(Gidan Aurena )
Tsananin azabar yunwa ta kusan wuni biyu babu cin abinci,yasa taa zube jikin bishiyar mainar dake tsakar gidan tana maida numfashi,kallon Tirtsetsan cikinta d’an kimanin watanni bakwai tayi wanda wani yayi tunanin ya kai wata tara saboda girmansa .
Hawaye na silalowa daga kyakyawar farar fuskarta, kimanin wata biyu kenan rabon da ko ‘kwayar giro ta fito daga hanun Mijinta Malan Suwid’i, ya basu suci a matsayinsu na Iyalansa,ba kuma ita kad’ai yakewa haka ba harda abokiyar zamanta Lubabatu wadda ta kasance itace Uwar gida. Ita inda Allah ya temaketa ‘Ya’yanta duk sun kawo ‘karfi, sukan temaka wani lokacin su siyo kayan abinci su kawo aringa dafawa duka gidan. Sai dai da ya ‘kyalla idano ya gani sai yabi dare ya kwashe, a nemesu a rasa.
Ba kuma dan bashi dashi ba sai dan kawai zalinci irin na wasu Mazan,ba kuma wannan ne karo na farko da yake hanasu abinci ba ko kuma ya tsallake ya bar gidan ba tare da sun san inda ya tafi ba.
Ganin haka ‘Ya’yan Lubabatu suka koma siyawa Mahaifiyarsu su zuba mata a d’akinta, a cewarsu ta ringa dafawa tana bawa Jiddo da Yaranta ko ba yawa.Itama dake me ba’kin hali ce sai ta dafa ta hanasu ko ‘Ya’yan bata bawa.
Wannan dalili yasa wasu daga ‘Yan uwa da abokan arzi’ke fahimtar halin da suke ciki ita da Yaranta,suka fara temaka musu ba tare da sanin Malan Suwid’i ba.
Lokacin da Malm Suwid’i ya farga da ana shiga da abinci gidansa daga ma’kota ‘kwafa yayi yaci gaba da aikin Tsubace-tsubacensa.
‘Bangaren Jiddo kawai gani tayi duk wad’d’anda suka fara temaka mata Ma’kotanta sun dena bataji haushinsu ba ko ganin laifinsu dan dama tasan mudi Malan Suwid’i ya gani bazai ƙyalesu ba.
Duk yanda Yayanta Ahamad yasu ya nema mata ‘Yanci ya rabata da Auren Maln Suwid’i abun ya gagara dan da kanta take saka kuka ta nuna nan Duniya babu wanda takeso sai Malan Suwid’i,wannan dalili yasa kowa ke fad’in ba haka ya barta ba.
A yanzu duk wasu dabaru da ta keyi sun ‘kare,jarin siye da siyarwar da take wanda Ahamd Yayanta kan saka mata lokaci zuwa lokaci,wannan karon takai babu sun cinye.
A yau ta wayi gari ko Yaran ma bata samu ko Koku ta basu ba, sai Asma’u da Abdull ta tura Gidan Hajiya Mariya Da ake rabon Abincin sadaka su karb’o ko sa samu abinda zasu sawa cikinsu,hawayen idanonta ta share tana me adu’a a ranta na Allah ya kawo musu d’auki na halin da suke ciki….
“Ammey yunwa zata kashemu,Ammey wai da gaske Baba Malan shine Baban mu?”
Muryar yarinya wadda ba zata wuce shekara ta’kwas A duniya ba ta katse mata tunani.
Kamo hanun yarinyar tayi ta zaunar da ita kusa da ita, d’ayan hannunta dafe da cikinta cikin sanyin muryar ta ta cije le’benta na ‘kasa sakamakon ciwon da cikinta ya keyi ta ce”Zainab Malan shene Babanku mana kuma yunwa ai bata kisa sai kwana ya k’are.”
“Ammey amma dai Baba baya son mu ko,tunda kullum baya bamu abinci, gidan su Ilham Babansu kullum sai ya kawo musu abinci’ idan naje Mamar Ilham har zuba min take.”
