Bismillahir Rahmanir Rahim
Falo ne ɗan madaidaici mai ɗauke da kayan alatu dai-dai karfi, dai-dai misalin rufin asirin mazauna gidan.
Ƙarar fanka ce ke ta shi a cikin falon kaɗan-kaɗan, hakan kuma bai hana tsinkayo maganar wata Dattijuwar mata ba, da ke zaune kan ɗaya daga cikin jerin kujerun da suke kewaye a falon, daga wajen ƙafafunta a ƙasan carpet wani matashin saurayi ne zaune a, duka-duka shekarunsa ba za su haura ashirin da takwas ba, a ido kuwa zaka yi tunanin bai kai hakan ba, sabida zubi da tsarin tsamurmurin jikinsa dai. . .