Skip to content
Part 3 of 10 in the Series Jini Ba Ya Maganin Kishirwa by Qurratul Ayn Salees

Sakinah ta share hawayen da ke zuba kan kuncinta kafin ta ce.

“Insha Allahu Umma zan yi aiki da dukkan abin da ki ka umarce ni da shi da yardar Allah, ba zan taɓa baki kunya ba.”

“Yauwa Sakinah Allah ya yi miki albarka.”

“Amin.”

Sakinah ta amsa, ya yin da Umman ta cigaba da faɗin.

“Kin yi waya da Yayanku kuwa? Ya ce min sun kusa dawowa mu taya shi da addu’a.”

“E ya kira ni jiya, ya ke faɗa min cikin satin nan zai kammala HND ɗin sa, zasu dawo gida amma bai faɗa min ranar da zasu dawo ba, wai ba zata zai yi mana.”

“To Allah ya ba da sa’a, ya dawo mana dasu lafiya.”

“Amin Ummata, a gaishe min da Abba da su Sajjad idan ya ta shi.”

“Za su ji insha Allah, a cigaba da hakuri dai Sakinah.”

“Insha Allah Umma nagode.”

Kusan a tare suka kashe wayar, Sakinah ta ajiye wayar gefan inda take zaune kan gado, fuskarta wasai da dukkan alamu ta ji daɗi matuƙa kan wayar da su kayi da Ummanta, sosai ka so goma daga cikin ashirin na damuwarta ya kau, hakan ne ya sanya nan ta ke ta ji ƙarfin gwiwar ya zo mata ta miƙewa tare cigaba da ayyukanta.

4:30pm

Ƙarfe huɗu da rabi ta kammala dukkan gyaran ɗakunan su har zuwa falo ta sanya turaruka masu daɗin ƙamshi da jan hankalin dukkan wanda ya shaƙesu, kicin ta faɗa domin ɗora musu sanwar dare abincin da Kamal yafi so da ƙauna ta ɗora jallof ɗin shinkafa da bushashshen kifi, ta yi mata haɗi na musamman, ba ta damu da haɗa lemo ba domin ba kasafai yake shan na haɗawa ba yafi son na kwali.

A gurguje ta kammala ta ɗauko kula ta zuba masa ta zubawa Hajiyarsa, ta gyare gurin tsab sannan ta koma ɗaki domin yin shirin wanka.

Cikin mintuna talatin da biyar ta kammala ta yi kwalliyarta cikin atamfa Hitarget yaluwa mai ratsin ja da baƙi riga da siket, sun mata kyau sosai duk da cewar ba wata kwalliya ta yi wa fuskarta ba, babu laifi Sakinah kyakkyawar maca ce, dukkan wani cikar halitta na matan hausa Fulani ta haɗa, maca ce son kowa ƙin wanda ya rasa, gata ko da yaushe fuskarta sake shiyasa ba lallai ne ka gane tana cikin damuwa ba in dai ba abin ya yi tsamari ba.

Kular abincin Hajiya ta ɗauka tare da sanya takalmi mai kamar silifas ta nufi ɗakin Hajiyar, da sallamarta ta sanya kai cikin falon, Hajiya dake zaune kan carpet a falon ta ɗago kai tare da amsa sallamar.

Sakinah ta ƙara so gareta haɗe da durƙusawa ta ajiye kular abincin a gefe, kafin ta gaishe da ita, Hajiyar ta amsa gaisuwar fuskarta wasai alamun jin dadin ganin Sakinah ya wanzu a kana fuskarta.

Maganin ciwon ƙafar Hajiya da ke riƙe a hannunta ta kalla tana faɗin.

“Kawo na shafa miki Hajiya, Farida bata dawo ba kenan?”

“E ta ce min zata biya dubo Husnah bata da lafiya.”

“Allah sarki Allah ya bata lafiya, yasa kaffara zazzaɓi ne ko?”

Sakinah ta yi tambayar tana mai amsar maganin ta fara shafawa Hajiyar tare da ɗan danna mata ƙafar dan ta ji daɗi.

“Kin san ciwon yanzu baya wuce maleria, abin sai addu’a ga zazzaɓin da nacin tsiya sai ya tafi ya dawo.”

“Wallahi kuwa Hajiya, ɗazu muka yi waya da Umma ma, ta ce a gaishe da ku, Sajjad ma yana kwance amma ta ce min da sauƙi sosai.”

“Allah ba shi lafiya, ciwon ya tashi kenan?”

“E wallahi?”

Hajiyar ta ɗan gyara zamanta kaɗan kafin ta cigaba da faɗin.

“Ai yaron na fama da jiki wallahi, sikila sai addu’a ciwo mai wuyar sha’ani ga wahalar da mutum.”

Sakinah ta ɗan yi murmushi, ba tare da ta ce komai ba, Hajiyar ce ta cigaba da magana.

“Sakinah ki yi haƙuri akan halayyar Kamal, ni kai na bani da yanda zan yi ne, dole ce ta sanya na amince da auren nan domin gudun abin da gobe zata haifar.”

“Babu komai insah Allahu Hajiya.”

“Da komai fa Sakinah..! ka da kiyi zargin laifina ne da ban hana shi ba, sanin kanki ne ya sauya matuƙa cikin kwanakin nan, ina tsoron ka da kafiyata akan ƙin yarda da auren ta sanya ya faɗa wata harkar ta da ban domin biyan buƙatarsa, na amince da auren Kamal ne dan ka da ya jefa kansa ga halaka, akan abin da bai taka kara ya karya ba, gara na amince ya yi auren akan na hana shi ya biyewa sharrin sheɗan da zugar zuciya ya kaucewa hanyar data da ce.”