“oh ni Jiddo Zainab bana hanaki Irin wannan maganar ba Babanku yana sonku kuma kuyi, tayi masa adu’a Allah ya bud’a masa ya dinga kawo wa ana dafa muku kinji!”
“Taff! Ammey d’azu fa ina ganinsa yana cin nama a d’qkinsa na soru bayan tafiyar ba’kinsa amma be bani ba,sai ya ce na tafi na bashi guri. Ammey indai na girma nayi kud’i zanna siyo miki buhun abinci kiyi ta dafawa kamar yadda Yaya Faruq d’in gidan Liman yake yi”.
Murmushin ‘karfin hali tayi cikin kaw da zanchan ta ce “kin ga le’ka waje ki gani ko Yayarku da Abdull sun tahu,yau sun dad’e da yawa”
tashi tayi ta nufi hanyar waje tana fad’in “Toh Ammey”
Cikinta da yake ta motsi ga ciwon da yake ta k’ara dafewa tana maida numfashi da k’yar, jin ‘kirjinta ma na neman fara ciwo ta fara adu’a a ranta na Allah ya kawo musu d’auki na wannan hali da suke ciki.
*****
Lubabatu ce ta fito daga d’akin girki hanunta d’auke da roba da abinci a ciki sai turiri yake jallof d’in shinkafa da wake ce harda kifi sai k’amshi take, wucewa tayi ta gaban JIDDO ta ajiye robar kan tabarmar dake ‘kofar d’akinta,ta zauna tana ‘Kwalawa ‘Yarta Salma sa’ar Asma’u kira fitowa tayi a d’aki tana mi’ka ta ce”Umarmu me muka samu ne kike ‘kwalan kira hak……!” Sauran maganar ta ce ta ma’kale ganin kwanon abinci gaban Umman tasu yana turiri,zama tayi tana cewa”Allah ya bar mana ke Umarmu shiyasa nake ‘kara sonki,kina kulawa da cikinmu yadda ya da ce”.
Dariya Lubabatu tayi tana ce wa”Ai Allah ya yiwa su Harisu albarka,dan’ banda Allah yasa ina da su haka zan dauwama gidan mamaguncin wannan Uban naku da be san ya sauke nauyin ha’ken Iyalanshi ba.”
“Amin Ummarmu amma wallahi ni har mamakin Baba nake yadda yake zabga Uban rawani ga wani k’aton Charbi,Mutane suyi ta layin zuwa gurinshi,inya zauna kan buzu kamar na Allah.ko da yake wasu suna cewa aji fad’ar Malan kar aduba abinda yake aikatawa,amma dai kam gaskiya Baba Allah sai ya kamashi in be sauya hali ba”.
Salma ta kai ‘karshin maganar tana kai laumar abinci bakinta.
“Duk Macen da tace sai shi ai ita ce a wahala” Lubabatu tayi magana tana wurgawa Jiddo harara.
“Kai Ummarmu wallahi nima nafara yarda da ba haka Baba ya kyale Ammeyn Asama’u ba,ni yasin tausayi take bani ki duba kiga yanayin da take ciki! Ummarmu dan Allah ko iya su Asama’u ne ki ringa bawa abinci ko ba yawa,abincin sadaka fa yanzu suke zuwa kar’ba”.
Tunda Salma ta fara magana ta dakata da cin abincin ta saki baki tana kallonta,cike da masifa rai ‘bace ta ce”Ah, babu shakka Salma tunda ni ce na ajesu ai dule kice na ringa basu abinci, to bazan bayar ba in mutum ya gaji ya cika rigarsa da iska mana, ko gaya akayi mu bayinta ne da zasu ringa yi man wahala tare,toh wallahi kika kuma yimin wannan batun halin Ubanki zai ja miki mitsuuu”.Lubabatu taja tsaki tana wargawa Jiddo harara kamar Idanonta zasu fad’o.
“Umma Allah ya baki ha’kuri, amma Dan Allah ki dena zagin Baba,ko mai lalacewarsa Babanmu…..”
