba wai abinda idanunka suka gane maka ba. Meyasa zan wahalar da kaina wajen yin bincike bayan naga abinda nake nema? Jabir mu ɗinga yi wa kanmu adalci mana. Na gaji da wannan wasan kwaikwayon. Ina ka taɓa ganin mace da ciki ba tare da tayi tarayya da wani ba? Ko kana nufin a ruwa tasha?”

Jabir ya zura masa idanu kawai yana duban yadda ya fusata. Don haka ya daina yi masa magana har sai da ya tabbatar da ya gama sannan ya miƙe, “Ina ganin babu amfanin zuwana tunda ba zaka saurareni ba. Amma ina tabbatar maka akwai dai wani abu da ke faruwa wanda har yanzu ka kasa kwantar da hankalinka bare har ka fahimta. Fushi da zuciya sun taru sun hanaka aiwatar da abinda ya kamata. Na tabbata yau idan Naylaa tana raye hakan ya faru da ita, ba zaka taɓa juya mata baya ba, hasalima cewa zaka yi fyaɗe akayi mata. Ina sake baka shawara ka ɗinga kyautata zato agun ‘yan uwanka musulmai, ta hakane zaka ɗinga fahimtar komai cikin sauƙi.”

“Assalamu alaikum.” Wata muryar mace ta kwaɗa Sallama. Daga Jabir har Mujaheed ita suke kallo. Ran Mujaheed ya sake ɓaci. Bai san meyasa Safina take ɗaya daga cikin jerin mayun ‘yan matan nan ba.

“Me kika zo yi anan? Iyye?” mujaheed ya buƙata a fusace.

Jabir yana tsaye bai ce masu komai ba, har lokacin da fuskar Safinar ta bayyana tsoro ƙarara, haka ta kasa ƙarasowa.

“Dama nazo ingaisheka ne.” Safina ta dawo masa da maryanin tambayarsa.

Da hannu ya nuna mata hanyar fita, “Na gode kina iya tafiya. Kada ki sake dawowa, na gaya maki kada ki sake dawowa. Idan kika dawo sai na rufe ki a cell. Kada ki ce ban gaya maki ba.”

Sum-sum ta fice tana satar kallonsa.

Jabir ya juya zai fita, Mujaheed ya dakatar da shi.

“Jabir tsaya mu samo mafita. Ba zaka gane abinda nake ji bane, sai ka tsinci kanka a irin halin da nake ciki.”

Jabir ya dawo yana dubansa, “Shawara ɗaya zan sake baka, ita ce ka sake tsananta bincike, na tabbata zaka zo ka gaya min.”

Mujaheed ya amsa masa kawai, ba don ya yarda da Jabir ba. Haka suka cigaba da tattaunawa, akan case ɗin Alhaji Musa.

Next >>

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×