“Da a ce yau jinina yana aikata mugun saɓo musamman zina, Gara a ce yau gudan jinina ya auri sa’ar kakarsa Sakinah, domin zina bashi ce, ba kai da ka ke aikatawa ake gujewa ba, ka jajawa wanda bai ji ba bai gani ba shi ake gudu, nasan Kamal na zalintarki domin ina hankalce da dukkan  abin da ke wakana agare ku, amma ba ni da yanda zan yi ne, ba ni da abin da  zan iya yi a halin yanzu wanda ya wuce addu’ar Allah ya dawo da shi hanya, ya sa ya gane gaskiya, kema ina roƙonki da ki da ge da addu’a Sakinah, addu’a makamin mumini ce kuma bata taɓa faɗuwa ƙasa banza, wata rana sai labari, nasan kina haƙuri amma ki ƙara akan na da kin ji.”

Sakinah ta yi murmushi daidai sanda take rufe kwalbar maganin Aboniki ɗin, ta ɗago kai ta dubi Hajiyar kafin ta sauke su ƙasa tana faɗin.

“In Allah ya yarda Hajiya zan yi aiki da shawararki a gare ni, nagode sosai da tunatar wa.”

Nan dai suka cigaba da hira jefi-jefi, yawancin hiran duk akan  tausar Sakinah ne Hajiyar ke yi tare da bata baki, haka ne yasa sosai Sakinah ke matuƙar son mahaifiyar Kamal da bata girma matuƙa, domin ita ba suruka ta dauki Sakinah ba ta ɗauke ta ne tamkar ‘Yar data haifa a cikin ta.

*****

Kamal ba su yi sallama da Hajiya Shema’u ya baro gidan ba sai ana kiraye-kirayen sallar maghriba, a masallacin unguwar ya yi sallah kafin ya nufo gida zuciyar na tunani kala-kala akan yanda zai je ya tadda Sakinan.

Sakinah bata bar ɗakin Hajiya ba  sai da aka kira sallar maghriba a masallacin unguwar, lokacin Farida ta jima da dawo wa sun ɗan yi hira kafin daga baya ta yi musu sallama ta nufi ɗakinta.

Tana shiga ban ɗaki ta nufa ta ɗauro alwala, tana fitowa ta shi ge ɗaki ta shimfiɗa abin sallah tare da sanya hijab ta tayar da kabbarar sallah.

Bata jima da idarwa ba tana cikin ninke hijab ta tsinkayo sallamarsa tsakar gidan, mudubi ta nufa ta ɗan sake gyara fuskarta tare da sake feshe dukkan sassan jikinta da turare kafin ta fito zuwa falon, ta nemi ɗaya daga cikin kujerun falon ta zauna tana jiran shigowarsa.

Sai da ya fara shiga ɗakin Hajiya ya yi mata barka da yanmaci kafin daga baya ya fito zuwa ɗakinsu, a can ƙasan maƙoshi ya yi sallama cikin falon nasu, Sakinah ta masa tare da miƙewa tsaye tana faɗin.

“Sannu da zuwa Habibina.”

“Yauwa.”

Ya amsa mata a taƙaice yana mai zama kan kujerar tare da ajiye ledar katunan bikin a gefansa sai faman wani cika yake da batsewa haɗe da shan ƙamari, Sakinah ta yi murmushi ta zauna a gefansa tana mai cigaba da faɗin.

“Ya jama’a da rana, yau naga an yi rana sosai.”

“Lafiya.”

Ya sake amsa mata, gyara zamanta ta yi, murmushi kan fuskarta har a lokacin bai gushe ba daga gareta.

“Nasan ka gaji Sweety, da me zaka fara wanka ko cin abinci? Sabida yau abin da ka fi buƙata na girka maka”.

Bai ko kalleta ba, bare ma ya nuna cewar yasan tana magana, illa ledar katunan bikin da ya buɗe ya ɗebo kusan guda biyar ya ɗora mata akan cinyarta, har a lokacin bai ce da ita komai ba.

Sakinah ta ɗauki katunan tana dubawa yayin da can ƙasan zuciyarta na ta yi mata lugude, ga wani irin zugin zafi da zuciyarta ke yi, da ƙyar ta yi ƙarfin halin ƙaƙalo murmushin dole tare da daidaita tsayuwar numfashinta kafin ta furta.

“Kai..! Masha Allah katunan sunyi kyau sosai matuƙa wallahi, Allah dai ya kaimu ranar ya nuna mana.”

Sai a lokacin Kamal ya ji yo ya dube ta baki galala cike da tsantsar mamakinta, akan kawaici da basarwa irin nata.

Kamal ya gayyato murmushi zuwa kan fuskarsa sosai ya nuna matuƙar jin dadin akan maganarta tunaninsa zata ji haushi, hakan ya sa cike da zaƙuwa ya amsa da.

“Ya burgeki sosai haka?”

“Sosai kuwa, ya yi kyau wallahi.”

Sakinah ta kai maganar tare da miƙe wa tana faɗin.

“Bari dai na je na haɗa maka ruwan wankan, domin nasan zaka fi buƙatar wanka a halin yanzu.”

Bata damu da amsawarsa ba ta yi wucewarta, Kamal ya bi bayanta da kallo a cikin ransa yana faɗin.

“Wannan kuma wacce irin mata ce haka?”

Murmushi ya yi tare da jan tsaki kaɗan, sosai kwalliyarta ta burgeshi amma girman kai da gadara yasa ba zai nuna mata ba,  yana gudun ka da ya nuna mata raini ya ɓulla har ya samu gurin zama a tsakaninsu.

<< Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 2Jini Ba Ya Maganin Kishirwa 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.