‘Bamm dukan da Lubabatu ta kaiwa bakinta yasa ta kasa ‘karasa maganar da ta fara.
Lubabatu ta inda ta shiga ba tanan take fita ba fad’i take “Salma na ‘kara fad’e kin ci Ubanki, yoh! Uba kuma dama ai dole ku kirashi Ubanku,tunda ba’a Sauyawa tuwo suna. Zagi kuwa ko kin’ki ko kinso dole a zagi Ubanku,in ni ban zaga ba wasu zasu zaga’bare ma ni ban ta’b’ba zagin Suwid’i ba duk rashin tausayin da yake yi min.
banda k’addara me zai zaunar da Mace gidan Suwid’i mitsssi….”ta saki Uban tsaki tana ci gaba da mita.
*****
Jiddo, ‘kamshin abincin da Maman Harisu (Lubabatu) ta zuba suna ci da Salma ya dad’a hargitsa min cikina wata sabuwar yinwa ta dad’a tasu min,tun tana girkin yawuna ke tsinkewa, ciwon da cikina yake be hanani jin hirar sa suke ba har na fara murna Jin Salma na yin maganar ko su Asma’u Lubabatu ta ringa bawa abinci, adu’a ta Allah yasa ta yarda jin maganar bata kar’bo ba da irin hararar da Lubabatu ke jefa min ya sani had’iye yawu mu’kut, cikina na kuma dafewa ina ambaton Sunan Allah,yin’kurawa nayi na tashi da k’yar d’akina na nufa ina d’aga k’afafuna da k’yar wad’d’anda suka d’ashe suka kumbura saboda rashin wadatacen jini,ina gaf da shiga d’akina hajijiyar da nake ji ta ‘karu na fara gani Bibiyu.
Laluben bango na farayi saboda hajijiyar ta fara fin ‘karfi na luuu najini gaba d’aya na tafi nayi baya.
Shigowar Asma’u da ‘Yan uwanta suka hango Ammeynsu zata fad’i da gudu suka nufeta,gudunsu yasa Salma da kanta ke k’asa tana hawaye saboda sababin da Lubabatu ke tayi mata kallon inda suke da gudu itama ta tashi tana nufar k’ofar d’akinsu dan ta fisu kusa da gurin a tare suka tarota tana gaf da kaiwa ‘kasa, dukansu suka zube a gurin sakamakon saki da jikin Jiddo yayi Asma’u ce ta fara kuka tana Jijigata “Ammey dan Allah ki tashi karki mutu,Ammey kinga abincin dana kar’bo mana ki tashi mu ci kinji Ammey!’
Asma’u tayi maganar tana ci gaba da jijigata.
Lubabatu ganin sun zagaye ta dukansu suna kuka k’irjinta yayi wata iriyar bugawa hango kamar Jiddo bata motsi yasa cikinta ya bada wani irin sautin “‘koolululuu!” wani tunani da yazu kanta yasa ta nufi gurin da sauri randar ruwansu ta fara zuwa ta d’ibo ruwa a ranta tana fad’in “Suwid’i baza kaja mana masifa ba yanzu in Jiddo ta mutu a gidan nan ai mun shiga uku, dan wannan Basamuden Yayan nata bazai barmu ba”.,Ajiye kofin ruwan tayi ta ce”kunga kuka ba shine mafita ba Asama’u matsa mugani ko suma tayi”matsawa Asma’u tayi gefe tana cigaba da kuka. Lubabatu zuba mata ruwan tayi a jikinta amma shiru bata ko mutsa ba cikin tashin hanakali Lubabatu da cikinta ya ‘kara bada sautin “‘kuuuu” muryarta har rawa take tace “Sal….Salma le’ka waje gurin Malan ki fad’a masa ya temaka yazu Jiddoo ta Mutu” Lubabatu tayi maganar, tana rushewa da kuka.
Asma’u da ‘kanenta ne suka fasa wani sabun kuka jin abinda Ummansu Salma ta faɗa…